Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/12/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Jama'a mun kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye, sai kuma gobe Juma'a ida Allah ya nuna mana.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. 'Tsananin sanyi a Gaza ne dalilin mutuwar ƴata'

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Mahaifiyar wata yarinya 'yar wata takwas da ke sansanin gudun hijira a Gaza ta shaida wa BBC cewa jaririyarta ta mutu sakamakon tsananin sanyi da ruwan sama mai karfi.

    Hijr Ibrahim Abu Jazar ta ce ta tashi ta tarar da ‘yarta Rahaf ba ta numfashi, kuma ta kankare. Ta ce Rahaf ta dan samu lafiya, amma tana fama da rashin issashen abinci mai gina jiki.

    An samu ambaliya a daruruwan tantunan da ke bai wa iyalan da suka rasa matsugunansu mafaka, sakamakon ruwan da ake yi kamar da bakin kwarya a kwanaki biyun da suka gabata a Gaza.

  3. Dole ƙasashen turai su fara shirin yaƙi - NATO

    Nato

    Asalin hoton, EPA

    Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO ya yi gargadin cewa wajibi ne kasashen kungiyar su shirya wa yaki a wani mataki kwatankwacin wanda kakanninsu suka fuskanta.

    Da yake gabatar da wani zazzafan jawabi a birnin Berlin, Marka Rutte ya ce mutane da dama na nuna halin ko-in-kula game da barazanar Rasha.

    Ya ce a lokacin da na zama sakatare janar na NATO a bara, na yi gargadin cewa abin da ke faruwa a Ukraine zai iya faruwa da kasashe kawayen Ukraine.

    Mark Rutte ya kuma yi kira ga kasashen Turai su yi gagagwar kara kudaden da suke kashewa a fannin tsaro.

  4. Akwai sauran rina a kaba kan kawo ƙarshen yaƙinmu da Rasha - Zelensky

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine Zelensky, ya ce akwai sauran batutuwa biyu da ba a daddale su ba a tattaunawar da suke yi da Amurka, game da kudurin zaman lafiya.

    Sun hada da matsayin wasu yankunan Donetsk da har yanzu ke karkashin ikon Ukraine, da kuma makomar tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia.

    Amurka dai na ci gaba da nazari kan Kudurin zaman lafiyar da Ukraine ta gabatar, wadda ta samar tare da hadin gwiwar manyan kasashen Turai.

    Mista Zelensky ya jaddada cewa, duk wani mataki na batun sallama yanki da aka amince da shi a karshe, to dole ne sai an gabatar wa yan Ukraine domin a yi zaben raba gardama.

    Wakilin BBC ya ce Zelensky ya ce Amurka na matsawa Ukraine lamba ta janye daga yankin Donbas, wani yanki da Rasha ta kusa mamaye wa.

  5. Gwarazan Hikayata ta 2025 su uku

    Hikayata

    Wannan hoto ne na gwarazan Hikayata ta bana su uku. Ta ɗaya ita ce Fadlia Lamiɗo sai ta biyu Jamila Lawal Zango, sai ta uku Hafsat Sani Tanko.

  6. Jamila Lawal Zango ce ta biyu a gasar Hikayata

    Hikayata

    Jamila Lawal Zango ce ta zo ta biyu a gasar Hikayata ta bana.

    Jamila ƴar asalin Zaria ce a jihar Kaduna. Ta zo ta biyu ne da labarinta na "Gobena."

    An haife ta ne a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2000.

  7. Fadhila Lamiɗo ce gwarzuwar gasar Hikayata ta 2025

    Hikayata

    Wadda ta zo ta ɗaya a wannan gasar ta Hikayata ta bana ita ce Faɗila Lamiɗo daga jihar Kaduna.

    Ta yi karatu a Kaduna, inda take da shaidar difloma, kuma matar aure ce da ƴaƴa.

    Labarin "Tsalla Ɗaya" da marubuciyar ta rubuta ne ya zama gwarzon Hikayata ta bana.

    Ta samu kyautar naira miliyan ɗaya da shaidar karramawa.

    An haife ta ne a ranar 10 ga watan Nuwamban shekarar 1996 a jihar Kaduna.

  8. Hafsat Sani Tanko ta zo ta uku

    Hikayata

    Marubuci Hafsat Sani Tanko ce ta zo ta uku a gasar Hikayata ta bana.

    Hafsat ƴar Jihar Kano ce kuma ta zo ta uku ne da labarinta mai suna "Samarin Shawo."

    An haife ta ne a 22 ga watan Yunin shekarar 1999 a jihar Kano.

  9. Yadda aka tantance labaran Hikayata ta bana

    Hikayata

    Game da yadda aka tantance tare da fitar da gwarazan da labaransu suka fi inganci, shugabar kwamitin alƙalan gasar, Farfesa Asabe Kabir ta ce sun yi aiki cikin tsanaki ne wajen fitar da su.

    A cewarta, bayan marubuta da dama da suka shiga gasar, "sai aka zaɓa wasu guda 30. Sai alƙalai mu uku muka zauna muka tantance, muka zaɓi guda uku."

    Ta ce sun tantance labaran ne ba tare da sani kowace marubuciya ba, "sannan mu kanmu alƙalan ba mu taɓa haɗuwa ba."

    Ta ce a ƙarshe sun yi taron ƙarshe ne ta intanet, domin tantance tare da cire na farko da na biyu da na uku.

  10. Hikayata: Muhawara kan ilimin mata

    Hikayata

    A yanzu haka ana tattaunawa ne kan muhimmancin ilimin ƴaƴa mata, inda Farfesa Abdullah Uba Adamu da Rahama Abdulmajid da Dr Ibrahim Sheme da Fatima Zahra Umar suke tattaunawa.

    A cewar Rahama, daga cikin abubuwan da suka janyo taɓarɓarewar ilimin mata a arewa, akwai rashin mayar da hanakli, inda a cewartsa, maza suna tunanin rashin ilimin mace ya fi muhimmanci.

    A nasa jawabin, Sheme cewa ya yi, "ina so in kalla abin ta fuskar al'ada. Asali Bahaushe har mazan ma bai yarda su yi karatu ba, da ƙyar aka fara amincewa."

    Ya ce bayan wannan ma akwai matsalar tsaro da talauci da suke taka rawa wajen daƙile karatun.

    Fatima Zahra Umar, a cewarta kusan kashi 60 na mutanen duniya mata ne, amma ta yi zargin an killace su, inda a cewarta ba sa samun wakilci wajen ɗaukar matakai masu muhimmanci.

    Abdallah Uba ya ce ya ce a jami'ar BUK da yake koyarwa, kusan kashi 90 na ɗaliban da yake koyarwa mata ne, sannan ya ƙara da cewa al'adar Bahaushe yana son mata masu cikakkiyar biyayya ne, wanda hakan ya sa suke ɗar-ɗar da karatun mata.

    Hikayata
  11. Yadda taron karrama gwarazan Hikayata ke wakana

    Hikayata

    Yanzu haka taro ya fara nisa na karramawa gwarazan gasar Hikayata ta bana.

    Ga wasu hotuna nan na yadda taron ke wakana.

    Hikayata
    Hikayata
  12. Abin da ya sa aka kirkiri gasar Hikayata - Jimeh Saleh

    Jimeh

    A yau, Alhamis 11 ga watan Disamba ne aka gudanar da bikin karrama gwarazan gasar gajerun labarai ta Hikayata wanda sashen Hausa na BBC ke shiryawa.

    A wajen taron, tsohon shugaban sashen Hausa na BBC, Jimeh Saleh ya ce an kirkiri gasar ne domin karfafa gwiwar marubuta mata tare da fito fasaharsu.

    Ya ce yana alfahari da tare da farin cikin ganin wannan shekarar da gasar ta cika shekara 10, sannan ya ce labaran da ake turowa za su yi kyau wajen shirya fina-finai, sannan ya ce tuni an nazarci labarai da nasarorin gasar a jami'o'i.

  13. Bikin Hikayata ya ɗauki harama

    Hikayata
    Bayanan hoto, Badariyya Kalarawi ce mai gabatarwa a taron

    Bikin gasar Hikayata - ta gajeru kuma ƙagaggun labarai cikin harshen Hausa - ya ɗauki harama a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Wannan ne karo na 10 da ake gudanar da gasar domin bai wa mata zalla damar nuna bajintarsu ta ƙirƙira a fannin adabi.

    Ku biyo mu a wannan shafi domin sanin yada bikin ke gudana.

  14. Austria na son saka dokar hana yara mata sanya ɗankwali a makarantu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Austria ta kada kuri’ar amincewa da wata doka da ke neman haramta wa mata ‘yan ƙasa da shekara 14 rufe kansu da dankwali a makarantun ƙasar.

    Gwamnatin haɗaka mai ra’ayin mazan jiya ce ta gabatar da ƙudurin tun farkon wannan shekarar, inda ta bayyana cewa matakin zai kare ‘yan mata daga cin zarafi ko wariyar da ka za su iya fuskanta.

    Sai dai jam’iyyar adawa ta Green ta ƙi goyon bayan dokar, tana mai cewa hakan ya saɓawa ƙundin tsarin mulki.

    Haka kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun soki matakin, wanda ya shafi duk wani nau’in mayafi na musulunci.

    A shekarar 2019, wata kotu a ƙasar ta soke yunkurin gabatar da irin wannan doka da ta haramta sanya dankwali a makarantun firamare.

  15. FRSC ta tabbatar da mutuwar ɗaliban jami'ar Jos 8 a haɗarin mota

    ...

    Asalin hoton, FRSC/FACEBOOK

    Hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya, FRSC a jihar Filato ta tabbatar da mutuwar daliban jami’ar Jos takwas sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya ritsa da su.

    Hadarin dai ya auku ne da misalin karfe biyu na dare a akan titin zuwa Zaria a birnin Jos inda wasu da dama suka jikkata.

    FRSC ta ce hadarin ya faru ne yayin da motar da ɗaliban ke ciki ta yi taho-mu-gama da wata motar kaya, lamarin da ya janyo mummunan lahani.

    Rahotanni sun ce ɗaliban na kan hanyarsu ta komawa ɗakunan kwanansu bayan fitowa daga shaƙatawar dare lokacin da abin ya faru.

    Ana dai cigaba da kula da wasu ɗalibai biyu da suka tsira daga hatsarin bayan an garzaya da su zuwa wani asibiti mafi kusa domin samun kulawar gaggawa.

    FRSC ta ce an fara bincike don gano ainihin musabbabin faruwar wannan mummunan haɗari, tare da kira ga direbobi da su rika tuki cikin natsuwa musamman a lokutan dare domin guje wa irin haka.

  16. Harin jiragen sojin Myanmar a asibiti ya kashe fiye da mutum 30

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 34 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan harin da jiragen sama na sojin Myanmar suka kai wa wani asibiti a yammacin ƙasar a daren Laraba, in ji majiyoyi daga ƙasa.

    Asibitin yana cikin garin Mrauk-U a jihar Rakhine, wani yanki da rundunar Arakan ke iko da shi, wanda shi ne wurin da ƙungiyoyin ƴanbindiga na ƙabilu ke fafutukar yaƙi da mulkin soja na ƙasar.

    Dubban mutane sun mutu kuma miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu tun bayan da sojojin suka ƙwace mulki a juyin mulkin 2021 wanda ya haifar da yaƙin basasa.

    A ‘yan watannin da suka gabata, sojojin sun ƙara yawan harin jiragen sama don karɓar yankuna daga hannun ƙungiyoyin ƴanbindiga na ƙabilu

    Sojin Myanmar ba su yi wani bayani kan harin ba, wanda ya zo yayin da ƙasar ke shirin gudanar da zaɓe a ƙarshen wannan watan – zaben farko tun bayan juyin mulki.

    Khaing Thukha, mai magana da yawun rundunar Arakan, ya shaida wa BBC cewa mafi yawan wadanda suka mutu su ne marasa lafiya da ke asibitin.

  17. EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige

    ...

    Asalin hoton, Federal Ministry of Labor Twitter

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, ta tsare tsohon ministan ƙwadago kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Chris Ngige.

    Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe, ya tabbatar da tsare shi da safiyar ranar Alhamis, bayan wasu rahotanni da aka yaɗa cewa an sace shi.

    Chukwuelobe ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Ngige yana tare da EFCC. Ba a sace shi ba.”

    Har zuwa yanzu, EFCC ba ta bayyana dalilin tsare Ngige ba amma kuma ana sa ran hukumar za ta fitar da cikakken sanarwa kan tsare shi da binciken da take yi a kansa.

    Ngige ya zama mutum na biyu daga cikin tsoffin ministocin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da aka tsare a kwanan nan. Kafin shi, an fara tsare tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, wanda shima yake hannun EFCC.

  18. Sabuwar tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Ukraine na iya janyo ɓata lokaci - Trump

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump na Amurka ya ce sabuwar tattaunawa da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da kuma sauran shugabannin Turai kan ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙi da Rasha, na iya janyo bata lokaci.

    Da yake magana a fadarsa ta White House, Trump ya ce ya tattauna ta waya da shugabannin ƙasashen Birtaniya da Jamus da kuma Faransa, inda ya ce ya yi musayar abin da ya kira kwararan bayanai.

    Ya ce har yanzu bai yanke shawara kan buƙatarsu ta yin wata sabuwar ganawa ba.

    Tun da farko a yau jami'an Ukraine sun ce sun miƙa shawarwarinsu ga gwamnatin Amurka kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin - shawarwarin da suka hada da sake duba shirin Amurka na farko - shirin da, da zai kunshi cewa Ukraine ta sallama wani yankinta da Rasha ba ta kama ba.

  19. Yadda kisan mata a Adamawa ke jan hankali a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Fresh Air Online TV

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'Adama ta Amnesty Internaltional ta buƙaci a gudanar da bincike na gaskiya, domin hakkake abin da ya auku, dangane da zargin kisan mutum tara da raunata wasu da dama da aka yi, yayin da wasu mata suka gudanar da wata zanga-zangar lumana a garin Lamurde na jihar Adamawa, ta Najeriya, ranar Litinin da ta gabata.

    Wannan kira ya biyo bayan zargin da ake ta yi ne, cewa sojoji ne suka buɗe wuta kan matan da ke zanga-zangar lumanar, amma kuma hukumomin sojan na musanta zargi.

    Yanzu dai, baya ga alhini da zaman makoki da ake yi, an shiga ja-in-ja, dangane da wanda ake zargin ya yi harbin bindiga da ya kashe matan, kuma ya raunata wasu da dama, yayin da suke gudanar da zanga-zangar.

    A tattaunawarsa da BBC daraktan ƙungiyar ta kare hakkin bil'Adaman ta Amnesty International a Najeriya Isa Sanusi ya ce tun daga lokacin da abin ya faru suke bin diddigi: ''Tun daga ranar Litinin da wannan abu ya faru, muna bin didddigin wannan lamari.

  20. Venezuela ta zargi Amurka da sata da kuma fashin teku

    ...

    Venezuela ta zargi Amurka da sata karara da kuma fashin teku bayan da dakarun Amurkan suka kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a gabar tekun Venezuela din.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce matakin wani shiri ne na lalata arzikin makamashi na Venezuela da gangan.

    Sai dai jami'an Amurka sun ce jirgin ruwan yana safarar man da aka sanya takunkumin sayar da shi ne zuwa Iran kuma kudin da ake samu daga cinkin ana taimaka wa kungiyoyin ta'addanci ne.

    Lamarin ya kasance ƙarin wata sabuwar dambarwa ta matsin lambar da Amurka ke yi wa shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro - mai ra'ayin gurguzu.

    Mai dai shi ne babbar hanyar samun kudade na kasar ta Venezuela