Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 05/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 05/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Laraba.

    Muna nan tafe da wasu rahotonnin gobe da safe. Kafin haka, ku duba ƙasa domin karanta rahotonnin da muka wallafa a yau ɗin.

  2. Hamas ta ce ta sake miƙa gawar ɗan Isra'ila

    Ƙungiyar Hamas ta miƙa gawar da ta ce ta wani ɗan Isra'ila ce ga ƙungiyar Red Cross.

    An miƙa gawar ga rundunar sojin Isra'ilar, wadda za ta kai ta asibiti a birnin Tel Aviv domin tabbatar da gawar ko wane ne.

    Bisa tanadin yarjejeniyar tsagaita wuta da Donald Trump ya shiga tsakani, Hamas ta amince ta saki duka Isra'ilawa 20 masu rai da kuma gawar 28 cikin awa 72.

    Sai dai Isra'ila na zargin Hamas ɗin da jan ƙafa da gangan, yayin da ita kuma ke cewa tana shan wahalar zaƙulo su daga ɓaraguzai sakamakon hare-haren da Isra'ilar ta kai a Gaza.

    Idan aka tabbatar da gawar ta wanda aka yi garkuwa da shi ce, ya zama saura gawa shida kenan a cikin Gaza ta 'yan Isra'ila da kuma 'yan ƙasar waje waɗanda Hamas ta kama a lokacin harinta na ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

  3. Majalisar Najeriya na shirin kafa dokar amfani da motoci masu amfani da lantarki

    Majalisar Dattawan Najeriya ta yi wa ƙudirin dokar amfani da ababen hawa masu amfani da lantarki.

    Ƙudirin mai taken Electric Vehicle Transition and Green Mobility Bill 2025, Sanata Orji Uzor Kalu (daga jihar Abia) ne ya gabatar da shi, wanda ke neman ɗora Najeriya kan "hanyar kyautata muhalli".

    Mista Kalu ya ce dokar "za ta taimaka wa ɓangaren ƙera ababen hawa, da makamashi, da ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma samar da ayyukan yi".

    "Dokar ta ba da damar yafe haraji, da harajin shigo da kaya, da harajin kan hanya, da bayar da tallafi ga masu amfani da motoci masu amfani da lantarki da masu samar da su," in ji shi.

    Ta kuma tilasta kakkafa tashoshin caji a duka gidajen mai da ke faɗin ƙasar.

  4. Gwamnatin Katsina za ta kashe naira biliyan 31 kan gina madatsar ruwa ta Zobe

    Gwamnatin jihar Katsina a Najeriya ta ƙaddamar da ci gaba da aikin madatsar ruwa ta Zobe a karamar hukumar Dan-Musa.

    Aikin wanda aka fara shi tun fiye da shekara 30 da suka gabata, za a kashe kuɗi naira biliyan 31 wajen kammala shi, kamar yadda hukumomi suka tabbatar, inda ake sa ran zai samar da ruwa mai tsafta ga kananan hukumomi bakwai ciki, har da Katsina babban birnin jihar.

    Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda ya ce aikin - wanda gwamnatocin baya suka gaza kammalawa - ana sa ran kammala shi kafin ƙarshen gwamnatinsa.

    "Daga sanya hannu a wannan kwangila, za mu ba su kashi 40 cikin 100 na wannan kuɗaɗe, wanda ya kama wajen biliyan 11 da wani abu domin kada aikin ya tsaya," in ji gwamnan a lokacin ƙaddamar da aikin.

    Ya ƙara da cewa daga nan za a ci gaba da biyan kuɗin har zuwa lokacin da za a kammala aikin.

    Shugaban hukumar samar da ruwan sha ta Katsina, Tukur Hassan, ya ce an tura ma'aikata zuwa ƙasashen Zambia da Rwanda da Jamus da Afirka ta Kudu domin samun horo kan yadda za su riƙa kula da tashar.

    Ƙananan hukumomin da za su amfana da shirin su ne Kankiya da Ɓatagarawa, da Katsina da Rimi da Caranci da kuma Dutsen-Ma.

  5. Kotun Ƙoilin Amurka ta ci gaba da sauraron ƙorafi kan haraje-harajen Trump

    Kotun kolin Amurka na ci gaba da sauraren korafe-korafe kan yadda Shugaba Donald Trump ya yi ta lafta haraje-haraje kan kasashe.

    Shari'ar za ta iya yin tasiri sosai kan sauran wa'adinsa na mulki bayan nasarar da ya yi a zaɓen watan Nuwamba na 2024.

    Yankasuwa da jihohi da dama da ke korafin sun ce ya kamata a soke akasarin haraje-harajen. Sun dage cewa yanmajalisa ne kaɗai ke da ikon sanya duk wani abu da ake kira haraji.

    Lauyoyin Mista Trump sun ce shugaban na da damar yanke hukunci kan abubuwa da dama da suka shafi harkokin kasashen waje, da kasuwanci, da kuma haraji.

  6. Majalisar dattawa ta ƙi tantance ministan Tinubu saboda rashin rahoton jami'an tsaro

    Majalisar Dattwan Najeriya ta dakatar da aikin tantance Kingsley Udeh a matsayin minista sakamakon rashin rahoton jami'an tsaro a kansa da ba a gabatar mata ba.

    Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya sanar cewa ba za su ci gaba da tantancewar ba sai an gabatar wa majalisar da rahoton jami'an tsaro a kan mutumin.

    A ranar Talata ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aike musu da sunan Mista Udeh ɗan asalin jihar Enugu cikin wata wasiƙa.

    Tinubu ya naɗa shi ne bayan ajiye aiki da Ministan Kimiyya Uche Nnaji ya yi bayan zargin sa da gabatar da shaidar kammala karatu na bogi, kuma shi ne minista ɗaya kacal daga jihar ta Enugu a kudancin Najeriya.

    Babu tabbas ko jami'an tsaron za su gabatar da rahoton nasu ga majalisar domin tantance shi a zamanta na gaba.

  7. Bangladesh za ta ba da lada ga duk wanda ya miƙa makaman da aka sace lokacin zanga-zanga

    Ƙasar Bangladesh ta sanar da shirin bayar da ladan kuɗi ga mutanen da suka miƙa makaman da aka sace makamai lokacin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a shekarar da ta gabata.

    Hukumomi sun ce an sace manyan bindigogi, da ƙanana daga taskar 'yansanda a watan Agustan bara, lokacin mummunar tarzomar da ta kai ga tumɓuke tsohuar Firaminista Sheikh Hasina daga mulki.

    An bayar da rahoton ɓatan makamai 13,000, kuma ladan yana kamawa daga dala 4,000 kan bindigar mashinga, zuwa 800 kan bindigar kai hari.

    Runudunar 'yansanda ta yi alƙawarin sirranta sunayen mutane tana mai shawartar su mayar da makaman kafin zaɓen da za a yi a shekara mai zuwa.

  8. Jirgin ƙasa ya kashe mutum biyu bayan murƙushe keke mai ƙafa uku a jihar Filato

    Wani jirgin ƙasa na ya murƙushe babur mai ƙafa uku a yankin Phototake da ke birnin Jos na jihar Filato a tsakiyar Najeriya, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana.

    Rahoton ya ce jirgin ya fito ne daga Bukuru zuwa Jos babban birnin jihar a yau Laraba, inda ya kashe direban da kuma raunata fasinjoji biyu.

    Wani mutum da abin ya faru a kan idonsa ya faɗa wa jaridar cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:00 na safe, inda ya kashe mutum biyu nan take ciki har da direban, da kuma wasu mata biyu da suka jikkata.

    Wani mazaunin yankin kuma ya ɗora alhakin faruwar hatsarin kan rashin mutumin da ke kula da shingen tsallaka titin jirgin, wanda ya ratsa titin motar a daidai shataletalen Phototake Abattoir.

  9. An kashe mutum 33 a rikicin manoma da makiyaya a Chadi

    Rahotonni daga ƙasar Chadi na cewa aƙalla mutum 33 ne suka mutu bayan wata arangama tsakanin manoma da makiyaya a kudu maso yamamcin ƙasar.

    Wani jami'in ƙasar da wani basaraken a yankin sun tabbatar da faruwar lamarin.

    Bayanai na cewa kawo yanzu ba a san adadin mutanen da suka jikkata a lamarin ba.

    Rikici tsakanin al'umomi ba sabon abu ba ne a ƙasar Chadi, musamman tsakanin ƙungiyoyin manoma da makiyaya a ke zargin juna kan wuraren kiwo.

    Wasu alƙaluma na cewa fiye da mutum 50 ne suka mutu a irin wannan rikici a ƙasar tun watan Mayun da ya gabata.

  10. Dole PDP ta bayar da gudunmawa don ceto Najeriya - Damagum

    Shugaban babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, Amb. Umar Iliya Damagum ya hori jagororin jam'iyyar su ɗauki gabarar abin da ya kira ceto Najeriya.

    Yayin da yake jawabi a wani taron gaggawa da kwamitin amintattun jam'iyyar ya shirya a gidan saukar baƙi na gwamnatin jihar Bauchi da ke Abuja, Damagum ya ce a matsayinta na jam'iyyar hamayya PDP na da rawar da za ta taka.

    Cikin waɗanda suka halarci taron har da mataimakin shugaban jam'iyyar na yankin kudancin ƙasar, Taofeek Arapaja da mai riƙon ƙwaryar muƙamin sakataren jam'iyyar na ƙasa, Koshedo Setonji da tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi da tsohon ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

    An gudanar da taron ne da nufin kammala duka wasu shirye-shirye domin tunkarar babban taron jam'iyyar na ƙasa da za a gudanar a Ibadan a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban da muke ciki.

    Babban taron dai ya riƙa fuskantar tarnaƙi bayan da a makon da ya gabata wata kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam'iyyar daga ci gaba da taron.

    To sai dai a ranar Talata babbar kotun jihar Oyo ta bayar da wani umarnin gudanar da taron, tare da bai wa hukumar zaɓen ƙasar umarnin sanya idanu kan taron.

  11. Yadda Akpabio da Barau suka yi ja-in-ja a kan barazanar Donald Trump ga Najeriya

    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau Jibrin sun yi ƴar ja-in-ja a majalisar dangane da barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ta kai wa Najeriya har bisa zargin "kisan gilla" ga Kiristocin ƙasar.

    An dai jiyo shugaban Majalisar yana cewa ba zai iya tattauna batun ba inda yake cewa "ni a su wa na taɓa Trump?", sai shi mataimakin shugaban, Barau Jibrin ya ce "kana tsoronsa ne?"

  12. Aƙalla mutum 10 sun jikkata bayan wani direba auka kan matafiya a Faransa

    Akalla mutum 10 ne su ka jikkata bayan wani direba ya auka kan wasu mutane da ke tafiya a ƙafa wasu kuma kan keke a tsibirin Oleron da ke Faransa.

    Huɗu daga cikinsu sun ji rauni sosai.

    Magajin garin tsibirin ya ce mutumin da ake zargin ya yi ƙoƙarin ƙona motarsa kafin a kama shi.

    Kafafen yaɗa labarai na Faransa na ruwaito cewa ƴansanda na duba yiwuwar direban na da matsalar ƙwaƙwalwa.

    Ministan harkokin cikin gida na Faransa ya wallafa a shafinsa na X inda ya tabbatar da cewa ana bincike kan harin wanda ake tunanin na na ta'addanci ne.

  13. Zan yi duk abin da ya kamata domin kama Sowore - Kwamishinan Ƴansanda

    Kwamishinan ƴansandan jihar Legas, CP Olohundare Jimoh ya jaddada cewa zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da kama fitaccen mai fafutikar ƙasar nan Omoyele Sowore da ƴansanda suka ayyana a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

    A ranar Litinin ne CP Jimoh ya ayyana Sowore a matsayin wanda hukumar ƴansanda ke nema ruwa a jallo bisa zarginsa da “haifar da ruɗani a zaman lafiyar al'umma da kuma aikata babban laifi ta hanyar shirin toshe hanyoyin ababen hawa a kan gadar Third Mainland.”

    Cikin wata hira da gidan talbijin na Channels, CP Jimoh ya ce har yanzu Sowore bai kai ansa hukumar ƴansandan ba, tun bayan ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

    Kwamishinan ƴansandan ya kuma karyata duk iƙirarin da Sowore ya yi a cewa babban sifeton ƴansanda ya bayar da umarnin harbe shi a duk inda aka gan shi.

    ''Wannan ikirari ne maras tushe, babau yadda z a yi babban sifeton ƴansanda ya bayar da irin wannan umarni'', in ji shi.

  14. Trump ɗan kama-karya ne mai ƙaramin tunani - Soyinka

    Fitaccen marubucin nan na Najeriya, Farfesa Wole Soyinka ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da zama ɗan kama-karya.

    Cikin wata hira da BBC, Farfesa Soyinka ya yi zargin cewa an samu ƙaruwar kashe-kashen baƙaƙen fata da waɗanda ba su da rinjaye a Amurka.

    A baya-bayan nan ne Amurka ta soke bizar Farfesa Soyinka.

    Mawallafin mai shekara 91 ya ce ayyukan Trump na tuna masa irin mulkin tsohon shugaban Ugana, Idi Amin.

    "An samu ƙaruwar kashe-kashe, kashe-kashe ba bisa ƙa'ida ba da 'yan sanda ke yi wa bakaken fata da waɗanda ba su da rinjaye, a lokacin da suke gina siyasarsu, a lokacin yakin neman zaɓen, a sanadiyyar wadannan kalaman, kalaman nuna ƙiyayya na wannan mutumin'', in ji shi.

    "Wannan mutumin ɗan mulkin kama-karya ne mai ƙarancin tunani, za ku shaida yadda yake mu'amala da nuna ƙiyayyarsa a fili."

  15. Wani sanatan Amurka ya soki nasarar Paul Biya

    Shugaban kwamitin majalisar dattawan Amurka kan dangantakar ƙasar da ƙasashen waje, Sanata Jim Risch ya bayyana sake zaɓen Paul Biya a matsayin abin kunya.

    Matakin ɗan majalisar dattawan na zuwa ne a daidai lokacin da jagoran adawar ƙasar, Issa Tchiroma Bakary ke ci gaba da iƙirarin nasara.

    A cikin jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Risch ya zargi gwamnatin Biya da abubuwa da dama, da suka haɗa ''far wa ƴan'adawa, da tsare Amurkawa ba bisa ƙa'ida.

    Haka ma ɗan'majalisar a Amurka ya zargi gwamnatin Biya da bai wa sojojin hayar Rasha na Wagner damar gudanar da abin da ya kira ''miyagun'' ayyuka da kuma samar da wani yanayi da ya bai wa Boko Haram da ISIS damar gudanar da ayyukansu.

    “Kamaru da ƙawar Amurka ba ce, hasalima tana haifar da barazanar tattalin arziki da tsaron Amurkawa,'' in ji shi.

    Ya ƙara da cewa ''lokaci ya yi da ya kamata a sake nazarin dangantakar ƙasashen biyu kafin lamarin ya yi ƙamari.''

  16. An sake buɗe filin jirgin saman Brussels bayan gilmawar jirage marasa matuƙa

    Jirage sun ci gaba da zirga-zirga bayan sake buɗe babban filin jirgin saman Brussels, babban birnin ƙasar Belgium.

    An dakatar da sufurin jirage a filin ne saboda gilmawar jirage marasa matuƙa a saman filin jirgin.

    Filin jirgin saman birnin Brussels ya saba dakatar da ayyuka saboda ayyukan jirage marasa matuƙa.

  17. RSF na tattara gawarwaki domin binne su a kaburburan bai-ɗaya a Sudan - Rahoto

    Wani rahoto da Jami'ar Yale da ke Amurka ta fitar ya nuna cewa mayaƙan RSF - da ake zargi da kashe-kashe - na tattara gawarwakin da ke yashe tare da binne su a kaburburan bai ɗaya a Darfur.

    Hotunan tauraron ɗan'adam daga birnin El-Fasher - da mayaƙan RSF suka ƙwace a makon da ya gabata - sun nuna yadda jini ya watsu a kan titunan birnin.

    Nazarin hotunan tauraron ɗan'adam ɗin ya nuna hujjar cutar da fararen hula a cikin El Fasher da kuma kan titunan fita daga birnin.

    Har yanzu akwai dubban mutanen ba a gansu tu bayan gumurzun ƙwace birnin daga hannaun mayaƙan gwamnati.

  18. Barazanar Amurka: Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya su kwantar da hankali

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƴan Najeriya su kwantar da hankulansu, yana mai cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da ingantuwar tsaron rayuka da dukiyoyinsu.

    Yayin isar da saƙon shugaban ƙasar, jim kaɗan bayan ganawa da shi, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris, ya ce shugaban na yin duk mai yiwuwa domin inganta tsaro a ƙasar.

    ''Mun tattauna batun barazanar da Trump ya yi wa ƙasarmu, kuma shugaban ƙasa na nazarin barazanar cikin tsanaki, inda yake ƙoƙarin fahimtar da ƙasashen duniya irin ƙoƙarin da ƙasarsa ke yi wajen magance matsalar tsaron ƙasar'', in ji shi.

    Cikin wani bidiyon hirar ministan da gidan talbijin na ƙasar, NTA ya wallafa , ministan ya ce ko sauya shugabannin tsaron da Tinubu ya yi a makonni biyu da suka gabata na da nasaba da ingantuwar tsaron ƙasar.

    ''Bayyana Najeriya da ƙasar ba a girmama addini, ba daidai ba ne, kundin tsarin mulkinmu ya yi tanadin cewa kowa na da damar yin addininsa ba tare da tsangwama ba'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa ''shugaban na nan yana nazarin waɗannan abubuwa cikin tsanaki, kuma da yardar Allah wanna abu zai wuce''.

  19. Gwamnan Kano ya bayar da tallafin ababen hawa ga dakarun da ke yaƙi da ƴanbidiga a jihar

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da tallafin ababen hawa ga dakarun tsaron da ke yaƙi da ƴanbindiga a wasu sassan jihar.

    Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya yaba wa dakarun da ke yaƙi da ƴanbidigar da ke addabar wasu ƙananan hukumomin jihr.

    Alhaji Abba Kabir ya sanar da bayar da motoci 10 ƙirar Hilux da babura 60 ga dakarun tsaron da ke yaƙi da ƴanbindiga a jihar, tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da bai wa jami'an tsaro goyon baya wajen yaƙar ayyukan ƴanbindigar a faɗin jihar.

    Matakin na zuwa ne a lokacin da babban kwamandan runduna da ɗaya ta sojojin Najeriya da ke Kaduna, Manjo Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, ya kai ziyara jihar domin duba dakarun da ke yaƙi da ƴanbidiga a jihar.

    A baya-bayan nan an samu rahotonnin ɓullar hare-haren ƴanbidiga a ƙananan hukumomin da ke iyaka da jihar Katsina mai fama da matsalar tsaro.

  20. An kama wata mata kan zargin kitsa garkuwa da kanta don karɓar kuɗi a wurin mijinta

    Rundunar ƴansandan jihar Edo da ke kudancin Najeriya sun kama wata mata, mai suna Chioma Success, bisa zargin kitsa garkuwa da kanta domin karɓar kuɗin fansa a wajen mijinta.

    Mataimakiyar kakakin rundunar ƴansandan jihar, ASP Eno Ikoedem, ta ce an kama matar ne tare da wasu mutum biyu da ake zargin sun taimaka mata wajen kitsa batun.

    ASP Ikoedem ta ce a ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata ne mijin matar mai suna Paul Adaniken ya kai rahoton ɓacewar matarsa da kuma ɗansu mai shekara uku, bayan da ya fita kasuwa ya bar su a gida.

    Daga baya ne kuma aka kira shi a waya tare da sanar da shi cewa an yi garkuwa da matarsa da kuma ɗansa, inda aka buƙaci naira miliyan biyar kafin a sako su.

    ASP Ikoedem ta ce bayan zurfafa binciken ƴansanda aka kama wani ɗan'uwan matar, wanda tun da farko yake taimaka wa binciken.

    Bayan da ƴansanda suka tuhume shi ne ya amsa laifin cewa sun haɗa baki ne da matar domin karɓar kuɗi daga hannun mijinta, lamarin da ya sa ƴansanda suka kamo matar bayan ya bayyana musu wurin da take ɓoye, kamar yadda ASP Ikoedem ta bayyana.

    Yanzu haka dai an tura batun gaban sashen binciken manyan laifuka na runduna ƴansandan jhar domin zurafafa bincike, kafin gurfanar da su a gaban kotu.