Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Nigeria 1-1 South Africa: Wasan neman shiga Kofin Duniya

Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 6 ga watan Yuni, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya, Nigeria 1-1 South Africa

    Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.

    Umar Mikail ne ke fatan za mu kwana lafiya.

  2. Yadda Najeriya da Afirka ta Kudu suka fafata, Nigeria 1-1 South Africa

    Tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta Super Eagles ta yi canjaras da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya.

    Yayin wasan da aka fafata a filin wasa na Godswill Akpabio a jihar Akwa Ibom, ɗan wasan gaba Zwane ne ya fara ci wa Afirka ta Kudu ƙwallo a minti na 29 bayan ya zagaye 'yan bayan Najeriya biyu kuma ya yarɓa ta a ragar Nwabali.

    Sai a minti biyu da komawa hutun rabin lokaci Dele Bashiru ya farke wa Najeriya, inda shi ma ya taƙarƙare ya zabga wa Romwen Williams ƙwallo daga yadi na 18.

    Ademola Lookman Samuel Chukwueze na Najeriya sun samu damarmakin da suka kamata su cinye wasan, amma ƙoƙarinsu bai kai ba.

    Najeriya ce ta fi mamaye wasan musamman bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    Da wannan sakamakon, Afirka ta Kudu ta koma mataki na huɗu da maki huɗu, Najeriya kuma ta biyar da maki uku.

    Sai a cikin shekara mai zuwa ne Najeriya za ta ziyarci Afirka ta Kudu don buga zagaye na biyu.

    Amma a ranar Litinin Najeriya za ta je Ivory Coast don karawa da Benin, yayin da Afirka ta Kudu za ta buga da Zimbabwe ranar Talata.

  3. WASA YA ƘARE, 90+5 Nigeria 1-1 South Africa

    An raba maki tsakanin giwayen Afirka a harkar ƙwallo da kuma tattalin arziki.

  4. Saura kiris Lookman, '92 Nigeria 1-1 South Africa

    Ademola Lookamn ya ɗaɗa wa Williams ƙwallo kuma da kyar ya tura ta kwana.

  5. An ƙara minti biyar, 90' Nigeria 1-1 South Africa

  6. Lookmaaaaaan, 87' Nigeria 1-1 South Africa

    Ademola Lookman ya zubar da dama mai kyau a cikin yadi na 18 ɗin Afirka ta Kudu.

    Ƙwallo ce suka yi ba ni in ba ka amma sai ya buga ta waje ba tare da wani haɗari ba ga gola Williams.

  7. Najeriya ta yi canji, Nigeria 1-1 South Africa

    Terem Moffi ya maye gurbin Onuachu. Sai kuma Onyedika da ya karɓi Ajayi.

  8. Tirkeeee, Nigeria 1-1 South Africa

    Chukwueze ya doko tirke bayan Alhassan ya ba shi wata ƙwallo mai ƙayatarwa.

    Dama ce mai kyau sosai, da tuni Najeriya ta shiga gaba ba don tirken sama ba.

  9. Iwobi ya ɓarar da dama, Nigeria 1-1 South Africa

    Alex Iwobi ya buga ƙwallo ta yi sama da yawa.

  10. Najeriyaaaaa, Nigeria 1-1 South Africa

    Osayi Samuel ya kusa ci wa Najeriya bayan ya ɗaɗa ƙwallo a cikin yadi na 18 - amma sai a hannun Williams

  11. Afirka ta Kudu ta yi canji, Nigeria 1-1 South Africa

    Foster ya maye gurbin Rayners

  12. NAjeriya ta yi canji, 70' Nigeria 1-1 South Africa

    Samuel Chukuwueze ya maye gurbin Kelechi Iheanacho.

  13. Najeriya ta yi canji..., '62 Nigeria 1-1 South Africa

    An sako Yusuf Alhassan a madadin Bashiru.

  14. Dele Bashiru a kwance, '59 Nigeria 1-1 South Africa

    Ɗan wasan tsakiyar Najeriya kuma maciyin ƙwallon, Dele Bashiru, ya kwanta yana nuna alamun ba zai iya ci gaba da wasa ba.

    Ko wane mataki mai horarwa Finidi George zai ɗauka?

  15. Katin gargaɗi, Nigeria 1-1 South Africa

    An bai wa Ngezana na Afirka ta Kudu katin gargaɗi.

  16. Katin gargaɗi, Nigeria 1-1 South Africa

    An bai wa Mudau na Afirka ta Kudu katin gargaɗi saboda ƙeta.

  17. GOAL Najeriyaaaaaaa, 46' Nigeria 1-1 South Africa

    Bashiru ya farke wa Najeriya ƙwallo minti biyu da komawa hutun rabin lokaci.

    Sai da ya bintsire 'yan bayan sannan ya sheƙa ta ragar Williams.

  18. An tafi hutun rabin lokaci, Nigeria 0-1 South Africa

    An tafi hutun rabin lokaci yayin da baƙi ke yin nasara 0-1.

    Matuƙar Najeriya na son zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026 wajibi ne ta farke kuma ta cinye wasan domin kuwa yanzu haka ita ce ta biyar a teburin rukunin.

    Tuni Afirka ta Kudu ta ɗare saman teburin sakamakon wannan ƙwallon da Zwane ya ci mata a minti na 29 da take wasa.

  19. An ƙara minti biyu, '47 Nigeria 0-1 South Africa

  20. Najeriyaaaaa, Nigeria 0-1 South Africa

    Paul Onuachu ya goga wa ƙwallo kai, inda ya kusa farke wa Najeriya. Sai dai Williams ya yi wuf ya rufe ƙwallon.