Ban ji haushi da PSG ta lashe UCL ba - Mbappe

Asalin hoton, Getty Images
Kylian Mbappe ya ce bai ji haushin nasarar da Paris St-Germain ta yi wajen lashe Champions League ba, shekara ɗaya bayan barin ƙungiyar zuwa Real Madrid.
Ɗan wasan gaban ya bar PSG a matsayin wanda ya fi ci mata kwallaye, sai dai ya ƙasa cin gasar Champions League a kaka bakwai da ya shafe a ƙungiyar - inda ya koma Madrid kyauta a watan Yulin bara.
PSG ta samu nasara ne bayan lallasa Inter Milan da 5-0, a ranar 31 ga watan Mayu a filin wasa na Munich Arena da ke Jamus.
"Ban bar ƙungiyar da wuri ba, tarihin rayuwata a PSG ya kare. Ba na jin haushi, saboda zama na a PSG ya kare," in ji kyaftin ɗin tawagar Faransa, wanda ya ci wa PSG kwallo 256.
Da yake magana da manema labarai gabanin karawar Faransa da Jamus a neman matsayi na uku a gasar Nation League, Mbappe ya ƙara da cewa: "Na yi iyakar ƙoƙarina, kuma haka Allah ya kaddara cewa za su ci Champions League ba tare da ni ba.
"Lashe Champions League ba tare da ni ba da PSG ta yi ba zai dame ni ba. Ina cikin farin ciki - Ina ganin sun cancanci lashe gasar.
"Sun shafe tsawon shekaru suna fuskantar kalubale. Tare da ni aka fuskanci hakan; na buga wasa a kowane mataki a Paris in ban da wanda suka yi nasara.
"Su ne ƙungiyar da ta fi hazaka a Turai. Ban taɓa ganin ƙungiyar da ta ci kwallo 5-0 a wasan karshe ba gaskiya."
Lokaci na karshe da Mbappe ya kusan lashe Champions League shi ne wasan karshe da suka buga da Bayern Munich a 2020, inda suka sha kashi da 1-0.

















