Wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Oyo ta Ibadan, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a A. L. Akintola, ta amince wa jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taronta da aka tsara yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025 a filin wasa na Lekan Salami Stadium, Adamasingba, Ibadan.
A hukuncin, kotun ta umarci jami’an PDP da wakilanta da su guji duk wani yunƙuri na dakile ko karya jadawalin da aka riga aka fitar dangane da babban taron.
Jam’iyyar ta sanar da hakan ne a shafin sada zumuntarta na Facebook.
Mai Shari’a Akintola ya ƙara da bayar da umurni ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta tura jami’anta domin sa ido da lura da dukkan abin da ke gudana a taron.
Wannan mataki, a cewarsa, "Zai tabbatar da cewa an bi doka da ka’idojin gudanar da zaɓe tare da inganta gaskiya da bayyana gaskiyar abin da ke faruwa a lokacin taron."
Kotun kuma ta ba da umurni ga Umaru Ahmadu Fintiri, wanda shi ne shugaban kwamitin shirya taron, da ya ci gaba da dukkan shiri da ya shafi gudanar da babban taron.
Wannan hukuncin ya cire duk wasu matsalolin doka da ke ƙoƙarin jinkirta gudanar ta taron.
Jam'iyyar ta ce wannan mataki babbar nasara ce ga jam’iyya, domin yanzu kwamitin shirya taron NCOC na da damar kammala shirye-shiryen karɓar sama da wakilai 3,000 da ake sa ran halartarsu daga jihohi daban-daban.