Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 16 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Mohammed

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Ƙasashen Larabawa da Turai sun yi Allah wadai da shirin Isra'ila na faɗaɗa matsunai a Gaɓar Yamma

    Ƙasashen Larabawa da ƙungiyar Tarayyar Turai sun yi Allah wadai da shirin Isra'ila, na ci gaba da shirinta na yi wa wasu sassan Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye rijista, a matsayin yankunan ƙasar.

    Wannan matakin zai bayar da damar faɗaɗa matsugunan Yahudawa a yankin Falasɗinu.

    Haka kuma matakin zai sa a soke ɗaɗaɗɗiyar dokar da ta hana waɗanda ba musulmai ba mallakar fili a Gaɓar Yamman.

    Ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen Isra'ila ta kare matakin da cewa shirin zai samar da tsari a yankin.

    Sai dai wasu ministocin ƙasar da dama sun bayyana matakin a matsayin yunƙurin ƙarfafa ikonsu a yankin.

  3. Hotunan ɓarnan gobarar Kasuwar Singa

    Hoton gobarar Kasuwar Singa

    Ƴan kasuwar Singa na ci gaba da alhihin asasar da syuka tafka sakamakon mummunar gobara da ta tashi a kasuwar.

    Hotunan Gobara

    Gobarar wadda ta tashi a maraicen ranar Asabar ta kai kai har ranar Lahadi ba ta mutu ba.

    Mutane

    Ma'aikatan kashe gobara da masu taimako sun ɗauki dogon lokaci suna ƙoƙarin kashe wutar.

    mutane

    Shugaban kasuwar, ya shaida wa BBC cewa gobarar ta shafi shaguna fiye da 1,000

    Mutane

    Kasuwar Singa da ke jihar Kano, ta yi fice wajen sayar da kayan masarufi

  4. Ƴankishin ƙasar Zimbabwe sun ƙalubalanci shirin tsawaita wa'adin Mnangagwa

    Wata ƙungiyar tsofaffin masu yaƙin neman ƴancin kai a Zimbabwe sun shigar da ƙara kotu domin ƙalubalantar shirin gwamnati na tsawaita wa'adin mulkin shugaba Emmerson Mnangagwa.

    An wallafa wata sanarwa a majalisar dokokin ƙasar da ke tabbatar da gabatar da ƙudurin dokar, wadda ta ƙunshi sauya kundin tsarin mulki.

    Sauyin zai bai wa Mista Mnangagwa, mai shekara 83 damar ci gaba da kasancewa kan karagar mulki har 2030.

    Idan an amince da sabuwar dokar, za ta soke babban zaɓe na gaba, wanda aka tsara yi nan da shekara biyu.

    A ƙarƙashin sabuwar dokar, ƴan majalisa ne za su zaɓi shugaban ƙasa na gaba, a maimakon alummar ƙasar.

  5. Hotunan bikin karɓar gwamnan Kano a APC

    Abba da Shettima da Barau da wasu manyan APC a Kano

    Asalin hoton, Kano State Govt.

    A yau ne mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya karɓi gwamnan Kano a hukumance cikin jam'iyyar APC.

    Gwamnan Kano

    Asalin hoton, Kano State Govt

    A watan da ya gabata ne Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC bayan ficewa daga NNPP.

    Mutane

    Asalin hoton, Kano State Govt

    An gudanar da taron ne a babban filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar mata

    Hoto Tinubu da Abba

    Asalin hoton, Kano State Govt

    Jihar Kano da daga cikin jihohin Najeriya masu muhimmanci a zaɓen shugaban ƙasar

    Mutane

    Asalin hoton, Kano State Govt

    Manyan ƴansiyasa daga ciki da wajen jihar ne suka halarci bikin

  6. Shugaban riƙo na Bangladesh ya yi murabus

    Muhammad Yunus

    Shugaban gwamnatin rikon ƙwarya na Bangladesh, Muhammad Yunus ya yi murabusb gabanin rantsar da sabuwar gwamnatin ƙasar ranar Talata.

    Cikin jawabin ban kwana da gwamnati da ya yi wa ƴanƙasar ta gidan talbijin, Yunus ya buƙaci ƙasar ta ɗore kan tafarkin dimokraɗiyya da ƴancin faɗin albarkacin baki da haƙƙin ɗan'adam.

    Mista Yunus, mai shekara 85 ya karɓi ragamar ƙasar a amtsayin shugaban riƙo a 2024 bayan da zanga-zanga ta kifar da gwamnatin tsohuwar firaministar ƙasar, Sheikh Hasina, wadda ta tsere zuwa Indiya.

    An haramta wa jam'iyyarta shiga zaɓukan makon da ya gabata, inda jam'iyyar Bangladesh Nationalist Party da jagoranta Tarique Rahman suka lashe da gagarumar tazara.

  7. Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka 100 a ƙasar

    Sojojin Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka 100 da wasu kayan aiki ƙasar.

    Cikin wata sanarwar daraktan yaɗa labaran shalkwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar, ya ce sojojin sun sauka ne a filin jirgin saman Bauchi

    Ya ƙara da cewa zuwan sojojin wani ɓangare ne na yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka cimma a lokacin wata ganawa da suka yi a baya.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa Najeriyar ce ta buƙaci Amurka ta tallafa mata da ƙwararrun sojoji masu horaswa da masu tattara bayanan sirri, domin taimaka wa dakarun ƙasar.

    A cikin makon da ya gabata ne dai Amurka ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin tura sojojinta 200 zuwa Najeriya a ci gaba da yunƙurin Amurkar na taimaka wa Najeriya wajen yaƙi da matsalar tsaro.

  8. Shettima ya karɓi gwamnan Kano cikin APC a hukumance

    Shettima da Abba

    Asalin hoton, Salisu Kosawa

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya karɓi gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf cikin jam'iyyar APC a hukumance.

    An gudanar da taron karɓar gwamnan a wani ƙwarya-kwaryar biki da aka gudanar a birnin da ke arewacin Najeriya.

    Mataimakin shugaban Najeriya na tare da shugaban jam'iyyar APc na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar, da jagoran APC a Kano kuma tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Ganduje.

    A watan Janairun da ya gabata ne gwamnan na Kano ya sanar da komawarsa APC a wani biki da aka gudanar a fadarsa, wanda wasu jiga-jigan APC na kano suka halarta.

  9. Indonesiya na shirin aika sojoji 1,000 zuwa Gaza

    Indonesia ta ce tana shirin aika sojoji 1,000 zuwa Gaza nan da watan Afrilu, saboda shiga cikin shirin samar da dakarun tabbatar da zaman lafiya na ƙasa da ƙasa.

    Wani mai magana da yawun sojin ƙasar ya ce adadin sojojin zai ƙaru zuwa 8,000 zuwa watan Yuni.

    Ya ce a matsayin Indonesia na ƙasar da ta fi kowacce yawan mabiya addinin musulunci, za ta taimaka wajen dawo da daidaito a Gaza.

    Sai dai Indonesia ta ce har yanzu ba za ta amince da dawo da hulɗar diflomasiyya da Isra'ila ba, ko kuma ta amince da tilasta wa Falasɗinawa barin muhallansu.

  10. Harin jirgi maras matuƙi ya kashe mutum uku a Sudan

    Jirgi maras matuƙi

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an kiwon lafiya a Sudan sun ce wani harin jirgi maras matuƙi da mayaƙan RSF suka kai ya hallaka mutum uku, tare da jikkata bakwai a wani asibiti a jihar Sennar.

    Ƙungiyar Likitocin Sudan ta ce harin na ranar Lahadi a asibitin Al-Mazmoum da ke kudu maso gabashin Sudan, shi ne hari na bakwai a cikin watan Fabrairu.

    Tun da farko hukumar lafiya ta duniya ta ruwaito cewa mutum fiye da 30 sun mutu a hare-haren jirgi maras matuƙi har sau uku kan cibiyoyin lafiya a yankin Kordofan.

    Ƙungiyar likitocin ta yi Alla wadai da hare-haren, waɗanda ta ce sun saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

  11. Binciken mutuwar Navalny ya tabbatar da zarginmu - Mahaifiyarsa

    Kabarinsa

    Asalin hoton, EPA

    Mahaifiyar tsohon jagoran adawar Rasha, Marigayi Alexei Navalny ta ce binciken da ya tabbatar da cewa guba ce ta kashe ɗanta ya tabbatar da zargin da ta jima da yi a ranta cewa kashe ɗan nata aka yi.

    A ranar Asabar ne Birtaniya da ƙawayenta na Turai suka fityar da wata sanarwa da ke cewa Navalny- wanda ya mutu a 2024 - kashe shi aka yi ta hanyar amfani da guba da aka samu da wani nau'in kwaɗo.

    Sanarwar ta kuma ce Rasha ce kawai ke da iko da damar shigar da gubar zuwa Rasha.

    ''Wanna ya tabbatar da imanin da muka yi tun da farko,'' a cewar Lyudmila Navalnaya lokacin da ta ziyarci kabarin ɗan nata domin cika shekara biyu da mutuwarsa a birnin Moscow a ranar Litinin.

    "Dama mun sani cewa ɗanmu ba mutuwa ya yi ba, kashe aka yi a gidan yari.''

    Rasha dai ta musanta musanta zargin.

  12. Kashim Shettima ya isa Kano domin karɓar gwamna Abba zuwa APC

    ...

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya isa jihar Kano domin karɓar gwamnan Abba zuwa jam’iyyar APC, a wani muhimmin taron siyasa da ya ja hankalin jama’a.

    An shirya taron karɓar gwamnan ne a hukumance a filin wasan Sani Abacha Stadium, inda dubban magoya baya da shugabannin jam’iyya suka fara taruwa tun da wuri.

    Rahotanni sun ce an ɗauki matakan tsaro na musamman domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da bikin.

    ...

    Shettima ya isa wurin ne tare da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa da mataimakin shugaban majalisar dattawa, tare da gwamnonin jihohin Jigawa, Kebbi, Sokoto, Imo, Yobe da Katsina, lamarin da ya nuna muhimmancin taron a fagen siyasar ƙasa.

    Haka kuma shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas na cikin manyan baƙin da suka halarci taron.

    ...

    Masu sharhi na ganin cewa wannan sauya sheƙa na gwamnan na iya sauya yanayin siyasar jihar da ma yankin Arewa, musamman ganin irin manyan shugabannin da suka halarta domin nuna goyon baya.

    ...
  13. Ƙasashen larabawa sun yi allawadai da shirin Isra’ila na faɗaɗa matsugunanta a Falasɗinu

    Ƙasashen larabawa da ƙungiyar Tarayyar Turai sun yi Alla wadai da shirin Isra'ila, na ci gaba da shirinta na yi wa wasu sassan gaɓar yamma da kogin Jordan da aka mamaye rijista, a matsayin yankunan ƙasar Isra'ila.

    Wannan matakin zai bayar da damar faɗaɗa matsugunan Israila a yankin Falasɗinu.

    Haka kuma matakin zai sa a soke ɗaɗaɗɗiyar dokar da ta hana waɗanda ba musulmai ba mallakar fili a gaɓar Yamman.

    Ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen Isra'ila ta kare matakin inda ta ce wani shiri ne da zai samar da tsari a yankin, sai dai wasu ministocin ƙasar da dama sun bayyana matakin a matsayin yunƙurin ƙarfafa ikonsu a yankin.

  14. Shirye-shiryen karɓar gwamnan Kano zuwa APC a hukumance

    ...

    Ga wasu hotuna da ke nuna yadda ake shirye-shiryen karɓar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zuwa APC a hukumance a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar.

    An ƙawata wurare da tutoci da allunan talla na jam’iyyar, yayin da magoya baya ke shirin halartar taron da ake sa ran zai ja hankalin jama’a da dama.

    Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne zai wakilci shugaban ƙasa Bola Tinubu a wajen taron karɓar gwamnan.

    Ana sa ran zuwansa zai ƙara wa taron armashi tare da nuna muhimmancin matakin sauya sheƙar a idon shugabancin ƙasa.

    An tanadi tsauraran matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da bikin.

    A watan Janairun da ya gabata ne gwamna Abba Kabir ya koma APC a hukumance bayan ficewa daga jam'iyyar NNPP da ke ƙarƙashin jagorancin Rabi'u Musa Kwankwaso inda ya ce rikicin cikin gida na ɗaya daga cikin abin da ya sa ya bar jam'iyyar.

    ...
    ...
    ...
    ....
  15. Jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga kan El-Rufai a Abuja

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu hatsaniya tsakanin waɗanda suka fito domin goyon bayan a binciki tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, da kuma magoya bayansa da suka raka shi zuwa hedikwatar EFCC a Abuja lamarin da ya sa jami’an tsaro suka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar bayan ɓangarorin biyu sun fara cacar baki a harabar ofishin.

    Bidiyoyin da ‘yan jarida da ke wurin suka ɗauka sun nuna wasu daga cikin waɗanda ba sa goyon bayan El-Rufai suna rere taken "El-Rufa'i bai fi ƙarfin doka ba'', ''a bar doka ta yi aikinta''.

    Haka kuma magoya bayansa sun riƙa rera taken cewa ''za su dawo'' duk da hayaƙi mai saka hawaye da aka harba musu" yayin da hayakin ya lullube yankin.

    Ɗaya daga cikin magoya bayansa ya shaida wa BBC cewa sun fusata ne saboda sun ce akwai wasu da ke adawa da shi da aka bari suka kusanci kofar ginin suna zaginsa, alhali su ba a bari sun ƙarasa kusa ba.

    El-Rufai, wanda ke cikin jagororin adawa na jam’iyyar ADC, na shirin ƙalubalantar shugaban ƙasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

    Ya zargi gwamnati da amfani da binciken rashawa a matsayin hanyar matsin lamba kan ‘yan adawa.

    Ya kuma bayyana cewa an riga an kama kusan mutane huɗu da suka yi aiki tare da shi a Jihar Kaduna, yana mai cewa tun da daɗewa yake sa ran za a gayyace shi.

    A cewarsa, abin da ya faru ya tabbatar masa da zaton da yake yi cewa shi ma lokaci ne kawai ake jira kafin a buƙaci ya bayyana domin amsa tambayoyi.

  16. Zanga-zanga ta dawo sabuwa kan batun tura sakamakon zaɓe ta na'ura

    ...

    Masu zanga-zanga sun sake bayyana a wasu sassan babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi kira ga Majalisar Dattawan Najeriya da ta amince da tilasta tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta na’ura kamar yadda dokar zaɓe da aka wa gyara ta amince da yin hakan.

    Sun ce wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya a zaɓe da kuma hana duk wani yiwuwar magudi.

    Daga cikin masu zanga-zangar akwai ƙungiyoyin farar hula da dama, waɗanda suka dage cewa tilasta aika sakamakon ta na’ura ne kaɗai zai kawo adalci da sahihancin zaɓe.

    Wannan sabuwar zanga-zanagar na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu bambancin ra'ayi tsakanin ƴan majalisar inda wasu suka amince da tilasta tura sakamakon zaɓe ta na'ura yayin da sauran kuma ba su amince ba, inda waɗanda ba su amince ba sun fi rinjaye.

    Dalilin hakan ne masu zanga-zangar suke so duka ɓangarorin sun amince da tilasta tura sakamakon zaɓen ta na'ura inda suka ce wannan rashin daidaito zai iya kawo rashin tabbas a sakamakon zaɓe a ƙasa baki ɗaya.

  17. Gwamnatin Najeriya ta maka El-Rufai a kotu kan satar jin wayar Nuhu Ribadu

    ...

    Asalin hoton, KDGOV

    Gwamnatin Najeriya ta shigar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ƙara a gaban kutun taraya bisa zargin sa da naɗar wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ba tare da izini ba.

    A ranar 13 ga watan Fabarairu ne lokacin da ya yi fira da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa'i ya bayyana cewa Nuhu Ribadu ne ya bayar da umarnin a kama shi, kuma ya gano hakan ne bayan "wani" ya saurari tattaunawar waya ta mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu.

    A cikin ƙarar da gwamnatin ta shigar, ta ce “Kai, Mallam Nasiru El-Rufai, ka amince a hirar da ka yi cewa kai da abokan aikinka kun naɗi wayar Nuhu Ribadu, ba bisa doka ba”.

    Wannan ya saɓa da sashe na 12 (1) na Dokar hanawa da daƙile laifukan Intanet ta 2024.

    A tuhuma ta biyu kuma gwamnatin tarayya na zargin Nasiru El-Rufai da cewa ya san wasu da suke naɗar wayar mutane ba bisa ƙa'ida ba amma bai kai ƙarar su ga hukumomin tsaro ba inda takardar ƙarar ta ce "wannan ya saɓa da sashe na 27 (b) na Dokar hanawa da daƙile laifukan Intanet, wanda hakan laifi ne.

    A makon da ya gabata ne wasu jami'an tsaro suka yi yunƙurin kama El-Rufai a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, bayan komawa Najeriya daga Masar.

    Sai dai ya ƙi bin jami'an tsaron, inda ya bukace su da su ba shi takardar gayyata.

    A wata hira da BBC, El-Rufai ya bayyana matakin a matsayin wata bi-ta-da-ƙullin siyasa, kuma ya zargi gwamnatin da yi wa ƴan adawar siyasa barazana domin tursasa musu sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

    Tsohon gwamnan na jihar Kaduna na cikin manyan ƴan siyasa da suka fita daga jam'iyyar ta APC bayan babban zaɓen 2023, inda suka koma jam'iyyar ADC da niyyar ƙalubalantar shugaban Najeriya Bola Tinubu a babban zaɓen ƙasar da za a gudanar shekara mai zuwa.

  18. An kashe sojoji 80 a harin ƴanbindiga a Burkina Faso

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Burkina Faso na cewa gomman sojojin ƙasar ne suka rasa rayukkansu bayan da mayaƙan Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaƙa da al-Qaeda suka mamaye sansaninsu da ke garin Titao a arewacin ƙasar a ranar Asabar din da ta gaba ta.

    Kawo yanzu dai babu wani bayani daga sojoji ko gwamnati.

    Amma wata kafar yaɗa labarai mai alaƙa da 'yan adawa mai suna Sahel Alerte, wadda ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna yadda mayaƙan ke daukar hoton gawarwakin, ta ce akalla sojoji da 'yan sa-kai masu goyon bayan gwamnati 80 ne suka mutu a harin

    Ita ma gwamnatin Ghana ta tabbatar da mutuwar 'yan kasar bakwai a Lamarin.

  19. Hotunan ɓarnar da gobarar kasuwar Singer a Kano ta haddasa

    ...

    Ga wasu hotuna da ke nuna ɓarnar da gobarar da ta tashi a kasuwar sayar da kayan masarufi ta Singer da ke jihar Kano ta haddasa.

    Gobarar dai ta ɓarke ne daga ranar Asabar inda ta ci har zuwa Lahadi a wasu rukunin shaguna da ake yi wa laƙabi da Gidan Gilas, inda aka yi asarar kayayyaki na miliyoyin naira.

    Hotuna da bidiyo da aka yaɗa sun nuna yadda hayaƙi suka turnuƙe saman kasuwar, yayin da shaguna suka kama da wuta tare da ƙonewar kayayyakin masarufi masu ɗimbin yawa

    Lamarin ya faru ne ƴan kwanaki bayan tashin wata gobara da ta haddasa mummunan ɓarna da asara a kasuwar, da ta yi fishe a arewacin Najeriya.

    ...
    ...
    ...
    ....
  20. Ghana ta ce ƴan ƙasarta sun tsinci kansu cikin harin ƴanbindiga a Burkina Faso

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Ghana ta bayyana cewa yan ƙasarta da ke kasuwancin sayar da tumatir sun tsinci kansa cikin harin yanbindiga a ƙauyen Titao da ke arewacin Burkina Faso a ranar 14 ga Fabrairu, amma ba a bayyana ko wani daga cikin fasinjojin ya jikkata ba.

    Ma’aikatar ta ce labarin harin, wanda rahotanni suka nuna ya kashe aƙalla jami’an tsaro 80 na Burkina Faso, ya “haddasa damuwa da tashin hankali."

    An ce an kai harin ne kan sansanin soji a Titao, inda aka lalata wasu gine-gine yayin arangamar.

    “Gwamnatin Ghana ta samu labari mai tayar da hankali daga Burkina Faso cewa wata mota da ke ɗauke da ‘yan kasuwar tumatir daga Ghana ta tsinci kanta cikin harin ƴanbindiga a Titao da ke ƙasar" in ji ma’aikatar.

    Haka kuma, ta ce ofishin jakadancin Ghana a Burkina Faso na tuntuɓar hukumomin ƙasar domin ziyartar wurin tare da tattara cikakken bayani da kuma taimakawa wajen gano ƴan Ghana da abin ya shafa.