Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin namu, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonni.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Amma kafin nan ku ci gaba da kasancewa da shafin BBCHausa.com don samun labarai da kallon bidiyo da hotuna.

  2. 'Hare-haren Isra'ila sun kashe falasɗinawa 40 a Gaza'

    Hukumomin kiwon lafiya a Gaza sun ce hare-haren Isra'ila a cikin dare sun kashe Falasɗinawa aƙalla 40.

    Tawagar masu aikin ceto sun kwaso gawarwakinsu daga wurere bakwai da aka kai harin.

    Guda daga cikin hari an kai shi ne sansanin mayaƙan Hamas da ke tsakiyar babbar kasuwar Gaza, wanda ya halaka mutum 18.

    Mazauna wajen sun shaida wa BBC cewa, jami'an tsaro na gudanar da bincike kan masu satar kayan agaji yayin da jirgin mara matuƙi ya kawo harin.

    Sai dai Rundunar sojin Isra'ila ba ta kai ga mayar da martani ba.

    Kasashen Egypt da Qatar na cigaba da ƙoƙari na ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

  3. An kaddamar da shirin karfafa wa mutanen arewa amfani da Gas wurin girki

    gas

    Asalin hoton, Sokoto State Gov

    Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin tabbatar da amfani da gas wurin girki ya shiga yankunan arewacin Najeriya.

    Karamin ministan man fetur na Najeriya, Ekperikpe Ekpo ne ya ƙaddamar da shirin yau Alhamis a garin Sokoto.

    Lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamar da shirin, gwamnan jihar Ahmed Aliyu ya ce matakin zai taimaka wajen rage dogaro kan amfani da itace a wajen girki, lamarin da ke cutar da muhalli musamman a jihohin Najeriya da ke iyaka da hamada.

    Sai dai ya buƙaci masu ruwa da tsaki su yi ƙoƙarin ganin farashin gas ɗin ya yi daidai da ƙarfin talaka.

    “Matuƙar ana so wannan shiri ya yi tasiri dole ne sai an samar da gas din LPG a wadace kuma cikin rahusa ga mutanen Najeriya masu matsakaicin karfi,” in ji gwamnan.

    gas

    Asalin hoton, Sokoto State

  4. An fara shagulgulan auren hamshaƙin attajirin duniya Jeff Bezos

    Jeff Bezos da amaryarsa

    Asalin hoton, Getty Images

    An rufe wasu sassan birnin Venice na Italiya a shirye-shiryen shagalin bikin auren ɗaya daga cikin hamshaƙan attajiran duniya, Jeff Bezos da zai angwance da amaryarsa Lauren Sanchez.

    Mamallakin kamfanin Amazon ɗin ya ware kimanin dala miliyan 50 domin gudanar da shagulgulan bikin da za a ɗauki kwanaki uku ana gudanarwa, wanda aka fara daga daren yau.

    Tuni aka soke tafiye-tafiye ƙafa da na ruwa a birnin a wani mataki na hana masu zanga-zanga kawo tarnaƙi ga manyan attajiran da za su halarci bikin, ciki har da ƴar shugaba trump, Ivanka Trump.

    Masu zanga-zanga na sukar matakin rufe wasu sassan birnin, da suka bayyana tafkar saye birnin.

  5. WHo ta shigar da agaji zuwa Gaza karon farko tun watan Maris

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce ta shigar da rukunin farko a kayan agajinta da suka ƙunshi kayyakin asibiti zuwa Gaza karon farko tun cikin watan Maris.

    An shigar da kayyakin ne da suka haɗa da jini a ranar Laraba sannan za a rabar da su a asibitocin yankin nan da ƴan kwanaki masu zuwa.

    Sai dai babban daraktan hukumar, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce kayan da aka shigar ɗin ba abin da za su yi la'akari da abin da ake buƙata domin ceto rayuka a Zirin na Gaza.

  6. Sai watan Janairun 2026 sabbin dokokin haraji za su fara aiki - Gwamnatin Najeriya

    Bola Tinubu da muƙarrabansa

    Asalin hoton, State House

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta fara aiwatar da sababbin dokokin haraji da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu ba sai a watan Janairun 2026.

    Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan bikin saka wa dokokin huɗu hannu a yau Laraba, shugaban kwamatinn hukumar tattara harajin Zach Adedeji ya ce za su kammala tsara komai kafin lokacin aiwatar da su.

    Ya ƙara da cewa za su yi amfani da tazarar wata shidan wajen bai wa waɗanda ke da alhakin aiwatar da dokar damar shiryawa da kuma tabbatar da cewa an wayar da kan dukkan 'yan Najeriya game da dokokin.

    Ya tabbatar da cewa saka wa dokokin hannu ya sauya sunan ma'aikatarsa daga Federal Inland Revenue Service (FIRS) zuwa Nigeria Revenue Service.

    Kuna iya karanta cikakken bayani game da dokokin a labarin da ke ƙasa:

  7. Iran ta amince da dakatar da hulɗa da hukumar kula da nukiliya ta duniya

    Iran

    Asalin hoton, Iran Government

    Majalisar shura a Iran ta amince da ƙudirin dokar da ya nemi ƙasar da dakatar da hulɗa da hukumar sa ido kan makamashin nukiliya ta International Atomic Energy Agency (IAEA).

    Dokar ta hana masu sa ido na IAEA shiga tashoshin nukiliyar Iran har sai an cika wasu sharuɗa. Daga ciki akwai amincewa da 'yancin Iran na inganta ma'adanin Uranium kamar yadda Aya ta 4 ta yarjejeniyar Non-Proliferation Treaty ta tanada.

    Tuni majalaisar dokokin ƙasar ta amince da ƙudirin, abin da ke nufin majalisar mulkin ƙasar da ta ƙunshi malamai da alƙalai kawai ake jira ta amice kafin ya zama doka.

    Yanzu babbar majalisar mulki ce, wadda Ayatollah Ali Khamenei ke jagoranta, za ta bayyana lokaci da kuma yadda za a aiwatar da dokar.

  8. Trump ya musanta iƙirarin cewa Iran ta kwashe kayayyaki daga tashar da aka kai wa hari

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa Iran ta kwashe makamashin Uranium da ta inganta daga tashar nukiliya ta Fordo kafin harin Amurka.

    Shi ma Sakataren Tsaro Pete Hegseth ya musanta iƙirarin.

    "Babu abin da aka fitar daga tashar," a cewar Trump cikin wani saƙo a dandalin sada zumunta. "Zai ɗauki lokaci mai tsawo, da kasada kafin a iya fito da abubuwan masu nauyi!"

    A madadin haka, Trump ya ce "manya da ƙananan motoci da aka gani a wurin" na "ma'aikata ne da ke ƙoƙarin rufe bakin ramin".

  9. Kwamitin amintattu na PDP ya yi watsi da matakin da shugaban jam'iyyar ya ɗauka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BoT) ta yi watsi da matakin da shugaban jam’iyyar Iliya Damagum, ya dauka na soke taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, 30 ga Yuni, 2025.

    Haka nan kwamitin ya ce matakin da Damagum ya ɗauka na mayar da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar ba shi da tushe a kundin tsarin mulki na PDP.

    A wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattun, Sanata Adolphus Wabara ya fitar, ya bayyana cewa "kundin tsarin mulkin PDP na shekarar 2017 ya bayyana ƙarara cewa babu wani mutum ko ɓangare da ke da ikon soke ko ɗage taron shugabannin jam'iyya da aka yanke shawarar gudanarwa a taro na 99 da aka yi a ranar 27 ga Mayu, 2025".

    Saboda haka, matakin soke taron da Damagum ya ɗauka ya saɓa wa kundin tsarin jam’iyyar.

    Sanarwar ta kuma bayyana cewa "iƙirarin da Damagum ya yi na sake dawo da Sanata Anyanwu matsayin sakataren jam’iyyar ba ya da tushe.

    Kwamitin ya ce har yanzu matakin da kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ya ɗauka a zamansa na 600 na mika wa mataimakin sakataren jam’iyya, Arc. Setonji Koshoedo, riƙon muƙamin sakataren jam’iyyar shi ne sahihi.

    Kwamitin ya kuma jaddada cewa "ba zai zuba ido yana kallon yadda wasu ke kokarin jefa jam’iyyar cikin rikici da rashin bin doka ba".

    Sanarwar ta bukaci dukkan ‘ya’yan jam’iyya da su girmama tsarin mulki da bin dokokin da suka kafa jam’iyyar domin kiyaye martaba da zaman lafiyarta.

  10. Turmutsutsu ta kashe ɗalibai 29 da ke rubuta jarrabawa a Afirka ta Tsakiya

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Ɗalibai 29 da ke rubuta jarabawar kammala sakandire a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun rasa rayukansu bayan wata fashewa ta janyo turmutsutus da firgici, kamar yadda wani daraktan asibiti ya shaida wa BBC.

    Fashewar da ta faru ranar Laraba, rana ta biyu da ake jarabawar ta auku ne a wani na’urar wutar lantarki, in ji Abel Assaye na asibitin al'umma da ke Bangui.

    “Hayaniyar fashewar da kuma hayaƙin da ya biyo baya” ne suka jefa daliban cikin tsoro da ruɗani, in ji gidan rediyon Ndeke Luka.

    Daliban kusan 6,000 ne ke rubuta jarabawar a wata makaranta da ke babban birnin ƙasar, Bangui.

    Shugaban ƙasa Faustin-Archange Touadéra ya ayyana zaman makoki na ƙasa.

    Haka kuma, ya bayar da umarnin a kula da fiye da mutum 280 da suka jikkata a cunkoson, ba tare da an karɓi kuɗin magani ba.

    Ɗalibai daga makarantu guda biyar ne suka taru a makarantar Lycée Barthélémy Boganda don rubuta jarabawar.

    Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai na fama da rashin kwanciyar hankali da ƙalubalen tsaro.

    Dakarun gwamnati tare da goyon bayan sojojin haya daga Rasha na yaƙi da kungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke barazanar kifar da gwamnatin Touadéra.

  11. Kotu ta yanke wa saurayin da ya kashe budurwarsa a Nasarawa hukuncin kisa

    ...

    Asalin hoton, Salome Adaidu Facebook/ Caeser.T

    Kotun babban birnin jihar Nasarawa ta yanke wa wannan mutumin, Oluwatimileyin Ajayi da ya kashe budurwarsa Salome Adaidu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kisa.

    Mai shari’a Simon Aboki ne ya jagoranci zaman kotun kuma ya yanke hukuncin a yau, ranar Alhamis.

    Kotun ta same shi da laifin kashe da kuma fille kan Salome Adaidu.

    An gurfanar da Ajayi bisa tuhuma ɗaya ta kisan kai da gangan, wanda ya saɓa da Sashe na 221 na Dokar Penal ta Arewacin Najeriya, wadda take ɗauke da hukuncin kisa.

    Timileyin Ajayi ya musanta laifin aikata kisan a gaban kotu lokacin da sauraron shari’ar ya fara.

    A ranar 12 ga watan Janairun 2025 ne dai Jami'an tsaro suka damƙe saurayin, wanda mawaƙin yabo na addinin kirista ne, ɗauke da kan Salome, kusa da wani coci.

  12. Trump ya buƙaci a dakatar da shari’ar cin hanci da ake yi wa Netanyahu

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci a “yafe wa” firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ke fuskantar shari’a bisa zargin cin hanci, ko kuma a dakatar da shari’ar gaba ɗaya.

    A wani sakon da ya wallafa a kafar sada zumunta ta X, Trump ya yi ikirarin cewa Amurka ce ta ceci Isra’ila – a yaƙin ƙasar da Iran – kuma yanzu za ta "ceci" Netanyahu.

    Firaminista Netanyahu dai ya musanta zarge-zargen cin hanci da almundahana da kuma cin amana, waɗanda ya ke fuskanta tun daga shekarar 2020.

    Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Isra’ila, Yair Lapid, ya soki furucin Trump, yana mai cewa bai kamata ya tsoma baki a cikin shari’ar wata kasa mai cikakken ƴanci ba.

    Furucin Trump ya zo ne kwanaki kaɗan bayan ya caccaki Isra’ila saboda kai hari kan Iran bayan ya ayyana yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan shafe kwanaki 12 ana musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila.

  13. Ayatollah ya ce Iran ta ci nasara kan Isra'ila

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana cewa Iran ce tayi nasara kan Isra’ila, yana mai taya al’ummar ƙasar murna a sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta na X.

    “Ina taya ƙasar murna kan nasarar da ta samu a kan gwamnatin yahudawa mai cike da kuskure. ” in ji Khamenei.

    Ya kuma ce Amurka ta shiga yaƙin kai tsaye ne saboda ta fahimci cewa idan ba ta shiga ba, to gwamnatin yahudawa za ta rushe gaba ɗaya.

  14. Hamas ta ce masu shiga tsakani na ƙara ƙaimi domin tsagaita wuta a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Wani babban jami’in Hamas ya shaida wa BBC cewa masu shiga tsakani sun ƙara ƙaimi wajen neman tsagaita wuta da sako fursunoni a Gaza, duk da cewa tattaunawa da Isra’ila na ci gaba da tafiyar hawainiya.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ana samun “gagarumin ci gaba” tun bayan da Isra’ila da Iran suka kawo ƙarshen yaƙinsu na kwanaki 12, yana mai cewa an kusa cimma yarjejeniya” tsakanin Isra’ila da Hamas.

    A ranar Larabar da ta gabata, hare-haren Isra’ila a Gaza sun kashe aƙalla Falasɗinawa 45, a cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas.

    Sojojin Isra’ila kuma sun ce wasu bamabamai sun hallaka sojojinsu 7 a wani hari da Hamas ta ɗauki alhakin aikatawa.

    Duk da furucin Trump, jami’in Hamas ya ce ba su samu wani sabon tayin yarjejeniya ba tukuna.

    Hakazalika, wani jami’in Isra’ila ya shaida wa jaridar Haaretz cewa babu ci gaba a tattaunawar saboda sabani da dama da ke akwai.

  15. Tinubu zai sanya hannu kan sabbin dokokin haraji na Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Tinubu/Facebook

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai sanya hannu kan sabbin dokokin sauya tsarin haraji na ƙasar a yau Alhamis, a wani mataki da ake sa ran zai sauya tsarin tattara haraji da kuma inganta yanayin kasuwanci a Najeriya.

    Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labaru, Bayo Onanuga ta ce sabbin dokokin huɗu sun haɗa da dokar haraji ta ƙasa da dokar tafiyar da lammuran haraji da dokar kafa hukumar haraji ta Najeriya da kuma dokar kafa ma'aikatar kula da hukumomin tattara haraji ta Najeriya.

    Majalisar Dokoki ta kasa ce za ta amince da su bayan shawarwari da dama daga masu ruwa da tsaki.

    Sabbin dokokin harajin na Najeriya sun tayar da ƙura sosai a lokacin da shugaban ƙasar ya gabatar da su ga majalisar dokokin ƙasar, lamarin da ya kai ga dakatar da tattaunawa a kan su a zauren majalisar.

    Tun da farko gwamnonin jihohin ƙasar da majalisar kula da tattalin arziƙi ta Najeriya da ƙungiyoyi sun buƙaci a sake duba dokar kafin sake gabatar da ita.

    Daga baya gwamnonin jihohin ƙasar sun gudanar da gyare-gyare kan dokar tare da gabatar wa shugaban ƙasa, wanda ya amince da su kafin majalisar dokokin ƙasar ta ci gaba da muhawara.

    Majalisar dokokin ƙasar ta ce a halin yanzu an gyara duk wasu ɓangarori da suka haifar da tayar da jijiyoyin wuya.

    Sai dai har yanzu al'umma da dama ba su da cikakkiyar masaniyar abubuwan da dokokin suka ƙunsa.

  16. Al'amura sun fara komawa daidai a Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafofin yaɗa labarai a Iran sun ce gwamnati ta fara buɗe filayen jiragen sama a gabashin ƙasar yayin da sannu a hankali al'amura ke komawa daidai.

    An dawo da layukan intanet sannan shaguna ma suna buɗewa.

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a hukumance ya zarce ɗari shida. Sun haɗa da shugaban dakarun juyin juya hali na Iran da za a yi jana'izarsa a yau.

    Jibi Asabar kuma za a yi jana'izar sauran kwamandoji da ƙwararrun masana kimiyya da suka mutu.

    A Isra'ila, shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar, Mossad ya jinjinawa jami'ansa bisa namijin ƙoƙarin da ya ce sun yi.

  17. Ɓarnar da hotunan tauraron ɗan'adam suka nuna a tashoshin nukiliyar Iran

    ...

    Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna sabbin alamomi na ɓarna a titunan shiga da hanyoyin ƙaƙashin ƙasa na tashar sarrafa nukiliyar Iran da ke ƙarƙashin tsaunuka a Fordo.

    Ranar 23 ga watan Yuni ne Isra'ila ta kai wa cibiyar hari, kwana guda bayan Amurka ta saki bama-bamai masu tarwatsa ginin ƙarƙashin ƙasa a wurin.

    Ɓarnar da ba na gani ba a baya ta kuma bayyana a kusa da mashigar cibiyar ƙarƙashin ƙasa ta Tashar Fasahar Nukiliyar Isfahan bayan Amurka ta kai mata hari. Haka kuma akwai alamomi da ke yadda ake ta aiki don cike ramukan da hare-haren Amurka suka yi a cibiyar sarrafa yuraniyam ta Natanz.

  18. An kashe aƙalla mutum 16 a zanga-zangar Kenya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun ce aƙalla mutum 16 ne suka mutu, kuma 400 suka jikkata, yayin da aka kama 61 a zanga-zangar da aka gudanar a fadɗin Kenya jiya, domin tunawa da shekara daya da zanga-zangar adawa da ta biyo bayan ƙarin haraji da gwamnatin ƙasar ta yi da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

    Hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasar (KNCHR) ta ce ta tabbatar da mutuwar mutum 8 da harbin bindiga ya kashe a wurare kamar Machakos da Makueni da Kiambu da Nakuru da kuma Nyandarua.

    Amma rahoton Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa Amnesty Kenya ta ce mutum 16 ne suka mutu.

    An samu hargitsi da tarzoma a wurare da dama, ciki har da toshe hanyoyi da jifa da duwatsu da amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwa zafi da kuma yunkurin mamaye Majalisa dokokin ƙasar.

    Hukumar sadarwa dai ta hana watsa shirye-shirye kai tsaye, amma gidajen rediyo da talabijin sun ƙi bin umarnin.

  19. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Alhamis.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.