Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/01/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ahmad Bawage da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Rufewa

    A nan muka kawo ƙarshen wannan shafi da muke kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fata kun ji daɗin kasancewa a tare da mu.

    Sai kuma gobe Juma'atu babbar rana, idan Allah ya nuna mana.

  2. M23 ta sha alwashin ci gaba da hare-hare har zuwa babban birnin DR Kongo

    M23

    Asalin hoton, AFP

    Jagoran ƴantawayen da suka ƙwace iko da birnin Goma da ke gabashin ƙasar Congo ya ci alwashin ci gaba da yaƙi har sai sun ƙwace iko da babban birnin ƙasar, Kinshasa.

    Ƙungiyar ce ta bayyana haka a wani taron ganawa da manema labarai na farko tun bayan ƙwace iko da Goma a daidai lokacin da rahotanni ke nuna dakarunta suna ƙara kutsawa kudancin ƙasar.

    Ƙwace iko da Goma na cikin manyan abubuwan da suka faru a rikicin wanda ya haifar da ɗar-ɗar a yankin.

    Jagoran ƴantawayen, Corneille Nangaa, ya ɗare shugabancin haɗakar ƙungiyoyi da dama ne cikin har da ta M23, wadda ita ce ta ci Goma da yaƙi.

    A taron menama labaran, ya ce dakarun M23 za su ci gaba da abin da ya kira gwagwarmayar ƙwace iko da Kinshasa.

  3. Kotu ta ɗage sauraron ƙarar tsohon shugaban inshorar lafiya, Farfesa Usman

    Wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta ɗage gurfanar da tsohon shugaban hukumar inshoran lafiya ta Najeriya, Farfesa Usman Yusuf, zuwa ranar Litinin 3 ga watan Febrairu.

    Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ce ta kai ƙarar Farfesa Usman Yusuf a gaban babbar kotun da ke zama a unguwar Kuje ta birnin, a bisa zargin almundahana da kuɗi.

  4. Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙaddamar da tallafin karatun yara mata

    Gwamnan Sokoto

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun yara mata a faɗin jihar, a wani yunƙuri na rage yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

    Shirin - wanda aka yi wa take da 'Adolescent Girls’ Initiative for Learning and Empowerment' (AGILE) - na da aniyar inganta bai wa mata yara damar samun karatu tare da ƙarfafa ayyukan koyo da koyarwa a faɗin jihar.

    Cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafin na Facebook ya ce ƙarƙashin shirin makarantun Sakandiren mata kimanin 240 za su amfana da tallafin kuɗaɗe.

    Kuɗi

    Asalin hoton, Sokoto State Governmert

    ''Makarantu 98 masu ɗalibai biyu zuwa 200 za su samu tallafin naira miliyan 23, yayain da makarantu 142 masu ɗalibai 202 zuwa 500 za su amfana da tallafin naira miliyan 46 kowanensu'', a cewar gwamnan.

    Shirin na AGILE zai mayar da hankali wajen gina sabbin azuzuwa tare da faɗaɗa makarun furamare da ƙananan makarantun sakandire domin bai wa yara masu yawa damar komawa makarantu a faɗin jihar.

    Yankin arewacin Najeriya na fama da matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a cewar Asusun tallafa wa ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef.

  5. Mahaifi ya kashe ƴarsa saboda bidiyon da take yi a TikTok

    TikTok

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani mahaifi da ya mayar da iyalinsa Pakistan daga Amurka ya tabbatar da kashe ƴarsa a sanadiyar bidiyo da take a TikTok, wanda shi kuma ya hana, kamar yadda ƴansanda suka bayyana wa BBC.

    An gurfanar da Anwar ul-Haq ne bisa zargin kashe kai bayan ya tabbatar da kashe ƴarsa ɗin mai suna Hira a kudu maso yammacin birnin Quetta a ranar. Da farko ya bayyana wa masu bincike cewa wasu ƴanbindiga ne suka kashe ta.

    Mahaifin, wanda yake da shaidar zama ɗan Amurka, ya ce ya gano bidiyoyin da ƴarsa ke saki ba su dace ba.

    Ƴansanda sun ce suna duba yiwuwar mayar da kisar a matsayin kisar wadda ta ɓata wa danginta suna da ake kira 'humanity killing', lamarin da ba sabon abu ne a Pakistan, musamman a kan mata.

    Ɗaruruwan mutane - musamman mata- ake kashewa duk shekara a irin wannan kisan a Pakistan, kamar yadda ƙungiyoyin kare haƙƙi ɗan'adam suka nuna. Yawanci ƴan'uwa ne suke kashe wadda suke ganin ta jawo wa danginsu abin kunya.

    A game da Hira Anwar, wadda take tsakanin shekara 13 da 14, kakakin rundunar ƴansanda sun ce danginta, "ba sa jin daɗin yanayin shigar da take yi da tsarin rayuwarta da mu'amalarta a kafofin sadarwa."

  6. Ƴanbindiga sun kai farmaki a Masallaci a Zamfara

    NPF

    Asalin hoton, NPF

    Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, wasu ƴan bindiga sun ƙaddamar da wani mummunan farmaki a Masallacin garin Shanawa da ke jihar a jiya da dare.

    An kai harin ne a daidai lokacin da ake sallar isha’i, inda suka harbi aƙalla mutum huɗu tare da yin awon gaba da wasu har kawo yanzu ba a san adadinsu ba.

    Rahotannin sun kuma tabbatar da cewa Turji ya sake afkawa garin Shinkafi duk dai a rana ɗaya, inda can ma ya sake kwasar ƙarin wasu mutane masu ɗimbin yawa.

  7. Tarayyar Afrika za ta ba da dala 800,000 don yaƙi da ta'ddanci a Tafkin Chadi

    Tarayyar Afrika

    Asalin hoton, African Union/X

    Tarayyar Afirka ta ce za ta bayar da tallafin dala 800,000 a matsayin sabon tallafi domin taimakawa yaƙi da ake yi da ƴan ta'adda a yankin Tafkin Chadi.

    Kwamishinan da ke kula da harkokin siyasa da zaman lafiya da kuma tsaro na Tarrayar Afrika, Adeoye Bankole ya ce manufar sabon tallafin ita ce inganta yakin da sojojin yankin suke yi da ƴan ta'adda tare da karfafa musu gwiwa wajen musayar bayanan sirri da kuma tabbatar da tsaro a yankin .

    Sai dai Mista Bankole ya yi gargaɗin cewa kuɗin da ake da su ba za su iya magance kalubalen tsaron da ake fuskanta a yankin ba don haka akwai buƙatar ganin cewa gwamnatocin yankin sun haɗa yaƙin da suke yi da ta'addanci a cikin kasafin kuɗin ƙasashensu.

    Yankin da ya kunshi Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya a matsayin ƙasashe mambobi, a halin yanzu yana fama da matsalar tsaro sakamakon hare-haren mayaƙa masu iƙirarin jihadi da kuma talaucin da sauyin yanayi ya haifar.

  8. Gobe Juma'a ne ɗaya ga watan Sha'aban a Najeriya da Saudiyya

    Sha'aban

    Asalin hoton, Inside the Haramain/Facebook

    Gobe Juma'a, wanda ya yi daidai da 31 ga watan Janairun 2025 ne ɗaya ga watan Sha'aban na shekarar 1446 a Najeriya da ƙasar Saudiyya.

    Shafin Haramain na Facebook ne ya ruwaito hakan, inda sanarwar ta ce an ga jinjirin wata wanda ke nuna zuwan ƙarshen watan Rajab.

    A Najeriya kuma, yau ne 30 ga watan Rajab, bayan hukumomi a ƙasar sun sanar da cewa ba a ga jinjirin watan ba a jiya Laraba, 29 ga Rajab ɗin.

    Da wannan ne ya kama saura wata ɗaya a fara azumin watan Ramadan.

  9. An kammala kwashe sojojin Faransa daga Chadi

    Chadi

    Asalin hoton, AFP

    Sansanonin sojin Faransa guda uku da suka rage a ƙasar Chadi sun koma na sojojin ƙasar, kamar yadda hedkwatar sojin ƙasar ta bayyana.

    An yi bikin miƙa sansanin sojin Sergent Kossei ne da ke babban birnin ƙasar N'Dajamena, wanda ya kawo ƙarshen gomman shekarun alaƙar soji da ke tsakanin Chadi da Faransa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

    A watan Nuwamba ne Chadi ta sanar da cewa za ta fice daga yarjejeniyar alaƙar soji da Faransa, wanda a sanadiyar haka, aka fara kwashe sojojin Faransa kusan 1000 da ke ƙasar.

    Sansanonin suna taimakon rundunar sojin Chadi ne wajen yaƙi da ƴanbindiga a ƙasar.

    Yanzu dai ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Fasp da Ivory Coast da ita Chadin ne ƙasashen da Faransa ta yi mulkin mallaka da suka yanke alaƙar soji da ita.

  10. Hamas ta tabbatar da sako fursunoni 110 daga Isra'ila

    Hamas

    Asalin hoton, Getty Images

    Fursunoni 110, yawanci Falasɗinawa ne Isra'ila ta saka a cikin matakan tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, inda ɓangarorin biyu suke musayar fursunonin yaƙi.

    Daga cikin mutum 110 ɗin, 32 daga cikin an yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai ne, sannan akwai 48 da suke da ɗaurin zaman gidan yari masu tsawo.

    Haka kuma a ciki akwai ƙananan yara, wanda ƙaramin ciki shi ne mai shekara 15.

    Kafar yaɗa labaran Hamas ce ta tabbatar da sakin fursunonin guda 110, bayan Hamas ɗin ta saki Isra'ilawa uku, da ƴan ƙasar Thailand biyar da ke hannunta.

    Wannan ce musayar fursunoni ta uku da aka yi tun bayan da aka shiga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanain Hamas da Isra'ila a ranar 19 ga Janairu.

  11. Ma'aikatar lafiyar Hamas ta ce Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 10

    Hamas

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar lafiya a Falasɗinu ta ce hari ta sama da Isra'ila ta kai yamma da gaɓar kogin Jordan da ta mamaye ya hallaka aƙalla Falasɗinawa 10.

    An kai harin ne a yankunan Tunbas da Samaria da ke arewacin kogin Jordan.

    Wakilin BBC ya ce ƴan makonnin nan Isra'ila ta zafafa kai hare-haren soji a arewacin yamma da gaɓar Kogin Jordan musamman a Jenin, inda hukumomin Falasɗinu suka gwabza faɗa da Hamas da mayaƙan jihadi.

    Hotunan bidiyo da ake kyautata zaton a garin Tamoun ne, ya nuna yadda mutane suka cika maƙil gaban wasu gine-gine da ya lalace domin zaƙulo waɗanda suka tsira da rai.

  12. Meta ya amince ya biya Trump dala miliyan biyar kan dakatar da shafinsa

    Meta

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Meta mamallakin Facebook ya amince ya biya Donald Trump dala miliyan biyar, kan dakatar da shafinsa da ya yi.

    Meta wanda shi ke da shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram, ya dakatar da Mista Trump bayan harin da magoya bayansa suka kai ginin majalisar dokokin Amurka shekaru huɗu da suka gabata.

    Sai dai Meta bai amince da aikata ba daidai ba.

    A ƙarshen wa'adin mulkinsa na farko, Trump ya maka Meta gaban shari'a.

    Wannan na zuwa ne bayan shugaban Meta Mark Zuckerberg, ya ba da tallafin dala mliyan ɗaya ga kwamitin yaƙin neman zaben Mista Trump, tare da sassauta wasu tsare-tsare na wallafa labarai a shafukansa na sada zumunta na Facebook da Instagram da kuma Threads.

  13. Uganda ta tabbatar da ɓullar Ebola

    ma'aikata

    Asalin hoton, EPA

    Ma'aikatar Lafiya a Uganda ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a Kampala, babban birnin ƙasar.

    Ta kara da cewa gwajin da aka yi wa wata jami'ar jinya da ta mutu a asibitin da ke babban birnin ranar Laraba, ya tabbatar da ta kamu da cutar mai haifar da zubar jini.

    Ba a samu wani majinyaci ko ma'aikacin lafiya ya nuna alamun kamuwa da cutar ba.

    Uganda ta yi fama da ɓarkewar cutar Ebola tsawon watanni huɗu a shekarun baya, lamarin da ya haifar da mutuwar mutane 55 da suka haɗa da jami'an aikin jinya.

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta kiyasta cewa Ebola na kashe mutum biyar cikin goma waɗanda suka kamu da cutar.

  14. Tinubu ya miƙa ta'aziyya ga gwamnatin Amurka kan hatsarin jirgin sama

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, PRESIDENCY

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mika ta'aziyyarsa ga gwamnatin Amurka kan mummunar haɗarin jirgin sama a Washington DC tsakanin jirgi mai ɗauke da fasinjoji da jirgin soji mai saukar ungulu da sukayi taho mu-gama a sararin samaniya ranar Alhamis.

    A shafinsa na X, Tinubu ya ce: "Na yi matuƙar kaɗuwa da hatsarin jirgi da ya afku a Washington D.C. A madadin ƴan Najeriya, muna miƙa ta'aziyyarmu ga ƴan uwan waɗanda abin ya shafa, da kuma dukkan Amurkawa.

    "Ina jinjinawa ƙoƙarin ma'aikatan ceto da tawagar jami'an agaji kan sadaukarwarsu da aiki cikin yanayi mara kyau.'' inji shi.

    Jirgin saman ya taso ne daga Wichita da ke Kansas kuma yana ɗauke da fasinjoji 60 da ma'aikata huɗu, yayin da jirgin sojin kuma ke ɗauke da sojoji uku.

    Zuwa yanzu rahotanni na nuna cewa an gano gawawwaki 27, sai kuma ɗaya daga jirgin sojin.

  15. Labarai da dumi-dumi, Gerrard ya raba-gari da Al-Ettifaq

    Steven Gerrard

    Asalin hoton, Getty Images

    Steven Gerrard ya amince ya kawo karshen yarjejeniyarsa da ƙungiyar Al-Ettifaq ta Saudiyya.

    Gerrard mai shekara 44, ya shafe tsawon shekara huɗu da rabi a ƙungiyar a matsayin kocinta, inda ya jagoranci wasanni 59 a dukkan fafatawa.

    A lokacinsa, Al-Ettifaq ta lashe wasanni 23 da canjaras 16 da kuma doke ta a wasanni 20.

    Al-Ettifaq ta kare a mataki na shida a kakar wasanni da ta gabata.

    Yanzu dai suna mataki na 12 a teburin gasar Saudiyya a kakar wasanni ta bana.

  16. Labarai da dumi-dumi, Isra'ila ta dakatar da sakin fursunonin Falasɗinawa

    Isra'ila ta dakatar da sakin fursunonin Falasɗinawa, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.

    Isra'ilar ta ce ta yi haka ne sakamakon yamutsi da aka samu a Khan Younis lokacin da aka saki ƴan ƙasar da aka yi garkuwa da su.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an faɗa wa motocin bas ɗauke da Falasɗinawan da aka tsaren ya koma zuwa gidan yari.

    Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce: "mun jinkirta sakin Falasɗinawan ne na tsawon kwanaki har sai mun tabbatar da cewa mutanen mu da aka tsare sun koma cikin koshin lafiya. "

  17. Kotu ta ɗage gurfanar da tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta Najeriya

    Usman Yusuf

    Asalin hoton, Usman Yusuf

    Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kuje, babban birnin tarayya Abuja, ta ɗage gurfanar da Farfesa Usman Yusuf tsohon shugaban hukumar inshora ta Najeriya zuwa 3 ga watan Febrairu.

    Mai shari'a Chinyere E. Nwecheonwu ce ta bayyana haka ranar Alhamis a harabar kotun.

    Tun da farko, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama Farfesa Usman ranar Laraba 29 ga watan Janairu kan zargin almundahanar kuɗaɗe.

    Yanzu dai an ɗage gurfanar da shi zuwa Litinin domin samun damar garanbawul kan zargin da ake yi masa.

    Kotun ta ki amincewa da buƙatar ba da belinsa da lauyansa ya nema, saboda ɗage lokacin gurfanarwa.

    Ta kuma ce a cigaba da tsare Farfesa Yusuf a ofishin EFCC har zuwa ranar gurfanar da shi.

  18. An harbe mutumin da ya ƙona Al-Qur'ani a Sweden

    Sweden

    Asalin hoton, Reuters

    An harbe har lahira mutumin da ya ƙona Al-Qur'ani a Sweden, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.

    An ruwaito kashe Salwan Momika mai shekara 38 ne a yammacin ranar Laraba a wani gida a birnin Södertälje.

    Zanga-zanga ta ɓarke bayan da Mista Salwan ya ƙona Al-Qur'ani a wajen babban masallacin birnin Stockholm a 2023.

    Wata sanarwa da ƴan sandan birnin suka fitar, sun ce an kama mutane biyar, bayan harbe mutumin a daren jiya.

    Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa Mista Momika na haska wani abu kai-tsaye a shafukan sada zumunta lokacin da aka harbe shi.

    Mista Momika ya kaddamar da zanga-zanga daban-daban na kin jinin Musulunci, abin da ya janyo bore a ƙasashen Musulmi da dama.

    Zanga-zanga ta barke a ofishin jakadancin Sweden a Baghdaza har sua biyu, yayin da aka kori jakadan Sweden ɗin daga birnin.

    Gwamnatin Sweden dai ta bai wa Momika damar yin zanga-zangar inda ya ƙona Al-Qur'ani, inda ta ce hakan na cikin tsarin dokar ƴancin faɗar albarkacin baki.

  19. Musayar fursunoni: Hamas ta saki Arbel Yehud

    Hamas ta saki Arbel Yehud, ƴar Isra'ila mai shekara 29 da aka yi garkuwa da ita.

    An miƙa ta hannun hukumar ba da agaji ta Red Cross domin zuwa gida, a cewar kafofin yaɗa labaran Isra'ila.

    Haka ma, kafofin yaɗa labaran kasar sun ruwaito cewa an saki Gadi Moses, mai shekara 80 - an kuma mika shi hannun jami'ai.

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

  20. Na faɗa wa Tinubu ba na sha'awar muƙami a gwamnatinsa - El Rufa'i

    Nasir El-Rufai

    Asalin hoton, Nasir El-Rufai/Facebook

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i ya ce ya faɗa wa shugaba Bola Tinubu cewa ba ya son wani muƙami a gwamnatinsa.

    El Rufa'i ya bayyana haka ne a shafinsa na X yayin martani ga babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan sadarwar tsare-tsaren gwamnati, Daniel Bwala, wanda ya ce El Rufa'i ya ji tsoron Allah bayan da ya fito fili ya caccaki jam'iyyar APC da kuma kiran ta mai mulkin da ta "sauka daga aƙidun dimkoraɗiyya da aka kafa ta a kai".

    "Na faɗa wa Tinubu ƙarara cewa ba na buƙatar kowane irin muƙami a gwamnatinsa," in ji El Rufa'i.

    Ya ce yana mamakin irin yadda Daniel Bwala da takwarorinsa da suka koma jam'iyyar APC a baya-bayan nan ke ta yayata batun cewa an hana shi muƙami, abin da ya ce ba ya so tun da farko.

    "Ina mayar maka da martani ne saboda ina tunanin cewa kai mai fahimta ne wanda ke neman aiki, ba irin wasu mutane ba.

    "Ku mutane ne da ke karɓar albashi kowane wata don ku fara fitowa a shafukan sada zumunta wajen kare kowane irin abu da gwamnatin Asiwaju ta yi ko kuma ta ƙasa yi," in ji tsohon gwamnan na Kaduna.

    Ya ce ko da ace yana cikin gwamnatin shugaba Tinubu - babu abin da zai hana shi furta kalaman da ya yi kan abin da ke faruwa a jam'iyyar da ya ce su suka kirkiro - har ma da kawo gwamnati mai ci.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X