Isra'ila ta gindaya tsauraran sharuɗɗa kan Falasɗinawa masu son yin ibada a Al-Aqsa

Asalin hoton, Getty Images
Isra'ila ta sake gindaya tsauraran sharudɗa kan Falasɗinawa daga gaɓar Yamma da kogin Jordan da ta mamaye, waɗanda za su halarci sallar Juma'a a massalacin Qudus a wannan wata na Ramadana.
Falasɗinawa 10,000 ne kawai za a bari su shiga massallacin, kuma wajibi ne su samu takardar izini.
Hakazalika maza da suka wuce shekara hamsin da biyar, da mata da suka wuce shekara hamsin, da kuma yara yan ƙasa da shekara 13 ne za a bari su shiga.
Kafin harin da Hamas ta kai na watan Oktoban 2023, dubban ɗaruruwan Falasdinawa ne ke zuwa sallar Juma'a a massalacin na al-Aqsa a watan Ramadan.

















