Chelsea ta kai wasan ƙarshe a gasar FA
Enzo Fernandez ne ya ci ƙwallo da Chelsea ta kai wasan karshe a FA Cup, bayan doke Leeds United 1-0 a Wembley ranar Lahadi.
Ƙungiyar Stamford Bridge ta samu wannan damar kwana huɗu tsakani da korar kociya, Liam Rosenior, saboda kasa samun nasarorin da ake bukata.
Chelsea, wadda ke fama da koma baya ta yi wannan namijin kokarin karkashin kociyan riƙon kwarya, Calum McFarlane da zai yi aiki zuwa karshen kakar bana.
Leeds ta sa ran za ta yi wani abun, ganin wasa na uku da ta fuskanci Chelsea da yin nasara 3-1 cikin watan Disamba a Elland Road da yin 2-2 a karawa ta biyu a Stamford Bridge a Premier League a bana.
Yanzu Dai Chelsea za ta sake komawa Wembley ranar 16 ga watan Mayu, domin buga wasan karshe da Manchester City, wadda ta yi waje da Southampton 2-1 ranar Asabar.