Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 6 ga watan Fabrairun 2026.
Haruna Kakangi da Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Alamy
An kama wasu mutane biyu da ake tunanin ƴan leƙen asirin China ne da ake zargi da amfani da wani ƙauye da ke yankin kudu maso yammacin Faransa wajen tattara bayanai.
Mazauna ƙauyen Camblanes-et-Meynac, mai tazarar Kilomita 9 daga Bordeaux, sun yi fara zargin mutanen ne a lokacin da aka ga sun kafa wani dogon ƙarfen sadarwa a farfajiyar gidan hayar da suke zama a ciki.
Masana harkokin leƙen asiri sun yi imanin cewa China da sauran ƙasashe masu leƙen asiri na ƙara kai wa kudu maso yammacin Faransa hari saboda kusancin da yankin ke da shi na wuraren da ke da alaƙa da tsaro, da shirye-shiryen sararin samaniya da kuma hanyoyin sadarwa.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne jami’an hukumar tsaron cikin gida ta Faransa (DGSI) suka kai samame gidan tare da ƙwace kayan aikin kwamfuta masu tarin yawa.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Manyan jami'an gwamnatin Amurka da na Iran sun tattauna a ƙasar Oman sakamakon rikicin da ke tsakaninsu da ya haifar da fargabar arangamar soji tsakanin ƙasashen biyu.
Tattaunawar ta kai tsaye da aka yi a birnin Muscat ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara jibge sojojin Amurka a yankin Gabas ta tsakiya domin mayar da martani ga mumunar murƙushe masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a faɗin ƙasar a watan da ya gabata, wanda ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama suka ce ya kashe dubban mutane.
Da yake magana ta gidan talabijin ɗin ƙasar bayan kammala tattaunawar, ministan harkokin wajen Iran Araghchi ya ce masu tattaunawa za su koma manyan biranen ƙasashensu domin tuntuɓar gwamnatocinsu, sai dai ya bayyana taron a matsayin "mafari mai kyau".
Tun da farko, Oman ta ce ministan harkokin wajenta ya yi wata tattaunawa ta daban da Araghchi, da wakilin Amurka na musamman Steve Witkoff da surukin shugaba Trump Jared Kushner.
A watan Yunin da ya gabata ne aka shirya gudanar da zagaye na ƙarshe na tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar Iran amma wannan shirin ya ruguje bayan harin ba-zata da Isra'ila ta kai wa Iran.

Asalin hoton, ANI
Aƙalla ma’aikatan haƙar ma’adinai 18 ne suka mutu sannan ɗaya ya samu munanan raunuka bayan fashewar wani abu a wata mahaƙar ma’adanin kwal da ba bisa ka’ida ba a jihar Meghalaya da ke arewa maso gabashin Indiya.
Ƴan sanda yankin sun ce ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a wurin lamarin ya auku, kuma ana fargabar wasu mutane sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai.
Sun ƙara da cewa fashewar ta faru ne da safiyar ranar Alhamis a yankin tsaunin gabashin Jaintia na jihar.
Sufeton ƴan sandan jihar Vikash Kumar ya shaidawa manema labarai cewa hatsarin ya afku ne sakamakon haƙar ma'adinai ta hanya mai hatsarin gaske wadda ta shafi amfani da nakiya wurin fasa ramukan da ma’aikata ke shiga domin hakar kwal.
Firaminista Narendra Modi ya ba da sanarwar tallafin kuɗi na rupee 200,000 ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma rupee 50,000 ga waɗanda suka jikkata.

Asalin hoton, Russian Defence Ministry
An harbi wani babban janar ɗin rundunar sojan ƙasar Rasha a birnin Moscow.
An Kai Laftanar Janar Vladimir Alexeyev, mai shekaru 64, asibiti bayan harin da aka kai a wani katafaren rukunin gidaje dake yankin arewa maso yammacin babban birnin ƙasar, kuma ana tunanin yana cikin wani mawuyacin hali yayin da maharin na sa ya tsere.
Alexeyev dai shine na biyu a jerin manyan daraktocin hukumar leƙen asirin soja ta Rasha (GRU) kuma shi ne babban jami'in soja na baya bayan nan da aka yi yunƙurin kashewa a ciki ko kusa da Moscow tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a watan Fabrairun 2022.
Ya zuwa yanzu dai babu wata ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin, amma nan take manyan jami'an Rasha suka zargi Ukraine da cewa tana ƙoƙarin kawo cikas ga batun tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin.

Asalin hoton, Atiku Abubakar/Facebook
Mai ɗakin tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari ta ziyarci jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar.
Cikin wani saƙo da Atikun ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce Aisha Buhari ta tare da ƴarta Hanan Buhari da wasu ƴan'uwanta sun ziyarce shi a masaukinsa da ke Saudiyya.
''Kamar dai ni, mai ɗakin tsohon shugaban ƙasar, da iyalanta na ƙasar Saudiyya domin gudanar da ibadar Umara'', kamar yadda saƙon Atikun ya bayyana.
Tun bayan mutuwar mijinta a watan Yulin 2025, Aisha Buhari ta fara takaba a garin Daura da ke jihar Katsina, kafin daga baya ta koma Kaduna, inda ta kammala a can.

Gwamnatin Birtaniya ta ce ƙasashen Angola da Namibia da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo sun amince su karɓi ƴan ƙasashensu da suka aikata laifuka a Birtaniya, ko suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, bayan ta yi barazanar sanya musu takunkumin biza.
Tun a shekarar da ta gabata Ma'aikatar cikin gida ta yi gargaɗin cewa za ta daina bayar da biza ga ƴan ƙasashen da ƙasar su ta ƙi amincewa da ƙarbar mutanen.
Ta kuma ce mutum fiye da dubu uku ne lamarin zai shafa.
Sauran ƙasashe kamar India da Pakistan da Najeriya sun ƙi amincewa da karɓar mutanensu, kuma akwai yiwuwar su fuskanci takunkumin bizar.

A yau ne Canada da Faransa za su buɗe ofisoshin jakadancinsu a Greenland, domin nuna goyon bayan su ga ƴancin tsibirin, kuma a matsayin martani ga buƙatar shugaba Trump na ƙwace ikon tsibirin.
Ƙwararru sun ce matakin ƙasashen biyu zai taimaka wa Greenland gwada rayuwar samun yancin kai, ciki har ma daga ita kanta Denmark ɗin.
A watan da ya gabata ne dai Mista Trump ya sassauta barazanarsa na ƙwace tsibirin da ke yankin arctic, bayan ya ce sun cimma matsaya da ƙungiyar tsaro ta NATO kan cewa Amurka za ta ƙarfafa tasirinta a tsibirin.

Asalin hoton, Centre for memories
Wata kotu a Najeriya ta umurci gwamnatin Birtaniya da ta biya diyar fam miliyan 20 ga iyalai 21 na masu haƙar kwal 21 da gwamnatin mulkin mallaka ta kashe a 1949 a kudu maso gabashin ƙasar.
Ƴan sandan mulkin mallaka da suka haɗa da ƴan Najeriya da Turawa sun harbe ma’aikatan da ke yajin aiki don neman a inganta musu yanayin aiki.
An kuma jikkata wasu da dama a wani abin da kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin munanan ayyukan danniya a ƙarƙashin mulkin Birtaniya a Najeriya.
Masana tarihi sun ce kisan ya taimaka wajen ba da goyon baya ga fafutukar masu neman ƴancin kai da aka cimma nasara shekaru 11 bayan haka, a shekarar 1960.
BBC ta nemi ma’aikatar harkokin wajen Biritaniya ta yi tsokanci kan lamarin amma ba ta ce uffan ba.
Iyalain waɗanda abin ya shafa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adan sun kwashe shekaru da dama suna yaƙin ganin an amince da aikata laifin an kuma biya diyyar da ta dace.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai daga Amurka da Iran na gudanar da wata tattaunawa a Oman, a yayin da Washington ke neman daƙile shirin nukiliyar Tehran.
Ana tattaunawar ne ta hanyar shiga tsakanin jam'ian diflomasiyyar Oman.
Ministan harkokin wajen Oman ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan shirya ƙaidojin da za a sanya na ci gaba da yarjejeniya.
Iran ta ce har yanzu a shirye ta ke ta tattunwa shirinta na Nukiliya, amma ta dage cewa ba za ta yarda a tattauna kan makamanta masu linzami ba.
Amurka ta girke sojoji a gaɓar Iran, kuma ta yi barazanar kai hari idan Tehran ba ta haƙura da wasu manya manyan abubuwa ba.

Asalin hoton, @kabiruturakisan
Jam'iyyar PDP ta yi gargaɗin cewa ɓangaren Tanimu Turaki zai ɗauki duk wasu matakai na shari’a domin ƙalubalantar abin da suka kira da yankan baya.
A farkon wannan mako ne hukumar zaɓen ƙasar INEC ta amince da kwamitin riƙon ƙwarya da Nyesome Wike ke goyon baya cewa shi zai samar da shugaban jam’iyya na riƙo da sakataren jam’iyya da sakataren tsare-tsare dukansu daga ɓangaren Nyesome Wike a matsayin waɗanda ta amince su halarci taron tattaunawar jam’iyyar na rubu’in shekara da zai gudana a Abuja.
Cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar a ranar Alhamis ta ce ta yi watsi da matakin.
Jam'iyyar PDP ƙarƙashin shugabancin Kabiru Tanimu Turaki dai ta yi watsi da matakin na hukumar zaɓen Najeriyar, inda ta ce kundin tsarin jam’iyyar PDPn ma bai yi wannan tanadi ba, kuma ba shi da hurumi a doka.
Mataimakiyar sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Farida Umar ta shaida wa BBC cewa a yanzu haka sun riga sun ɗaukaka ƙara kuma suna jiran ranar da kotu za ta kira su domin jin bahasi
Mataikiyar ta kuma yi zargin cewa wasu ne ke amfani da kotu wajen ruruta rikici a cikin gidan jam'iyyar, inda ta jaddada cewa suna nan a matsayin shugabannin jam'iyyar PDP da doka ta sani
BBC ta tuntuɓi hukumar zaɓen Najeriyar INEC domin jin ta bakinsu, inda mai magana da yawun hukumar Zainab Aminu, ta ce hukumar ta yi amfani ne da umurnin da kotu ta bayar wajen ɗaukar matakin.
Kafin nan dai a ranar 30 ga watan Janairun da ya gabata, wata babbar kotun tarayya a Badun, babban birnin jihar Oyo, ta rusa shugabancin jam'iyyar PDP ƙarƙashin Kabiru Tanimu Turaki da ta ce ya saba doka.
Haka kuma Alkalin kotun, mai shari'a Uche Agomoh, ya soke babban taron da jam'iyyar za ta gudanar nan gaba.
Har ila yau, kotun ta amince da ɓangaren shugabancin riƙon ƙwarya na Mohammed Abdulrahman a matsayin shugaban jam'iyyar, wanda aka ruwaito yana samun goyon bayan ministan babban birnin tarayya Najeriya, Nyesom Wike har zuwa lokacin da aka gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa.
Hukumar tattara bayanan sirrin tsaron Ukraine ta ce an gano gawarwakin ’yan Kenya biyu da ke wa Rasha faɗa bayan ta ɗauka suaiki domin yaƙin da take yi da Ukraine .
An gano gawarwakin a kusa da birnin Lyman da ke yankin Donetsk, sai dai ba ta bayyana sunayen mamatan ba.
Wannan lamari ya biyo bayan mutuwar wani ɗan Kenya, Clinton Nyapara Mogesa mai shekaru 29, wanda aka kashe mako guda da ya gabata.
An gano gawarsa ne a yankin Donetsk bayan wani hari da bai yi nasara ba.
Game da Mogesa, jami’an Ukraine sun ce an samu gawarsa dauke da fasfo na wasu ’yan Kenya biyu, waɗanda suke zargin su ma Rasha ta ɗauke su aiki ne kuma ana shirin tura su fagen daga nan gaba.
Gwamnatin Kenya ba ta tabbatar da mutuwar ’yan ƙasar nata da aka kashe a Ukraine ba har yanzu.
A watan Nuwamban da ya gabata, ministan harkokin wajen Kenya ya ce kimanin ’yan Kenya 200 ne aka sani suna yaƙi a gefen Rasha inda kwanan nan aka ceto ’yan Kenya 18 da ke yaƙi a Rasha tare da dawo da su gida.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin kare haƙƙin bil-adama da masu fafutuka a ƙasar Gambiya sun bayyana damuwarsu kan cewa wata babbar kotun ƙolin kasar mai yiwuwa ta soke dokar hana kaciyar mata a ƙasar.
Sun bayyana cewa idan aka soke haramcin yiwa mata Kaciya hakan zai iya haifar da matsaloli da kuma mace-mace mata musamman jarirai.
Kashi 76 na mata da 'yan mata a ƙasar wadda ke da yawan musulmai ana yi musu kaciya saboda al'adu da addini.
A duk duniya, sama da mata da 'yan mata miliyan 230 ne aka yi wa wannan aikin kuma suna buƙatar sabis na kulawa a yayin da duniya ke bikin ranar rashin juriya ga kaciyar mata ta duniya.

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Aƙalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar wani abu da ta auku a wani masallacin ‘yan Shi’a yayin sallar Juma’a a birnin Islamabad, babban birnin Pakistan, a cewar jami’an ƙasar.
Fashewar ta faru ne a yankin Tarlai na birnin, lamarin da ya sa aka ayyana bukatar taimakon gaggawa a asibitoci uku, inda wani jami’in gwamnati ya ce fiye da mutane 160 ne suka jikkata.
Har yanzu ba a bayyana ainihin abin da ya haddasa fashewar ba, sai dai rahotanni na nuna cewa dan ƙunar bakƙn wake ne ya tayar da bam ɗin.
Shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, ya yi kakkausar suka kan harin, yana mai cewa, “kai hari kan fararen hulan da ba su ji ba su gani ba laifi ne ga hakkin bil’adama baki ɗaya.”
Ya kuma jaddada cewa dukkan al’ummar Pakistan suna tare da iyalan waɗanda abin ya shafa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Asalin hoton, Getty Images
Wani hari da ake zargin dakarun RSF ne suka kai da jirgin sama marar matuƙi a jihar Kudu Kordofan ya kashe ƙaalla mutum 22, ciki har da ma’aikatan lafiya guda huɗu kamar yadda gidan jaridar Sudan Tribune ya ruwaito.
Harin na cikin ƙaruwar farmakin sama da RSF ke kai wa kan biranen da ke hannun sojoji a jihar, inda wanna farmakin da aka kai a kan Asibitin Al-Kuweik da sojoji ke gudanarwa ne aka kai.
Rahoton ya kuma bayyana cewa waɗanda suka mutu sun haɗa da daraktan asibitin da wasu ma’aikatan lafiya guda uku.
Jihar ta Kordofan ta Kudi wadda take kan iyaka da Kudancin Sudan, tana ci gaba da fuskantar tashin hankali, bayan da sojoji da ƙungiyoyin haɗin gwiwa suka karya ƙawanyan shekaru biyu da aka yi wa biranen Kadugli da Dilling a jihar.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗanadam na Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Türk, ya yi kira ga hukumomin soji na Burkina Faso da su soke shawarar rushe dukkan jam’iyyun siyasa, inda ya ce matakin na kaucewa batun kare haƙƙin ɗan adam.
“Madadin haramta jam’iyyun siyasa da kuma tsare mutane saboda bayyana ra’ayinsu, ya kamata hukumomin Burkina Faso su bude fili ga ƙungiyoyin farar hula, ciki har da masu aikin jin kai,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa: “Wannan ba shi ne mataki mai kyau wajen kare haƙƙin ɗanadam a Burkina Faso ba.”
A yayin da ake nuna damuwa kan take haƙƙin 'yan adawa da masu rajin kare farar hula, da ‘yan jarida, shugaban ya jaddada buƙatar girmama ’yancin haɗin kai da fadin ra’ayi.
Hukumomin Burkina Faso sun rushe dukkan jam’iyyun siyasa a ranar 29 ga Janairu, suna mai cewa yawaitar jam’iyyun na haifar da rabuwar kai da raunana hadin kan ƙasa.
Haka kuma, sun soke dokokin da ke kula da ayyukansu da kudaden su.
Amma wasu masana sun ce haramta jam’iyyun siyasa na nufin ƙoƙarin rundunar sojin na raunana yan adawa da kuma ci gaba da rike iko.
Matakin na zuwa ne bayan dakatar da jam’iyyun siyasa tun daga shekarar 2022, bayan sojoji sun ƙwace iko cikin juyin mulki.
Ƙungiyar ta yi kira ga al’ummar duniya, musamman Kungiyar Tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da su dauki mataki

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a ƙasar Mali sun kama daraktan jaridar weekly L'Alternance wadda ta shahara wajen wallafa rahotannin da ke sukar ƙasashen ƙungiyar haɗaka ta AES.
An kama Youssouf Sissoko ne bayan wallafa wani labari da hukumomi suka ce yana sukar shugaban mulkin soja na Nijar, Janar Abdourahamane Tiani. kamar yadda shafin labarai mai zaman kansa, Mali Actu
Masu gabatar da ƙara sun tuhume shi da laifuka da suka haɗa da “yaɗa labaran ƙarya”, “lalata martabar ƙasa” da kuma “zagin wani shugaban ƙasa na waje”.
Rahoton, wanda aka fara wallafa shi a shafin intanet ya zargi Tiani da gazawa ko kuma yin ƙarya da gangan.
Ƙungiyoyin kare ’yancin ’yan jarida sun yi Allah-wadai da kama ɗan jaridar, amma sun bayyana taka-tsantsan a martaninsu.
Tun bayan karɓar mulki, shugabannin sojoji a yankin Sahel sun kama ’yan siyasa masu adawa da masu kare haƙƙin ɗan Adam da ’yan jarida da ake ganin suna sukar gwamnatocinsu, a abin da masu sharhi ke kallon yunƙurin murƙushe duk wani mai adawa da gwamnati.

Asalin hoton, Getty Images
Ofishin jakadanci Amurka a Najeriya ya fitar da wata sanarwa a yau Juma'a inda ya yi Alla-wadai da "mummunan harin da aka kai a jihar Kwara" da ke arewacin Najeriya, inda aka kashe mutanen da har yanzu ba a kammala tantance yawansu ba.
Sanarwar da ofishin ya fitar a shafukan sada zumunta ta ce "muna miƙa alhininmu ga iyalan waɗanda wannan kisa na rashin hankali ya shafa, kuma muna maraba da matakin shugaba Tinubu na tura dakaru domin tsare ƙauyukan da ke yankin".
A ranar Talatar makon nan ne wasu mahara da ake zargin masu tsattsauran ra'ayin addini ne suka kai hari kan ƙauyukan Woro da kuma Nuku a ƙaramar hukumar Kaiama da ke jihar Kwara, inda suka kashe mutanen da ake hasashen sun zarta 100.
Ɗan majalisar jihar Kwara mai wakiltar yankin, Sa'idu Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa an yi jana'izar mutum 78 a yammacin ranar Laraba.

Shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya ɗora alhakin harin kan ƙungiyar Boko Haram wadda ta shafe sama da shekara 15 tana kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
A baya-bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista a Najeriya kisan gilla, lamarin da gwamnatin ƙasar ta musanta.
Gwamnan jihar Kwara ya ce a harin na ranar Talata an kashe "Musulmai 75" yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ƙididdige yawan mutanen da aka kashe.
Haka nan gwamnan ya ce an kashe mutanen ne saboda sun ƙi bin wani baƙon koyarwar Musulunci da maharan suka so su ƙaƙaba musu.

Majalisar ƙoli kan harkokin shari'ar musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake nanata kiranta da a tsige shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar (INEC), Joash Amupitan, domin a cewarta, ba zai iya yin adalci a babban zaɓen ƙasar mai zuwa ba.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, wadda sakatare-janar ɗinta, Nafi’u Baba Ahmad ya sanya wa hannu, inda ta ce kiran bai da alaƙa da addininsa ko ƙabilanci.
Ta ce wannan takardar da ta fitar, ƙarin bayani ne kan wadda ta fitar a baya a ranar 28 ga watan Janairu, wadda a cewar majalisar aka canja wa fassara. "Wannan ne ya sa muka saka zama domin fitar da sabuwar takarda domin fayyace matsayarmu."
"Babu ruwanmu da batun addini, magana ake yi ta nagarta da inganci. Najeriya ta gudanar da zaɓuka da dama tun daga samun ƴancin kai a 1960 zuwa yanzu, kuma ba a taɓa samun lokacin da aka yi amfani da addini wajen amincewa ko ƙin amincewa da sakamakon zaɓe ba."
Majalisar ta ce daga shugaban hukumar zaɓen Najeriya na 1960, Eyo Esua zuwa yanzu, hukumar ta yi shugabanni guda 13, "amma a ciki Farfesa Attahiru Jega da Farfesa Mahmood Yakubu ne kawai musulmai, kuma duk da haka ba a taɓa samun lokacin da musulman Najeriya suka ƙi amincewa da zaɓe saboda bambancin addini ba."
Sanarwar ta ƙara da cewa buƙatar cire shugaban na yanzu, Farfesa Amupitan ba magana ake yi ta addininsa, "magana ake yi ta abubuwan da ya aikata a baya, musamman takardar da ya jagoranci rubutawa a 2020, wadda a ciki ya yi amfani da kalamai masu zafi da cin zarafi da cin mutunci musulman Najeriya da yankin arewa da Usman Ɗanfodio."
Majalisar ta ce a cikin takardar koken ya yi zargin ana yi wa kiristocin Najeriya "kisan kiyashi", "sannan ya yi yunƙurin alaƙanta matsalar tsaro da ake fuskanta a arewacin Najeriya da jihadin Ɗanfodio na ƙarni na 19, wanda ba daidai ba ne, kuma yunƙuri na tayar da zaune tsaye. Sannan abin ban haushi suka miƙa wannan ƙanzon kuregen zuwa ƙasashen waje domin nuna Najeriya a matsayin ƙasar da kiristoci ba su da ƴancin addini."
Majalisar ta ƙara da cewa tun bayan fitar da takardar da ake magana, har yanzu shugaban na INEC bai fito ya nesanta kansa ba, sannan ta ƙara da cewa shugabantar hukuma irin ta zaɓe na buƙatar mutum wanda ba ya nuna bambancin addini da ƙabilanci.

Asalin hoton, Bola Tinubu da Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai iya sake ƙaddamar da hare-hare a Najeriya matuƙar bai gamsu da ƙoƙarin ƙasar ba wajen daƙile hare-hare a kan kiristoci.
Trump ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokaci da yake jawabi a ranar addu'a ta ƙasar Amurka karo na 74, wadda aka yi a birnin Washington.
"Duk wanda ya kai wa kiristoci hari, ya san dole Trump zai mayar da martani mai zafi. Na san maganar babu daɗi, amma ita ce magaar gaskiya," in ji shi.
A lokacin taron addu'ar, Trump ya bayyana zuwan uwargidan Shugaban Najeriya, Remi Tinubu a addu'ar, inda ya yaba mata, sannan ya ce mata ce mai mutunci da ƙima.
Trump na bayani ne kan zargin da ake yi cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, lamarin da Amurka ta sa baki, har ta ƙaddamar da hare-hare a ƙasar a bara.
Sai dai Najeriya ta sha nanata cewa kashe-kashen da ake yi a ƙasar ba su da alaƙa da bambancin addini ko ƙabilanci, sannan ta ƙara da cewa tana ƙoƙarinta na magance matsalar.
Trump ya ce hare-haren da ya kai a Najeriya, ya yi ne tare da haɗin gwiwar hukumomin Najeriya, inda ya ce ya amince a kai harin ne domin fatattakar mayaƙan IS.