Mu kwana lafiya
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Juma'a, kafin mu zo da wasu rahotonnin sababbi gobe da safe.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/12/2025.
Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Juma'a, kafin mu zo da wasu rahotonnin sababbi gobe da safe.
Mu kwana lafiya.
Hukumomi a Indiya sun ce sun kama ɗaya daga cikin mutanen da aka fi nema a duniya kan safarar sassan jikin damisa.
An kama Yang-chen La-chun-gpa bayan shafe watanni ana bibiyarta a jihar Sikkim da ke kan iyakar Indiya da China.
Ana zargin ta da taka muhimmiyar rawa wajen ƙirƙirar hanyoyin yin safarar sassan jikin damisa da wasu dabbobi daga Indiya zuwa ƙasashen Nepal da Tibet da kuma China.
Ms Yangchen na cikin jerin mutanen da 'yansandan ƙasa da ƙasa ke nema, kuma kama ta muhimmiyar nasara ce a yaƙin da ake yi da kashe dabbobi domin yin safarar gaɓoɓinsu.

Asalin hoton, BUA Group
Wasu 'yanbindiga sun yi garkuwa da 'yan ƙasar China biyu da ke aiki kan wani titi a jihar Kwara.
Mutanen na cikin ma'aikatan da ke aiki da kamfanin BUA a kan titin Saadu–Kaiama–Kosubosu lokacin da maharan suka isa wurin suna harbi kan mai tsautsayi.
Kwamashinan 'yansandan jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya shaida wa jaridar TheCable a yau Juma'a cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata a ƙaramar hukumar Moro.
A kwanan nan 'yanbindiga masu garkuwa da mutane sun matsa wa jihar Kwara da ke tsakiyar Najeriya. Maharan sun kai hare-hare a coci-coci, inda suka yi garkuwa da masu ibada.

Asalin hoton, Social Media
Ministan Abuja babban birnin Najeriya ya ce 'yanmajalisar dokokin jihar Rivers 16 da suka fita jam'iyarus ta PDP zuwa APC mai mulki na da 'yancin su yi hakan.
'Yanmajalisar ƙarƙashin jagorancin shugabansu Martins Amaewhule sun fice daga PDP, wadda Nyesom Wike ke ci gaba da iƙirarin yana cikinta, bayan sanar da hakan yayin zaman majalisar na yau Juma'a.
Mista Amaewhule da yake yi wa Wike biyayya a rigimar neman iko da siyasar jihar, ya ce rarrabuwar kai ce ta sa ya koma APC mai mulkin Najeriya.
Wike ya bayyana matakin nasu a matsayin "abin takaici", amma ya ce rikicin da jam'iyyar ke ciki ya taimaka wajen fitar 'yanmajalisar.
"Abin takaici ne. Jam'iyyar a rarrabe take, kuma tsarin mulki ya ce idan jam'iyya ta shiga ruɗani suna da damar fita daga cikinta," in ji shi. Sai dai rahotonni na cewa 16 ko 17 cikin 27 ne suka koma APC ɗin.
Wike ya haɗa kai da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu duk da cewa yana jam'iyyar adawa ta PDP.

Asalin hoton, Reuters
Ruɗni tsakanin matafiya a Indiya ya girmama bayan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama mafi girma a ƙasar IndiGo ya soke tashin ɗaruruwan jirage a yau Juma'a.
Kamfanin da ke da kashi 60 cikin 100 na kasuwar Indiya gaba ɗaya kuma yake da jiragen fasinja fiye da 2,000 duk rana, ya sha fama da ƙarancin matuƙa jirgi saboda gaza fara amfani da sabon tsarin aiki na gwamnati.
Dubban fasinjoji ne suke ƙasa jibge a Indiya a daidai lokacin da ake yawan tafiye-tafiye na ƙarshen shekara, kuma a yanzu an soke dukkan jirage daga Delhi babban birnin ƙasar.
IndiGo ya ce za a koma bakin aiki nan da 10 ga watan Fabrairu, amma ya nemi a sassauta sababbin dokokin da suka bai wa direbobi lokutan hutu da kuma rage ayyukan dare.

Asalin hoton, PA Media
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta bai wa Shugaban Amurka Donald Trump kyautar zaman lafiya ta Fifa Peace Prize.
Da yake miƙa masa kyautar yayin bikin raba jadawalin gasar Kofin Duniya ta 2026 a birnin Washington, Shugaban Fifa Giani Infantino ya ce an bai wa Trump kyautar ne saboda ƙoƙarinsa na kawo zaman lafiya a duniya.
Infantino ya sanar da kirkiro sabuwar lambar yabon ce a watan da ya gabata, jim kaɗan bayan da Mista Trump ɗin ya rasa lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya.
Bikin raba jadawalin na gudana yanzu haka, inda ake sa ran za a rarraba ƙasashe 48 zuwa rukunnai 12 a gasar da ƙasashen Amurka da Canada da Mexico za su karɓi baƙunci.
Sauran shugabannin ƙasashen da za su shirya gasar na halartar bikin da ke wakana a Amurkar.

Asalin hoton, Nigeria Police
Rundunar 'yansanda ta Najeriya reshen jihar Gombe ta ce ta yi nasarar lalata sansanin 'yanbindiga da kama bakwai daga cikinsu da makamansu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito rundunar na cewa ta gudanar da samamen ne tare da hadin gwiwar ƙungiyar mafarauta.
Nasarar ta fara ne da kama wani mai suna Abdullahi Ibrahim a ƙauyen Tilde ranar 23 ga watan Nuwamba, inda ya bayyana sunayen abokan hulɗarsa da ke garkuwa da mutane a Gombe da Bauchi da Adamawa.
Dakarun 'yansanda da na mafarauta sun kai ga kama mutum shida bayan wata fafatawa da 'yanbindigar, inda suka ƙwace makamai.
Ta ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amince cewa sun samu kuɗaɗe da satar mutane da suka kai kusan naira miliyan 150.

Asalin hoton, Social Media
Kotun Ƙolin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da jihar Osun ta shigar da gwamantin tarayya game da riƙe kuɗaɗen wasu ƙananan hukumomi na jihar, kamar yadda kafofin yaɗa labarai suka ruwaito.
Alƙalan kotun shida cikin bakwai sun ce Kwamashinan Shari'a na Osun Oluwale Jimi-Bada ba shi da haƙƙi a shari'ance ya shigar da Ministan Shari'a Lateef Fagbemi a madadin ƙananan hukumomin Osun 30.
Kotun ta ce shugabannin ƙananan hukumomin da ka rantsar bayan sun ci zaɓe su ne ke da alhakin shigar da ƙarar ko kuma a shigar da su ƙara kai-tsaye.
Mai Shari'a Mohammed Idris wanda ya karanto hukuncin, ya ce gwamnatin tarayya ta yi kuskure wajen riƙe kudin ƙananan hukumomin yana mai cewa ya saɓa wa tsarin mulki.
Ta kuma nemi gwamnatin ta APC ta tabbatar ta aika musu kasonsu daga asusun haɗaka.
A watan Maris na 2025 ne Mista Fagbemi ya bayar da umarnin riƙe kason nasu har sai gwamnatin jihar ta sasanta rikicin da ya biyo bayan zaɓen ƙananan hukumomin, inda aka samu ɓangarori biyu na iƙirarin nasara a zaɓukan.

Asalin hoton, PA Media
Tarayyar Turai ta ci tarar kamfanin X, wadda aka fi sani da Twitter, kusan dala miliyan 150 sakamakon saɓa dokokin intanet.
Hukumar Tarayyar ta ce barin ɗaiɗaikun mutane su sayi alamar tantance sahihancin shafuka da X ya yi, ya sa a yanzu ba za a iya dogaro da alamar ba wajen tantance sahihancin wani shafi.
Hukumar ta kuma gano cewa X ba ya fitar da bayanai kan tallace-tallace, kuma ba ya bai wa masu bincike damar samun wasu bayanan al'umma.

Asalin hoton, Reuters
Shugaba Putin ya ce Rasha a shirye take ta samar wa India man fetur ba kakkautawa, a yayin da kasar ke fuskantar matsin lamba kan ta daina sayen man Rasha.
Mista Putin wanda a yanzu haka ke ziyara a India, ya shaida wa Firaminista Narendra Modi cewa kasarsa ta kasance abar dogaro wajen samar wa Indiya duk abin da take nema a fannin makamashi.
Amurka na zargin Indiya da tallafawa yakin Rasha a Ukraine da kudi ta hanyar siyan man Rasha, kuma ta sake kakaba wa kayyayakin India ta ake shigarwa kasar takunkumai.
Wakiliyar BBC ta ce wannan ziyara na aika wani muhimmin sako daga indiya cewa ba za ta bari matsin lambar Amurka na sanya mata haraji ya yi tasiri a kanta ba.
Wani bincike da Birtaniya da Sweden suka yi kan tasirin hako ma'adinai daga karkashin teku, wanda shi ne bincike mafi girma da aka yi zuwa yanzu, ya tabbatar da cewa hakan na yin mummunar tasiri kan halittun ruwa.
Binciken ya yi nazari ne kan hako ma'adinai a tekun Pacific.
Binciken ya gano cewa adadin halittun ruwa da ke tekun sun ragu da kashi talatin da bakwai a wuraren da aka hako ma'adinai.
Akwai dimbim albarkatun kasa da ake bukata wajen samar da wasu fasahohi masu kare muhalli a karkashin teku.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin fina-finai ta Netflix ta amince da siyan wata babbar kamfani na fina-finai mallakar Warner Bros a wata cinikayya da ta girgiza masana'antar Hollywood da darajarta ta kai aƙalla dala biliyan 72.
Kamfanin ya zama mafi rinjaye a cikin masu neman siyan Warner Bros, inda ya doke abokan hamayya kamar Comcast da Paramount Skydance.
Kamfanin Warner Bros na da manyan jerin fina-finai da suka shahara a duniya baki ɗaya, ciki har da Harry Potter da Game of Thrones, da kuma manhajar kallon fina-finai kai tsaye ta HBO Max.
Ana sa ran wannan cinikayar zai sauya fasalin masana’antar fina-finai ta Amurka da kafofin watsa labarai amma masana sun yi gargadin cewa hakan zai iya haifar da wani babban kamfani da zai ƙwace harkar nishadantarwa a faɗin duniya.
Shugaban Netflix mai raba iko, Ted Sarandos, ya ce haɗa fitattun fina-finan Warner Bros da suka haɗa da Casablanca da shahararren fim ɗin Friends na Netflix, zai ba su damar “ƙara bai wa masu kallo abin da suke so tare da taimakawa wajen tsara yadda labarai da fina-finai za su kasance a ƙarni na gaba.”

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Eritrea ta saki mutum 13 da aka tsare a gidan yarin soji na Mai Serwa kusan shekaru 18, kamar yadda ƴan uwan waɗanda aka tsare suka shaida wa BBC.
Rukunin waɗanda aka saki ya haɗa da ‘yan kasuwa da jami’an ‘yan sanda da ƙwararru yayin da aka miƙa su ga iyalansu ranar 4 ga Disamba.
Wani mutum da ke cikin waɗanda aka tsare da ba a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa an kama waɗannan mutane a watan Oktoba 2007, bayan ƙoƙarin kisan tsohon Shugaban Tsaro na cikin gida a lokacin, Colonel Simon Gebredingil.
An danganta tsarewar da wani shari’a da ta shafi ‘yan kasuwa biyu, in ji shi.
A cewar wannan majiya, kimanin mutum 30 ne aka fara tsarewa. Wasu an sake su a tsawon shekaru, yayin da aka ci gaba da tsare kusan mutane 20 a kurkukun.
Daga cikin waɗanda aka sake akwai tsohon mai hawan keke na Olympics kuma ɗan kasuwa Zeragabir Gebrehiwot; fitattun ‘yan kasuwa Tesfalem Mengsteab da Bekure Mebrahtu; da kuma ‘yan uwan biyu, injiniya David Habtemariam da geometer Matthews Habtemariam.

Asalin hoton, State house
Sabon Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya shiga ofis cikin girmamawa ƙasa da sa'o'i 24 bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da shi.
Musa ya isa hedkwatar ma’aikatar tsaro a Abuja inda jami’ai suka yi masa maraba.
Babban hafsan hafsoshin tsaro, janar Olufemi Oluyede ne ya jagoranci sauran shugabannin rundunar wajen tarbar ministan yayin da zai fara ayyukansa na farko.
Ana sa ran sabon ministan zai yi wa manyan jami’an soja jawabi da duba ayyukan tsaro na yanzu, sannan ya bayyana manyan manufofin gwamnatin a fannin tsaro a cikin kwanaki masu zuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Kenya da Amurka sun rattaba hannu kan wata muhimiyar yarjejeniya ta kawar da cututtuka na shekaru biyar, wadda ta zama ta farko tun bayan da gwamnatin Donald Trump ta sake fasalin shirin taimakon ƙasashen waje.
An ware dala biliyan 2.5 don yaki da cututtuka masu yaduwa a Kenya, kuma ana sa ran irin waɗannan yarjejeniyoyin za su faɗaɗa zuwa wasu ƙasashen Afirka da ke daidaita manufofinsu da na Trump a harkokin diflomasiyya.
Yarjejeniyar na da nufin ƙara gaskiya da ingancin aiki, amma hakan ya janyo damuwa cewa hakan zai iya bai wa Amurka damar samun muhimman bayanai kan lafiya, ciki har da bayanan sirrin majiyyata.
Ministan Lafiya na Kenya, Aden Duale, ya yi ƙoƙarin kawar da waɗannan damuwar, inda ya ce "bayanan da aka haɗa ba tare da sunayen mutane ba nekawai za a raba."
A ranar farko da ya hau kujerar shugabanci a watan Janairu, Trump ya sanar da dakatar da wasu tallafin ga ƙasashen da ke tasowa.

Asalin hoton, Getty Images
Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a asibitin haihuwa da kula da yara ta Turai Umaru Musa Yar’adua da ke jihar Katsina, bayan zargin cewa wani ma’aikacin asibitin ya ƙi yarda a aike da kuɗin amfani da iskar oxygen da matar ke buƙata.
Ma'aikacin ya nace da cewa dole sai sun kawo kuɗi a hannu kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin bayan da aka kai matar cikin mawuyacin hali, tana buƙatar samun iskar oxygen cikin gaggawa.
Wani ganau ya bayyana a ranar Juma’a cewa mai karɓar kuɗi na asibitin ya ƙi yarda a tura kuɗi ta waya inda ya ce dokar asibitin ba ta yarda da hakan ba, kuma dole ne su bi umarni.
"Na yi ƙoƙarin shiga tsakani inda na roƙi mai karɓar kuɗin da ya amince a tura masa kuɗin ta waya amma ya ƙi, ganin halin da matar ke ciki, sai na ce zan biya kuɗin har da ƙarin har na fito da dala 100 na miƙa wa ma'aikacin, amma ya ƙi." in ji mutumin.
"Mai cikin ta riƙa kuka tana neman taimako har sai da ta mutu da misalin ƙarfe 11:30 na dare." ya ƙara da cewa.
Amma kuma, asibitin ta ce ba su karɓi takardar koke kai tsaye daga jama’a ba game da lamarin, sai dai ta hannun wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam, IHRAAC.

Asalin hoton, @Martin Amaewhule/Facebook
Kakakin majalisar dokokin jihar Rivers, Martin Amaewhule, ya sauya sheƙa tare da wasu ƙarin mambobi 16 na majalisar a ranar Juma’a, lamarin da ya ƙara dagula harkokin siyasar jihar wadda ke fama da rikice-rikicen cikin gida tun watanni da dama.
Rahotanni sun nuna cewa sauya sheƙar na da alaƙa da rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.
Wannan mataki ya mayar da adadin mambobin majalisar da suka koma jam’iyyar APC zuwa 16 gaba ɗaya.
Sauya sheƙar ya faru ne a wani zama na musamman da majalisar ta yi inda mambobin suka bayyana cewa sun yanke shawarar komawa APC

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Zamfara ta ce ta yi nasarar shawo kan ɓarkewar cutar kwalara da ta addabi al’ummomi da dama a ƙananan hukumomi 14 na jihar, tare da tabbatar da cewa yanzu babu wani sabon lamari na cutar a kowace hukuma.
Wata sanarwa daga ma’aikatar lafiyar jihar ta ce kwamishiniyar lafiya, Dr Nafisa Maradun, ta bayyana hakan yayin taron duba matakan da aka ɗauka wajen yaƙi da kwalara, da aka gudanar a cibiyar ayyukan gaggawa ta kiwon Lafiya a Gusau.
A yayin bayanin yadda aka yaƙi cutar, Dr Nafisa ta bayyana cewa an samu adadin mutum 15,464 da suka kamu da kwalara, inda aka yi wa 15,265 magani kuma aka sallame su, yayin da mutum 192 suka rasa rayukansu a kananan hukumomi 14 na jihar.
Kwamishiniyar ta ce gwamnatin jihar ta samar da ingantaccen tsarin shirin kariya daga Annoba domin magance duk wani barazana ga lafiyar jama’a nan gaba.
Waɗannan barazanar sun haɗa da kwalara da gudawa da sankarau da sauran cututtuka masu hatsari ga lafiyar al’umma.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta bayyana sunan mutumin da aka kama da zargin dasa wasu bama-bamai da aka hada a gida a hedikwatar jamiyyun Democrat da Republican na Washignton a watan Janairun 2021, a matsayin Brian Cole Jr - mai shekara 30 daga Virginia.
An gano bama-baman ne a ranar da magoya bayan Donald Trump suka yi tarzoma a cikin ginin majalisar dokokin Amurka.
Masu bincike sun ce an dasa bama-baman ne a yammacin ranar da ta gabata.
Duk da dai ba su fashe ba, hukumomi sun ce akwai yiwuwar da sun hallaka ko jikkata mutane da dama.
A tsawon shekara biyar da hukumar ta FBI ta yi tana bincike ta fitar da hotuna da bidiyo da yawa tare da alkawarin bayar da tukuicin dala miliyan dubu 500, don samun bayanai.

Asalin hoton, Bayelsa state ministry of transport
Kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun tarayya da ta hana jami'an VIO tsayawa ko ƙwace motoci a hanya ko kuma ƙaƙaba tara ga direbobi.
Kotun, wacce ta ƙunshi alkalai guda uku, ta ce ba ta ga wani dalili ba da zai sa a rushe hukuncin kotun Tarayya na ranar 16 ga Oktoba, 2024 ba, wanda ya haramta wa jami'an VIO ƙwace motocin direbobi ƙwace motoci ko musu barazana.
Saboda haka kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da VIO ta shigar, tana mai cewa ba ta da wani ingantaccen hujja.
A baya, mai Shari’a Nkeonye Maha ta kotun tarayya ta bayyana cewa babu wata doka da ta bai wa VIO ikon tsayawa da kwace ko ƙaƙaba tara ga direbobi saboda wani laifi.
Wannan hukunci ya samo asali ne daga karar kare hakkin dan adam da lauya Abubakar Marshal ya shigar.
Mai karar ya ce an tare shi da karfi a unguwar Jabi ranar 12 ga Disamba, 2023, kuma aka ƙwace motarsa ba tare da wani dalilin doka ba inda ya buƙaci kotu ta tantance ko abin da jami’an VIO ɗin suka yi ba cin zarafi ba ne ko danniya da kuma saɓawa haƙƙinsa na dan Adam.
Kotun, yayin amincewa da bukatunsa, ta umarci VIO da duk jami'ansu su daina ƙwace motoci ko ƙaƙaba tara ga direbobi, domin hakan ba bisa ka’ida ba ne, kuma danniya ce.