Zambia ta naɗa tsohon ɗan wasanta, Moses Sichone sabon kociya
Zambia ta naɗa tsohon mai tsaron bayanta, Moses Sichone a matakin sabon kociya da zai ja ragamar kasar a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fara a cikin watan karshen shekarar nan
An sanar da hakan ranar Alhamis, bayan da Avram Grant ya ajiye aikim a lokacin da za a fara wasannin cin kofin Afirka da za a yi a Morocco daga 21 ga watan Disamba.
Sichone, mai shekara 48, ya buga gasar Bundesliga a FC Cologne da wakiltar Zambia karo uku a gasar kofin Afirka daga 1988 zuwa 2002.
Tun a baya Sichone ne mataimakin Grant, zai kuma yi aikin tare da tsoffin ƴan ƙwallon Zambia da ya haɗa da Andrew Sinkala da kuma Percy Mutapa.
Wasan farko da Sichone zai ja ragama, shi ne na sada zumunta da Afirka ta Kudu ranar 15 ga watan Nuwamba da kuma da Burundi kwana uku tsakani.
Zambia tana rukunin farko a gasar cin kofin Afirka da za a fara daga 21 ga watan Disamba, inda za ta fuskanci tsibirin Comoros da Mali da mai masaukin baƙi, Morocco.