Simeone ya ce bai ƙyauta ba kan abin da ya yiwa Vinicius, Spanish Super Cup

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Atletico Madrid, Diego Simeone, ya bayar da uzuri kan halayen da ya nuna a gefen fili, yayin da ƙungiyarsa ta sha kashi a wasan daf da ƙarshe a Spanish Super Cup a hannun Real Madrid a Saudiyya. Ya ce yana baƙin ciki kan yadda ya tsokani Vinícius Jr., amma bai bukaci a yafe masa ba.
Wata ƙyamara ce ta nuna kocin ɗan Argentina yana ta tsokanar ɗan ƙwallon tawagar Brazil, Vinícius Jr., a tsawon wasan.
Rahotanni sun ce yana ta faɗawa ɗan wasan Real Madrid: “Florentino zai kore ka — ka tuna abin da nake gaya maka,” yana nufin rade-radin makomar Vinícius kan mika masa sabuwar yarjejeniya, bayan da wadda yake da ita a Real Madrid wa’adinta ke gab da ƙarewa.
Real Madrid ta yi nasara da ci 2–1, inda ta samu gurbin buga wasan ƙarshe, amma daga bisani ta sha kashi da ci 3–2 a hannun abokan hamayya Barcelona.
Atletico Madrid na matsayi na huɗu a teburin La Liga da tazarar maki 11 tsakanin da Barcelona.

















