Jana'izar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shafin bayani kai-tsaye kan binne gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Aisha Aliyu Jaafar, Isiyaku Muhammed, Umaymah Sani Abdulmumin da Usman Minjibir

  1. Bankwana

    Masu bibiyar mu a wannan shafi da haka muke bankwana da ku. Allah ya jikan tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Ya yi masa rahama.

  2. 'Yana tashi daga barci kafin sallar asuba'

    Makusancin Buharin ya ce tsohon shugaban ƙasar kan tashi daga barci, tun kafin ketowar asuba, sannan ya kammala shirin zuwa masalllaci domin yin sallar jam'i.

    ''Bayan kammala sallar asuba yakan zauna ya yi azkar daidai gwargwado kafin ya koma gidansa, kuma ba ya komawa barci''.

    Idan lokacin da yaransa ke zuwa makaranta ne zai tabbatar da yaransa sun tashi domin su tafi makaranta a kan lokaci, a cewar Hadi Sirika.

    ''Bayan hakan yakan zagaya gidansa kaf, domin yadda kowa ya tashi a gidan'', in ji Hadi Sirika.

  3. 'Mutum ne mai barkwanci ga iyalansa'

    Makusancin Buharin ya ce tsohon shugaban ƙasar mutum ne da ya gina kyakkyawar alaƙa da iyalansa.

    ''Duk da cewa ba zan iya cewa komai game da rayuwar matarsa ta farko ba, amma dai ga ƴaƴansa mutum ne mai kyakkyawar alaƙa da su''.

    ''Rayuwar da yake yi da ƴaƴansa rayuwa ce ta barkwanci da wasa da dariya da tsausaya da kuma ƙaunar juna''.

    ''Idan ka ga yadda yake rayuwar barkwanci da ƴayansa sai ka ɗauka jikokinsa ne ba ƴaƴa ba'', in ji Hadi Sirika.

    Yakan zauna da iyalansa su ci abinci tare su yi raha su yi barkwanci, a cewar Sirika.

  4. Kabarin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

    Nan ne inda aka binne tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a garin Daura da ke Katsina.

    Iyalai da dangi da masoyan tsohon shugaban na cigaba da dafifin zuwa kabarin suna masa addu'o'i

    Image

    Asalin hoton, Social

  5. Yanayi na alhini da iyalai da 'yan uwan Buhari ke ciki

    MB

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Bayanan hoto, Matar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ɗiyarsa, Zahra Buhari lokacin da ake kokarin binne shugaban a Daura
    MB

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu na kokarin miƙawa matar marigayin da ɗansa Yusuf Buhari tutar ƙasar da aka naɗe daga gawar marigayi Muhammadu Buhari
    MB

    Asalin hoton, State House

    MB

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Shugaba Tinubu ya girmama gawar marigayi da salama da shi kafin a sa shi a kabari
    MB

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Yadda masoyan Muhammadu Buhari ke kukan rashinsa an lokacin jana'izarsa a Daura
    MB

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Wata 'yar uwar marigayi Muhammadu Buhari lokacin da ake kokarin binneshi a gidansa da ke Daura
  6. Yadda aka binne Muhammadu Buhari a Daura

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya girmama gawar tare da bankwana karshe a lokacin da ake shirin binne shi.

    Asalin hoton, Rahama Abdulmajid

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya girmama gawar tare da bankwana karshe a lokacin da ake shirin binne shi.
    k

    Asalin hoton, Rahama Abdulmajid

    Bayanan hoto, Mataimakin shugaban ƙasa Kashin Shettima da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo da sauran manyan mutane a lokacin da suke kokari sa gawar Buhari a kabari
    Dan marigayin, Yusuf Buhari tare da sirikan tsohon shugaban lokacin da ake sa gawar a Kabari

    Asalin hoton, Rahama Abdulmajid

    Bayanan hoto, Dan marigayin, Yusuf Buhari tare da sirikan tsohon shugaban lokacin da ake sa gawar a Kabari
    Binne shugaba Buhari

    Asalin hoton, Rahama Abdulmajid

    Yusf

    Asalin hoton, Rahama Abdulmajid

  7. 'Yana yawan nasiha da riƙon amana'

    Tsohon ministan jiragen sama na Najeriya a zamanin mulkin Buharin - wanda kuma ke da alaƙa ta kut da kut da shi, da kuma iyalinsa - ya bayyana wa BBC yadda tsohon shugaban ƙasar ke gudanar da harkkin rayuwarsa daga asuba zuwa kwanciya barci.

    Tsohon Ministan ya ce a mafi yawan lokuta idan sun zanuanda marigayin kana yawaita yi musu nasiha da riƙon amana.

    ''Idan aiki aka ba ka to ka riƙe amana, domin ai shugaban ƙasa na shi ne kadai ke mulkin ƙasar ba''.

    ''Yana yawan yi magana game da yadda tsarin mulki yake, (kowane mai muƙami yana da da rawar da zai taka)''. in ji shi.

  8. Yadda aka yi jana'izar Buhari a Daura

    ..

    Asalin hoton, TVC News

    A ranar Talata ne aka yi wa marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari jana'iza, bayan sallar La'asar a wani fili da ke kusa da gidansa, sannan aka binne shi a cikin gidansa da ke mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina.

    Sakamakon dubban jama'a da suka halarci taron jana'izar ba a samu an fito da gawar marigayin fili ba domin a sallace ta inda aka sallace ta alhali tana cikin motar.

    Bayan kammala sallar, sojoji sun ɗauki gawar zuwa inda aka binne ta a cikin gidan marigayin bayan yin faretin bangirma a karo na biyu.

    An dai nannaɗe gawar Buhari da tutar Najeriya mai launin fari-kore-fari, inda kuma aka cire ta lokacin da za a saka gawar a cikin kabari sannan kuma aka bai wa ɗansa, Yusuf Buhari tutar.

  9. An kammala binne gawar tsohon shugaba Muhammadu Buhari a Daura

    An binne gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura na jihar Katsina da misalin karfe 5:50 na yamma.

    A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli ne Muhammadu Buhari ya rasu a birnin Landan na Birtaniya bayan shafe dogon lokaci yana jinya.

    Muhammadu Buhari ya rasu ne yana da shekara 82 a duniya, shekara biyu bayan sauka daga muƙamin shugaban ƙasa.

    Buhari ya mulki Najeriya a matsayin soja daga watan Disamban shekara ta 1983 zuwa watan Agustan 1985 kafin tuntsurar da gwamnatinsa.

    Sai dai a shekara ta 2015 Buhari ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa bayan kayar da shugaba mai ci a wancan lokaci Goodluck Jonathan.

    An rantsar da shi a matsayin shugaban farar hula, inda ya yi mulki Najeriya wa'adi biyu (shekara 8) daga ranar 29 ga watan Mayun 2025 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.

    Sai dai Buhari ya yi ta fama da jinya tun farko-farkon mulkinsa na farar hula, inda ya riƙa safa da marwa daga Najeriya zuwa Landan domin neman lafiya.

    Masharhanta na ganin cewa rashin lafiyar tasa ta rage karsashinsa a harkar shugabanci.

    A ɓangare ɗaya kuma masu suka sun zargi gwamnatinsa da ɓoye rashin lafiyar da ke damun sa.

    Muhammadu Buhari ya rasu ya bar mata ɗaya - A'isha Buhari - da ƴaƴa 10.

  10. An sa gawar Buhari a kabari

    An sa gawar Muhammadu Buhari a kabari cikin yanayi na alhini da juyayi.

    Lokacin da aka saka gawar Muhammadu Buhari cikin kabari

    Asalin hoton, TVC

    Bayanan hoto, Lokacin da aka saka gawar Muhammadu Buhari cikin kabari
    Lokacin da aka saka gawar Muhammadu Buhari cikin kabari

    Asalin hoton, TVC

    Bayanan hoto, Lokacin da aka saka gawar Muhammadu Buhari cikin kabari
    Bayan sanya gawar cikin kabari an yi amfani da itace da tabarmar kaba kafin rufewa da ƙasa

    Asalin hoton, TVC

    Bayanan hoto, Bayan sanya gawar cikin kabari an yi amfani da itace da tabarmar kaba kafin rufewa da ƙasa
  11. An ninke tutar Najeriyar da aka naɗe gawar Buhari da ita

    An naɗe tutar Najeriya da aka sa gawar Buhari domin ba wa iyalansa.

  12. An harba bindiga domin bankwana da marigayi Buhari

    Sojoji sun busa sarewa, sannan an rinƙa harba bindiga domin bankwana da gawar Buhari.

    Dubban mutane sun yi wa garin Daura cikar kwari.

  13. Sojoji na yi wa gawar Buhari faretin ban girma na karshe

    Sojojin da suka kawo gawar marigayi Muhammadu Buhari na yi masa faretin ban girma a gaban kabarin da za a binne shi.

    Ana gudanar da faretin ne gaban shugaban ƙasa Bola Tinubu da sauran manyan baƙi.

    An lullube gawar a cikin tutar Najeriya.

  14. An kai gawar Muhammadu Buhari bakin kabari

    ...

    Asalin hoton, TVC

    Bayanan hoto, Ɗan Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari a gefen gawar mahaifinsa yayin da sojoji ke masa ban-girma na ƙarshe
    Gawar Muhammadu Buhari a gefen kabari kafin binnewa

    Asalin hoton, TVC

    Bayanan hoto, Gawar Muhammadu Buhari a gefen kabari kafin binnewa
  15. Ana dab da binne gawar Buhari a Daura

    Cikin yanayi na ban girma an kawo gawar Muhammadu Buhari bakin kabarin da za a binne shi.

    Sojoji ne suka kawo gawar. Sannan shugaban ƙasa da sauran manyan baƙi na kokarin ganin sun taimaka an binne gawar marigayin.

  16. Yanayin zafin rana a Daura na kan ma'aunin celcius 38

    Yayinda ake shirin sa gawar tsohon shugaba Muhammadu Buhari a kabarinsa rahotanni na cewa yanayin zafin rana ya kai ma'aunin celcius 38.

    Manyan baki da iyalan shugaban na ta kai komo domin tabbatar da cewa an kammala binne tsohon shugaban a gidansa da ke Daura.

  17. An mayar da gawar Muhammadu Buhari gida domin binnewa

    ...

    Asalin hoton, TVC

    An kammala yi wa gawar Muhammadu Buhari sallar jana'iza inda yanzu haka aka mayar da ita gida domin binnewa.

    An gudanar da sallar ne bayan iyalansa sun yi bankwana da shi a cikin gida - inda aka kai shi bayan isar sa Daura daga birnin Katsina.

    ...

    Asalin hoton, TVC

    Makabartar Buhari

    Asalin hoton, TVC

  18. An yi sallar jana'izar Muhammadu Buhari a Daura

    An gudanar da sallar jana'izar gawar marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ya rasu shekaranjiya Lahadi.

    An gudanar da sallar jana'izar ce bayan Sallar La'asar a wani fili da ke kusa da gidan marigayin a Daura, bayan an ɗauki gawar daga jihar Katsina.

    Daga cikin waɗanda suka sallaci gawar, akwai shugaban Najeriya na yanzu, Bola Tinubu da shugabannin ƙasashen duniya irin su na Gambia Adama Barrow da na Chadi Mahamat Déby da na Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló, sai kuma tawagar gwamnatin sojin na Jamhuriyar Nijar a ƙarƙashin jagorancin Firaministan ƙasar Ali Lamine Zeine da wasu ministoci da malaman addini.

    Tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou shi ma ya samu halartar jan'izar.

    Shi kuwa tsohon shugaban ƙasar Ghana ma Nana Akufo Addo ya yi wa iyalan marigayin ta'aziyya a Landan tun a jiya Litinin kafin gawar ta bar Landan.

  19. An kai gawar Muhammadu Buhari gidansa da ke Daura

    Gawar Muhammadu Buhari a cikin motar ɗaukar gawa a cikin gidansa da ke Daura

    Asalin hoton, TVC

    Bayanan hoto, Gawar Muhammadu Buhari a cikin motar ɗaukar gawa a cikin gidansa da ke Daura

    Gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta isa garinsa na haihuwa, Daura da ke jihar Katsina.

    Iyalai da ƴan'uwan mamacin sun taru a jikin motar ɗaukar gawar, inda suke kuka tare da yi masa addu'a.

    Bayan kammala addu'a ne za a ɗauki mamacin zuwa inda za a yi masa sallah kafin a sake mayar da shi gida inda za a binne ta.

    Kafin tafiya da shi, an bai wa ƴaƴansa damar shiga motar ɗaukar gawar domin suyi bankwana da shi.

  20. Gawar Muhammadu Buhari ta isa Daura

    Gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ta isa garin Daura na jihar Katsina

    Asalin hoton, TVC

    Bayanan hoto, Gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ta isa garin Daura na jihar Katsina

    Gawar marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta isa mahaifarsa Daura domin yin jana'iza da kuma binnewa.

    Gawar ta bar filin jirgin sama na Katsina bayan isa daga Landan, tare da rakiyar shugaba Tinubu, da mataimakinsa Kashim Shettima, da uwargidan marigayin, Aisha Buhari da kuma wasu daga cikin yaransa.

    Za a gudanar da sallar jana'iza sannan a binne shi a gidansa.

    Mahaifar marigayin na cike da mutane waɗanda suka shafe sa'oi suna dakon jiran isar gawar domin yi mata Sallah.

    Manyan jam'ian gwamnatin Najeriya na baya da na yanzu, da shugabanni ƙasashen waje, da iyalansa na zaman jira cike da alhinin rasuwarsa.