Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/12/2025.

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. An tsare tsohon ministan jamhuriyar Benin kan zargin juyin mulki

    Rahotanni daga Jamhuriyar Benin sun ce an tsare tsohon ministan tsaron ƙasar, Candide Azannai gabanin kammala shari'ar da ake ta zarginsa da hannu a yunƙurin juyin mulki a farkon watan nan.

    Ofishin dillancin labaran Faransa ya ce ana zarginsa da yi wa ƙasa zagon ƙasa da kuma tunzura bore.

    Mako ɗaya kenan da aka kama shi a hedikwatar jam'iyyarsa da ke kudancin birnin Cotonou.

    Mr Azannai ya yi Allah wadai da yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Patrice Talon, inda aka kashe mutane da dama.

    Tuni aka ɗaure mutane 30, mafi yawan su sojoji, inda ake zargin su da cin amanar ƙasa.

  2. Dubban mutane na zanga-zanga kan kisan shugaban ɗalubai a Bangladesh

    Bangladesh

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban mutane sun halarci jana'izar wani fitaccen shugaban ɗalubai da aka kashe, a birnin Dhaka na Bangladesh.

    An Sharif Osman Hadi ne a kai lokacin da ya ke dawowa daga sallar Juma'a, kuma ya rasu bayan jinyar kwana shida a wani asibiti a Singapore.

    Mummunar zanga-zanga ta ɓarke a birnin Dhaka, inda aka shafe kwana biyu ana yin ta.

    An jibge sojoji da ƴansanda domin daƙile yunƙurin tayar da tarzoma.

    Gwamnati ta sanar da zaman makoki na kwana ɗaya amma magoya bayan Hadi sun ci gaba da zanga-zanga a dandalin Dhaka.

    Shugaban hukumar kare ƴancin ɗan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya yi kiran a gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano masu hannu a kisan Hadi

  3. Kotu ta sake ɗaure Imran Khan da matarsa

    Imran Khan

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Pakistan ta yanke wa tsohon firaiminista Imran Khan da matarsa Bushra Bibi hukuncin ɗaurin shekara 17 kan laifin karɓar kyauta daga dukiyar ƙasar a lokacin da suke mulki.

    Hukuncin na yanzu ƙari ne kan wanda dama can aka yanke wa mutanen biyu, kuma hakan na nufin za su yi zaman yarin ne a jere.

    Imran Khan ya ce tuhumar da ake masa ba wani abu bane illa siyasa.

    Daga laifin da aka same su da shi harda karɓar kyautar sarƙar da Bushra Bibi ta yi daga yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, a 2021.

    Lauyoyin Khan sun ce za su ɗaukaka ƙara.

  4. Tinubu ya yi barazanar tura wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye

    TINUBU

    Asalin hoton, Tinubu X

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin ƙasar su yi biyayya ga umarnin kotun ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancin tafiyar da kuɗaɗensu.

    Shugaban ya yi gargaɗi gwamnonin da ba su biyayya ga umarnin su sani cewa za su tilasta mashi zartar da wata doka da za ta ba shi ikon aikewa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun kwamitin rabon arzikin tarayya.

    Tinubu ya yi gargaɗin ne a wajen taron majalisar zartarwar jam'iyyar APC karo na 15 a Abuja.

    “Kotun ƙoli ta bayar da umarni gare ku, inda ta ce ku bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye. Idan kuka jihar har sai na yi amfani da dokar shugaban ƙasa, domin wuƙa da doya duk suna hannuna, to zan yanke ta.

    “Ina matuƙar mutumta ku ne kawai, a matsayin gwamnonina. Amma idan ba ku fara aiwatar da wannan umarni daki-daki ba. za ku ga abin da zai faru,'' in ji Tinubu. .

    A ranar 11 ga watan Yulin 2024 kotun ƙoli ta bayar da hukuncin da ya tabbatar da wanda buƙatar gwamnatin tarayya ta bai wa ƙananan hukumomin Najeriya ƴancin tafiyar da kuɗaɗensu.

    Dukkan alƙalan kotun bakwai sun amince da hukuncin cewa riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi ke yi ya saɓawa tanadin kundin mulkin ƙasa.

  5. Joshua ya doke Paul a Miami

    Anthony Joshua ya doke Jake Paul a zagayer na shida na karawar su a birnin Miami

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan danben Birtaniya, Anthony Joshua ya doke Jake Paul a zagaye na shida na karawar da suka yi a birnin Miami na Amurka.

    Joshua ya sha fama da Paul a karawar, saboda tsohon ɗan YouTube ɗin ya ƙi tsayawa a kara, inda ya riƙa tsalle-tsalle yana ja da gefe, amma daga baya Joshua ya gano makasar shi har ya kifar da shi sau biyu a zagaye na biyar.

    Paul ya sake faɗuwa a farkon zagaye na shida, kafin daga baya Joshua ya yi mashi nushi mai ƙarfin gaske da hannun dama, lamarin da ya kawo ƙarshen fafatawar da aka yi a cibiyar Kaseya ta birnin Miami.

    A karshen karawar Joshua ya ce "Ina ganin wannan ba abin da na yi zato bane, ban yi bajinta ba," in ji ɗan damben mai shekara 36.

    Ya ƙara da cewa "A ƙarshe dai abin da ake muradi shi ne sanya Jake Paul a tsaka mai wuya kafin kifar da shi. An ɗauki lokaci kafin hakan ta samu, amma daga ƙarshe dai an kai wajen da ake son kaiwa."

    Dama dai an yi hasashen sakamakon damben zai zamo haka, amma an yi mamakin yadda aka ɗauki tsawon lokaci ana fafatawa kafin Joshua ya doke Paul ba.

    Joshua ya yi nasarar lashe wasa na 29 kenan daga cikin 33 da ya fafata a rayuwarsa ta dambe, kuma a yanzu zai mayar da hankali ne ga babban ƙalubalen da ke gabansa, na karawa da Tyson Fury a shekara mai zuwa.

  6. Rundunar sojin Amurka ta kai jerin hare-hare kan kungiyar IS a Syria

    Jirgin yaƙin Amurka da wani soja yana loda makamai

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka ta kai wasu jerin hare-hare a kan kungiyar IS a cikin Syria, a matsayin martanin kisan sojojinta biyu.

    Rundunar sojin Amurkar ta ce, an kai harin kan wurare sama da 70, da jiragen sama na yaki, da masu saukar ungulu da kuma makaman atilare.

    Mouaz Moustafa babban darektan wata kungiyar kamun kafa ta Syria da ke Amurka ya ce da alamu wasu hare-haren za su biyo baya:

    Ya ce, lalle za a ci gaba da ganin matakin Amurka da ma na gwamnatin Syria musamman a yankin Baadiya.

    Shugaba Trump ya ce kamar yadda ya yi alkawari, Amurka na mayar da martani mai tsanani - kuma gwamnatin Syria da Ahmed al Sharaa ke jagoranta na bayar da cikakken goyon baya.

  7. Kotun Brazil ta bai wa Bolsonaro damar zuwa asibiti

    Bolsonaro

    Asalin hoton, ANDRE BORGES/EPA/Shutterstock

    Kotun ƙolin Brazil ta bai wa tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro dama ta dan lokaci ya bar kurkutu a Brasilia domin ya je asibiti.

    Ana sa ran yi wa Mista Bolsonaro tiyata, amma kuma ba a sanya ranar da za a yi masa aikin ba.

    Kotun ta zartar da hakan ne bayan da ƴansanda suka tabbatar da cewa lalle, tsohon shugaban, yana bukatar a duba lafiyarsa, ba da wani jinkiri ba.

    Bolsonaro na zaman gida yari ne na shekara 27 bayan da kotu ta same shi da laifin shirya juyin mulki lokacin da ya fadi zaben shugaban kasar Brazil din a 2022.

    Majalisun dokokin kasar biyu ta dattawa da ta wakilai sun amince da zaftare masa yawan shekarun hukuncin amma sai shugaban kasar na yanzu, Luiz Inácio Lula da Silva wanda abokin hamayyarsa ne ya amince tukuna.

  8. Assalamu alaikum

    Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Asabar daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.