Mafi yawan tititan birnin Akure sun kaance fayau babu zirga-zirga
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad
Masu zanga-zangar ƙin gwamnati a Abkhazia ta Georgia sun mamaye majalisa
Masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a yankin Abkhazia da ke ƙasar Georgia sun ƙi ficewa daga harabar majalisar dokokin ƙasar.
Kafofin yaɗa labaran Rasha sun ce masu zanga-zangar sun yi watsi da shawarar da shugaban ƙasar Aslan Bzhania ya gabatar ta cewa zai yi murabus.
Shugaban ya ce a shirye yake ya sauka daga mulki, ya kuma gabatar da kira da a yi zaɓe zai bar mataimakin shugaban ƙasa ya karɓi ragamar mulkin ƙasar, yayin da shi kuma zai tsaya takara.
Masu zanga-zangar sun mamaye majalisar dokoki da harabar fadar shugaban ƙasa a ranar Juma'a don nuna ɓacin rai kan wani ƙudurin doka mai goyon bayan Rasha da majalisar dokokin kasar ke shirin amincewa da shi.
Ana ci gaba da ƙirga ƙuri'un zaɓen gwamnan jihar Ondo
Asalin hoton, bbc
Yanzu haka ana ci gaba da ƙirgen ƙuri’u bayan rufe rumfunan zaɓen gwamnan jihar Ondo da aka gudanar a
yau, Asabar.
‘Ƴantakara 17 ne su ka fafata,
to sai dai takarar ta fi zafi tsakanin Lucky Ayeditiwa na jam’iyyar APC da Agboola Ajayi na Jam’iyyar PDP.
ƘungIyoyin sa-ido sun yaba da
yanayin zaɓen cikin kwanciyar hankali, sai dai kuma sun yi zargin cewa an tafka
maguɗin siyan ƙuri’u - inda aka riƙa siyar da ƙuri’a ɗaya kan naira dubu goma
zuwa naira dubu ishirin, a wasu daga cikin mazaɓun jihar.
Zaɓen ya samu fitowar
jama’a dai dai gwargwado a faɗin ƙananan hukumomin jihar 18.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) da ƙungiyoyin
sufuri sun yi nasarar tura jami’an zaɓe da kayayyakin aiki a faɗin jihar.
Jami’an tsaro sun
kama wasu da suka tayar da hayaniya a wasu yankunan jihar.
Biden zai yi ganawar ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa da shugaban China
Asalin hoton, Getty Images
Joe Biden zai yi ganawarsa ta ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa da shugaban ƙasar China Xi Jinping a cikin sa'o'i masu zuwa.
Fadar White House ta ce tattaunawar, a gefen taron ƙungiyar APEC da za a yi a ƙasar Peru, za ta mayar da hankali ne kan abin da ta kira "lokacin miƙa mulki mai cike da sarƙaƙiya.
Shugabannin biyu dai sun yi gargaɗin yiwuwar haɗarin da ke tafe yayin da Donald Trump ke shirin sake karbɓar ragamar mulki.
Mista Trump ya yi alƙawarin ɗora haraji mai yawa kan kayayyakin da China ke shigarwa Amurka..
Ƙungiyar RSF ta kashe mutum goma a jihar Gezira - Likitoci
Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyar likitoci a Sudan ta ce mutum goma sha bakwai sun mutu wasu sama da ashirin kuma sun ɓace a wani hari da dakarun ƙungiyar RSF suka kai kan wani ƙauye a kudancin jihar Gezira.
Ko a jiya juma'a hukumar jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutUM dubu ɗari uku da arba'in ne suka rasa matsugunansu a Gezira a cikin watan jiya.
Dakarun RSF sun kai hare-hare kan ƙauyuka da dama bayan wani kwamandan RSF wanda dan jihar ne ya sauya sheka zuwa ɓangaren sojoji a watan Oktoba.
Ministan kuɗi na Sudan Ibrahim Jibril ya ce yana fatan sabuwar gwamnatin Amurka da za ta karɓi mulki za ta shawo kan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta daina mara baya ga ƙungiyar RSF.
To amma daman Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan na musanta goyon bayan RSF.
Harin Isra'ila kan makaranta a Gaza ya kashe mutum goma da raunata da dama - Jami'an lafiya
Asalin hoton, reuters
Jami'an lafiya sun ce aƙalla Falasɗinawa goma ne suka mutu a wani hari da Isra'ila ta kai ta sama kan wata makaranta da 'yangudun hijira ke zaune a birnin Gaza.
Masu aikin ceto na ci gaba da aikin neman waɗanda ke da sauran numfashi da ke ƙarƙashin ɓuraguzai a makarantar ta Abu Assi a sansanin 'yangudun hijira na Shati.
Ana ganin akwai mutane da dama da ɓuraguzai suka binne.
Har yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba a kan harin..
Akwai kuma wasu mutane tara daban da suka rasu a wasu hare-haren na Isra'ila a birnin na Gaza.
Haka kuma a can Lebanon ma, ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta ce hare-haren Isra'ila a wani ƙauye da ke gabashin yankin Baalbek, sun kashe mutum shida da suka haɗa da yara uku.
Mun ceto mutum 58 da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna - Ribadu
Gwamnatin Najeriya
ta miƙa wa gwamnatin jihar Kaduna mutum 58 da ta ce ta kuɓutar daga hannun ‘yan bindiga
a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar ta Kaduna.
Gwamnatin ta miƙa mutanen
ne ta hannun ofishin mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro Malam
Nuhu Ribadu, bayan kula da lafiyarsu da aka yi a asibiti na tsawon kwana biyu.
Mutanen da aka ceto daga hannun ‘yan bindigar su 58 waɗanda suka haɗa da mata 23 da maza 35 an kama su ne a ƙaramar hukumar Ɗan-Musa ta jihar Katsina a hare-hare daban-daban - mafi yawan shekarunsu shi ne Malam Ibrahim Audu mai shekara 65, mafi ƙanƙantarsu kuuwa shi ne wani jariri mai ƙasa da shekara ɗaya wanda aka kama mahaifiyarsa wata uku baya.
Babban hafsan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa ya ce aikin haɗin kai da suke yi tsakanin gwamnatoci da mutanen gari da suke bayar da bayanai shi ya kai ga samun nasarar kuɓutar da waɗannan mutane.
“shugaban ƙasa da ofishin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro suna ba mu gudunmuwar da ta kamata wajen aikinmu. In ka ga mutanen da aka kama sai ka yi mamakin mai ya sa mutane za su kama su? Domin babu wani abu da za a samu a hannunsu. Mutane ne da ke neman abin sawa a baka.
“Muna so mu gaya wa ‘yan ƙasa muna aiki ba dare ba rana domin tsare su. Ba mu biya ko sisi ba aka sake su. Sai da aka kai su asibiti aka duba lafiyarsu waɗanda ba su da lafiya aka ba su magani aka kuma ba su abinci da sutura suka sa,” in ji Janar Christopher Musa.
Sani Liman Kila shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Kaduna wanda ya karbi mutanen a madadin gwamnan jihar Sanata Uba Sani - ya ce ba kodayaushe ne ake buƙatar yaƙi da ‘yanbindiga ba domin kuwa a lokuta da dama sulhu na taka muhimmiyar rawa wajen ceto mutanen da ake garkuwa da su.
“Dole mu yi godiya ga shugaban ƙasa da NSA, kuma a madadin gwamnan jihar Kaduna za mu ci gaba da bayar da haɗin kai ga jami’an tsaro.
“Babu shakka a sakamakon sulhun da aka yi ne da ‘yan bindigar suka sako mana waɗannan mutane, da sulhu ba ya aiki da ba a yi haka ba,” in ji Kila.
Sadi Adamu ɗaya ne daga cikin waɗanda aka kama, kuma ya shafe shekara ɗaya da wata biyu a hannun ‘yan bindigar.
“Na gode wa Allah da kuma gwamnati, wallahi ba ma cin komai sai masara ɗanya da totuwarta. Ni har na haƙura da iyalaina na ce su koma gida amma yanzu na ce su dawo,” in ji Sadi.
A nata ɓangaren Shafa’atu Idris ta ce ta kwashe makonni 11 a hannun ‘yanbindigar.
“Randa suka kama ni a cikin jini na tsallake mijina na bar shi. Sun tafi da ni da ɗana. Abin takaicin shi ne sai su tambaye ka kuɗin fansar da watakila kai da danginku baki ɗaya ba ku da shi. Amma na yi godiya ga gwamnatin Najeriya,” in ji Shafa’atu.
Akwai mutane da dama irin waɗannan da har yanzu suke hannun ‘yanbindiga a sassa daban-daban a Najeriya, sai dai gwamnati na jaddada alƙawarin ba za ta huta ba har sai ta ga yadda za ta kuɓutar da su, ta sake haɗa su da iyalansu, wani abu da ke zama ƙwarin gwiwa ga waɗanda suke tsaren.
Matsalar tsaro a Najeriya na neman zama irin abin da ‘yan magana ke cewa ana maganin ƙaba kai na ƙara kumburi - yayin da gwamnati ke cewa tana samun nasara a yankuna irin na su Birnin Gwari a can jihohin Sokoto da Kebbi kuma an samu ɓullar wata ƙungiya da ake kira Lakurawa. Kodayake gwamnati ta ce ba za ta huta ba har sai ta kawo ƙarshen wannan ƙungiya.
Wani mahari ya kashe mutum takwas da jikkata 17 da wuƙa a wata kwaleji a China
Asalin hoton, Getty Images
Wani mahari ya kashe mutum takwas da raunata wasu goma sha bakwai da wuƙa a wata kwaleji da ke gabashin China.
'Yansanda sun ce sun kama wanda ake zargi da kai harin - wani mutum mai shekara 21, da ya yi karatu a kwalejin ta Wuxi Technical College.
Sun ce ya amince da kansa shi ya kai harin - saboda makarantar ta ƙi ba shi takardar shedar difloma ta karatun da ya yi.
Haka kuma an ce yana fama da damuwa a kan alawus ɗin da ake ba shi a inda yake aiki na neman sanin makamar aiki, da ya ce ba shi da yawa duk da irin daɗewar da yake yi ta tsawon sa'o'i.
Ko a ranar Litinin da daddare an kashe mutum 35 a kudancin ƙasar ta China bayan da wani mutum ya kutsa da mota cikin taron mutane a wajen wani filin wasa.
Rikicin ƙabilanci ya sa an katse hanyoyin waya da intanet a jihar Manipur ta India
Asalin hoton, AFP
Jami'ai a jihar Manipur da ke arewa maso gabashin India sun dakatar da hanyoyin intanet da waya tare da sanya dokar hana zirga-zirga har sai abin da hali ya yi.
An shiga zaman ɗar-ɗar tun bayan da aka gano gawarwakin wasu mutum shida na garin Meitei waɗanda aka yi amanna 'yantawaye ne suka sace su a makon da ya gabata.
Samun labarin ganin gawarwakin ke da wuya sai aka fara kai hari kan gidajen wasu 'yansiyasa su bakwai na yankin.
Jihar Manipur na fama da mummunan rikicin ƙabilanci tsakanin ƙabilun Meitei 'yan Hindu da suka fi yawa a jihar da kuma al'ummar Kuki waɗanda yawanci Kiristoci ne - rikicin da ya wuce sama da wata goma sha takwas.
Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 200 da raba wasu sama da 600 da muhallinsu.
Rugujewar bene mai hawa hudu ta kashe mutum biyar da jikkata sama da 40 a Tanzaniya
Mutum biyar sun mutu wasu sama da 40 sun ji rauni bayan da wani bene mai hawa hudu ya ruguje a unguwar Kariako, da ke zaman cibiyar kasuwanci mafi girma a babban birnin kasuwanci na Tanzania, Dar es Salaam.
Rugujewar ta faru ne da misalin karfe 06:00 na safe agogon GMT, kuma ana fargabar cewa ta rutsa da mutane da dama a karkashin buraguzai.
Jami'an tsaro da masu aikin ceto na ta amfani da motocin tonon kasa wajen zakulo wadanda buraguzai suka binne a ginin.
Hukumomi na fargabar cewa yawan wadanda suka mutu ka iya karuwa, yayin da ake ci gaba da aikin ceton.
Shugabar kasar ta Tanzania Samia Suluhu ta mika sakon ta'aziyya da wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma iyalansu.
Wadanda suka ga yadda lamarin ya faru sun ce ko a jiya Juma'a ma ana aikin gini a gidan, kafin ya ruguje.
Hukumomi ba su kai ga gano dalilin rugujewar ginin ba, amma ana sa ran masu bincike su dukufa gano musabbabin da an kammala aikin ceto.
An ɗaura auren 'yar Kwankwaso da ɗan Mangal
Asalin hoton, Stanley Nkwocha
A yau ne aka ɗaura auren 'yar gidan jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da ɗan gidan hamshaƙain ɗan kasuwar nan Dahiru Mangal.
Asalin hoton, Kano State Gov
An ɗaura auren Aisha Rabiu Musa Kwankwaso da angonta Injiniya Fahad Dahiru Mangal a fadar sarkin Kano na 16 na Muhammadu Sanusi ll.
Asalin hoton, Stanley Nkwocha
Manyan baƙi da dama ne suka halarci ɗaurin auren, ciki har da tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da kakakin majalisar wakilan ƙasar, Hon Tajudeen Abbas, da jagoran adawar ƙasar Atiku Abubakar.
Asalin hoton, Stanley Nkwocha
An ɗaura auren ne a kan sadakin naira miliyan guda.
Asalin hoton, Stanley Nkwocha
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ne ya kasance waliyyin Amarya, yayin da mataimakain shugaban ƙasa ya kasance wakilin Ango.
Asalin hoton, Kano State Gov
Asalin hoton, Stanley Nkwocha
Bayanan hoto, Kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Hon Tajudeen Abbas na daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren
An fara ƙirga ƙuri'u a zaɓen gwamnan jihar Ondo
An fara ƙidaya ƙuri'u a wasu sassan Akure, babban birnin jihar Ondo.
A rumfar zaɓe mai lamba 17 da ke Akure, malaman zaɓe sun fara ƙirga ƙuri'u a gaban wakilan jam'iyyun da suka fafata a zaɓen.
Ƙungiyoyin da ke sanya ido a zaɓen Ondo sun yi zargin sayen ƙuri'a
Gamayyar ƙungiyoyin da ke sanya idanu a zaɓen gwamnan jihar Ondo ta yi zargin samun matsalar sayen ƙuri'a a zaɓen.
Yayin zantawarsa da BBC, Dakta Chris Kwaja, daraktan ƙungiyar 'US Institute of Peace' a Najeriya, kuma mamba a ƙungiyar YAGA Africa, ya koka kan yadda ya ce wasu 'yan siyasa na sayen yancin al'umma ta hanyar sayen ƙuri'unsu.
Mista Kwaja ya kuma ɗora alhakin matsalar kan halin talauci da al'umma ke ciki.
Ya kuma yi kira ga masu zaɓe su kauce wa wannan ɗabi'a yana mai cewa hakan tamkar sayar da 'yanci ne.
''Yancin mutane shi ne zai sa mutane su yi abin da suke so, wajen sauya shugabaninsu'', in ji shi.
Dakta Kwaja ya kuma ce ya zuwa yanzu sun gamsu da irin rawar da hukumar INEC da jami'an tsaro suka yi a lokacin zaɓukan.
An fara kammala kaɗa ƙuri'a a wasu rumfunan zaɓe
An kammala kaɗa ƙuri'a a mafi yawan rumfunan zaɓe a wasu sassan jihar da aka samu ƙarancin fitowar masu zaɓe.
Wakilin BBC ya ce fiye da kashi 50 na rumfunan zaɓen da ya ziyarta a yankin ƙaramar hukumar Akure ta Kudu da wasu sassan karamar hukumar Idanre, ba a samu fitowar masu kaɗa ƙuri'a ba.
Hukumar zaɓen dai ta ce za a fara tantance ƙuri'u da ƙirga su da misalin ƙarfe 2:30 na yamma
Wakilan Tarayyar Turai na sanya idanu a zaɓen gwamnan Ondo
Asalin hoton, EU in Nigeria Twitter
Wakilan Tarayyar Turai na sanya idanu a zaɓen gwamnan jihar Ondo.
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, EU ta ce tawagarta da ke sanya idanu a zaɓen sun ziyarci muhimman wurare a jihar da ke kudu maso yammacin Najeriya.
'Yan takara 18 ne ke fafatawa a zaɓen ciki har da gwamnan jihar mai ci Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC.
Ministan harkokin cikin gida ya kaɗa ƙuri'arsa
Asalin hoton, Olubunmi Tunji-Ojo/X
Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen Ondo da ke gudana.
Tunji-Ojo ya kaɗa ƙuri'ar ne a rumfar zaɓe mai lamba 17 a yankin ƙaramar hukumar Akoko North-West.
Yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri'ar tasa, ministan ya ce zaɓen na gudanar cikin kwanciyar hankali da lumana.
"Zaɓen na gudana babau wata tangarɗa, kuma jami'an zaɓe suna nuna ƙwarewar aiki, kuma na ji daɗin yadda mutane suka fito domin kaɗa ƙuri'unsu'', in ji ministan.
Jami'an tsaro na sintiri a faɗin jihar Ondo
Jami'an tsaro cikin cikakken shiri na ta sintiri domin tabbatar da tsaro a faɗin jihar Ondo yayin da ake ci gaba da kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar.
Jami'an 'yansanda da na sojoji da jami'an civil defence sun kakkafa shingayen bincike a kan manyan titunan jihar domin aiwatar da dokar taƙaita zirga-zirga.
Tuni dai rundunar 'yansandan ƙasar ta ce ta aike da jami'an 34,657 domin tabbatar da tsaro a lokacin zaɓen.
Rundunar 'yansandan ta ce za a aika jami'ar huɗu zuwa kowace rumfar zaɓe.
Babban sifeton 'yansandan ƙasar Kayode Egbetokun, ya ce ana sa ran jami'an tsaro 43,157 ne za su tabbatar da tsaro a lokacin zaɓen.
Tinubu ya buƙaci mutanen Ondo su yi zaɓe cikin lumana
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya buƙaci masu zaɓe da masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓen su gudanar da zaɓen gwamnan jihar cikin kwanciyar hankali da lumana.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta ftar ranar Juma'a, Shugaba Tinubu ya ce tsarin dimokraɗiyya shi ne cikakken tsarin da ke tabbatar da zaɓin al'umma a shugabanci.
Shugaban ya kuma ce tsarin ne ke bai wa 'yan ƙasa damar zaɓar mutanen da za su mulkesu, don haka ne ya kira ga al'ummar jihar su fito domin bayyana 'yancinsu da kundin tsarin mulki ya tanadar musu.
Dan takarar PDP Agboola Ajayi ya kaɗa ƙuri'arsa
Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi ya kaɗa ƙuri'arsa a rumfar zaɓe mai lamba 4 da ke yankin ƙaramar hukumar Ede-Odo.
Mista Ajayi mai shekara 54 tsohon matamakin gwamnan jihar ne a wa'adin mulkin tsohon gwamnan jihar, marigayi Romiti Akeredolu na farko.
Ya isa rumfar zaɓen sannan ya shiga layin masu zaɓe, inda aka tantance shi gabanin ya kaɗa ƙuri'ar tasa.
Tsofafffi da dama sun fito zaɓen gwamnan Ondo
Asalin hoton, INEC/X
An samu fitowar tsaffafi da dama domin kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen gwamnan jihar Ondo.
Mutanen da suka manyantan sun ce sun fito zaɓen ne saboda imanin da suka yi cewa da ƙuri'arsu ce kawai za su iya sauya komai na shugabanci.
Asalin hoton, INEC/X
Gabon na ƙuri'ar raba gardama don amincewa da sabon kundin tsarin mulki
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Ƙasar Gabon na gudanar da ƙuri'ar raba gardama domin amincewa da sabon kundin tsarin mulki, wanda ake gani a wani mataki na mayar da ƙasar tafarkin Dimokraɗiyya.
Shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Brice Oligui Nguema - wanda ya kawo ƙarshen mulkin iyalin gidan Bongo na tsawon shekara gomman shekaru - ya alƙawarta mayar da mulki zuwa farar hula cikin shekara biyu.
Wasu goyon bayan sabon kundin tsarin mulkin sun bayyana matakin a matsayin wani mataki na sabunta makomar ƙasar, bayan tsawon shekara 50 na mulkin iyalan gidan Bongo.
Amma masu suka na cewa an tsara sabon kundin tsarin mulkin ta yadda zai taikama wa masu mulkin ƙasar, inda suke gargaɗin hakan ka iya haifar da mulkin mulaka'u.
Sabon kundin tsarin mulkin ya tanadar wa shugaban ƙasa wa'adin mulkin biyu na shekara bakwai-bakwai.
Haka kuma akwai wasu sabbin dokokin da suka shafi asali da za su iya hana hamɓararren shugaban ƙasar Ali Bongo tsayawa takara - saboda ya auri wata Bafaranshiya - kuma hakan zai iya hana 'ya'yansa tsayawa takara.