Bankwana
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, a nan muka kawo ƙarshen rahotannin na yau Asabar.
Ku tara gobe Lahadi idan Allah Ya kaimu domin samun wasu sabbin rahotannin.
Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/07/2024
Daga Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, a nan muka kawo ƙarshen rahotannin na yau Asabar.
Ku tara gobe Lahadi idan Allah Ya kaimu domin samun wasu sabbin rahotannin.

Asalin hoton, Reuters
Harin Rasha a kan cibiyar samar da lantarki ya jefa mutane 100,000 cikin duhu a garin Sumy da ke arewa maso yammacin Ukraine.
Hukumomi sun ce ana aiki domin dawo da lantarkin a cibiyar Ukrenergo, a birnin mai iyaka da Rasha.
Babu rahoton mutuwa ko rusa wani waje na daban da cibiyar samar da lantarkin, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito.
Rasha na ci gaba da kai hari a kan cibiyoyin makamashi a Ukraine, lamarin da ya jefa mutane da dama cikin ƙarancin ruwan sha da kuma tsananin zafi.
A cikin wata uku kacal, Ukraine ta tafka asarar wutar lantarkin da take samarwa, kuma kamfanin Ukrenergo mai samar da wutar ya ce harin Rasha na jirage marasa matuƙi ne suka haifar da wannan ɓarna.

Asalin hoton, Reuters
Wasu shugabannin duniya sun taya Masoud Pezeshkian murnar lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran.
Shugaban China, Xi Jinping da na Rasha, Vladimir Putin sun ce suna fatan ƙulla alaƙa mai kyau da tsohon likitan zuciyar.
Shi kaɗai ne mai ra'ayin kawo sauyi da aka bai wa damar tsayawa takara a zaben na ranar Juma'a, kuma ya doke abokin karawar sa mai ra'ayin riƙau.
Bayan nasarar ta sa, Mr Pezeshkian ya ce akwai namijin aiki a gaban sa, na ceto Iran.
Ya yi alkawarin ƙulla sabuwar yarjejeniyar makamin nukiliya da ƙasashen Yamma da cire takunkumin Amurka da kuma kawar da ƙungiyar Hisba.
Amma jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei ne mai ƙarfin ikon yanke hukunci a kan duk wata doka ko zartar da wani tsari a ƙasar.

Asalin hoton, ANADOLOU VIA GETTY IMAGES
Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce Isra'ila ta kashe mutum aƙalla 16, ta kuma raunata wasu da dama a harin da ta kai wata makaranta da ke kusa da kasuwa.
Rundunar sojin Isra'ila ba ta tabbatar da harin ba, amma ta ce tana gudanar da bincike a kai.
Shaidu sun faɗa wa BBC cewa an kai harin ne a saman ginin makarantar Al-Nuseirat, a tsakiyar Gaza, wajen da dubban Falasɗinawa ke gudun hijira.
Wani shaidar ya ce an kai harin ne a wani ɗaki da ƴan sandan Hamas ke amfani da shi.

Asalin hoton, Federal Ministry of Information and Culture
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta maka jaridar Daily Trust a kotu, tare da shigar da korafi game da ita, a gaban ƙungiyar masu gidajen jarida ta Najeriya saboda abin da ta kira ''yaɗa kalaman neman tayar da rikici da karya aikin jarida''
Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin tana sane da yadda a cikin ƴan watannin baya, jaridar Daily Trust ke yada labaran da ke neman gogawa gwamnatin kashin kaji.
Da ya ke magana a wajen wani taron manema labarai a yau Asabar, ministan yada labaran ya kafa hujja da labaran da jaridar Daily Trust ta wallafa a game juyin mulkin Nijar, da wanda ya ce jaridar ta rubuta a kan shirin sauya sunan titin Murtala Muhammad da ke Abuja zuwa Wole Soyinka da kuma na baya bayan nan a game da sanya hannu a kan yarjejeniyar da ta shafi amincewa da auren jinsi.
Ya yi bayanin cewa a dukkan labaran, gwamnatin ta gano yadda jaridar ta bayar da rahoto ba tare da gabatar da hujja ko shaidun zargin da ta yi ba, lamarin da kuma gwamnatin ke kallo a matsayin wani yunƙuri na wallafa ƙarya domin tunzura jama’a.
Ya ce: ‘’Ba mu taɓa tunanin Daily Trust da mutanen da ke da ita za su kai wannan mataki ba wajen neman tayar da rikici a ƙasar nan, ta hanyar zargin cewa gwamnati ta sanya hannu a kan yarjejeniyar tallata auren jinsi. Wannan tsabar zalumci ne saboda babu wannan tanadi a cikin yarjejeniyar.’’
Ministan ya koka da yadda wannan labarin ya janyo huɗuba mai zafi daga wasu malaman addini da kuma jefa jama’a cikin halin ɗar-ɗar, wanda kuma ya ce jaridar ce ta janyo.
Saboda haka, ministan ya ce ‘’Gwamnatin tarayya za ta bi duk hanyoyin da doka ta amince da su, domin neman haƙƙi a kotu.’’

Asalin hoton, SHUTTERSTOCK
Firaiministan Slovakia ya bayyana a bainar jama'a, a karon farko bayan an yi yunƙurin kashe shi da bindiga.
An harbi Robert Fico da bindiga a ranar 15 ga watan Mayu, lokacin da ya ke gaisawa da mutane cibiyar bunƙasa al'adu ta Handlova, miai nisan kilomita 180 daga babban birnin ƙasar, Bratislava.
Daga nan ne aka garzaya da shi asibiti inda aka yi masa aiki, aka kuma ci gaba da duba lafiyar sa.
A ranar Juma'a, Mr Fico ya bayyana a wani wajen biki a Bratislava, inda ya yiwa jama'a jawabi.
Mr Fico, mai shekara 59, ya yi amfanin da jawabin nasa wajen sukar tsattsauran ra'ayi da kuma matsayar ƙasashen Yamma a kan yaƙin Rasha da Ukraine.
A cikin wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, Mr Fico ya ce ya yafe wa mutumin da ya kai masa harin, kuma baya riƙe dashi a zuciya.

Asalin hoton, BURKINA FASO PRESIDENCY
Shugabannin gwamnatin mulkin soji a Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun ce ba zasu koma ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin yammacin Afirka, Ecowas ba.
Shugabannin uku sun gana a karon farko, domin ƙulla wata haɗaka da za ta fuskanci ƙalubalen da suke fuskanta daga ƙasashe maƙwabtan su.
A tsakanin 2020 zuwa 2023 sojoji suka ƙwace mulki a Mali da Burkina Faso da kuma Nijar, a wata guguwar juyin mulki da yankin ya yi fama da ita.
Dukkan ƙasashen uku da ke ƙarƙashin ƙawancen na Alliance of Sahel States suna fama da rikicin ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi, wanda kuma yana daga cikin dalilan da sojojin suka ce sun tilasta masu ƙwace mulki.
Da yake jawabi a wajen taron ƙasashen uku a Nijar, shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya ce ƙasashen sun yanke shawarar kafa wata haɗaka da za ta kula da muradun jama'arsu, ba tare da shisshigin ƙasashen waje ba.
''Za mu samar da gamayya ta zaman lafiya da taimakon juna da kuma kawo ci gaba a bisa mutumta al'adunmu na Afirka.'' Inji Jana Tchiani.
A cikin watan Janairu ƙasashen suka sanar da shirin su na ficewa daga Ecowas, wadda itama za ta gudanar da taron ta a ranar Lahadi.
Janar Tchiani ya yi jawabin ne a gaban takwaransa na Burkina Faso’s, Kaftin Ibrahim Traoré da kuma na Mali, Kanal Assimi Goïta.

Asalin hoton, Getty Images
Ba'afirke na farko da ya taɓa zama ɗan majalisar dokokin Jamus, Karamba Diaby, ya ce ba zai tsaya takara a zaɓe mai zuwa ba.
Ɗan majalisar, ya ce ya ɗauki matakin ne domin samun ƙarin lokacin iyalinsa da samar da ayyukan yi ga matasa.
Mista Diaby, na jam'iyyar SPD, ya shiga majalisar dokokin ƙasar a shekarar 2013 tare da Charles M Huber na jam'iyyar Christian Democrats.
Zaɓen 'yan majalisar biyu waɗanda 'yan asalin Afirka ne ya kasance irinsa na farko a tarihin siyasar Jamus.
Haifaffen Senegal, Diaby ya koma gabashin Jamus a shekarar 1985 inda yake digiri na uku a fannin chemistry.
To sai ɗan majalisar ya fuskancin tsangwamar wariyar launin fata a tsawon wa'adin mulkinsa, ciki har da harbin bindiga a ofishin mazaɓarsa tare da yi wa ma'aikatansa barazana, amma hakan bai hana shi jajircewa a kan aikinsa ba, kodayake ana ganin hakan na daga cikin dalilan da suka sanya shi ɗaukar matakin sauka daga muƙamin.
"A shekarun da suka gabata na fuskanci barazanar kisa. amma yanzu hakan zai zo ƙarshe,'' in ji shi.
Yayin da yake rubuta wasiƙa ga takwarorinsa, Mista Diaby ya alƙawarta ci gaba da bai wa jam'iyyar SDP gudunmowa, musamman cikin wata 15 da suka rage a yi babban zaɓe'', yana mai cewa ''mun fuskanci manyan ƙalubale''.
Zaftarewar ƙasa da aka samu sakamakon mamakon ruwan sama ta kashe mutum biyu a arewa maso gabashin Indiya.
Kawo yanzu mutum 52 ne suka mutu a yankin Assam cikin makonnin baya-bayan nan, sakamakon bala'o'in da ruwan sama ke haddasawa.
Jami'ai sun ce fiye da mutum miliyan biyu ne lamarin ya shafa, inda ambaliya ta yi awon gaba da gidaje da gadoji, tare da lalata abubuwan more rayuwa.
An samu katsewar wutar lantarki a wasu sassan Assam.
Jami'an gandun daji sun ce dabbobin dawa da dama sun mutu a gandun dajin Kaziranga sakamakon ƙaruwar ruwan sama.

Asalin hoton, Hon. Abdulmalik Zubairu
An ɗaura auren wasu ‘yan mata marayu fiye da 100 a garin Bungudu na jihar Zamfara.

Asalin hoton, Hon. Abdulmalik Zubairu
Dukkanin ‘yan matan dai waɗanda suka rasa iyayensu ne sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa kan ƙauyuka a jihar.
Dan majalisar wakilan yankin, Hon. Abdulmalik Zubairu Bungudu - wanda ya ɗauki nauyin ɗawainiyar auren - ya shaida wa BBC cewa tuna ya tanadi kayan ɗaki da jari da aka raba wa amaren a lokacin bikin.

Asalin hoton, Hon. Abdulmalik Zubairu

Asalin hoton, Hon. Abdulmalik Zubairu
An dai raba wa amaren kayan ɗaki da suka ƙushi gado da katifa da kujeru da sauran kayayyakin ɗaki
''A lokacin bikin kowace amariya za mu ba ta jarin naira 100,000 yayin da kowane ango kuma zai samu naira 50,000 a matsayin tallafi.

Asalin hoton, Hon. Abdulmalik Zubairu
Hon. Bungudu ya ce an bi matakai kafin zaɓo marayun, inda aka ware wa kowacce mazaɓa marayu biyar da za su amfana da tsarin.

Asalin hoton, PA Media
Sabon Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya alƙawarta sanya muradun ƙasar a gaba saɓanin na jam'iyyarsa.
Yayin da yake jhawabi a taron manema labarai a fadar gwamnati, jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa na farko a gwamnatinsa, mista Starmer ya ce gwamnatin jam'iyyarsa ta Labour ta zo da sauye-sauye da za ta yi wa al'ummar Birtaniya.
Ya ce zai yi aiki tare da 'yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban domin ciyar da ƙasar gaba ta fannoni daban-daban, ciki har da inganta tattalin arzikin ƙasar.
Mista Starmer ya ce shi ba ɗan siyasa ne mai nuna ƙabilanci ba, don haka ne ya ce zai jaddada wa ministocinsa su yi aiki tuƙuru don bauta wa al'ummar Birtaniya.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurta Joe Biden ya shaida wa magoya bayansa a jihar ta Wisconsin cewa zai ci gaba da takara babu gudu ba ja da baya, kuma zai doke Donald Trump a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan Nuwamba.
Hakan na zuwa ne bayan kiraye-kirayen da wasu jiga-jigan jam'iyyar Dimokrat ke yi masa cewa ya haƙura da takara, sakamakon rashin tabuka abin kirki a muhawararsa da abokin karawarsa, Donald Trump.
Mutum na baya-bayan nan da ya yi kira shi ne ɗan majalisar wakilai Mike Kali.
To sai dai cikin wani martani da ya mayar a shafinsa na X, Shugaba Biden ya jaddada cewa shi ne cikakken ɗan takarar jam'iyyar.
''Ina son fayyace muku cewa, ni ne shugaban Amurka, kuma ni ne ɗan takarar jam'iyyar Dimokrat, kuma zan ci gaba da takara''.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Shugaba Biden ya sake ɗora alhakin rashin kataɓus da ya yi a muhawa - da Mista Trump - kan rashin lafiya.
A wata hira ta farko tun bayan muhawarar, Mista Biden ya ce sa'ar da aka yi muhawarar yana fama da matsanancin zazzaɓi, ga shi ya yi tafiye-tafiye, don haka jinkinsa ya yi la'asar.
Shirin na wannan makon ci gaba ne kan kan rashin haihuwa tsakanin ma'aurata da aka tattauana cikin shirin makon da ya gabata.
A wannan shirin likitoci sun bayyana hanyoyin da za a bi domin samun mafita idan ma'aurata na fuskantar matasalar.

Asalin hoton, Reuters
Hukumomin lardin Sindh na Pakistan sun haramta wa malaman addinin Musulunci fiye da 140 yin wa'azi har na tsawo wata biyu.
Hukumomin sun ce sun ɗauki matakin ne don kauce wa ɓarkewar rikici, sakamakon sukar juna da malaman ke yi musamman cikin watan Muharram wanda shi ne wata na farko a shekarar musulunci.
Pakistan ƙasa ce da mabiya mazhabar sunna suka fi yawa, kuma ƙasar ta sha fuskantar rikici tsakanin ɓangarorin addini a cikin watan Muharram, inda ake yawan sukar mabiya mazhabar Shi'a marasa rinjaye a ƙasar.
Wani jami'in gwamnatin ƙasar ya ce dokar ta haramta wa malaman tafiye-tafiye da yin wa'azi har na tsawon wata biyu don hana sukar mazhabobin juna.
Haka kuma gwamnatin lardin ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu shafukan sada zumunta a kawanaki 10 na farkon watan.
Shirin Ra'ayi Riga na wannan mako ya tattauna da likitoci da sauran masu ruwa da tsaki kan hanyoyin kamuwa da cutar amai da gudawa, tare da dabarun kaucewa ko na yaƙi da cutar.
A baya-bayan nan dai Najeriya na fuskantar ɓarkewar cutar ta kwalara a wasu sassan ƙasar, inda har ta yi sanadin kashe wasu mutane.
Likitoci dai na alaƙanta cutar da rashin tsaftar abinci da na ruwan sha

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewar 'yan Najeriya miliyan 82 - kimanin kashi 64 na 'yan ƙasar - ka iya fuskantar matsalar yunwa nan da shekarar 2030.
Haka kuma MDD ta yi kira da gwamnatin ƙasar ta magance matsalar sauyin yanayi da matsalar ƙwari da sauran abubuwan da yi wa harkar noma barazana.
Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya alƙaluma daga binciken shekara-shekara Abinci sun nuna cewa nan da shekaru masu zuwa lamurra za su ta'azzara a ƙasar.
“Gwamnatin Najeriya tare da haɗin gwiwa masu ruwa da tsaki, sun gudanar da bincike na shekara-shekara da suka saba gudanarwa kan abinci. Sakamakon binciken ya tayar da hankali, kimanin mutum miliyan 82 ne za su fuskanci yunwa nan da 2030,” kamar yadda Jaridun ƙasar suka ambato jami'in Majalisar, Taofiq Braimoh na bayyanawa a wurin wani taron kan haɓaka ayyukan noma a Abuja.
Ya ci gaba da cewa matsalar rashin abinci da ƙasar ke fama da shi, baya rasa nasaba da matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da ita, da matsalar ƙwari da wasu abubuwa da ke yi wa harkar noma barazana a ƙasar.
Hasashen na Majalisar Dinkin Duniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsadar abinci, lamarin da ya tilasta wa gidaje da dama haƙura da sayen abincin da suka saba ci.
A cikin rahotonta baya-bayan nan, hukumar ƙididdigar ƙasar ta ce farashin abinci a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 40.66 a watan Mayu, matakin da aka jima ba a ga irinsa ba.

Asalin hoton, PA Media
Sabon firaministan Birtaniya Sir Keir Starmer, zai gabatar da taron majalisar zartaswarta na farko bayan kafa gwamnati.
Jim kaɗan bayan karɓar takardar kama aiki daga hannun Sarki Charles ranar Juma'a, sabon firaministan ya sanar da naɗin ministocin nasa.
Sir Keir ya naɗa mata 11 daga cikin ministocinsa 25, ciki har da Angela Rayner mataimakiyarsa da kuma Rachel Reeves, da ta zama ministar kuɗi.
Babban abin da gwamnatinsa za ta sanya a gaba shi ne inganta tattalin arziki da rage tsadar ayyukan lafiya.
A ɗaya gefen kuma jam'iyyar Conservatives da ta sha kaye a zaɓen, na duba yiwuwar sauya Rishin Sunak a matsayin shugabanta.
Tsohon firaministan ya ce zai sauka daga muƙaminsa idan an kammala tsare-tsaren samun wanda zai gaje shi.