Labaran abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni

Wannan shafi ne da zai kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 28 ga watan Yuni zuwa Juma'a 5 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Umar Mikail

  1. An naɗa Ahmed Musa sabon shugaban gudanarwar Kano Pillars

    Ahmed Musa

    Asalin hoton, Ahmed Musa/X

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa kaptin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa a matsayin sabon shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.

    Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce naɗin wani ɓangare ne ƙoƙarin ƙarfafa ƙungiyar gabanin fara sabuwar kakar Premier Najeriya.

    Dawakin Tofa ya ce an naɗa Ahmed Musa - wanda ɗan wasan ƙungiyar ne - bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni a faɗin jihar.

    A watan Octoban 2024 ne Kano Pillars ta sanar da ɗaukar kyaftin ɗin na Najeriya, Ahmed Musa domin buga mata wasanni Premier Najeriya.

  2. An zargi Thomas Partey da laifin aikata fyaɗe

    Thomas Partey

    Asalin hoton, Getty Images

    An zargi tsohon ɗan wasan Arsenal Thomas Partey da laifuka biyar na aikata fyaɗe da kuma cin zarafi na lalata.

    An ruwaito cewa an aikata laifukan tsakanin shekarar 2021 zuwa 2022, a cewar ƴansandan birnin Landan.

    Mata uku ne suka yi zargin cewa an musu fyaɗe.

    Kwantiragin ɗan shekara 32 ɗin da Arsenal ta kawo karshe ranar Litinin, bayan da ya koma ƙungiyar a 2020.

    BBC ta tuntuɓi ƙungiyar domin ji daga gare ta.

    Zarge-zargen sun zo ne bayan bincike da aka gudanar, wanda aka fara a watan Fabrairun 2022, bayan da ƴansanda suka samu rahoton zargin aikata fyaɗe.

    Ana sa ran Mista Partey wanda ke zaune a Hertfordshire, zai bayyana a gaban kotun majistre a Westminster ranar Talata, 5 ga watan Agusta.

    Ya koma Arsenal kan fam miliyan 45.3 daga Atletico Madrid a watan Oktoban 2020.

    Ya buga wasanni 35 a kakar wasanni da ta gabata, inda ya zura kwallo huɗu yayin da ƙungiyar ta kare a matsayi na biyu kan teburin Premier.

  3. Mutuwar Jota mummunan labari ne - Salah

    Salah and Jota

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Liverpool Mohammed Salah ya wallafa a shafin sada zumunta cewa, mutuwar Jota "mummunan labari ne".

    Salah ya bayyana haka lokacin da yake miƙa ta'aziyya kan rasuwar abokin wasan nasa

    "Na rasa abin da zan faɗa," kamar yadda ɗan wasan gaban na Masar ya wallafa a shafin X.

    "Har zuwa jiya, ban taɓa tsammanin akwai abin da zai firgita ni ba idan na zo komawa Liverpool bayan hutu.

    "Abokan wasa suna zuwa su tafi amma ba irin haka ba.

    "Mummunan labari ne da ba za a iya ɗauka ba cewa ba za mu ga Diogo ba idan muka koma daga hutu."

    Ya ƙara da cewa: "Ina miƙa ta'aziyya ga matarsa, yaransa da kuma mahaifansa waɗanda suka rasa ƴaƴansu. Waɗanda ke kusa da Diogo da kuma ɗan uwansa André na buƙatar dukkan kulawa da ta kamata a yanzu. Ba za su taɓa manta wannan lamari ba.

  4. Rashford zai koma atisaye da Man United ranar Litinin

    Marcus Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Aston Villa na da zaɓin sayen Marcus Rashford kan fam miliyan 40

    Ɗan wasan gaban Manchester United, Marcus Rashford zai koma atisaye da ƙungiyar ranar Litinin.

    Ɗan wasan ya shafe rabin kakar da aka kammala a matsayin aro a Aston Villa, bayan da ya samu saɓani da kocin Man United Ruben Amorim, wanda ya dakatar da shi.

    Har yannzu babu wata ƙungiya da ta nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan - duk da cewa a baya-bayan nan ya nuna sha'awar taka leda tare da Lamine Yamal a Barcelona.

    United za ta fara buga wasannin sada zumunta ranar 19 ga watan Yuli domin tunƙarar sabuwar kakar wasanni.

    Rashford ya zura wa Man Unted ƙwallo 138 a wasa 426 - yanzu dai za a jira a ga ko wata ƙungiya za ta biya fam miliyan 40 da ƙungiyar ke nema kan ɗan wasan.

  5. Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa kan rasuwar tsohon golan Super Eagles Peter Rufai

    Peter Rufai

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa kan rasuwar tsohon mai tsaron ragar Super Eagles, Peter Rufai.

    Ya rasu ranar Alhamis bayan shafe dogon lokaci yana jinya.

    Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya nuna alhininsa kan mutuwar zaƙaran kwallon kafar, wanda masoya kwallo za su fi tunawa da "Dodonmayana".

    Peter Rufai na cikin ƴan wasan Najeriya da suka lashe gasar cin kofin Afirka a shekarar 1994 - ya mutu yana da shekara 61.

    "Zan iya tuna irin ƙoƙarin da Rufai ya yi a lokacin da Najeriya ta lashe gasar kofin Afrika a 1994 a Tunisiya," in ji Tinubu.

    Shugaban ya ce tarihin ɗan wasan zai ci gaba da wanzuwa a cikin zuƙatan ƴan Najeriya da kuma masoya kwallon kafa a faɗin duniya.

  6. Nico Williams ya tsawaita zamansa a Bilbao zuwa 2035

    Bilbao

    Asalin hoton, Getty Images

    Nico Williams ya amince da tsawaita kwantiraginsa a Athletic Bilbao zuwa 2035.

    Ɗan wasan na Sifaniya, ya sanya hannu kan yarjejeniyar ƙarin shekara takwas a kwantiraginsa wanda ya kamata ya ƙare a 2027, kamar yadda Athletic Bilbao ta sanar.

    Sabon kwantiraginsa na nufin cewa farashinsa wanda ya kai aƙalla yuro miliyan 60, zai ninka da kashi 50.

    Nico Williams ya ce "Idan lokacin ɗaukar mataki ya zo, abin da ya fi muhimmanci shi ne ka bi ra'ayin zuciyarka, ina nan inda nake so, tare da mutane na, nan ne gida.

    Tun da farko dai Barcelona ta riƙa zawarcin ɗan wasan, har ma rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar tana daf da kammala cinikin ɗan wasan, kafin wannan sanarwar tsawaita zamansa.

  7. Nasarorin da Jota ya samu kafin rasuwarsa

    Diogo Jota

    Asalin hoton, EPA

    Diogo Jota ya kai ƙololuwa a sana'arsa ta ƙwallon ƙafa ne bayan taimaka wa Liverpool lashe kofin gasar Premier League a watan Mayu, da kuma ƙasarsa Portugal wajen ɗaukar kofin Uefa Nations League a watan Yuni.

    Ya fara taka leda a kulob ɗin Pacos de Ferreira na Portugal, kafin ya koma Atletico Madrid a 2016.

    Jota ya samu nasarar buga wasannin aro a FC Porto da Wolves, inda ya taimaka wa Wolevs ɗin samun gurbi a gasar Premier ta 2018, kafin ya zama ɗanwasanta na dindindin a ƙarshen kakar.

    Bayan shekara biyu a can ne kuma ya koma Liverpool kan kuɗi fan miliyan 41, kuma tun daga 2021 ya ci mata ƙwallo 65 cikin wasa 182 da ya buga a kaka biyar.

    Kofunan da ya ɗauka a Liverpool sun ƙunshi FA Cup biyu (a 2022), da EFL Cup biyu (a 2022 da 2024).

    A wasannin ƙasa da ƙasa kuma, Jota ya ci wa Portugal ƙwallo 14 a wasa 49 da ya taka mata leda.

  8. Magoya bayan Liverpool na ta alhinin mutuwar Jota

    Jota

    Asalin hoton, Reuters

    Magoya bayan Liverpool na ta taruwa a filin wasa na Anfield tare da ajiye fulawa domin nuna alhininsu kan rasuwar ɗanwasansu Diogo Jota sakamakon hatsarin mota.

    'Yan Liverpool na ƙaunar Jota sosai - wata waƙa da suke yi masa mai taken "to victory" na cikin mafiya shahara a kwanan nan.

    Yana yawan cin ƙwallaye, baya ga jajircewarsa, da shuru-shuru, halayen da suka sa ya ƙara zama a zukatan magoya baya.

    Mazauna garin na Liverpool kansu na cikin alhini.

    Jota

    Asalin hoton, Reuters

  9. Liverpool ta ƙi sallama tayin da Bayern Munich ta yi wa Diaz

    Diaz

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta ƙi sallama tayin da Bayern Munich ta yi wa Luis Diaz.

    An sanar da ƙungiyar dake buga Bundesliga cewar, Liverpool ba ta niyyar sayar da ɗan ƙwallon, kenan ba za ta shiga batun wata tattaunawar ba.

    Tun farko Barcelona ce ta fara taya Diaz, mai shekara 28, amma Liverpool ta sanar mata da cewar ba za ta sayar da shi ba.

    Liverpool ta ci gaba da nanata cewar ba za ta sayar da Diaz ba, koda nawa za a taya shi, domin kashin bayan ƙungiyar ne tun bayan da ya koma Anfield da taka leda daga Porto a 2022.

    Ɗan wasan tawagar Colombia ya ci ƙwallo 22 a kasarsa da Liverpool a kakar da aka kammala, sannan yana cikin kashin bayan ƙungiyar da Arne Slot ke jan ragama.

    Ya ci ƙwallo 13 da bayar da bakwai aka zura a raga a Premier League da Liverpool ta lashe kofin da tazarar maki 10.

    Diaz, wanda yake da sauran kwantiragin kaka biyu a Anfield, kungiyoyi da dama na son zawarcinsa ciki har da Manchester City da wasu dake buga babbar gasar tamaula ta Saudiyya.

  10. Ban da ƙwarewarsa, Jota mutumin kirki ne - Tawagar Portugal

    Tawagar ƙwallon ƙafa ta Portugal

    Asalin hoton, Reuters

    Tawagar ƙwallon ƙafa ta Portugal ta bayyana ɗanwasanta Diogo Jota a matsayin "mutumin kirki".

    Wata sanarwa da ta fitar ta ce Jota "wanda ya buga mata kusan wasa 50 ba ƙwararren ɗanwasa ba ne kawai, mutumin kirki ne" wanda kowa ke girmamawa a tawagar da ma abokan hamayya.

    Tawagar ta ce "mutum ne mai faran-faran" kuma "wanda ake misali da shi a unguwarsu"

  11. Mutuwar Jota ba ta yi ma'ana ba - Ronaldo

    Ronaldo da Jota

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jota da Ronaldo kenan yayin wasan gasar European Championship ta 2024 da Jamus ta karɓi baƙunci

    Tauraro kuma abokin wasan Diogo Jota a Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana alhinin mutuwar ɗanwasan mai shekara 28 sakamakon hatsarin mota.

    Kyaftin ɗin na Portugal mai shekara 40 ya wallafa alhininsa a shafukan sada zumunta yana cewa: "Wannan abu bai yi ma'ana ba. Babu daɗewa muke tare a tawagar Portugal, kwanan nan ka yi aure.

    "Na san za ka ci gaba da kasancewa tare da su a kodayaushe. Ku huta Diogo e Andre. Za mu yi kewarku."

    A watan da ya gabata ne Jota da Ronaldo suka jinjina kofin Uefa Nations League tare bayan doke Sifaniya a wasan ƙarshe, kuma shi ne kofi na biyu da Jota ya ɗauka tare da tawagar ƙasar tasa.

  12. Mutuwar Jota ta yi matuƙar kaɗa mu - Liverpool

    Diego Jota

    Asalin hoton, EPA

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta ce "ta kaɗu" sakamakon "rashi maras misaltuwa" na ɗanwasanta Diogo Jota, wanda ya rasu a hastarin mota yana da shekara 28.

    Ɗanwasan na ƙasar Portugal da ɗan'uwansa Andre Silva mai shekara 25, sun mutu ne bayan motar da suke ciki ta sauka daga kan titi saboda fashewar taya a yankin Zamora na ƙasar Sifaniya.

    A watan da ya gabata ne Jota ya auri matar da suka daɗe suna soyayya, har ma suka haifi 'ya'ya uku.

    Cikin wata sanarwa, Liverpool ta ce mutuwar Jota "ta kaɗa su sosai".

    "Kulob ɗin Liverpool ba zai sake yin magana ba a wannan lokaci kuma yana neman a mutunta iyalan Diogo da Andrey, da abokansu, abokan aikinsu, da ma'aikatan kulob ɗin yayin da suke tsaka da alhinin maras misaltuwa."

  13. Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Liverpool Diogo Jota ya rasu a hatsarin mota

    Diogo Jota

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan ƙwallon ƙafar Liverpool kuma ɗan ƙasar Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a birnin Zamora, ƙasar Spain, kamar yadda hukumar Guardia Civil ta tabbatar wa da BBC.

    A cewar rahoton, ɗan uwansa, Andre Felipe, shima ya rasu a hatsarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na dare (BST).

    Mota kirar Lamborghini da suke ciki ta fita daga hanya bayan tayar ta fashe yayin da suke ƙoƙarin wuce wata mota a gaba. Bayan haka motar ta kama da wuta, kuma an tabbatar da mutuwarsu a wajen hatsarin.

    Rasuwarsa ya girgiza duniyar wasanni, musamman masoya ƙwallon kafa da magoya bayan Liverpool, inda ake ci gaba da aika saƙon ta'aziyya ga iyalansa da ƙungiyarsa.

  14. Gosip

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United a shirye ta ke ta rage farashin da ta ƙaƙabawaTyrell Malacia bayan PSV Eindhoven ta yanke shawarar ƙin amincewa da yarjejeniyar zaman dindindin da ɗan wasan na Netherlands mai shekara 25 bayan zaman aro da ya yi a ƙungiyar a kakar da ta gabata. (Mirror)

    Sunderland na daga cikin ƙungiyoyin gasar Premier da dama da ke son ɗaukar ɗan wasan bayan Toulouse da Ingila ƴan ƙasa da shekara 21, Charlie Cresswell, mai shekara 22, wanda ke dafarashin fam miliyan 18 a kwantiraginsa. (Sun)

    Qatar ta tattauna da Fifa kan yiwuwar karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi na shekarar 2029, wanda zai zame dole a gudanar a cikin hunturu. (Guardian)

  15. Jarrad Branthwaite zai ci gaba da taka leda kaka biyar a Everton

    Everton

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Everton, Jarrad Branthwaite ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda kaka biyar a ƙungiyar Mersyside.

    Sau biyu Everton tana ƙin sallama tayin da Manchester United ta yi wa dan wasan a bara, wanda ya koma ƙungiyar daga Carlisle a Janairun 2020.

    Wasu ƙungiyoyin suna son zawarcinsa daga ciki har da Chelsea da kuma Tottenham.

    To sai dai Everton tana ganin Branthwaite daga cikin kashin bayan Everton, wadda ta bar filin wasa na Goodison Park a karshen kakar da aka kammala zuwa Hill Dickson.

    Yarjejeniyar Branthwaite, za ta karkare a Everton a 2027.

  16. William zai ci gaba da taka leda a Nottingham Forest

    Neco William

    Asalin hoton, Getty Images

    Neco Williams ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Nottingham Forest.

    Mai shekara 24, wanda ya koma Forest a 2022, bayan da kungiyar ta koma buga Premier League, ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen 2029.

    Dan wasan tawagar Wales ya buga karawa 39 a Forest, wadda za ta buga Europa Conference League da kai wa zagayen daf da karshe a FA Cup.

  17. Bayan da Al-Hilal ta yi waje da Manchester City a zagaye na biyu a Club World Cup da ake yi a Amurka, wadda ita ce ke rike da kofin.

    Shi ne karon farko da kungiyar Asia ta yi nasara a kan ta Turai a wasan da Fifa ke gudanarwa, inda kungiyoyin Turai suka ci wasa 18 daga 20 da suka fuskanci juna.

    Haka kuma an takawa Pep Guardiola birki a tarihin da ya kafa a Club World Cup a Barcelona da Bayern Munich da kuma City.

    Dan kasar Sifaniya ya ci wasa 11 a gasar da aka zura masa kwallo hudu.

  18. Rukunin gasar cin kofin Nahiyar Turai ta mata da za a fara ranar Laraba

    Rukunin farko: Switzerland, Norway, Iceland, Finland.

    Rukuni na biyu: Spain, Portugal, Belgium, Italy.

    Rukuni na uku: Germany, Poland, Denmark, Sweden.

    Rukuni na huɗu: France,England, Wales, Netherlands.

  19. Wasannin Euro 2025 da za a fara a Switzerland

    Women Euro

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a fara buɗe labulen gasar cin kofin nahiyar Turai a ƙwallon kafar mata ranar Laraba, inda za a kece raini tsakanin Iceland da Finland.

    Daga baya ne Switzerland za ta fara a St Jakob-Park - wadda za ta kece raini da Norway.

    Ranar Lahadi 27 ga watan Yuli za a karkarewa wasannin.

    Wannan shi ne karon farko da Switzerland za ta gudanar da babbar gasar tamaula ta mata a kasar.

    • Iceland da Finland
    • Switzerland da Norway
  20. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Sporting ɗan ƙasar Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, ya shaida wa kulob ɗin cewa ba zai koma taka leda a ƙungiyar ba domin yana son ya sauya sheƙa a wannan bazarar. (Record)

    Sunderland ta miƙa wa Reinildo Mandava kwantiragin shekara biyu kan albashin fam 65,000 kowanne mako bayan da Atletico Madrid ta sallami ɗan wasan bayan Mozambique mai shekara 31. (Guardian)

    Nottingham Forest na daf da kammala cinikin ɗan wasan gaban Botafogo ɗan ƙasar Brazil Igor Jesus mai shekara 24 kan farashin fam miliyan 10. (Telegraph)