Rufewa
A nan muka kawo karshen wannan shafin na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe Laraba idan Allah Ya nuna mana.
Da fata kun ji dadin kasancewa tare da.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/12/2025.
Daga Aisha Babangida
A nan muka kawo karshen wannan shafin na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe Laraba idan Allah Ya nuna mana.
Da fata kun ji dadin kasancewa tare da.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai yiwuwar za fara buƙatar masu yawon bude ido daga kasashe da dama da ke neman izinin shiga Amurka, su gabatar da tarihin abubuwan da suka yi, a shafukansu na sada zumunta na shekaru biyar da suka gabata kafin a basu izini.
Kudurin zai shafi mutanen da aka ba su damar shiga Amurka na tsawon kwana 90 ba tare da biza ba, a karkashin wani sabon tsare tsaren neman biza da ake kira ESTA.
An zayyana sabin shirye-shiryen ne a wata takardar bayanai da hukumar kwastam da kare iyaka ta gabatar.
Wakiliyar BBC ta ce shirin ya kuma kunshi bayar da lambobin waya da sakonnin emel na shekaru biyar da suka gabata, da kuma tattara wasu bayanai game da iyalan mutum.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai yiwuwar za fara buƙatar masu yawon bude ido daga kasashe da dama da ke neman izinin shiga Amurka, su gabatar da tarihin abubuwan da suka yi, a shafukansu na sada zumunta na shekaru biyar da suka gabata kafin a basu izini.
Kudurin zai shafi mutanen da aka ba su damar shiga Amurka na tsawon kwana 90 ba tare da biza ba, a karkashin wani sabon tsare tsaren neman biza da ake kira ESTA.
An zayyana sabin shirye-shiryen ne a wata takardar bayanai da hukumar kwastam da kare iyaka ta gabatar.
Wakiliyar BBC ta ce shirin ya kuma kunshi bayar da lambobin waya da sakonnin emel na shekaru biyar da suka gabata, da kuma tattara wasu bayanai game da iyalan mutum.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai yiwuwar za fara buƙatar masu yawon bude ido daga kasashe da dama da ke neman izinin shiga Amurka, su gabatar da tarihin abubuwan da suka yi, a shafukansu na sada zumunta na shekaru biyar da suka gabata kafin a basu izini.
Kudurin zai shafi mutanen da aka ba su damar shiga Amurka na tsawon kwana 90 ba tare da biza ba, a karkashin wani sabon tsare tsaren neman biza da ake kira ESTA.
An zayyana sabin shirye-shiryen ne a wata takardar bayanai da hukumar kwastam da kare iyaka ta gabatar.
Wakiliyar BBC ta ce shirin ya kuma kunshi bayar da lambobin waya da sakonnin emel na shekaru biyar da suka gabata, da kuma tattara wasu bayanai game da iyalan mutum.

Asalin hoton, AFP
Ministan harkokin wajen Burundi ya bayyana ci gaba da gwabza yaki a gabashin jamhuriyar dimokradiyyar Kongo a matsayin abin kunya ga shugaba Trump.
Kungiyar M23 masu samun goyon bayan Rwanda sun shiga tungar karshe ta gwamnatin Congo a lardin kudancin Kivu, wanda ya sa dubban mutane tserewa zuwa Burundi mai makwaftaka.
Wakilin BBC ya ce wata majiya daga gwamnatin Congo ta ce dakarun kasar sun ja baya domin gudun kar a samu asarar rayukan fararen hula.
Shigar M23 yankin na zuwa ne mako guda bayan da Congo da Rwanda suka amince da yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta gabatar musu.

Asalin hoton, Reuters
Jagorar adawa ta Venezuela, Maria Corina Machado, ta buƙaci ƴan kasar su yaƙi abin da ta kira ''ta'addancin da ƙasar ke ciki''.
Ta bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ƴarta ta gabatar a lokacin da ta wakilce ta domin karɓar lambar yabon zaman lafiya ta Nobel a birnin Oslo.
Miss Machado ta kuma yi Alla wadai da sace mutane da azarbtar da su da ake yi karkashin shugaban Venezuela Nicolas Maduro.
Ana Corina Sosa Machado kenan ta ke cewa ta zo taron a madadin mahaifiyarta wadda ta haɗa kan miliyoyin ƴan Venezuela, da ya sa a yau aka bata kyautar Nobel ta zaman lafiya. An shafe watanni rabon da a ga Miss Machado a bainar jama'a.

Asalin hoton, @kabiruturakisan
Shugaban jam'iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki ya ce yanzu jam'iyyar ta ɗinke ɓarakar da ta daɗe tana ciki, inda ya ce komai ya wuce a yanzu.
Turaki ya bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da yake zantawa da shugabannin jam'iyyar PDP na jihohi, waɗanda ya ce sun kai masa ziyara ne domin taya tsaginsa murna tare da nuna mubaya'a kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Shugabannin jam'iyyar sun kai ziyarar ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar PDP na jihar Edo, Tony Aziegbemi tare da wasu shugabannin jihohin guda 29.
A jawabinsa na maraba, ya buƙaci shugabannin na jihohi da su ba shi shawarwari kan hanyoyin da za a bi domin jam'iyyar ta samu nasara, sannan ya yi watsi da iƙirarin tsagin Ministan Abuje Nyesom Wike cewa su ne asalin shugabannin jam'iyyar.
Ana dai ci gaba da fafatawa kan shugabancin jam'iyyar a matakin ƙasa, inda bayan tsagin Kabiru Turaki da ke samun goyon bayan Gwamnan Oyo Seyi Makinde da Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, akwai kuma tsagin da ke samun goyon bayan Wike.

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Najeriya sun ce sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Kallamu, wanda na hannun damar Turji ne a ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust mai zaman kanta ce ta ruwaito daga wata majiya cewa an kashe ɗanbindigar ne a ranar Laraba, inda ta ce an samu nasarar kashe Kallamu ne tare da taimakon ƴan sa kai.
Kallamu ɗan asalin garin Garin-Idi ne da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, inda rahotanni suka ce Kallamu ya tsira daga wasu hare-haren sojoji a baya, inda aka ce ya tsere zuwa jihar Kogi.
Jihar Sokoto ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro, duk da irin nasarorin da sojojin Najeriya suke cewa suna samu.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a ƙasar Ghana sun sanar da korar ƴan ƙasar Isra'ila uku zuwa ƙasarsu a matayin martani ga abin da suka kira rashin adalci da aka yi wa ƴan Ghana a Isra'ila.
Gwamnatin Ghana ta yi zargin an muzguna wa ƴan ƙasarta a filin jirgin sama na Ben Gurion da ke babban birnin Tel Aviv na ƙasar Isra'ila ta hanyar kama su, da tsare su "ba bisa ƙa'ida ba."
"Ghana na girmama alaƙarta da ƙasashen waje, amma tana buƙatar a riƙa girmama ƴan ƙasarta da mutunci kamar yadda wasu ƙasashen suke so Ghana ta girmama ƴan ƙasarta," kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta bayyana.
Tun da farko, an tsare ƴan Ghana guda bakwai ne ciki har da ƴan majalisa guda huɗu da suka je Isra'ila domin halartar taro a Tel Aviv, duk da cewa an sake su daga baya, amma sai aka mayar da guda uku Ghana.
"Ghana ta ɗauki wannan a matsayin rashin adalci ga ƴan ƙasarta, sannan ba za ta lamunci duk wani irin wulaƙanci da za a yi wa ƴan ƙasarta ba," in ji sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Ghana.
BBC ta yi yunƙurin jin ta bakin ofishin jakadancin Isra'ila a Accra, amma ofishin bai ce komai ba har zuwa lokacin haɗa labarin.

Asalin hoton, Tinubu X
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nanata ƙudurinsa na janye ƴansanda daga gadin manyan mutane a ƙasar, inda ya ce janyewar ta zama tilas.
Ya ce babu gudu babu ja da baya a matakin da ya ɗauka, sannan ya yi kira ga dukkan ministocin ƙasar su yi abin da ya dace ba tare da ɓata lokaci ba.
Tinubu ya bayyana haka ne a taron majalisar zantarwa na ƙasar, inda ya yi gargaɗin ɗaukar mataki kan waɗanda suka saɓa umarnin.
"Idan dole kana buƙatar ƴansanda saboda yanayin aikinka, sai ka yi magana da babban sufeto janar na ƴansa, sai a nema sahalewa ta," in ji shi.
Shugaban ya buƙaci mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da ministan ƴansanda Ibrahim Geidam da shugaban ƴansanda Kayode Egebtokun su tabbatar an aiwatar da umarnin.
Tinubu ya ce kariya ga manyan mutane ba aikin ƴansanda ba ne, inda ya ce ministan harkokin cikin gida Olobunmi Tuni-Ojo zai yi tsare-tsaren maye gurbin ƴansanda da suke aiki da manyan mutane a ƙasar da jami'an tsaron civil defence, waɗanda an horar domin "ba manyan mutane kariya, kuma suna ɗaukar bindiga."
Kasashen da ke cikin hukumar kare haƙƙin ɗanadam ta Tarayyar Turai za su gana domin tattaunawa akan yadda za a yi wa dokar kare haƙƙin 'yanci-rani garanbawul.
Taron da ƙasashe 46 za su yi ya zo ne a yayin da ake kara nuna damuwa akan yadda ake amfani da dokokin kare haƙƙin dan adam akan 'yanci rani da kuma lalubo hanyoyin da za a yi gyara.
A yayin taron, za a duba yiwuwar ko za a sake yiwa dokar gyaran fuska ta yadda zata hana safarar mutane da kuma bayar da damar mayar da 'yanci ranin kasashensu.
Yunkurin dai ya samu goyon bayan shugabannin kasashe Turai da dama, ciki har da firaministan Birtaniya da na Denmark - wanda ya ce akwai bukatar a kare iyakokin ƙasashen.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC na ci gaba da tsare tsohon ministan shari’a kuma tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN), saboda zarginsa da hannu wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci a ƙasar.
Binciken ya kuma shafi zuba jarin da ake zargin ya kai kusan naira biliyan 10 a Jihar Kebbi, da kuma batun dawo da dala miliyan 322 na kudaden Abacha daga Switzerland, da ƙarin dala miliyan 22 daga tsibirin Jersey. Hukumar ta ce tana buƙatar cikakken bayani game da waɗannan al'amura kafin ta sake shi daga tsarewa.
EFCC ta ci gaba da tsare Malami har zuwa ƙarfe 10 na daren Talata saboda rashin cika sharuddan belinsa.
Ana binciken zargin amfani da asusun da ake zargin an ƙirƙire su ne domin karkatar da kuɗi, tare da yiwuwar ƙwace wasu kadarorinsa idan hujjoji sun tabbata.
Sai dai a nasa bangaren, Malami ya karyata duk tuhume-tuhume, yana jaddada cewa a lokacin da yake minista, shi ne ma ya jagoranci tsare-tsare da suka taimaka wajen cire Najeriya daga jerin ƙasashen da ake zargi da taimaka wa halatta kudaden haram.
A cikin sakon da ya wallafa a shafin X, ya ce ba a taɓa zarginsa ko gayyatarsa ko bincikar shi kan batun daukar nauyin ta’addanci ba, a Najeriya ko a waje.
Tsohon ɗan majalisar jihar Kebbi kuma na kusa da Malami, Abubakar B. Sabo, ya ce ba su ga dalilin da zai sa a alakanta shi da ta’addanci ba.
A cewarsa: “Ai kowa ya san cewa mutum da ya rike mukamin ministan shari’a na ƙasa ba zai iya zamewa wanda ke ɗaukar nauyin ta’addanci ba; kawai bita da kulli ake masa.”
Ya kuma kara da cewa: “Tunda an ce yana da hannu, muna jira mu ga ko za a iya tabbatar da hakan. Amma abin da ya dace shi ne a yi masa shari’a, ba kawai a kama shi ba tare da hujja ba.”
Ana sa ran Malami zai ci gaba da kasancewa a hannun EFCC har sai ya kammala cika dukkan sharuddan belinsa, tare da bayar da bayanan da masu bincike ke bukata.

Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL
Kungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya su gudanar da cikakken bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima da sojoji suka yi, wanda ake zargin ya yi sanadin mutuwar aƙalla mata tara a yayin zanga-zanga a Karamar Hukumar Lamorde ta jihar Adamawa.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafin sada zumuntarta na Facebook.
Ƙungiyar ta ce harbin da aka yi wa masu zanga-zangar da harsasai kai tsaye ba tare da gargadi ba ya saɓa ƙa’ida kuma ba ya kan doka.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda suka jikkata sun samu harbin bindiga a sassan jikinsu daban-daban, ciki har da kai da wuya da baya da kirji da kafada da kafa da kuma hannuwa, wasu ma an harbe su sau da dama.
Amnesty International ta kara jaddada cewa akwai buƙatar ɗaukar mataki domin dakile rikicin kabilanci da ya ta'azzara tsakanin ƙabilun Bachama da Chobo, rikicin da ya samo asali daga taƙaddama kan fili da zargin satar babur.
Kungiyar ta ce rikicin ya haifar da munanan laifuka da kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a yankin, tare da bayyana cewa halin ko-in-kulin da hukumomin Najeriya suke nunawa ya kara dagula lamarin.
Wata kotu a Amurka ta yanke wa wasu Amurkawa biyu ‘yan asalin kasar Kamaru hukunci bisa laifin tallafawa ayyukan ta’addancin mayakan ‘yan aware na Anglophone a Kamaru.
An samu Francis Chenyi mai shekaru 52 da Lah Nestor Langmi, mai shekaru 49, da laifuka da dama, ciki har da haɗa baki don bayar da tallafin kayan aiki ko kuɗade don kashe mutane da garkuwa da mutane, da kuma nakasa su.
Za suyi hakan ne ta hanyar amfani da makaman kare dangi, a wata kasar waje.

Gwamnatin jihar Neja ta mika yara 100 da aka ceto, wadanda aka sace daga Makarantar Katolika ta St Mary’s da ke Papiri ga iyayensu bayan makonni biyu a hannun waɗanda suka sace su.
Harabar makarantar ta cika da iyaye, waɗanda ke cikin murna da kuma fargaba yayin da suke jiran ganin ’ya’yansu da aka kuɓutar, a lokacin da aka tafi da yaran gida daga Minna, babban birnin jihar.
Kwamishinan ’yan sanda ya bayyana cewa an duba lafiyar yaran, kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya
Iyayen da suka kwana suna jiran wannan rana sun bayyana cewa ganin ’ya’yansu cikin koshin lafiya ya kasance babban abin farin ciki a gare su.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da aiki tukuru domin ganin an sako sauran dalibai 153 da ma’aikata 12 waɗanda har yanzu suke hannun ƴan bindiga.
Gwamnatin ƙasar ta yi alkawarin karfafa tsaro a makarantu domin hana faruwar irin wannan hari a nan gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Rwanda ta musanta cewa ba ita ke haddasa sabbin rikice-rikicen da ya kunno kai a Kivu ta Kudu da ke DR Congo.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da ma’aikatar harkokin wajen Rwanda ta fitar.
Rwanda ta kuma zargi rundunar DRC da ta Burundi, tare da mayakan FDLR da Wazalendo da wasu ‘yan kasashen waje da kai hare-hare da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan ƙauyuka kusa da kan iyakar Rwanda.
Rwanda ta ce hakan ya tilasta wa sama da ‘yan Congo 1,000 tserewa zuwa ƙasar, inda aka basu masauki a Bugarama.
Haka kuma, Rwanda ta ce Burundi ta tura sojoji 20,000 a Kivu ta Kudu domin yi wa al’ummar Banyamulenge a Minembwe ƙawanya.
Rwanda ta yi gargadi cewa irin waɗannan matakai na kawo barazana ga zaman lafiya a yankin, tana mai kira a koma ga yarjejeniyar da Amurka ke mara wa baya da kuma kammala sauran sashe na yarjejeniyar Doha tsakanin DRC da M23/AFC.

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images
Fittaccen marubucin nan, Wole Soyinka ya soki tare da nuna damuwa kan yawan jami’an tsaro da ke tare da ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu.
A yayin jawabi a bikin lambar yabo da ake bai wa waɗande suke ƙoƙari a aikin jarida ta WSCIJ a Legas, Soyinka ya ce irin wannan yawan jami’an tsaro na nuna rashin daidaito a tsarin tsaro da kuma abubuwan da Najeriya ke fifitawa..
Ya bayyana cewa; "Yayin da nake fito wa daga otal ɗin da nake, sai na ga taron mutane, ni na ɗauka ma ana ɗaukar fim ne a filn otal din saboda yadda kusan duka rundunar tsaro suka mamaye filin otal ɗin da ke iIkoyi."
"Sai kuma na ga cewa ba haka bane, ashe wai jami'an tsaro ne da ke kare ɗan shugaban ƙasa ciki har da jami’an SWAT masu bindigogi da yawa, har kimanin 15,zagaye a wurin.
Soyinka ya ce abin ya ba shi mamaki har sai da ya kira mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, domin tabbatar da cewe hukumomi ne suka ba shi yawan jami'an tsaro kuma hakan ya dace.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai sun ce mutane fiye dubu 500 ne kawo yanzu aka tursasawa barin muhallansu a Thailand da kuma Cambodia a yayin da rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari.
Rundunar sojin Thailand ta ce Cambodia ta harba mata dubban makaman roka tun bayan da suka soma rikici da juna.
Dubban mutane ne suke guduwa domin tserewa lugudan makaman roka da ake harbawa daga Cambodia.

Asalin hoton, Getty Images
Kazalika Thailand ma na ci gaba da ke kai wa Cambodia hare-hare ta sama.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana kyautata tsammanin zai wayar tarho da shugabannin kasashen biyu wanda ya matsa musu lamba aka cimma kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yulin da ya gabata.
To sai dai ministan harkokin wajen Thailand ya gargadi Amurka akan amfani da wata barazana ko haraji domin tursasa komawa teburin sulhu don cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Siminalayi Fubara/Facebook
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana takaici kan ficewar gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, zuwa jam’iyya mai mulki ta APC tana mai cewa "ya ƙwari kansa ne kawai”.
A cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar, jam'iyyar ta ce Fubara ya fice ne da kansa kuma hakan ba zai musu illa ba saboda haka babu wanda za zargi jam'iyyar da yin watsi da shi.
Jam’iyyar ta ce tun farkon rikicin da ya dabaibaye gwamnatin Rivers, PDP da al’ummar Najeriya sun tsaya tsayin daka wajen kare martabarsa.
Ta kuma ce Fubara ba shi da dalilin ganin laifin jamʼiyyar game da halin da ya shiga a jiharsa, wanda ya sa ya koma APC
Sanarwar ta kuma gargaɗi Fubara cewa "Kada ya faɗa cikin halin da mutum ke fara goyon bayan wadanda suka tauye masa ’yanci inda jam’iyyar ta bayyana cewa tana masa fatan alheri ga duk matakin da ya dauka.

Asalin hoton, PDP
Jam’iyyar ta kuma yi nuni da cewa rikicin Rivers ya sake bayyana lalacewar tsarin dimokuradiyya a Najeriya, inda mutane ke zama mafi karfi da tasiri fiye da cibiyoyi da dokoki.
PDP ta zargi wasu a gwamnatin tarayya da amfani da karfin gwamnati wajen murkushe masu adawa, lamarin da ta ce barazana ce babba ga dimokuradiyya a kasar.
Jam'iyar ta kuma ce halin da ake ciki na nuna ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai bin tsarin jam’iyya ɗaya.

Asalin hoton, Getty Images
Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo da Burundi sun zargin Rwanda da karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla a ƙarƙashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump a ranar 4 ga Disamba, tsakanin Shugaba Félix Tshisekedi na DR Congo da Shugaba Paul Kagame na Rwanda a birnin Washington.
Shugaba Tshisekedi ya shaida wa majalisa cewa tashin tarzomar da ta sake kunno kai a lardin Sud Kivu, ciki har da harbe-harbe daga yankin Rwanda, na nuna “ƙin bin yarjejeniyar” da Rwanda ke yi.
Ya ce shekarar 2025 ta kasance ɗaya daga cikin lokaci mafi muni, domin ‘yan tawayen M23 da ake zargin Rwanda na goyon bayan su sun mamaye sassa na Nord da Sud Kivu masu arzikin ma’adinai.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yaƙi da abin da ya kira mamayar Rwanda a yankunan DR Congo, yana mai cewa matsalar tana da nasaba da kwasar ma’adinan kasar.
Tshisekedi ya ce M23 ba tawayen cikin gida ba ne yana mai bayyana rikicin a matsayin yaƙin wakilai da ke ƙoƙarin ƙalubalantar ikon DR Congo a yankin da ya kasance mahaɗa ga ma’adanan ƙasar.
Duk da kalubalen, ya ce DR Congo na nan kan bin tsarin zaman lafiya da Amurka ta ke mara wa baya.