Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 24/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 24/11/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jafar

  1. Kotu ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa tsohon shugaban FBI

    Wani alƙali ya yi watsi da tuhumar da ake yi wa tsohon shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, James Comey da tsohuwar mai shigar da ƙara a birnin New York, Letitia James.

    Alƙalin ya yanke hukuncin cewa naɗin da aka yi wa lauyar ma'aikatar shari'a, Lindsey Halligan a matsayin babbar lauyar Amurka na wucin gadi ya saɓawa doka kuma ya saɓa wa ƙa'idar naɗi a kundin tsarin mulkin Amurka.

    An tuhumi Comey ne da laifin yin kalaman ƙarya da kuma kawo cikas a harkar lshari'a a cikin watan Satumba, bayan da shugaba Donald Trump ya yi kira da a gurfanar da shi gaban kuliya tare da naɗa sabon mai shigar da ƙara na gwamnatin tarayya da zai binciki lamarin.

    Bayan matsanancin matsin lamba daga shugaban Amurka Donald Trump, ma'aikatar shari'a ta tuhumi Comey a watan Satumba.

    Dukkan tuhume-tuhumen biyu sun shafi kalaman Comey ne ya yi wa kwamitin shari’a na Majalisar dattawa a shekarar 2020 lokacin da aka tambaye shi game da yadda ya tafiyar da binciken da ma'aikatar shari'a ta yi kan saƙƙwannin imel na Hillary Clinton da kuma wani bincike kan katsalandan da Rasha ta yi a zaben Trump.

    Ya dai musanta aikata laifin.

    Comey ya kasance daraktan hukumar FBI na kusan shekara huɗu, daga 2013 zuwa 2017.

    An kore shi kimanin watanni huɗu a wa'adin farko na Donald Trump a matsayin shugaban Amurka.

  2. Tsauni ya yi aman wuta a Habasha

    Wani tsauni a yankin arewa maso gabashin Habasha ya yi aman wuta a karo na farko cikin fiye shekara dubu goma sha biyu.Tsaunin na Hayli Gubbi, ya fitar da talgen wutar inda hayaƙi ya turnuke sararin samaniya da nisan tafiyar kilomita goma sha huɗu.Aman wutar ya haddasa fitar toka mai tsanani da ta mamaye yankunan.

    Cibiyar da ke lura tsaunuka masu aman wuta ta ƙasar ya ce toka da tarkacen da aman wutar ya haifar ta mamaye wasu sassan sararin samaniyar ƙasashen Yemen da Indiya da Oman da kuma arewacin Pakistan.

    Kawo yanzu dai abu wani rahoto game da adadin mutanen da suka jikkata sakamakon aman wutar.

  3. Gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya sun gana kan matsalar tsaro

    Gwamnonin jihohin kudu-maso-yammacin Najeriya sun yi wani taron sirri a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

    Taron ya samu halartar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin.

    Sauran sun haɗa da Lucky Aiyedatiwa (Ondo), Ademola Adeleke (Osun), Dapo Abiodun (Ogun), Biodun Oyebanji (Ekiti), da gwamnan mai masaukin baƙi, Seyi Makinde (Oyo).

    Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa an gudanar da taron ne sakatariyar Jihar Oyo da ke Agodi, Ibadan, inda ofishin Makinde yake.

    Majiyoyi sun ce gwamnonin za su yi shawarwari kan barazanar tsaro, da hanzarta samar da ababen more rayuwa, da kuma ƙarfafa haɗin kan yankin a ƙarƙashin shirin raya yammacin Najeriya (DAWN).

    Ana kuma sa ran za su sake duba ayyukan samar da tsaro na haɗin gwiwa da ke gudana, ciki har da ayyukan rundunar Amotekun, da nufin bunƙasa ƙarfinta a domin fuskantar ƙalubalen da ke kunno kai.

  4. Zelensky yayi kashedi game da ƙwace yankunan Ukraine domin samun zaman lafiya

    An kammala tattaunawar da aka yi a birnin Geneva tsakanin Amurka da Ukraine da nufin kawo ƙarshen yakin da ake yi da Rasha, inda jami'an ɓangarorin biyu suka bayar da rahoton "ci gaba" da kuma aniyar ci gaba da tattaunawa.

    Duk da haka, babu cikakken bayani kan yadda za a ɗinke ɗarakar da ke tsakanin Moscow da Kyiv kan batutuwan yankuna da kuma tabbatar da tsaro ga Ukraine.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi marhabin da "muhimman matakai" da ake neman ɗauka amma ya yi gargadin cewa "babban matsalar" da ke fuskantar tattaunawar zaman lafiya ita ce buƙatar Vladimir Putin na duniya ta amince da yankunan da Rasha ta mamaye a gabashin Ukraine.

    Tattaunawar ta Geneva ba ta samu halarcin wakilan Rasha ba kuma fadar Kremlin ta ce ba ta sami wani bayani kan sakamakon tattaunawar ba.

    Kakakin gwamnatin Rasha Dmitri Peskov ya lura cewa Moscow na sane da cewa an yi kwaskwarima kan shirin da Putin ya yi maraba da shi.

    A makon da ya gabata ne aka gabatar da wani shiri na zaman lafiya mai dauke da sharuɗɗa 28 da jami'an Amurka da na Rasha suka tsara kan Ukraine.

    Da yawa daga cikin abubuwan da ke cikin shirin sun yi kamar sun fi dacewa da bukatun Moscow, abin da ya haifar da firgaba a Kyiv da kawayenta na Turai.

  5. 'Najeiya da Amurka za su ƙarfafa ƙawancen tsaro'

    Fadar shugaban Najeriya ta ce hukumomin Amurka sun ce za su ƙarfafa ƙawanec tsaro da Najeriya, domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ya ce shirin ya haɗa da samar da ingantattun fasahohin leƙen asiri, da kayayyakin tsaro, da kuma sauran bayanai da za su ƙarfafa ayyukan da ake yi na yaƙi da ƴan ta'adda da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a ƙasar.

    Matakin na zuwa ne bayan ganawar da aka yi a makon jiya tsakanin wata tawagar manyan jami'an Najeriya da jami'an Amurka.

    Ƙasashen biyu sun amince da ƙarfafa dangantakar tsaro da kuma lalubo sabbin hanyoyin haɗin gwiwa.

    Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce tawagar Najeriyar, ƙarƙashin jagorancin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ta gana da manyan jami'an majalisar dokokin Amurka, da ofishin kula da harkokin addini na fadar White House, da ma'aikatar harkokin wajen Amurka, da majalisar tsaro ta kasa, da kuma ma'aikatar tsaro.

    Tawagar Najeriyar ta ƙaryata zargin kisan kiyashi da ake yi a Najeriya, inda ta jaddada cewa munanan hare-hare na shafar iyalai da al'ummomi daban-daban.

    Tawagar ta kuma yi watsi da irin kalaman da ake amfani da su wajen siffanta lamarin, inda ta ce irin wannan abu zai iya raba kan ƴan Najeriya ba, tare da gurɓata haƙiƙanin abin da ke faruwa a ƙasa.

    A cewar Mallam Nuhu Ribadu, ƙasashen biyu sun amince da aiwatar da wani tsarin haɗin gwiwa cikin gaggawa, da kuma kafa ƙungiyar haɗin gwiwa don tabbatar da tsarin bai ɗaya na haɗin gwiwa a ɓangarorin da aka cimma matsaya a kai.

  6. Mutum 5 sun mutu sakamakon harin ƙunar baƙin wake a Pakistan

    Wasu ƴan ƙunar baƙin wake biyu sun kai hari a hedkwatar rundunar sojin Pakistan a ranar Litinin, inda suka kashe jami’an tsaro uku tare da jikkata aƙalla mutane 12.

    Ƴan sanda sun shaida wa BBC cewa maharan na ɗauke da muggan makamai yayin da suka dumfari hedkwatar Constabulary da ke Peshawar a yankin arewa maso yammacin Pakistan.

    Ya zuwa yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

    Ginin ofishin yana cikin wani yanki mai tsaro sosai a Peshawar, kuma maharan sun keta matakan tsaro da dama kafin kai wa ga wurin.

    An killace wurin da lamarin ya auku, kuma wani jami'i ya ce jami'an tsaro biyar da fararen hula bakwai ne sun jikkata.

    Hukumomin Pakistan sun bayyana harin a matsayin wani shirin ‘yan ta’adda da aka rusa, tare da yin la’akari da cewa an bindige maharan ne a kofar gidan, kafin su samu shiga ginin.

    Kungiyar Taliban ta Pakistan, wadd aka fi sani da Tehreek-i-Taliban Pakistan (TTP), tana aiki a lardin kuma a baya ta ɗauki alhakin kai hare-hare makamantan haka a faɗin ƙasar.

  7. TikTok ya amince ya sayar da hannun jarinsa ga kamfanonin Amurka - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ƙarin haske kan yarjejeniyar da ya ce an samu da mamallakan kamfain TikTok, waɗanda asali ƴan ƙasar China ne.

    Ya ce masu kamfanin fasahar sadarwa ta zamanin sun amince za su sayar da kaso mafi yawa na kamfanin ga kamfanonin Amurka.

    Sanata Ed Markey na jam'iyyar Democrats ne ya rubuta takarda zuwa ga shugaban, inda ya buƙaci ya ƙara nazari tare da bayar da gamsassun amsa kan buƙatun ƴan ƙasar na fargabar illa ga tsaron ƙasar da ake hasashen samu daga dandalin matuƙar aka tabbatar da yarjejeniyar da aka shiga a watan Satumba.

    Trump ya ce kamfanin ByteDance zai sayar da kaso mafi girma na hannun jarinsa ga kamfanonin Amurka da wasu kamfanonin duniya, amma dai ba a samu cikakken bayani kan yarjejeniyar ba.

  8. Manyan jami'an BBC na shan tambayoyi a majalisar Birtaniya

    Wani kwamitin zaɓaɓɓun ƴan majalisar dokokin Birtaniya za ya soma binciken wasu daga cikin mutanen da ke da hannu cikin badaƙalar gyara jawabin Shugaba Trump da BBC ta yi a cikin wani gajeren shiri na musamman.

    Shugaban hukumar gudanarwa na BBC, Samir Shah, da tsohon mai bai wa BBC shawara, Micheal Prescott, waɗanda fitar sakonninsu ya yi sanadiyyar ajiye aikin babban daraktan BBC da shugaban sashen labarai, na daga cikin waɗanda za a yi wa tambayoyi domin bayar da shaida.

    Shugaba Trump ya yi barazanar maka BBC a kotu kan gyara jawabinsa na gabanin zanga zangar da aka yi a majalisar dokokin Amurka a 2021.

    BBC ta nemi afuwa, amma ta ƙin amincewa da batun biyan diyya.

  9. Ƴanbindiga sun kashe fararen hula 40 a Ethiopia

    Aƙalla fararen hula 40 da suka haɗa da yara da wata mata mai juna biyu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kashe a yammacin ƙasar Habasha, kamar yadda shaidu da hukumomin yankin suka shaida wa BBC.

    An kai harin ne a ƙarshen makon da ya gabata a ƙauyen Bekuji da ke yankin Benishangul-Gumuz na ƙasar, inda aka gina madatsar ruwa mafi girma a Afirka a kan kogin Nilu.

    Waɗanda suka tsira da rayukansu da kuma iyalan waɗanda abin ya shafa sun bayyana cewa an kai musu hari yayin da suke cikin barci.

    Sun zargi ƙungiyar ƴan tawaye - Oromo Liberation Army (OLA) da kai hare-haren.

    Ƙungiyar dai ba ta mayar da martani kan wannan zargi ba amma a baya ta musanta kai hare-hare kan fararen hula.

    An yi jana'izar waɗanda suka mutu bayan da aka tura sojojin tarayya domin shawo kan lamarin.

    Yankin dai ya sha fama da hare-haren masu nasaba da ƙabilanci da kuma faɗa a tsakanin ƙabilu a cikin ƴan shekarun da suka gabata.

  10. Nijar ta aika tankar fetur 82 zuwa Mali

    Jamhuriyar Nijar ta aika da tankunan man fetur 82 zuwa Mali, kuma tuni suka isa kasar duk da ikirarin kungiyar JNIM na hana tankokin mai shiga babban birnin kasar.

    Tankokin sun isa birnin Bamako daga Yamai a matsayin tallafi da nufin sassauta wahalhalun da 'yan Mali ke fama da su sakamakon matsalar karancin man fetur na watanni.

    Sojojin Nijar wasu a mota wasu kan babura ne suka raka ayarin waɗannan motoci daga Yamai zuwa Bamako mai tazarar kilomita 1400.

    Ƙasar Mali dai na fama ne da matsalar ƙarancin man fetur a sanadiyar ƙawanyar da mayaƙa ƴan ƙungiyar JNIM suka yi mata, lamarin da ya yi sanadiyar hana shigar da fetur ƙasar.

  11. Ɗalibai da malaman St. Mary 265 ne suka rage a hannun ƴanbindiga - CAN

    Cocin Katolika a Najeriya ya ce mutum ɗari biyu da sittin da biyar ne ke hannun ƴan bindiga har yanzu, bayan da suka yi garkuwa da gomman mutane daga wata makaranta a jihar Neja a ranar Juma'ar da ta gabata.

    A cikin wata sanarwar da ta fitar, Cocin ɗarikar Katolika ta Kontagora, ta fitar da cikkaken jadawalin yara da manya da aka sace daga makarantar St Mary da ke garin Papiri.

    Waɗanda ake neman sun haɗa da malamai 5 da sauran ma'aikatan makarantar su 7.

    Sanarwar ta kuma ce an sace yara ƴan ajin sakandire 14, da yara 39 ƴan ajin nazire sai kuma yara 62 ƴan ajujuwan firamare.

    Akwai kuma wasu ɗaliban makaranta da shekarunsu ya ɗara na sauran, waɗanda aka haɗa jimilla, ɗaliban da aka sace sun kai 253.

  12. Dole Rasha ta shiga tattaunawar tsagaita yaƙin Ukraine - Shugaban Jamus

    Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce wajibi ne Rasha ta hau teburin tattaunawa a yanzu, bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Ukraine kan kawo ƙarshen yaƙin.

    Mista Merz ya ce ya yi maraba da abin da ya kira 'sakamako na wucin gadi', bayan Washington da Kyiv sun jinjina ci gaba da aka samu a tattaunawar da aka yi a ranar Lahadi.

    Sai dai ya ce baya sa ran za a samu wani ci gaba na azo a gani a wannan makon, kuma wajibi ne Rasha ta ɗauki wani mataki.

    Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov ya ce a hukumance Rasha ba ta karɓi wani bayani a kan sakamakon tattaunawar Geneva ba.

    Da BBC ta tambaye shi ko yana sa ran jami’an Rasha da na Amurka za su gana a wannan mako, Dmitry Peskov ya amsa cewa “tukunna dai” ko da yake mahukuntan birnin Moskow, in ji shi, “ƙofofinsu a buɗe suke da irin wannan tuntuɓa da tattaunawa.”

    Tun da farko dai Ukraine da ƙawayenta na Turai sun ce shirin da aka gabatar ya fi bai wa Rasha fifiko.

  13. 'Ƙin ɗaukar matakai kan sauyin yanayi na iya zama take haƙƙin bil'adama'

    Shugaban hukumar kare haƙƙin bil 'adama ta majalisar ɗinkin duniya ya bayyana takaicin sa kan abin da ya kira 'sakamakon da ba na a zo a gani ba' a taron sauyin yanayi da aka kammala a baya bayan nan a Brazil.

    Volker Turk ya ce nan gaba ƙin ɗaukar matakan da suka dace daga shugabanni zai iya kasancewa laifin take haƙƙin bil'adama.

    Sanarwar da aka fitar a ƙarshen taron COP30 bai gabatar da wani sabon mataki ba game da yadda za a daina amfani da makamashi mai gurɓata muhalli.

    Ƙasashe fiye da tamanin sun so a cimma yarjejeniyar da za ta faɗaɗa alƙawuran da aka ɗauka a baya na soma daina amfani da man fetir da kwal da kuma iskar gas da ke dumama duniya.

  14. Atiku ya yi rijista da jam'iyyar haɗaka ta ADC

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya karɓi katin kasancewa ɗan jamʼiyyar ADC a mazaɓarsa ta Jada da ke jihar Adamawa.

    Hakan ya kawo ƙarshen tsawon lokacin da ya ɗauka bai bayyana sauyin sheƙar ba, bayan da ya bar PDP.

    Ya sanar da hakan ne a shafinsa na X, inda ya wallafa hotunan sa riƙe da katin sabuwar jami'yyarsa, da gajeren rubutu da ke nuna ya shiga jam'iyyar a hukumance.

    A ranar 14 ga watan Yulin 2025 ne cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce ya fita daga PDP ba tare da ɓata lokaci ba.

    Atikun ya kuma ce wajibi ne ya raba gari da jam'iyyar a yanzu bisa la'akari da yadda ta sauka daga harsashinta na asali.

  15. Al-Qaeda ta yi iƙirarin ɗaukar alhakin hari a Najeriya a karo na farko

    Ƙungiyar Al-Qaeda ta yankin Sahel, wadda ke mubaya ga ƙungiyar Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) ta fitar da sanarwar da a ciki ta yi iƙirarin samun nasarar "kai hari kan shingen jami'an tsaron Najeriya'' a wani yanki da alamu suna nuna a yankin jihar Kwara ne da ke maƙwabtaka da bakin iyakar Benin.

    Wannan ne karon farko da JNIM ta yi iƙirarin ɗaukar nauyin kai hari a Najeriya.

    JNIM ta fitar da sanarwar ce a kafarta ta al-Zallaqa a ranar 22 ga watan Nuwamba, duk da cewa ƙungiyar ba ta fitar da cikakken bayani kan harin ba, sannan ba ta bayyana haƙiƙanin inda ta kai harin ba, sannan ba ta bayyana adadin waɗanda harin ya rutsa da su ba.

    Sai dai ta ce harin ya auku ne a wani ƙauye da ta kira da Larabci da "Duruma" a jihar da ta kira da "Tinkandu" wanda ke nufin garin bakin iyaka na Chikanda.

    Sai dai rahotanni na cewa Duruma wani ƙauye ne da ke bakin iyakar Najeriya da Benin a ƙaramar hukumar Baruten da ke jihar Kwara.

  16. Ba a canja taswirar tsakanin ƙasashe da yaƙi - Zelensky

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce babbar matsalarsu a yanzu a game da a daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasarsa da Rasha da aka tsara, ita ce batun ƙwace wasu yankunan ƙasar da Rasha za ta yi.

    Zelensky ya bayyana haka ne a jawabinsa a gaban majalisar ƙasar Sweden game da yaƙin da ya yi ajalin mutane da dama.

    Ya ce, "babbar matsalar da yunƙurin samar da maslahar ke fuskanta ita ce buƙatar da Shugaban Rasha Vladimir Putin ya miƙa cewa a amince da yankunan da "ƙwace" su koma Rasha a hukumance.

    "Idan muka amince, hakan zai saɓa da dokokin ƴancin ƙasa da darajarta," in ji shi, sannan ya nanata cewa, "ba a raba ƙasa ko canja taswirar tsakanin ƙasashe da yaƙi."

    A ƙarshe ya ce Rasha na ci gaba da luguden wuta da kashe-kashen mutanen ƙasarsa, inda ya yi kira da "a matsa mata lamba domin ta tsagaita wuta."

  17. Muna shakku kan iƙirarin CAN game da ɗaliban Neja da suka kubuta - Ƴansanda

    Rundunar ƴansandan jihar Neja ta dasa alamar tambaya kan batun Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN, wadda ta ce ɗalibai guda 50 sun tsere daga hannun ƴanbindiga.

    Tun da farko, ƙungiyar ta ce daga cikin ɗaliban makarantar St. Mary da ke Neja da ƴanbindiga suka yi garkuwa da su, guda 50 sun tsere, har ma sun koma gida.

    Ko a saƙon da ya wallafa ranar Lahadi a shafukansa na sada zumunta, Shugaban Ƙasar Bola Tinubu ya nanata ikirarin na CAN game da kuɓutar ɗaliban 50

    Sai dai ƴansandan sun ce sun buƙaci ƙungiyar ta ba su hujjar cewa ɗaliban sun koma, amma ba su samu, don haka rundunar ta ce, "ba mu da tabbacin alƙaluman yaran da suka tsere da ma inda sauran suke a yanzu."

    BBC ta yi ƙoƙarin neman bahasin waɗanda suka tsere daga ƙungiyar, amma haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.

  18. Jarumin finafinan Bollywood Dharam ya rasu

    Fitaccen jarumin finafinan masana'antar Bollywood ta Indiya, Dharmendra wanda ake kira da Dharam ya rasu a birnin Mumbai na Indiya yana da shekara 89 a duniya.

    Firaministan India Narendra Modi ya bayyana jajensa ga iyalan mamacin da ƴan ƙasar baki ɗaya, sannan ya bayyana rasuwar jarumin da "ƙarshen zangon jaruman sinima a Indiya."

    Dharmendra, wanda ya kasance yana bayyana da "mutum mai sauƙin kai" ya daɗe yana jan zarensa a harkar fim, inda yake nishaɗantar da miliyoyin masoyansa a duniya.

    Ya yi fice da sunan Veeru saboda rawar da ya taka a fim ɗin Sholay a shekarar 1975, sannan ya fito a finafinai sama da 300 a gomman shekaru da ya yi a masana'antar.

    An haife shi ne a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 1935 a ƙauyen Nasrali da ke lardin Punjab Ludhiana. Malaminsa a makaranta ne ya saka masa suna Dharam Singh Deol.

    A tattaunawarsa da BBC a 2018, ya ce mahaifinsa karatu ya so ya yi, amma shi tun da farko fim yake sha'awa, wanda hakan ya sa ya fi mayar da hankali kan harkar ta nishaɗi.

  19. Dole Ukraine ta ci gaba da kasancewa ƙasa ƴantacciya - Amurka

    Amurka da Ukraine sun bayar da bayanai akan tattaunawar da suke yi a Geneva domin kawo karshen yakin da ake da Rasha.

    Fadar gwamnatin Amurka ta ce dole ne yarjejeniyar ta kunshi cewa dole ne Ukraine ta ci gaba da kasancewa kasa mai cikakken 'yanci.

    Sakataren harkokin wajen Amurka Marci Rubio, ya ce an samu ci gaba sosai a tattaunar dan abin da ya rage bai taka kara ya karye ba.

    Wani babban jami'in Ukraine da ke cikin wadanda ake tattaunawar da su Rustem Umerov, ya ce abin da aka cimma yanzu yawanci ya shafi manyan bukatun Ukraine.

    Wakilin BBC ya ce fadar gwamnatin Amurka ta ce wakilan Ukraine sun yi amanna cewa daftarin yarjejeniyar shirin zaman lafiyar da aka sabunta ya tabo muradun kasarsu sannan kuma zai bawa kasarsu damar kare 'yancinta.

  20. Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar ƴansanda 30,000

    Shugaban Najeriya ya bayar da umarnin a dauki yannanda 30,000 bayan sace-sacen mutanen da aka yi a kwanakin baya bayannan.

    Ofishin Shugaban kasar Bola Tinubu, ya kuma sanar da cewa duk jami'an tsaron da ke kare manya masu fada aji a kasar a mayar da su sauran fagen daga domin su ji su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar kasar.

    Wannan yunkurin ya zo ne bayan da yara 50 daga cikin fiye da 300 da aka sace a makarantar sakandire st Mary da ke jihar Neja suka kubuta daga hannun wadanda suka sace su.

    Wakiliyar BBC ta ce an umarci makarantu a wasu sassan jihohin Najeriya da su rufe makarantun bayan sace sacen daliban da a ka yi a baya bayannan, sannan kuma bayan shafe mako guda a hannun masu satar mutane an sako mutum 38 da aka sace a wani coci a jiya Lahadi.