Rufewa,
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Ku tara da mu gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/01/2026.
Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida, Abdullahi Diginza da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Ku tara da mu gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Greenland ya yi maraba da sanarwar haɗin gwiwa da shugabannin ƙasashen Turai suka fitar, inda suka yi alƙawarin kare yancin yankin, bayan Donald Trump ya sake barazanar ƙwace tsibirin.
Birtaniya da Faransa da Jamus da Italy da Poland da kuma Spain, sun ce yankin mai kwarya-kwaryar ƴanci da ke ƙarƙashin yankin Denmark, mallakin mutanen yankin ne.
Firaministan ya ce goyon bayan da suka nuna na da muhimmanci sosai, a wani lokaci da ake yi wa dokokin ƙasa da ƙasa karan tsaye.
Sai dai a yanzu ana ganin iƙirarin Amurka na ƙwace yankin ya ƙara ƙarfi, idan aka yi la'akari da abin da ta yi a Venezuela.

Asalin hoton, Getty Images
Venezuela da Cuba sun ce aƙalla jami'an soji 55 ne aka kashe a lokacin da dakarun Amurka na musamman suka kai hari, da ya kai ga kama shugaba Nicolas Maduro.
A cikin jerin sunayen da sojin ƙasashen biyu suka wallafa, sun ce sojin Cuba aƙalla 32 da na Venezuela 23 ne aka kashe a harin.
A can Venezuela kuwa, gwamnatin ƙasar ta tsananta kamen ƴan adawa.
Mazauna babban birnin ƙasar sun bayyana yadda sojoji ke sintiri a lungu da sako na unguwanni, yayin da ƴansanda ke duba wayoyin fararen hula.
Wasu ƴan Venezuela sun shaida wa BBC cewa suna tsoron fitowa daga gida, saboda jam'ian tsaro na sintiri har a kasuwanni.

Asalin hoton, Tammy Danagogo/Facebook
Tsohon ministan wasanni a Najeriya, dakta Tammy Danagogo, ya musanta zargin da ake yi cewa yana da hannu a wani yunkurin kashe ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike.
Cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Fatakwal da yammacin ranar Litinin, tsohon Ministan wasannin ya yi watsi da zarge-zargen da aka yi masa, inda ya ce ba su da tushe balle makama.
Sanarwar wadda mataimakinsa na musamman, Barista Obele Briggs ya sanya wa hannu, ta ce Danagogo bai taɓa shiga wata tattaunawa, ko taro ko shiri da ya shafi kitsa tashin hankali, ko kuma wani aiki da ya saɓa wa dokar Najeriya ba.
A ɗaya gefe, rahotannin sun ce jami’an tsaro na sashen leƙen asiri daga ofishin babban sufeton ƴansandan Najeriya sun kama wani likita kuma fasto da ke birnin Fatakwal na jihar Rivers, mai suna Tombari Gbeneol, bisa zarginsa shi ma da ƙitsa yadda za a hallaka ministan.
Rahotanni sun ce kamen ya biyo bayan gano wata tattaunawa ta wayar tarho da ake zargin an yi tsakanin Fasto Gbeneol da Danagogo, wanda shi ne tsohon sakataren gwamnatin jihar Rivers.
A cikin tattaunawar da aka ce an naɗa, ana zargin sun tattauna shirin shigo da wasu ‘yan Isra’ila domin aiwatar da kisan ministan babban birnin tarayyar.
Rahoton ya ƙara da cewa an kammala tattaunawar da zargin shirin neman kuɗin aiwatar da kisan, daga hannun gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.
Sai dai, dakta Danagogo ya ƙi amincewa da zarge-zargen baki-ɗaya, yana mai cewa ƙarya ce tsagwaronta kuma an ƙirƙire ta domin ɓata masa suna.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan rahotanni da ya bayyana a matsayin ƙarya kuma masu tayar da hankali.

Asalin hoton, Bayo Oyanuga/X
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Dakta Olugbemisola Titilayo Odusote, shugabar makarantar horar da Lauyoyi ta Najeriya.
Wannan naɗi na nufin cewa ta zama mace ta farko da za ta jagoranci makarantar tun bayan kafa ta a shekara ta 1962.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce naɗin zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Janairun, 2026 na tsawon shekara huɗu.
Dakta Odusote mai shekara 54, ita ce mataimakiyar shugabar makarantar a halin yanzu.
Sanarwar ta ce Odusote za ta gaji shugaban makarantar ta horar da lauyoyi mai barin gado, Farfesa Isa Hayatu Chiroma wanda wa'adinsa zai kare ranar 9 ga watan Janairun, 2026, bayan shafe tsawon shekara takwas.

Asalin hoton, EPA
Shugabar Mexico Claudia Sheinbaum, ta yi kira ga Washington ta tabbatar an yi wa hamɓararren shugaban Venezuela, Nicolas Maduro shari'a bisa adalci a Amurka.
Ta ce duk da ƙasar ba ta ɗasa wa da gwamnatin Maduro amma kuma wani abin ne daban a ce wata ƙasa ta cire shugaban wata ƙasar da ƙarfin tsiya.
A gefe guda kuma Colombia ta bayyana damuwa game da kalaman Donald Trump na cewa zai iya ɗaukar mataki irin na Venezuela a ƙasar.
Ministar harkokin wajen ƙasar ta ce wajibi ne rundunar sojin Colombia ta kare ƙasar da ƴancinta.
A ranar lahadi ne mista Trump ya bayyana Colombia da cewa ''ita ma ƙasa ce da bata da lafiya''.

Asalin hoton, Lookman/IG
Ɗan wasan gaban Najeriya Ademola Lookman ya ce babu wani saɓani tsakaninsa da abokin wasansa Victor Osimhen.
Hakan na zuwa ne bayan da aka ga Osimhen ya je gaban Lookman yana yi masa ihu kan cewa bai ba shi kwallo ba, yayin buga wasa tsakanin Najeriya da Mozambique ranar Litinin.
Magoya bayan tawagar Super Eagles da dama sun nuna ɓacin ransu kan abin da Osimhen ya yi.
Sai dai Lookman ɗin ya wallafa hotonsa tare da Osimhen a shafin Instagram inda ya ce "Muna tare a kowane lokaci".
Najeriya dai ta samu damar zuwa zagayen kwata-fainal a gasar cin kofin Afirka da ake yi a Moroko, bayan doke Mozambique da ci 4-0.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile yunkurin garkuwa tare da ceto wasu mutum uku a jihar Taraba.
Wata sanarwa da mai magana da yawun burget na shida a jihar, Umar Muhammad ya fitar, ya ce sun kai samamen ne a ranar Litinin bayan samun bayanan sirri na yadda masu garkuwan ke gudanar da ayyukansu a ƙauyen Sangai da ke karamar hukumar Karim Lamido na jihar.
Ya ce sun fatattaki waɗanda ake zargin zuwa kan iyakar Taraba da jihar Filato, inda suka tsere suka bar mutum uku da suka kama.
Rundunar sojin ta ce yanzu haka mutanen na wurinsu kuma suna samun kulawa - daga bisani za a miƙa su ga ƴan uwansu.

Asalin hoton, Getty Images
Gamayyar ƙungiyoyin kwadago na Malamai a Jamhuriyar Nijar, za su fara yajin aiki na kwanaki uku daga gobe laraba, 7 ga watan Janairun, 2026 zuwa Juma'a 9 ga watan.
Wata sanarwa da gamayyar ƙungiyoyin ta fitar, ta koka da halin ko in-kula da rashin mutunta yarjejeniyar da suka saka wa hannu daga ɓangaren gwamnati.
Malaman sun buƙaci gwamnati ta biya su illahirin albashin da suke bin ta, da batun biyan albashin kowane kowane wata kamar yadda yarjajeniyar 2022 ta yi tanadi.
Don haka suka buƙaci gwamnati ta mutunta yarjejeniyar 2025 kan batun ɗaukar malaman aiki na dindindin da batun biyan alawus da albashi ga wasu malamai na dindindin da ke karkashin ƙungiyar.

Asalin hoton, Getty Images
An ci gaba da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Tehran, babban birnin ƙasar Iran.
Dandazon mutane ne suka yi zaman dirshan a babbar kasuwar Bazaar da ke birnin, suna rera waƙoƙin nuna adawa ga jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.
An samu arangama tsakanin masu zanga-zangar da ƴansanda, inda jami'an suka riƙa harba hayaƙi mai sa hawaye tare da rufe wasu yankunan kasuwar mai tarihi.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta ƙasar ta ce aƙalla mutum 35 ciki har da jami'an tsaro biyu aka kashe tun fara zanga-zangar kwanaki 10 da suka gabata.
Wata ƙungiyar ta ce fiye da mutum 1200 aka tsare yayin da zanga-zangar ta bazu zuwa lardunan ƙasar 27 cikin 37.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Venezuela ta zafafa kamen da take yi wa ƴan'adawar siyasa bayan hamɓarar da shugaban ƙasar, Nicolas Maduro tare da kama shi.
Jami'an ƴansandan riƙe da makamai sun zafafa sintiri a kan titunan Caracas, babban birnin ƙasar.
Ministan Shari'ar ƙasar, Diosdado Cabello, ya wallafa wani hoto da ya ɗauka da jami'an tsaron a shafinsa ranar Litinin da daddare.
A ɗaya daga cikin bidiyoyin da ya wallafa an jiyo jami'an tsaron na cewa ''biyayya koyaushe, bijirewa babu''.
Rahotonni na cewa ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya - bisa umarnin gwamnati - na cusguna wa mutane da ke murnar hamɓarar da Maduro a wani harin Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin ƙasashen Turai sun bayyana cewa ba za su daina kare yankin Greenlanda ba.
Cikin wata kakkausar sanarwa da suka fitar sun ce za su ci gaba da kasancewa a yankin domin kare shi.
Sanarwar na zuwa ne kwana biyu bayan Shugaban Amurka, Donald Trump ya nanata cewa - Amurka ce za ta yi iko da ƙaramin tsibirin da ke ƙasar Denmark.
Shugabannin na Turai sun jaddada cewa yankin Greenland nasu ne, suna masu cewa kasancewar Amurka mamba a ƙawancen tsaro na Nato, na da rawar da za ta taka wajen tsaron yankin.

Asalin hoton, Getty Images
Ministan harkokin wajen Isra’ila, Gideon Sa’ar, ya isa birnin Hargeisa, babban birnin Somaliland, inda ya gudanar da ziyara ta farko a hukumance tun bayan da Isra’ila ta amince da ‘yancin kan yankin.
Majiyoyi masu tushe a Somaliland sun shaida wa BBC Somali da kafafen labarai na cikin gida cewa Sa’ar ya sauka a birnin ne a ranar Talata da safe.
A yayin ziyarar, ana sa ran zai gana da shugaban Somaliland, Abdirahman Mohamed Abdullahi, inda shugabannin biyu za su yi jawabi ga manema labarai a fadar shugaban ƙasa.
Wani jami’in diflomasiyya ya bayyana cewa ziyarar na da nufin bunƙasa haɗin gwiwar siyasa da dabaru tsakanin Isra’ila da Somaliland, inda ya bayyana hakan a matsayin mataki na ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Har zuwa yanzu, ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ba ta yi wani bayani a fili game da ziyarar ba.
Tun daga shekarar 1991, Somaliland ta bayyana ‘yancinta daga Somalia, amma ba a amince da ita sosai a duniya ba.

Asalin hoton, Nigerian Army/X
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce sojojin ƙasar za su yi duk mai yiwuwa don daƙile ƙaruwar hare-haren ƴanbindiga a jihar Neja da sauran sassan ƙasar.
A ƙarshen makon da ya gabata ne dai wasu mahara suka far wa Kasuwan Daji da ke jihar ta Neja, inda suka kashe fiye da mutum 40 tare da yin garkuwa da wasu kafin su ƙona kasuwar.
Laftanar Janar Shu'aib ya ce sojojin ƙasar za su mayar da hankali wajen aiwatar da umarnin shugaban ƙasa na kakkaɓe ayyukan ƴanbindigar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ambato shi yana cewa.
Bayan harin na Neja shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci jami'an tsaron ƙasar su yi duk mai yiwuwa don kuɓutar da mutanen da maharan suka sace a lokacin harin.
“Za mu baza jami'an tsaronmu a sassan ƙasar nan domin cimma ƙudurinmu na mayar da Najeriya mai zaman lafiya da bin doka'', in ji shi.

Asalin hoton, TV3 Ghana
Mutum 22 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 65 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a garin Semera, babban birnin yankin Afar na Ethiopia, a ranar 6 ga Janairu, 2026 kamar yadda rahotanni daga kafafen yaɗa labaran ƙasar suka bayyana
Hatsarin ya auku da ƙarfe 5 na safe a lokacin da wata babbar mota ɗauke da ƴan ci-rani ke ƙoƙarin barin ƙasar ta hanyar gabas ta kife a cikin garin Semera.
Mohammed Ali Biedo, jami’in sadarwa na yankin Afar, ya tabbatar da mutuwar mutum 22, sai dai ya yi gargaɗin cewa adadin na iya ƙaruwa, saboda daga cikin waɗanda suka jikkata, 30 suna cikin mawuyacin hali.

Asalin hoton, Getty Images
Sakamakon farko na zaɓen shugaban ƙasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da aka gudanar a watan da ya gabata ya nuna cewa shugaban ƙasa mai ci, Faustin-Archange Touadéra, ya samu nasara a wa’adin mulkinsa na uku.
Hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa Touadéra mai shekaru 68, wanda malamin lissafi ne, ya samu sama da kashi 75 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.
Tun kafin bayyana sakamakon, da dama na hasashen cewa shi ne zai lashe zaɓen.
Touadéra ya gudanar da yaƙin neman zaɓensa ne bisa alƙawarin ƙara inganta tsaro, musamman bayan shigar da sojojin haya na Rasha da kuma dakarun Rwanda cikin ƙasar.
A makon da ya gabata, masu sanya ido na Tarayyar Afirka (AU) sun bayyana zaɓen a matsayin wani mataki na cigaba ga dimokuraɗiyya, duk da cewa babbar jam’iyyar adawa ta kaurace wa zaɓen.

Asalin hoton, RMK/X
Jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar ranar haihuwarsa.
A cikin sakon taya murna da Kwankwason ya wallafa a shafinsa na X ya bayyana godiyarsa da darajar shekaru da suka yi tare a harkokin siyasa.
Saƙon taya murnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da tambarwar ficewar Abba daga NNPP zuwa APC.
Kwankwaso ya ce Abba ya taka muhimmiyar rawa a tafiyar siyasar Kano, tun daga lokacin da ya kasance mataimakina na musamman, sannan ya zama kwamishina kafin yanzu ya zama gwamnan jihar Kano.
Jagoran NNPPn ya ce gudunmawar Abba Kabir a fannin ci gaban jihar Kano tana da matuƙar amfani, musamman wajen aiwatar da shirye-shirye da manufofin da suka shafi cigaban al’umma da tattalin arziki.
Kwankwaso ya yi addu’ar "Allah ya ba Abba Kabir ƙarin hikima da lafiya da ƙarfin zuciya da kuma fayyace dalilansa a koyaushe''.

Asalin hoton, Iinec nigeria/facebook
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta fara mataki na biyu na aikin rijistar masu zaɓe a fadin Najeriya bayan kammala mataki na farko a hukumance ranar 10 ga Disamba, 2025.
Aikin ya fara ne daga jiya, ranar Litinin, inda hukumar ke bai wa ‘yan Najeriya damar yin rajista ta intanet ko ta hanyar gaba da gaba a cibiyoyin rijistar zaɓe da aka keɓe.
INEC dai ta fara rajistar zaɓe ta intanet ne a ranar 18 ga Agusta, 2025, sannan ta fara rajistar gaba da gaba daga 25 ga Agusta, 2025.
A mataki na farko, mutum miliyan 9,891,801 ne suka fara rajista ta intanet daga ciki mutum miliyan 2,572,054 ne suka kammala rajistarsu gaba ɗaya, inda mutum miliyan 1,503,832 suka kammala ta intanet yayin da kuma mutum 1,068,222 ta gaba da gaba.
Sai dai hukumar ta jaddada za a ci gaba da dakatar da aikin rijistar zaɓen a jihar Anambra da Babban Birnin Tarayya, Abuja saboda wasu muhimman ayyukan zaɓe da ke gudana.

Asalin hoton, Isma'il Misilli/X
Gwamnatin jihar Gombe ta haramta sana’ar jari bola a duka faɗin jihar, bisa dalilai na tsaro.
Gwamnatin ta amince da matakin ne bayan taron Majalisar Tsaro na musamman tare da manyan jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya domin nazarin sabbin ƙalubalen tsaro da faruwar wasu abubuwa masu tayar da hankali a jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa haramcin zai fara aiki nan take kuma zai ci gaba har sai an tsara harkar a ƙarkashin shugabanci da kulawa ta musamman.
A baya-bayan nan gwamnatin jihar ta ce ta samu rahotannin satar kayan more rayuwa da kuma lalata kayan gwamnati da na makarantu, waɗanda galibi suke shiga hannun masu sana’ar bola jari.
Majalisar Tsaron ta nuna damuwa kan yadda rashin tsari da shugabanci na masu sna'ar ke haifar da wahalar sanya ido da kiyaye ayyukansu.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa, nan gaba, za a kafa kwamitin aiwatarwa da sa ido kan harkar domin tabbatar da bin doka a dukkan ƙananan hukumomi.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Angola, Joao Lourenco, ya gabatar da “wasu shawarwari” don kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, in ji fadar shugaban ƙasar Congo.
An bayyana shawarwarin a matsayin “masu matuƙar ban sha’awa,” amma ba a fitar da cikakkun bayanai ba.
Ofishin shugaban Angola ya ce ya gana da takwaransa na Congo, Felix Tshisekedi, a Luanda na tsawon sa'o'i domin tattauna rikicin da kuma ƙoƙarin kawo ƙarshen sa.
Tshisekedi ya bayyana cewa shawarwarin Lourenco na iya “taimakawa matuƙa” wajen neman zaman lafiya.
Lourenco shi ne shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka a halin yanzu.
Ganawar ta zo ne kwanaki kafin taron kwanaki uku da ministocin tsaro na ƙasashen tsakiya da gabashin Afirka za su yi a Zambia domin tattauna halin tsaro a Congo.
Duk da yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka cimma a baya, sabon rikici ya ɓarke a ranar 3 ga Janairu tsakanin ƙungiyar M23 da ke samun goyon bayan Rwanda da sojojin gwamnatin Congo.