Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 29 ga watan Maris 2025

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. An ga watan Ƙaramar Sallah a Najeriya

    Sallah

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin duban wata a Najeriya ya sanar da cewa an ga jinjirin watan Shawwal, wanda ya kawo ƙarshen azumin watan Ramadan na shekarar 1446/2025.

    Mai alfarma Sarkin musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ne ya sanar da ganin watan a madadin ƴan kwamitin.

    Hakan na nufin gobe Lahadi, 30 ga watan Maris na 2025 ne za a yi idin Ƙaramar Sallah na bana a faɗin Najeriya.

    Sanarwar ta Najeriya ta zo ne bayan ƙasar Saudiyya ta sanar da nata ganin watan tun da yammacin yau, wato sa'o'i kaɗan kafin ganin na Najeriya.

    A Jamhuriyar Nijar ma rahotanni suna nuna cewa an ga jinjirin watan na Shawwala.

  2. Magoya bayan Wike za su yi gangami a Bayelsa duk da hanin gwamnan jihar

    Nyesom Wike

    Asalin hoton, Nyesom Wike/Twitter

    Waɗanda suka shirya gangamin nuna goya baya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, sun ce babu gudu ba ja da baya sai sun gudanar da taronsu kamar yadda suka shirya.

    Wannan na zuwa ne bayan Gwamnan jihar, Douye Diri ya hana taron, inda ya ce taron zai tayar da zaune tsaye ne a jiharsa, kuma ba zai bar hakan ya faru ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Gwamnan ya bayyana a wani taron dattawa da jami'an tsaron jihar cewa bai amince a gudanar da taron ba a jiharsa.

    Amma a wata sanarwa da kakakin sakataren jam'iyyar PDP na yankin kudu maso kudu, George Turnah ya fitar, wanda shi ne yake jagorantar shirya gangamin, ya ce babu gudu babu ja da baya.

    Turnah ya ce siyasar ƙabilanci ba ta mazauni a siyasar Najeriya, inda ya ƙara da cewa suna da ƴancin shirya gangami na lumana kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

    Ya ce ba su da wata manufar tayar da zaune tsaye, inda ya ƙara da cewa za su shirya gangami ne kawai domin nuna goyon bayansu ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Nyesom Wike.

  3. Girke-Girken Ramadan: Fried rice mai nama da kayan miya

    A filinmu na girke-girken Ramadan na yau, Hafsat Usman wadda aka fi sani da Muhafoven za ta nuna muku yadda ake yin fried rice mai nama da kayan lambu a cikinsa.

    Bayanan bidiyo, Girke-Girken Ramadan: Fried rice mai nama da kayan miya
  4. Waɗanda suka rasu a girgizar ƙasar Myanyar sun kai 1,600

    Myanmar

    Asalin hoton, Reuters

    Waɗanda suka rasu a girgizar ƙasar Myanmar sun haura 1,600 kamar yadda alƙaluman hukumomin ƙasar suka nuna.

    Zuwa yanzu gwamnatin sojin ƙasar ta tabbatar d mutuwar 1,644, sannan waɗanda suka jikkata sun saura 3,408.

    A ɗaya gefen kuma, har yanzu akwai ɗaruruwan mutane da baraguzan gine ya danne, waɗanda ake cigaba da nemansu har zuwa wannan lokaci.

  5. An ga watan Ƙaramar Sallah a Saudiyya

    Sallah

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Shawwal, wanda ke alamta kawo ƙarshen azumin watan Ramadan.

    Shafin Inside the Haramain ne ya ruwaito hakan, inda ya ce kwamitin duba watan ne ya cimma matsaya bayan ɗaukar awanni ana neman wata.

    Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar Ƙaramar Sallah a ƙasar ta Saudiyya.

    Yanzu dai abin jira a gani shi ne sakamakon kwamitin duba watan a Najeriya da sauran ƙasashe.

  6. Yadda batun kayyade shekarun masu son takarar shugaban Najeriya ya fara tayar da kura

    Majalisa

    Asalin hoton, BENJAMIN KALU

    Jam'iyyun adawa a Najeriya sun fara nuna adawarsu kan wani matakin da 'yan majalisar wakilan kasar suka dauka da zai kayyade shekarun 'yan takarar da za su tsaya neman mukamin shugaban kasa da gwamna da cewa kada su zarce sittin.

    Kudurin dokar ya tsallake karatu na farko da na biyu, wanda hakan ke nufin ya na daf da zama doka.

    ldan kudurin ya samu sahalewar yan majalisar Najeriyar har ya kai ga zama doka, zai hana mutane da dama tsayawa neman takarar shugabancin kasar.

    Ƙarin bayani - https://trib.al/MaaK62w

  7. Ƙarya da ƙage tsohon shugaban ma'aikatan Rivers ya yi mini - Fubara

    Fubara

    Asalin hoton, X/@SimFubara

    Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar, Siminalaya Fubara ya ce maganganun da tsohon shugaban ma'aikatan jihar, Dokta George Nwaeke ya yi a game da shi ƙage ne.

    Fubara ya bayyana haka a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce ya yi haka ne domin ya kare kansa daga zargin da aka yi masa.

    "Maganar cewa wai ina shirin goyon bayan Bala Mohammed a zaɓen 2027 abin dariya ne saboda idan ma za a yi maganar, ta yaya shugaban ma'aikata zai shiga ciki, ballantana ma a ce mun zauna domin tattaunawa da ƴanbindiga masu fasa bututun mai. Wannan magana ce kawai domin babu inda aka taɓa yin zama irin wannan."

    Fubara ya ce Bala Muhammed ya kawo masa ziyara ne a matsayinsa na shugaban gwamnonin PDP, kuma a bayyane aka yi komai, kuma duniya ta gani.

    "Abin ban mamaki ne Nwaeke ya yi ikirarin cewa na zauna da masu fasa bututun mai. Kowa ya san ni mutum ne mai son zaman lafiya, kuma mai kira da a zauna lafiya.

    "Alamu suna nuna cewa akwai lauje cikin naɗi kan bayanan Nwaeke, kuma duk abin da yake faɗa kawai yana faɗa ne domin cika alƙawarin da ya ɗauka wa waɗanda suka biya shi, ko suka tursasa shi ya min ƙarya. Don haka nake kira ga al'ummar Najeriya, musamman ƴan jihar Rivers da su yi watsi da abin da Nwaeke ya faɗa domin ya yi haka ne domin ya ɓata min suna, sannan ya ɓata min gwamnati da ma yunƙurin shugaban ƙasa na wanzar da zaman lafiya."

  8. Ina alfahari da alaƙata da Tinubu - Buhari

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Muhammadu Buhari/Facebook

    Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce yana alfahari da alaƙarsa da shugaban ƙasar na yanzu, Bola Ahmad Tinubu.

    Buhari ya bayyana haka ne a saƙonsa na taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, wadda mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar.

    Sanarwar ta ce Buhari da Tinubu sun gana ta wayar tarho a ranar Juma'a, inda a ciki Buhari ya yi Tinubu addu'ar tsawon rai da ingantacciyar lafiya da, sannan ya yi masa fatan samun nasarar a mulkinsa.

    "Idan muka yi wa shugabanninmu addu'a, muna yi wa kanmu ne. Ƙasarmu na buƙatar addu'o'inmu," in ji Buhari a ganawarsa da Tinubu.

    Tsohon shugaban ya ce shi da iyalansa suna godiya ga Tinubu da sauran jagororin jam'iyyar bisa ƙoƙarin da suka yi wajen kafa jam'iyyar APC, inda har ya samu nasarar zama shugaban ƙasa har sau biyu, bayan bayan ya sha gwadawa a baya ba tare da samun nasara ba.

    "Lokacin da ƴan Najeriya suka zaɓi APC a 2025, zaɓi suka yi domin tsara dandamalin gina sabuwar Najeriya inda talakawa za su samu damarmakin da suke buƙata, kuma ina jin daɗi har yanzu ba a kauce daga tsarin ba."

  9. Tsohon shugaban ma'aikatan Rivers ya zargi Fubara da 'alaƙa da masu fasa bututun mai'

    Rivers

    Asalin hoton, Screenshot/Channels

    Tsohon shugaban ma'aikatan jihar Rivers, George Nwaeke ya ce yana cikin ƙoshin lafiya, kuma yana nan a Abuja.

    Jawabinsa na zuwa ne bayan wata hira da ya yi, inda a ciki ya zargi dakataccen gwamnan jihar, Siminalaya Fubara da abubuwan da ya ce ba daidai ba ne.

    Daga cikin akwai abubuwan da ambata akwai cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammad ne Gwamna Fubara zai goya wa baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

    Haka kuma ya ce Fubara ya gana da ƴanbindiga masu fasa bututun mai domin kai hare-hare kan bututun mai da wasu kadarorin ƙasar, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Haka kuma Nwaeke ya ce bidiyon da matarsa, Florence ta yi tana kuka cewa ba ta san inda yake ba kuma ba ta san halin da yake ciki ba, tsara mata aka yi.

    "Na ga bidiyon matata tana kuka wai an sace ni saboda an tsara mata ƙarya.

    "Ina so mutane su gane cewa babu abin da matata ta sani game da aikina, ba na tattauna komai da ita. Tsakanina da ita maganar gida ce kawai.

    "Don haka duk da aka tsara mata take faɗa ƙarya ne. Na zo Abuja ne domin ina tunanin zan fi samun tsaro. Amma duk abin da na faɗa (game da Fubara) gaskiya, kuma daga zuciyata na faɗa."

  10. Yadda karatun addinin ya zamo zaɓi ɗaya tilo ga matan Afghanistan

    Taliban

    Amina ba za ta taba mantawa da lokacin da yaruntarta ta canza ba. Tana 'yar shekara 12 kacal, aka shaida hana ta zuwa makaranta akasin sauran ‘yan’uwanta yara maza.

    Sabuwar shekarar karatu a Afghanistan ta fara ne ranar Asabar, 22 ga watan Maris, amma shekaru hudu a jere ke nan, da hana 'yanmatan da suka haura shekaru 12 zuwa makaranta.

    "Burina na rayuwa ya watse'' in ji ta cikin murya mai sanyi.

    Ƙarin bayani - https://trib.al/ZWML2m4

  11. Ƴansanda sun kama mutum 14 da ake zargi da kashe matafiya a Edo

    Edo

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan jihar Edo ta sanar da kama mutum 14 da ake zargi suna da hannu a kashe matafiya a ranar Alhamis.

    Matafiyan dai sun ratsa ta jihar ne a hanyarsu daga Fatakwal da ke kudancin Najeriya zuwa Kano da ke arewacin ƙasar, inda wasu ƴan sa-kai suka tare su a yankin Uromi bisa zargin masu garkuwa da mutane ne, wanda hakan ya sa mutanen yankin da suka musu aika-aikar.

    A cewar kakakin rundunar ƴansandan jihar Edo, Moses Yamu, ya ce an kama wasu waɗanda ake zargi da hannu a kisan.

    "A cigaba da bincike da muke yi, zuwa yanzu mun kama mutum 14 da ake zargi suna da hannu, sannan an yi taron gaggawa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki na yankin domin a kwantar da hankalin jama'a," in ji Yamu a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a.

    Sai dai rundunar ta ƙara da cewa kawo ɗauki da ta yi ne ya taimaka wajen ceto mutum 10 daga cikin matafiyan.

  12. Mece ce gaskiyar asalin mutanen da aka kashe a Edo?

    Edo

    Asalin hoton, FB/Multiple

    A ranar Juma'a shafukan sada zumunta musamman a arewacin Najeriya sun cika da fushi da alhini na abin da ya faru a Edo, ɗaya daga cikin jihohin kudancin ƙasar.

    Hotunan da aka riƙa yadawa, waɗanda BBC ba ta tantance da kanta ba sun nuna yadda aka yi wa wasu mutane jina-jina, sannan aka riƙa jefa tayoyin mota a kansu.

    Haka nan an ga yadda wasu ke dukan wani mutum da katako a cikin kwalbati, sannan a wani hoton kuma an ga wuta na ci daga nesa.

    Ƙarin bayani - https://trib.al/CtEMah4

  13. Ƴanbindiga na ƙara ƙarfi a Haiti - MDD

    Babban jami'in kare haƙƙin bil adama a Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce rikicin Haiti ya ƙara ta'azzara yayin da ƴanbindiga ke ƙara samun ƙarfi tare da kai wa farar hula hari.

    Volker Turk ya shaida wa hukumar kare haƙƙin bil adama cewa gungun ƴanbindigar sun mamaye muhimman yankuna da ke Port-au-Prince, babban birnin ƙasar inda suke amfani da muggan makamai domin fatattakar jami'an tsaro tare da jefa ƙasar cikin tashin hankali.

    Tun watan Yuli, ofishinsa ya samu rahoton mutuwar fiye da mutum dubu huɗu da ɗari biyu, da garkuwa da sama da mutum 100 da kuma ƙaruwar cin zarafi ta hanyar lalata domin nuna iko.

  14. Ƴan Afirka ta Kudu na tsammanin diyyar mulkin wariyar launin fata

    Afirka ta Kudu

    Asalin hoton, Reuters

    A Afirka ta Kudu, ana ci gaba da nuna damuwa game da wani asusun gwamnati da aka yi nufin biyan waɗanda aka zalunta a lokacin mulkin wariyar launin fata.

    Wannan asusu, wanda aka sani da Asusun Shugaban Ƙasa, yana da kusan rand biliyan biyu (sama da dala miliyan 100 ke nan) a ajiye amma waɗannan kuɗaɗe ba a kashe su ba.

    Da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa da iyalansu na ci gaba da jiran a yi musu adalci da kuma biyan diyya.

    Yanzu dai kimanin shekara 30 ke nan bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata a ƙasar.

  15. Sama da mutum 1000 ne suka mutu a girgizar ƙasar Myanmar

    Myanmar

    Asalin hoton, EPA

    Gwamnatin soji da ke mulki a Myanmar ta ce mutum 1,002 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske da ta faru jiya Juma'a.

    Gwamnatin ta ƙara da cewa fiye da wasu dubu biyu sun ji raunukai yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin zaƙulo mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓuraguzai.

    Tawagar jami'an agaji sun bayyana irin ɓarnar da aka yi a Mandalay - birni mafi kusa da inda girgizar ƙasar ta afku, sannan asibitoci sun cika da mutanen da lamarin ya shafa.

    Shugaban mulkin soji a Myanmar ya nemi taimakon ƙasashen duniya sai dai yaƙin basasar da ake ci gaba da yi zai yi tarnaƙi ga ayyukan jin-ƙai.

    Wani jami'in hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce Myanmar ta kasance a cikin yaƙi na tsawon shekara huɗu, wanda hakan ya sa ake zargin sojojin da ke mulki a ƙasar suna tsare gomman mutane.

  16. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da war waha, barkanmu da sake saduwa a wannan shafi namu na kai-tsaye, inda a yau ma za mu cigaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Isiyaku Muhammed ne zan jagoranci shafin zuwa na wani lokaci. Da fata za ku kasance tare da mu.