Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/09/2025.

Taƙaitattu

  • Latsa nan ku shiga tasharmu ta WhatsApp
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki
  • Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara
  • Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya
  • 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'
  • Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike
  • An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muke rufe wannan shafin namu na labaran kai-tsaye na wannan rana ta Asabar.

    Sai kuma gobe Lahadi.

    Da fata kun ji daɗin kasancewa a tare da mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Takunkumi ba zai hana mu bunƙasa shirin nukiliya ba - Iran

    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian, ya ce matakin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya dauka jiya Juma'a na sake kakaba wa kasarsa dukkanin takunkumin da ya danganci shirinta na nukiliya, ba zai hana kasar bunkasa shirin ba.

    Ya kara da cewa, kwamitin tsaron ya rufe dukkanin kafofin diflomasiyya - kuma hakan ba zai zama wani gargadi ba.

    Dangane da harin da Isra'ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin nukiliya na Iran din a watan Yuni, shugaban ya ce - a duk lokacin da suka kai wa cibiyoyin hari, Iran za ta sake gina wadanda suka fi na baya - wadanda aka kai wa harin.

    Rasha ta yi suka kan matakin kwamitin tsaron na sanya wa kawarta takunkumin - tana mai gargadin cewa ba abin da hakan zai haifar illa zaman tankiya.

  3. Fashewar kayan haɗa bam ta kashe mutum ɗaya a kamfanin ƙera makamai na Kaduna

    Kamfanin ƙera makamai na rundunar tsaron Najeriya, DICON ya tabbatar da fashewar wasu sinadaran da kamfanin ke amfani da su wajen haɗa makamai da bama-bamai a ma'adinarsa da ke Kaduna, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗaya da jikkata wasu.

    A wata sanarwa da jami'ar hulɗa da jama'a ta kamfanin, Maria Sambo ta fitar a madadin darakta-janar na kamfanin, ta ce lamarin ya auku ne a wurin a suke ajiye kayayyakin aiki.

    "A ranar Asabar, 20 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 10 na safe, wasu kayayyakin haɗa makamai da lokacin amfanin su ya wuce sun fashe, inda mutum ɗaya ya mutu, sannan mutane da dama suka jikkata," in ji ta.

    Ta ce daga cikin kayayyakin da suke cikin ma'adanar akwai sinadarin Ammonia Nitrates da sauran wasu sinadarai da suke adanawa, waɗanda ta ce lokacin amfani da su ya wuce.

    Ta ce a watan Yulin wannan shekarar ne suka fara "lalata dukkan sinadaran da lokacin su ya wuce. Amma sai aka samu matsala a daidai lokacin da masana suke ci gaba da aikin lalata sinadaran a wannan watan," in ji sanarwa, sanan ta ƙara da cewa waɗanda suka ji rauni suna ci gaba da samun kulawa a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna.

    Ta kuma ce an kafa kwamiti domin gano asalin musabbain aukuwar lamarin.

  4. 'China ta amince Amurkawa su mallaki sashen TikTok na Amurka'

    Fadar gwamnatin Amurka ta ce kamfanin TikTok ta China ya amince ya sayar da sashensa na Amurka ga wani kamfani da mafi akasarin mallakin Amurkawa ne.

    Sakataren watsa labaran Shugaban Amurka ta ce shida daga daraktocin kamfanin da zai mallaki hannun jarin, za su kasance Amurkawa ne.

    Karoline Leavitt ta ƙara da cewa kamfanin na Amurka mai suna Oracle zai kasance mai kula da adana bayanai, sannan duk abubuwan da ake yi a Amurka ciki har da bidiyo da sauran su, duk a ƙasar ne za a riƙa kula da su.

    Ta ce nan da wasu kwanaki kaɗan za a tsara tare da shiga yarjejeniyar, duk da cewa ba a samu bayanai masu yawa daga ɓangaren Beijing ba.

  5. Manyan jam'iyyun Malawi na zargin juna da tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasar

    Ƴan ƙasar Malawi suna jiran sakamakon babban zaɓen ƙasar da aka gudanar a wannan makon, inda manyan jam'iyyun ƙasar suke zargin juna da tafka maguɗi.

    Jam'iyyar United Democratic Front ta hammaya ta bi sahun jam'iyya mai mulki a ƙasar wajen miƙa ƙorafinta ga hukumar zaɓen ƙasar, inda ta buƙaci a fito tare da bayyana sakamakon wasu mazaɓun waɗanda dukkan wakilan jam'iyyu suka saka hannu.

    An dai kama aƙalla jami'an zaɓe guda takwas bisa zargin su da aikata laifukan zaɓe.

    Yanzu dai zaɓe ne da ake jira a ga wanda zai samu nasara tsakanin Shugaban ƙasar Lazarus Chakwera da tsohon shugaban ƙasar Peter Mutharika.

    Idan babu wanda ya samu da kashi 50 na ƙuri'un da aka kaɗa, za a yi zaɓen zagaye na biyu a cikin kwana 60 kamar yadda dokar ƙasar ta tanada.

    Ƙasar Malawi dai na da fama da matsalolin hauhawar tashin farashin kayayyaki da talauzi da sauran su.

  6. 'Yansanda sun kashe 'masu garkuwa' tare da kuɓutar da mutum uku a Abuja

    Rundunar 'yansanda a Abuja babban birnin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe 'yanbindiga uku bayan kuɓutar da mutanen da suke garkuwa da su.

    Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Josephine Adeh ta ce kafin kashe su gungun 'yanbinidigar sun yi yunƙurin sace wasu 'yanmata biyu a yankin Guzape, amma ɗaukin da dakarun rundunar suka kai ya sa ska kuɓutar da su. Sai dai wani ɗan sa-kai Bako Pwaza ya rasa ran sa a yunƙurin.

    "A ranar Laraba ma, gungun suka sace wani mai suna Nafiu Idris a Karu. Bayan tattara bayanan sirri dakaru suka kai samame maɓoyarsu a Dajin Zinda mai maƙwabtaka da jihara Nasarawa bisa rakiyar mafarauta," in ji ta.

    "An yi ɓarin wutar da kai ga kashe jagoransu mai suna Abdullahi Umar da kuma mayaƙansa biyu, Buba Ahmadi da Habu Sule."

    Ta ƙara da cewa dakarun sun yi nasarar ƙwace bindiga ƙirar AK-49 biyu, da adakar harsashi bakwai, da wayoyin hannu biyu, da katikan ATM, da ƙahon dabbobi, da kuɗi naira 10,000.

  7. Filayen jirgi a Turai na fuskantar matsala saboda harin intanet

    Filin jirgin sama na Heathrow a birnin Landan na cikin filayen nahiyar Turai da harkoki suka tsaya saboda kutsen intanet da suka fuskanta a yau Asabar.

    Hukumar filin jirgin ta yi gargaɗin cewa za a samu tsaiko "saboda matsalolin na'ura" da za su shafi manhajar Collins Aerospace.

    Filin jirgi na Brussels a Belgium ma ya ce harin intanet a ranar Juma'a ya sa ana tantance fasinjoji da hannu, yayin da filin jirgi na Brandenburg a Jamus ya bayar da rahoton dogon jira da matafiya ke sha saboda matsalar.

    RTX, wanda ya mallaki kamfanin Collins Aerospace, ya ce "yana sane da matsalar intanet" da aka samu a "wasu filayen jirgi" kuma yana aikin gyara ta cikin gaggawa.

    "Matsalar a kan na'urori tantance fasinjoji kawai ta tsaya, da kuma wurin ajiye jakunkunan matafiya, wadda za a iya rage matsalar ta hanyar amfani da hannu," in ji wata sanarwar RTX.

  8. 'Yansandan Bauchi na zargin mata da yi wa yarinya azaba da wuta a gabanta

    Wannan labarin zai iya tayar da hankalin masu karatu

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta tsare wata mace mai suna Zuwaira Hassan da zargin yi wa yarinya mai shekara 10 azaba da wuta a gabanta bayan saka cokali a wuta.

    Kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya faɗa cikin wata sanarwa jiya Juma'a cewa matar ta bayyana musu cewa ita da 'ya'yanta maza biyu ne suka aikata hakan.

    A cewar sanarwar: "Zuwaira ta ce a ranar 8 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 11:00 na dare ne yarinyar [da ba a bayyana sunanta ba] ta faɗa mata cewa ɗakin da suke ciki ita da 'ya'yanta zai rushe kuma ya kamata su sauya wurin kwana. Sannan 'ya'yan nata biyu suka faɗa mata yadda suke yin mummunan mafarki da yarinyar.

    "Bisa wannan dalilin ne wadda ake zargin [Zuwaira] ta kai 'ya'yan nata wajen wata mai maganin gargajiya Fatima Abdullahi, wadda ta ce yarinyar mayya ce, kuma ta bai wa wadda ake zargi magungunan kariya.

    "Bayan haka ne matar ta saka cokali a wuta, ta umarci 'ya'yanta Umar Ibrahim da Abubakar Ibrahim su ɗaure hannaye da ƙafafuwan yarinyar, sannan ta saka cokalin mai zafi a gaban yarinyar a matsayin hukunci, tana mai cewa mai maganin ce ta umarce ta da yin hakan.

    "Mai maganin ta buƙaci Zuwaira ta biya ta naira 150,000 kuɗin maganin, amma suka daddale kan naira 40,000, inda aka ba ta maganin wanka da kuma na hayaƙi."

    CSP Wakil ya ce dakarunsu sun kai yarinyar Babban Asibitin Toro domin kula da lafiyarta, kuma suna tsare da mai maganin ita ma.

  9. Najeriya ta ci alwashin hukunta Qatar Airways kan wahalar da fasinja

    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta ci alwashin ɗaukar matakin ladaftarwa kan kamfanin jirgin Qatar Airways saboda zargin sa da "wahalar" da fasinjan ƙasar.

    Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA) ta faɗa cikin wata sanarwa ranar Juma'a cewa kamfanin bai bi ƙa'idojin kare haƙƙin fasinjoji ba na hukumar bayan wata ma'aikaciyar jirgin ta zargi wani fasinja da cin zarafi ta hanyar taɓa bayanta.

    "Qatar Airways bai kawo wa NCAA rahoton fasinjan ba, har sai da suka sauka a birnin Doha na Qatar sannan aka tsare shi kusan awa 18, aka ci tarar sa, sannan aka tilasta masa saka hannu kan wata yarjejeniya da Larabci," in ji kakakin NCAA Michael Achimugu cikin wani saƙo a dandalin X.

    Kazalika, "an tilasta wa fasinjan sayen wani tikitin domin ƙarasawa Amurka bayan Qatar Airways ya ƙi amincewa ya kai shi". Jirgin ya tashi ne daga Legas zuwa Amurka bayan ya yi zango a Doha.

    Achimugu ya ce da ma kamfanin ya sha nuna rashin ɗa'a ga hukumar a baya, "abin da ya sa dole ne a dakatar da wannan ɗabi'ar a yanzu".

  10. Indiya ta tuhumi 'yan Najeriya 106 da safarar miyagun ƙwayoyi a 2024

    Hukumomi a Indiya sun tuhumi 'yan Najeriya 106 da laifin safarar miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024 da ta gabata, kamar yadda jaridar Indian Express ta ruwaito.

    Rahoton ya ce 'yan Najeriyar na cikin jimillar mutum 660 ne da rahoton shekara na hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ya bayyana tare wasu daga ƙasashen Nepal (203), da Myanmar (25), waɗanda su ne suka fi yawa a jerin.

    Kazalika, akwai 'yan Bangladesh (18), da Ivory Coast (14), da Ghana (13), da Iceland (10) waɗanda aka tuhuma da laifukan ta'ammali da ƙwayoyi.

    "Indiya na fama sosai wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi saboda faɗin ƙasa da take da shi," a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida Amit Shah.

  11. Amurka ta sake kashe mutum uku a Tekun Caribbean

    Shugaba Trump ya ce Amurka ta sake lalata wani jirgin ruwa a Tekun Caribbean da take zargin yana safarar kwayoyi zuwa ƙasar.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce an kashe mutum uku yayin harin.

    Sa'o'i kaɗan kafin hakan, Venezuela ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta gudanar da bincike kan jerin hare-haren da Amurka ta kai kan jiragen ruwan ƙasar waɗanda tuni suka halaka fiye da mutum 10 a cikin wannan watan.

    Ministan Tsaron Venezuela Vladimir Padrino Lopez ya bayyana hare-haren a matsayin wani yakin sunƙuru.

    Kwararru kan kare haƙƙin ɗan'adam da MDD ta nada sun bayyana hare-haren a matsayin kisan kai ba bisa ƙa'ida ba.

  12. Sojojin Najeriya sun kama 'kayan haɗa bamabamai' a jihar Yobe

    Rundunar sojan Najeriya ta ce ta yi nasarar kama motoci maƙare da kayayyakin da take zargi na harhaɗa bama-bamai ne da ake shirin tsallakwa da su Jamhuriyar Nijar.

    A ranar 16 ga watan Satumba dakarun rundunar musamman ta Operation Hadi Kai ne suka kama wata babbar mota ɗauke da buhuhunan takin zamani 700 a kan hanyar Nguru zuwa Gashuwa na jihar Yobe.

    "A wannan ranar ce binicke ya nuna cewa motar na ɗauke da buhun takin zamani 700, wanda ake haɗa bamabamai, da ƙwayoyi daban-daban, waɗanda aka ɓoye cikin kaya," a cewar wata sanarwa da Kanal Sani Uba ya fitar.

    "Bayanai sun nuna cewa an yi niyyar kai kayan ne Jamhuriyar Nijar, abin da ke nuna ayyukan safarar kayan ta'addanci tsakanin ƙasa da ƙasa."

    A cewarsa, sun kuma kama wata mota ɗauke da farantan samar da lantarki daga hasken rana da sauran kayayyaki, waɗanda bayanai suka nuna "'yanta'adda na shirin tattara kayayyaki dinka wa mayaƙansu kakin soja ne".

  13. Ambaliya ta kashe mutum uku a jihar Adamawa - Nema

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce ambaliyar ruwa ta kashe mutum uku a jihar Adamawa da ke arewacin ƙasar.

    Wata sanarwa da National Emergency Management Agency (Nema) ta fitar ranar Alhamis ta ce aƙalla mutum 1,415 ne ambaliyar ta shafa bayan ruwan sama mai ƙarfi tun daga ranar Talata.

    Ta ce an zabga ruwan ne a yankunan Yola ta Arewa da Yola ta Kudu, inda fiye da mutum 40 suka ji raunuka sannan ruwan ya rusa gidaje da kuma shafe gonaki da dama.

    Jimilar unguwanni 13 lamarin ya shafa, in ji Nema.

  14. Rasha ta kai hare-hare a Ukraine cikin dare

    Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare.

    A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine din.

    A kudancin ƙasar ma, hukumomi a Mykolaiv sun bayar da rahoton tashin gobara bayan harin da aka kai kan wasu masana'antu.

    Yankunan yammacin Lviv da Ivano-Frankivsk ma sun fuskanci gobara sakamakon hare-haren da aka kai masu.

    Suna kusa da iyakar Poland, inda sojoji suka ce sun tura jiragen sama domin tabbatar da tsaron sararin samaniyar yankin.

  15. Maraba

    Barka da hantsin Asabar daga sashen Hausa na BBC.

    Wannan shafi zai fi mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Umar Mikail ne zai kawo rahotonnin zuwa ƙarfe 4:00 na rana.