Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/07/2024

Taƙaitattu

  • 'Na shanye harsashi saboda ƙarfafa dimokuraɗiyya'
  • Isra'ila ta yi iƙirarin daƙile hare daga Yemen
  • Shugaban Colombia ya nemi afuwa kan badaƙalar cin hanci tsakanin ministocinsa
  • Bayanai na ƙara fitowa kan yunƙurin kisan Trump
  • Shugaban Uganda ya ce masu shirin zanga-zanga a ƙasar na 'wasa da wuta'
  • Kotun ƙoli ta haramta ware guraben aiki ga keɓaɓɓun mutane a Bangaldesh
  • NDLEA ta bankaɗo masu safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya

Rahoto kai-tsaye

Daga Badamasi Abdulkadir Mukhtar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Isra'ila ta ce ba za ta bai wa mabiya addinin kirista na gargajiya kariya ba

    Sojojin Isra'ila sun ce ba za su bai wa dubban mabiya addinin kirista na gargajiya kariya ba, a wani mataki da ake ganin zai kara rura wutar rikici tsakanin mabiya addinin da 'yan Isra'ilar.

    Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da kotun kolin Isra'ila ta yanke a watan jiya, kan cewa ma'aikatar tsaron Isra'ila ba za ta bai wa dalibai da ke karatun a makarantun Yadudawa kariya ba.

    David Mizrahi dalibi mai shekara 24 ya bayyana cewa; Duk wanda bai san darajar littafin Attaura, ba zai fahimci dalilin da ya sa ba ya son shiga wannan harkar ba.

    Na tabbatar wadabda suka sami sakon nan za su yi amfani da fadar malamanmu na cewa mu yi shiru.

  2. Joe Biden ya haƙura da takarar shugabancin Amurka

    Shugaban Amurka Joe Biden ya haƙura da takarar shugabancin Amurka a wa'adin mulki na biyu.

    Cikin jawabin da ya yi a wani taron manema labarai, shugaban ya ce ya yi hakan ne domin ''masalahar jam'iyyarsa da kuma ƙasarsa''.

    Ya ce cikin shekara uku da rabi da ya yi yana jagorantar Amurka, ƙasar ta samu gagarumin ci gaba.

    ''A yau Amurka na da ƙarfin tattalin arziki a duniya, mun kafa tarihi a fannin zuba jari domin sake gina ƙasarmu''.

    A baya-bayan nan dai shugaban ya fuskanci matsin lamba daga manyan 'yan jam'iyyarsa da ke kiraye-kirayen ya haƙura da takara, tun bayan rashin katabus a muhawarsa da Donald Trump.

  3. 'Yan tawayen Houthi sun ce sun kai harin makami mai linzami zuwa Isra'ila

    'Yan tawayen Houthi na ƙasar Yemen sun ce sun kai harin makami mai linzami birnin Eilat na ƙasar Isra'ila a matsayin martani ga harin da Isra'ila ta kai wa tashar jiragen ruwa ta birnin Hodeidah ranar Asabar.

    Wannan ikirari na zuwa ne bayan sanarwar da sojojin Isra'ila suka yi a baya cewa na'urorin tsaronta na sama sun dakile wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen da ya nufi ƙasarta.

    Harin da Isra'ila ta kai ranar Asabar ya shafi rumbun ajiyar man fetur da ke birnin Hodeidah, lamarin da ya haddasa mummunar gobaara.

    Ma'aikatar lafiya ta Houthi ta ce an kashe mutane shida tare da jikkata 80.

    Kungiyar - da ke samun goyon bayan Iran - ta yi barazanar mayar da martani.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana mayar da martani ne kan daruruwan jiragen yakin Yemen marasa matuƙa da makamai masu linzami da ake kai wa yankunanta a 'yan watannin nan.

  4. Soyayya da Bature daban take - 'Yar Kanon da ta auri Baturen Turkiyya

    Wata matashiyar 'yar Kano mai suna Hauwa Ahmed Sabo ta bayyana yadda ta fara soyayya da wani Baturen Turkiyya har ta kai ga sun yi aure.

    Amariya Hauwa ta ce sun fara haɗuwa da angon nata a lokacin da take rubuta furojet ɗinta a makaranta, a birnin Santambul na ƙasar Turkiyya.

    Ta ƙara da cewa ta samu duk wata kulawa da ta dace a lokacin da suke soyayya har ma bayan aurensu.

    Shi kuwa angon mai suna Umut Aziz Goksel, ya ce akai bambance-bambancen da ke tsakanin al'adunsa da na amariyar tasa, amma ba su hana aure tsakaninsu.

    Ya kuma ce yana son cin tuwo, saboda daɗinsa, musamman ya ce idan an haɗa shi da miyar ganye.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  5. Real Madrid za ta gabatar da Endrick ranar Asabar

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ta sanar da cewar za ta gabatar da matashin ɗan wasan da ta ɗauka Endrick a gaban magoya baya ranar Asabar 27 ga watan Yuli a Santiago Bernabeu.

    Shugaba, Florentino Perez ne zai yi wa ɗan wasan tarbar girma a birnin Madrid, daga nan zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida.

    Bayan an gabatar da ɗan wasan ɗan kasar Brazil, daga nan zai gana da ƴan jarida a Bernabeu.

    Shin wane ne Endrick?

  6. Shugaba Ruto ya sha alwashin kawo ƙarshen zanga-zanga a Kenya

    Willim Ruto

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Kenya, Willim Ruto ya yi alƙawarin kawo ƙarshen zanga-zangar da ake yi, wadda ya ce tana barazanar rusa ƙasar.

    Zanga-zangar da matasa suka shafe makonni suna yi ta tilasta wa Mista Ruto janye shirin ƙara haraji kuma daga baya ya sallami ministocinsa.

    An kashe mutane da dama a lokacin zanga-zangar, kuma ana zargin wasu sun mutu ne bayan ƴan sanda sun harbe su.

    Da yake jawabi ga magoya bayansa bayan kammala taron ibada a wata coci, Mr Ruto ya ce an riga an biya buƙatar masu zanga-zangar sannan ya koka da abin da ya kira ''ƙoƙarin wasu na tarwatsa ƙasar''

    Masu fafutuka na ƙara kiran ci gaba da wata zanga-zangar a mako mai zuwa.

    Ana dai ganin kalaman na Mr Ruto za su iya tunzura matasan Kenya masu rajin yaki da rashawa da samar da mulki nagari.

  7. An ceto ƴan Najeriya 58 da aka yi safarar su zuwa Ghana

    ABIKE DABIRI

    Hukumar da ke kula da ƴan Najeriya a ƙasashen waje, NIDCOM ta ce ta ceto mata da ƙananan yara 58 daga hannun masu safarar mutane a Ghana.

    Shugabar NDICOM, Abike Dabiri-Erewa ta ce wannan na zuwa ne bayan hukumar ta samu nasarar kuɓutar da wata yarinya ƴar mai shekara 15 zuwa 16 daga hannun masu neman yin safarar ta.

    Sanarwar da kakakin hukumar, Abdur-Rahman Balogun ya fitar ta ce Abike Dabiri-Erewa ta samu labarin ceto ƴan Najeriyar daga Ghana ne a lokacin da ta kai ziyara domin ganin mutanen da aka yi safara zuwa birnin Accra na ƙasar Ghana.

    Sanarwar ta ce daga cikin wadanda aka ceto akwai 47 ƴan asalin jihar Kano da biyar daga Katsina da biyu daga Jigawa da kuma huɗu daga jihar Kaduna.

    Balogun ya bayyana cewa a cikin wata uku jimillar ƴan Najeriya 105 kenan Nidcom ta samu nasarar cetodaga hannun masu safara a birnin Accra.

    Hukumar ta ce ta riga ta mayar da zangon farko na mutanen ceto zuwa gida Najeriya.

    Ta kuma bayyana cewa mafi yawan waɗanda ake safarar suna faɗawa tarko ne a bisa alƙawarin za a samar masu aiki a ƙasashen waje, wanda kuma hanya ce kawai ta yaudara ba gaskiya ba.

  8. Zakarun ƙwallon kwandon Amurka sun sha da ƙyar a hannun Sudan ta Kudu

    NBA

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon kwandon Sudan ta Kudu ta kusa kafa tarihi a wasan da ta buga da tawagar ƙwararrun ƴan wasan Amurka.

    Sudan ta kudu ta ja ragamar wasan har zuwa ƴan daƙiƙu a tashi, lokacin da LeBron James ya jefa ƙwallon da ta baiwa ƙwararrun Amurkan nasara, aka kuma kammala wasan na shirin wasannin Olympics Sudan tana cike da alfahari.

    Mai horar da tawagar Sudan ta matasa ƴan ƙasa da shekara 16 Wani Joseph, ya bayyana yadda ƴan wasan da ma magoya bayan su suka ji lokacin da suka kusa yin nasara a wasan: ''Mun buga wasa mai kyau, dukkan ƴn wasan sun yi ƙoƙari sosai. Sun samo maki da yawa kuma sun tsare gida da kyau. mun ji daɗi sosai yadda muka kara da tawagar Amurka kuma da ƙyar suka doke mu da tazarar maki ɗaya tilo.''

  9. NDLEA ta bankaɗo masu safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya

    NDLEA

    Asalin hoton, NDLEA

    Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi a jihar Lagos da kuma wasu wurare na daban a cikin jihar.

    Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya ce sun kama ƙwayoyin ne a cikin wasu kayan da ake safara, inda aka kumshe tabar wiwi da hodar iblis da sauyan miyagun ƙwayoyi a ciki.

    Sanarwar da Femi Babafemi ya fitar a yau Lahadi ta ce NDLEA ta kama kayan laifin ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagos.

    Kakakin hukumar ta NDLEA ya ce sun kama wasu daga cikin mutanen da ake zargi da yunƙurin fita da kuma shiga da kayan laifin a ƙasar.

    Ya ce jami'an NDLEA sun yi samame a sassa da dama na jihar Lagos inda suka kama mutanen da ake zargin da safarar waɗannan kayan laifi, kuma tuni aka fara bincike.

    Hukumar ta sha alwashin ci gaba da zaƙulo masu safarar ƙwayoyi da sauran kayan laifi dangin ƙwayoyi a duk inda suke.

  10. Kotun ƙoli ta haramta ware guraben aiki ga keɓaɓɓun mutane a Bangaldesh

    Bangaldesh

    Asalin hoton, BBC BANGLA

    Kotun ƙoli a Bangaldesh ta yi soke mafi yawan sassan dokar da suka yi tanadin guraben aiki ga keɓaɓɓun mutane da ya janyo zanga-zanga a sassan ƙasar.

    Tun a farkon wata dubban ɗalibai ke zanga-zanga a ƙasar domin nuna rashin amincewa da tsarin da ya ware ayyukan gwamnati ga wasu keɓaɓɓu da suke makusantan gwamnati ne.

    Kotun ta bayar da umarnin keɓe kashi 93 na gurabn aiki a ƙasar domin bai wa duk wanda ya dace, yayin da ta ware kashi biyar ga iyalan ƴan mazan jiya da suka yi yaƙin ƙwatar ƴancin ƙasar na 1971.

    Kotun ta kuma ware kashi biyu ga mutanen da suka fito daga ƙananan ƙabilu marasa rinjaye ko kuma masu buƙata ta musamman.

    A baya dai ana ware kashi ɗaya cikin uku na guraben aikin yi a ƙasar ne ga iyalan ƴan mazan jiya.

    Yanzu haka dai babu mutane a kan titunan birnin Dhaka, saboda dokar hana fita da gwamnati ta sanya bayan ɓarkewar zanga-zanga.

    Mutane aƙalla 115 aka kashe tun bayan fara zanga-zangar amma wasu rahotanni na cewa adadin ya zarce haka.

  11. Shugaban Uganda ya ce masu shirin zanga-zanga a ƙasar na 'wasa da wuta'

    Yoweri Museveni

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Uganda, Yoweri Museveni, ya gargadi masu shirya zanga-zangar yaƙi da cin hanci da rashawa da aka shirya yi a ranar Talata cewa ahir dinsu, don kuwa a cewar sa "suna wasa da wuta".

    Ya ce zanga-zangar ba za ta kasance bisa ka'ida ba, kuma masu zanga-zangar suna "aiki da wasu kasashen wajen don haifar da hargitsi a Uganda.

    Zanga-zangar kin jinin karin haraji a Kenya ce ta zaburar da matasan Ugandan.

    Tun da farko a ranar Asabar, 'yan sandan Uganda sun shaida wa masu shirya zanga-zangar cewa ba za su amince da ita ba.

    Sai dai masu shirya ta sunce babu gudu ba ja da baya.

    Sun kuma yi fatan za su wuce majalisar dokokin kasar, wadda suke zargin da taimaka wa gwamnati wajen aiwatar da cin hanci da rashawa.

  12. Bayanai na ƙara fitowa kan yunƙurin kisan Trump

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Jami’an da ke binciken yunkurin kashe Donald Trump a ranar Asabar din da ta gabata sun shaida wa kafafen watsa labaran Amurka cewa, sun yi imanin dan bindigar da ya yi harbin ya tashi wani jirgin nadar bayanai da ke dauke da na’urar daukar hoto zuwa wurin da Trump din ke yakin neman zabe a jihar Pennsylvania gabanin harbin.

    Sun ce sun gano wani jirgi mara matuki ne a cikin motar Thomas Mathew Crooks bayan da jami’an leken asirin suka harbe shi, kuma sun yi imanin cewa an yi amfani da shi ne wajen zabar wurin da ya fi dacewa a yi harbin.

    A wata hira da ya yi da Fox News, Mista Trump ya ce babu wanda ya gargade shi kafin ya hau kan dandamalin yakin neman zaben.

  13. Shugaban Colombia ya nemi afuwa kan badaƙalar cin hanci tsakanin ministocinsa

    Gustavo Petro

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Colombia, Gustavo Petro, ya nemi afuwa game da wata babbar badakalar cin hanci da ta shafi wasu manyan ministocin gwamnatinsa.

    Da yake jawabi a wajen bude taron majalisar dokokin kasar, Mista Petro ya ce zai yi kokarin kwato kudaden da aka karkatar tare da tabbatar da cewa wadanda ake da hannu sun fuskanci shari'a.

    Masu gabatar da kara sun ce an karkatar da miliyoyin daloli na kudaden jama'a da nufin jika maƙoshin ƴan siyasar da suka yi alkawarin tallafa wa gwamnati wajen amincewa da kudurorinta a Majlisa.

  14. Isra'ila ta yi iƙirarin daƙile hare daga Yemen

    iSRAEL ATTACK

    Asalin hoton, AP

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce garkuwar tsaron samanta da aka fi sani da Iron Dome ta dakile wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen kafin ya surare ya fada yankin Eilat da ke kudancin kasar.

    Harin na zuwa ne bayan jiragen yakin Isra'ila sunka kai wasu jerin hare-hare a ranar Asabar a tashar ruwan Hodeidah da ke karkashin ikon Houthi a kasar Yemen.

    Kafofin watsa labaran gwamnatin Houthi sun ce harin ya shafi wani rumbun adana man fetur, lamarin da ya yi ajalin mutane uku.

    Houthi dai ta ce Isra'ilar za ta dandana kudarta.

    Tun da farko, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga bangarorin biyu da su maida wukarsu cikin kube.

  15. 'Na shanye harsashi saboda ƙarfafa dimokuraɗiyya'

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Donald Trump ya shaidawa dubban magoya bayansa a wani gangamin yakin neman zaben jam'iyyar Republican a jihar Michigan cewa yana da tabbacin zai lashe zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.

    Ya musanta cewa yana barazana ga dimokuradiyya, yana mai cewa garin kare dimukradiyyar ne ma ya kusa rasa ransa.

    Mista Trump ya yi ta yi wa Joe Biden shaguɓe, yana mai cewa har yanzu jam'iyyar Democrat ba ta san wanda zai zama dan takararta a watan Nuwamba ba.

    Ya kuma sake nanata ikirarin cewa, idan aka zabe shi, zai gudanar da abin da ya kira korar bakin haure mafi girma a tarihin Amurka.

    Jihohi a tsakiyar yammacin kasar ciki har da Michigan ne ake sa ran za a kai ruwa rana a kansu a zaben na Nuwamba mai zuwa.

  16. Barka da zuwa

    Barka da zuwa shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa