Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/10/2025.

Taƙaitattu

  • Latsa nan ku shiga tasharmu ta WhatsApp
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki
  • Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara
  • Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya
  • 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'
  • Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike
  • An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    A nan za mu tsaya da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya nuna mana.

  2. Isra'ilawa da ke hannun Hama sun kusa komawa gida - Wakilin Trump

    Jakadan musamman na Shugaba Trump a yankin gabas ta Tsakiya ya shaida wa dandazon magoya baya da 'yan uwan ragowar 'yan Isra'ila da Hamas ke ci gaba da garkuwa da su, a Tel Aviv cewa za a saki 'yan uwan nasu, su koma gida.

    Steve Witkoff ya bayyana hakan ne yayin da Hamas ke shirin sakin 'yan Isra'ilar arbain da takwas (48 ) - wadanda ke raye da wadanda suka mutu, a jibi Litinin, kamar yadda yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza ta tanada.

    Mr Witkoff ya yaba wa Shugaba Trump - wanda dandazon mutanen suka rika jinjina wa - amma kuma da yake yaba wa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu - sai dandazon mutanen suka rika yi masa ihu - da kuma jagororin Larabawa da ke da hannu a yarjejeniyar.

    Surukin Trump, Jared Kushner, da 'yar shugaban, Ivanka, su ma sun yi jawabi ga taron.

  3. Ana fargabar ƴanbindiga sun yi garkuwa da ƴansanda a Pakistan

    Ƴansanda a birnin Lahore na Pakistan sun ce an raunata jami'ansu sama da 100 a dauki-ba-dadi da mayaka masu ikirarin jihadi, wadanda ke kokarin shiga babban birnin kasar, Islamabad.

    Wani babban jami'in 'yansandan kasar ya ce, jam'iansu da dama sun bace, inda ake fargabar magoya bayan kungiyar Tehreek-e-Labbaik ta Pakista din, sun kama su.

    Kungiyar ta ce tana son gudanar da gangami ne na goyon bayan Falasdinawa a wajen ofishin jakadancin Amurka.

    An kuma raunata gomman masu zanga-zangar. Jami'an tsaro sun girke manyan sundukai ko kwantainoni a babban birnin kasar ta Pakistan domin toshe titunan shiga birnin, an kuma zuba karin masu sintiri.

    Gwamnati ta katse hanyoyin samun intanet ta waya a birnin na Islamabad da kuma mai makwabtaka, Rawalpindi.

  4. Tinubu ya yi afuwa ga Maryam Sanda wadda ta kashe mijinta Bilyaminu

    Maryam Sanda wadda kotu ta yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bayan samunta da laifin kashe mijinta mai suna Bilyaminu Bello na cikin gomman mutanen da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa afuwa.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce ƴanuwanta ne suka nema mata afuwar "domin ta kula da ƴaƴanta biyu, sannan kuma ta nuna halaye na ƙwarai a lokacin da take zaman gidan yari.

    Kotun ta ɗaure Maryam ne a gidan yarin Suleja, inda sanarwar ta ce zuwa yanzu ta yi shekara shida da wata takwas, amma yanzu ta faɗa cikin waɗanda shugaban ya cire daga cikin waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa, aka mayar da hukuncinsu ɗaurin rai da rai.

    A shekarar 2017 ne saɓani ya shiga tsakanin Maryam da mijinta Bilyaminu, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa, wanda hakan ya sa Mai shari'a Yusuf Halilu na babban kotun tarayya da ke Abuja ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 27 ga watan Janairun 2020 bayan samunta da hannu a mutuwar mijinta.

  5. Rikici ya fara zafi tsakanin Pakistan da Afghanistan

    Rikici ya ƙazance a tsakanin jami'an tsaron Pakistan da dakarun Taliban na ƙasar Afghanistan a bakin iyakar ƙasashen biyu.

    Rahotanni sun ce ƙasashen biyu suna gwabzawa ne da juna ta hanyar amfani da ƙananan makamai a yankin Kunar-Kurram.

    Rikicin ya yi zafi ne bayan hukumomin Taliban na Afghanistan sun zargi Pakistan da yin karan-tsaye kan ƴancin ƙasarsu ta hanyar ƙaddamar da hare-hare a bakin iyakar ƙasashen da ke Paktika.

    Pakistan dai ba ta ce komai ba kan zargin na kai hare-haren a cikin ƙasar ta Afghanistan.

    Sai dai Pakistan ta daɗe tana zargin Taliban da taimakon ƴan Taliban na ƙasar Pakistan suna kai mata hare-hare daga ƙasarta.

    Ko a bara, ƴan Taliban na Pakistan sun kai hare-hare da dama kan jami'an tsaron Pakistan.

  6. Me ya sa Trump zai ƙara lafta harajin kashi 100 kan kayayyakin China?

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai ƙara lafta harajin kashi 100 kan kayayyakin ƙasar China daga watan gobe.

    Trump ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya wallafa a shafukansa na kafofin sadarwa.

    Tun kafin wannan barazanar, Trump ya yi wani jawabin a ranar Juma'a inda ya caccaki matakin China na saka wasu dokokin kan fitar da duwatsu masu daraja daga ƙasar, lamarin da Trump ya zargi China da yunƙuri "na juya ƙasashen duniya."

  7. Harin jirgi mara matuƙi ya yi ajalin aƙalla mutum 12 a Sudan

    Sama da mutum 10 ne suka rasu bayan wani harin jirgi mara matuƙi a sansanin ƴan gudun hijira da ke birnin El-Fasher, babban birni a arewacin Dafur.

    An dai ɗaura alhakin harin ne kan dakarun RSF da ke gwabza yaƙi da sojojin gwamnatin ƙasar Sudan, yaƙin da ya ci rayukan mutane da dama.

    Harin ya sauka ne a sansanin na ƴan gudun hijira da ke Jami'ar El-Fasher a daren ranar Juma'a, wanda ya tarwatsa mutanen da ke samun mafaka.

    Rahotannin kwamitin mazauna sansanin ya nuna cewa akwai yiwuwar kusan mutum 60 ne suka rasu, amma jaridar Reuters da wasu hukumomin duniya sun ce mutum 12 ne suka tabbatar da mutuwarsu a harin.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla mutum 250,000 ne suke zaune a El-Fasher inda suke rayuwa cikin tsananin buƙatar abinci da ruwan sha, sannan ta yi gargaɗin cewa ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula na iya zama laifin yaƙi.

  8. Dubun dubatar masu goyon Falasɗinawa na zanga-zanga a Landan

    Dubun dubatar mazauna birnin Landan na zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa da yin tir da hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza.

    Zanga-zangar da aka saba yi duk ranakun ƙarshen mako, ta wannan makon na zuwa ne yayin da dakarun Isra'ilar suka janye daga sassan Gaza bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta ranar Juma'a.

    Sai dai masu zanga-zangar goyon bayan Isra'ila ma sun fito, amma 'yansandan birnin sunn saka iyaka tsakanin ɓangarorin biyu domin kauce wa rikici.

  9. Yadda Tinubu yake facaka na nuna bai damu da talaka ba - Dino Melaye

    Wani babban ɗan adawa daga jam'iyyar haɗaka ta ADC ya ce har yanzu 'yan Nijeriya suna mutuwa sanadin yunwa da matsin rayuwar da manufofin Tinubu suka jefa su.

    Sanata Dino Melaye ya yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu bai cika ko ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗaukar wa al'umma ba.

    Tsohon ɗan majalisar dattijan ya zargi shugaban Nijeriya da kashe-kashen kuɗi na facaka ta hanyar sayen jirgin ruwan alfarma da danƙareren jirgin sama da kuma motar da babu irinta.

  10. Hamas ta kira dakarunta 7,000 domin aikin tsaro a Gaza

    Ƙungiyar Hamas ta kira dakarun tsaronta 7,000 domin aikin bayar da tsaro a Zirin Gaza bayan ficewar dakarun Isra'ila sakamakon fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Matakin ya ƙunshi naɗa gwamnoni biyar masu ƙwarewa a aikin soji, daga cikinsu har da kwamandojinta, kamar yadda majiyoyi daga yankin suka bayyana.

    An ruwaito cewa an bayar da umarnin naɗin ne ta saƙon tas da kiran waya da ke cewa: "Muna sanar da kiran mambobi ne domin amsa kiran yi wa ƙasa da addini hidima na kawar da masu laifi da kuma waɗanda suka taimaka wa Isra'ila. Dole ne ku je wurin aikinku cikin awa 24 ta hanyar amfani da lambobinku."

    Tuni wasu masu gadin Hamas suka hau titunan Gaza, wasu da kayan gida, wasi sanye da kakin 'yansandan Gaza.

    Batun wanda zai mulki Gaza na cikin muhimman abubuwan da za a tattauna a kai domin kawo ƙarshen yaƙi baki ɗaya.

  11. An zaƙulo gawar Falasɗinawa 150 daga ɓaraguzai zuwa yanzu

    Hukumar tsaron fararen hula a Gaza ta ce Falasɗianwa 300,000 ne suka koma Birnin Gaza tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Ku san mutum 700,000 ne suka tsere daga yankin sakamakon hare-haren Isra'ila.

    Ta ce zuwa yanzu ta yi nasarar zaƙulo gawar mutum 150 daga ƙarƙashin ɓaraguzai a Birnin na Gaza.

    Hukumar Ta ce akwai jimillar mutum 9,500 da ke ƙarƙashin ɓaraguzan a fadin zirin.

    Kazalika, ta ce ta samu kiran gaggawa 75 tun daga asubahin yau Asabar, inda ta nemi ƙungiyar Red Cross ta haɗa kai da Isra'ila domin taimakawa wajen gano mutanen da suka ɓace saboda ba ta da kayan aikin lalubo mutanen da aka kashe.

  12. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'yanbindiga biyar a jihar Borno

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yanbindiga biyar a jihar Borno da ke arewacin ƙasar ranar Juma'a bayan wani samame.

    Kakakin rundunar Operation Hadin Kai ta sojojin ƙasar, Kanar Sani Uba, ya ce dakarunsu sun fafata da mayaƙa 24 da ke tafe a ƙafa ne a yankunan Magumeri da Gajiram.

    Sanarwar da Kanar Sani ya fitar ta ce sun yi nasarar kashe biyar da kuma ƙwace kuɗi naira miliyan biyar.

    "An hangi 'yanta'addan na cinna wa gidaje wuta da kuma kai wa mutane hari...kuma nan take dakaru suka far musu, inda suka gudu zuwa ƙauyen Damjiyakiri," in ji sanarwar.

    "Bayan awa huɗu ana bin sawunsu, dakaru sun ƙaddamar da hari a kansu, inda aka kashe 'yanta'adda biyar daga cikinsu sauran 19 suka tsere da raunuka."

    Ya ƙara da cewa sauran abubuwan da dakarun suka ƙwace har da bindiga ƙirar AK-47, da adakar harsashi biyar, da wayar salula ɗaya, da wuƙa ɗaya.

  13. Isra'ila ta kai hare-hare a kudancin Lebanon cikin dare

    Isra'ila ta kai hare-hare ta sama a kudancin Lebanon cikin dare, kamar yadda rundunar sojin sojin ƙasar ta IDF ta bayyana.

    "Da tsakar dare, IDF ta kai hari tare da lalata kayan aikin Hezbollah a kudancin Lebanon," in ji rundunar.

    Kafar yaɗa labarai a Lebanon ta ambato ma'aikatar lafiyar ƙasar na cewa harin da aka kai a al-Msayleh ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da raunata wasu bakwai.

    Rikici ya yi ƙamari tsakanin Hezbollah da Isra'ila tun bayan harin Hamas na watan Oktoban 2023, inda suka gwabza yaƙi kafin ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Nuwamban 2024.

    Sai dai Isra'ila na ci gaba da karya ƙa'idojin yarjejeniyar ta hanyar kai hare-hare lokaci zuwa lokaci a kudancin Lebanon, inda nan ne tungar Hezbollah.

  14. Hannayen jarin Amurka da kuɗaɗen kirifto sun faɗi saboda barazanar Trump ta ƙaƙaba wa China haraji

    Hannayen jarin Amurka da kuɗaɗen intanet na kirifto sakamakon barazanar Shugaba Trump ta sanya haraji kan kayayyakin China.

    Bitcoin ya faɗi da sama da kashi 10 cikin 100, kodayke ya ɗan farfaɗo daga baya.

    Haka ma sauran kudin kirifto sun faɗi sakamakon sanarwar Trump ɗin, wadda ta biyo bayan yunƙurin China na tsaurara dokoki kan fitar da ma'adanai masu daraja zuwa Amurkar.

  15. 'Yansanda sun ceto mutum 10 daga hannun 'yanfashi a Kaduna

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce ta ceto mutum 10 da 'yanbindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Kagarko tun a wata huɗu da suka wuce.

    Wata sanarwa da kakakin rundunar DS Mansir Hassan ya fitar ta ce daga cikin mutanen akwai yara masu shekaru ɗaya, da uku, da kuma 13.

    Sanarwar ta ce 'yanbindigar sun sace mutanen ne daga gidajensu lokacin da suka kai hari ƙauyen Kushe Makaranta kuma suka kai su dajin da ke kusa da Rijana.

    Ya ce aikin ceton na haɗin gwiwa ne tsakanin dakarunsu, da na rundunar farin kaya ta DSS, da kuma sojojin Najeirya.

  16. An fara zaƙulo Falasɗinawa daga ɓaraguzai bayan janyewar Isra'ila a Gaza

    Jami'an agaji na ci gaba da zakulo gawawwakin mutane daga ɓaraguzan gini a Gaza yayin da janyewar dakarun Isra'ila ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a ranar Juma'a.

    An kiyasta cewa mutum 200,000 ne suka koma gidajensu a yankin arewaci zuwa yanzu. Da dama sun ce sun kaɗu matuƙa da irin girman ɓarnar da aka yi.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya kara bayar da tabbacin cewa za a mutunta jarjejeniyar, yana mai cewa "dukkaninsu sun gaji da yaƙin, wannan lamari ya sha gaban Gaza, wannan zaman lafiya ne a Gabas ta Tsakiya.

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce za ta shigar da kayan agaji cikin Gaza, kodayake ba za su wadata ba.

    Yanzu mataki na gaba shi ne Hamas ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su, Isra'ila kuma ta sako ɗaruruwan Falasdinawan da ta kama.

  17. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da hantsin Asabar.

    Ni ne Umar Mikail zan kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya - zuwa ƙarfe 4:00.

    Ku biyo mu.