Gwamnatin Jihar Yobe ta yi ƙarin haske kan harin jirgin sojojin Najeriya da aka kai a yankin da ke kan iyaka da Jihar Borno, tana mai cewa wurin da aka kai harin “ba mallakar kowa ba ne kuma an kai harin ne kan sansanin ‘yan Boko Haram, ba kan fararen hula ba.
Rahotanni sun ce an kashe daruruwan mutane a ranar Asabar a lokacin harin kan abin da aka bayyana a matsayin babban sansanin ƙungiyar ISWAP a arewa maso gabas.
Wasu rahotanni daga mazauna yankin da hukumomin agaji sun ce adadin waɗanda suka mutu na iya kai wa kusan 200, yayin da wasu kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ce adadin ya bai kai ba wanda suka ce daga mutum 10 zuwa sama da 50 ne suka mutu, tare da wasu da suka jikkata da ake kula da su a asibiti.
A cikin sanarwa da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Birgediya-Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya, ya fitar a ranar Litinin, ya ce harin ya faru ne a Jilli da ke Ƙaramar Hukumar Gubio a Jihar Borno, wadda ya bayyana a matsayin sansanin ‘yan tada ƙayar baya da ake amfani da shi wajen shirye-shiryen hare-hare.
Ya ce wasu mazauna Ƙaramar Hukumar Geidam a Jihar Yobe sun je kasuwar mako ta Jilli ne, inda harin ya rutsa da su.
Ya kuma bayyana Jilli a matsayin “yanki da ba mallakar kowa ba ne,” yana mai cewa babu wata kafaffen mazauni na fararen hula a wurin. Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ayyukan soji domin rushe sansanonin ‘yan bindiga da dawo da tsaro a yankin.
A halin yanzu, rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta fara bincike kan zargin asarar rayukan fararen hula da ke da alaƙa da farmakin.