Rufewa
A nan kuma muka kawo ƙarshen wannan shafin na yau. Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
A madadin sauran abokan aikina, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/10/2024
Umar Mikail da Nabeela Mukhtar da Badamasi Abdulkadir Mukhtar
A nan kuma muka kawo ƙarshen wannan shafin na yau. Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
A madadin sauran abokan aikina, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam a yankin Darfur na ƙasar Sudan ta ce dakarun ƙungiyar RSF da ƙawayensu sun ɗauki wani sabon salon kai farmaki kan ƙabilar Zaghawa.
Ƙungiyar mai suna The Human Rights and Advocacy Network for Democracy, ta ce hare-haren da ake kai wa ƙauyukan da ke Arewacin Darfur, sun faru ne a tsakanin 5 zuwa 7 ga watan Oktoban da muke ciki.
Ta ce an kashe mutum 40, sannan a ƙona ƙauyuka 16 ƙurmus sannan kuma yara da dama sun ɓace.
Tun a watan Afrilun bara ake fafata yaƙi tdakanin dakarun ƙungiyar RSF da sojojin Sudan don ƙwace ikon ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi Allah-wadai da hare-haren Isra'ila da suka yi sanadiyar illata dubban fararen hula a arewacin Gaza.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dubban mutane na cikin tsananin rashin abinci da sauran kayan buƙatun yau da kullum.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta zargi Isra'ila da wargatsa Gaza da kuma cutar da Falasɗinawan da ba su ji ba, ba su gani ba.
Sanarwar ƙungiyar ta biyo bayan harin da Isra'ila ta kai a wajen rabon abinci a sansanin ƴan gudun hijirah na Jabalia da ke arewacin Gaza lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 10.

Asalin hoton, TCN
Babban layin wutar lantarki na Najeriya ya samu tangarɗa, wanda hakan ya jawo rashin wuta.
Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja, wato AEDC ya fitar, inda a ciki yake ba kwastomominsa haƙurin rashin wutar.
A sanarwar, AEDC ya ce, "muna sanar da kwastomominmu cewa rashin wutar da suka fuskanta ya samo asali ne daga tangarɗar da aka samu daga babban layin lantarki na Najeriya yau (Litinin) da misalin ƙarfe 6:58."
A ƙarshe sanarwar ta tabbatar da cewa suna yin duk mai yiwuwa domin dawo rutar.
Idan babban layin lantarki ya samu tangarɗa, ana ɗauke ne baki ɗaya a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Asalin hoton, BBC/GIFT
Gwamnatin Najeriya ta yi hasashen kwashe kwana biyar ana mamakon ruwa, wanda zai iya jawo ambaliya a jihohi 22 na babban birnin tarayyar ƙasar, inda ta yi gargaɗi ga garuruwan da suke bakin tekunan Donga da Binue da Ogun su tashi daga yankunan.
Jaridar Punch ce ta ruwaito hakan a ranar Litinin daga ma'aikatar muhalli.
Rohoton na kwamitin bayar da gargaɗi na ma'aikatar ya ƙara da cewa za a iya fuskantar ambaliyar ne a ranar 14 da 18 na watan Oktoba.
Jihohin da yankunan da za su iya fuskantar ambaliyar sun haɗa da jihar Osun (Ede, Ile-Ife, Ilesa, Osogbo); jihar Delta (Escravos); jihar Kuros Riba (Ikom); jihar Anambra (Onitsha); jihar Taraba (Donga, Ibi, Wukari, Bandawa, Beli, Bolleri, Dampar, Duchi, Garkowa, Gassol, Gungun Bodel, Kambari, Kwata Kanawa, Lau, Mayo Ranewo, Mutum Biyu, Ngaruwa, Serti, Yorro); jihar Nasarawa (Rukubi); jihar Kebbi (Argungu, Birnin-Kebbi, Gwandu, Kalgo, Ribah, Sakaba, Yelwa); jihar Gombe (Bajoga); jihar Katsina (Bakori, Funtua); jihar Borno (Biu, Briyel); jihar Kaduna (Birnin-Gwari, Buruku, Kaduna, Jaji); jihar Niger (Bida, Kontagora, Lapai, Lavun, Magama, Mashegu, Mokwa, New Bussa, Rijau, Sarkin Pawa, Suleja, Wushishi).
Sauran su ne jihar Yobe (Dapchi); Adamawa (Demsa, Farkumo, Ganye, Gbajili, Jimeta, Mayo-Belwa, Mubi, Natubi, Numan, Song, Shelleng, Wuro Bokki); Kogi (Ibaji, Omala); Kwara (Jebba, Kosubosu); Bauchi (Kari, Tafawa Balewa, Kirfi); Plateau (Shendam); babban birnin tarayya Abuja (Kubwa, Gwagwalada, Bwari); Kano (Sumaila); Oyo (Kishi); Sokoto (Silame); da Zamfara (Majara).

Asalin hoton, Tinubu X
Shugaban ƙasan Najeriya Bola Tinubu ya yi wa ƴanwasan tawagar Super Eagles maraba da dawowa Najeriya bayan matsalar da suka fuskanta, sannan ya buƙaci a gaggauta bincike, tare da tabbatar da hukunci na adalci game da tirka-tirkar da ta faru da ƴanwasan Super Eagles a Libya.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai shi shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.
Tinubu ta buƙaci kwamitin ladabtarwa na CAF, "ta yi bincike, sannan ta bayar da shawarwarin irin hukuncin da ya kamata a ɗauka a kan waɗanda suka saɓa ƙa'idoji da dokokin hukumar."
Shugaban ya kuma yaba da ƙoƙarin ma'aikatar harkokin ƙasashen waje da ma'aikatar wasanni bisa ƙoƙarin da suka yi wajen shawo kan lamarin.
Haka kuma ya yaba da juriyar da ƴanwasan suka nuna duk da matsalar da suka fuskanta.
A ƙarshe ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa da su yi duk mai yiwuwa domin hana sake aukuwar irin wannan lamarin.

Asalin hoton, NTA/Facebook
Ƴan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya sun koma gida Najeriya, inda suka sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano da ke jihar Kano.
Wannan ya biyo bayan tirka-tirka da aka samu bayan ƴan wasan sun isa Libya domin fafatawa da abokan karawarsu na ƙasar Libya, duk da cewa hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta Libya ta ce ba ta da hannu a lamarin.
Najeriya ta je Libya ne domin fafata wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka ta 2025, inda aka samu tsaiko, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman a kafofin sadarwa, inda a ƙarshe hukumomi a Najeriya suka buƙaci ƴanwasan su koma gida, sannan ita ma CAF ta ce ta ƙaddamar da bincike a kan lamarin.
Yanzu da ƴan wasan na Najeriya sun sauka a Kano, kamar yadda shafin intanet na tashar talabijin NTA, mallakin gwamnatin Najeriya ya ruwaito.

Asalin hoton, AHMED ALIYU FACEBOOK PAGE
Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da yunƙurinta na fara sayar da shinkafa da sauran kayayyakin abinci, inda za ta sayar da su da ragowar kashi 55 na farashin kayayyakin abincin, wanda da ta sayo na naira biliyan 14.
Gwamna Ahmed Aliyu ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin bibiya da sa ido a kan sayar da kayan abinci a yau Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin rage wa mutane raɗaɗdin da suke ciki na tsananin rayuwa tun bayan cire tallafin man fetur, inda ya ce abincin zai kai dukkan mazaɓun jihar guda 244.
"Ku guji sanya bambancin siyasa ko addini wajen sayar da kayayyakin abincin. Wannan abinci ne na dukkan ƴan jihar Sokoto." in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiwatar da tallafi irin haka har zuwa lokacin da tattalin arzikin ƙasar zai bunƙasa.
A ƙarshe ya yi kira ga masu hannu da shuni a jihar da kamfanoni, da su taimaka wajen rage wa mutane halin raɗaɗin da mutane suke ciki.

Asalin hoton, AFP
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Falasɗinu, UNRWA, ta sanar da cewa, "sojojin Isra'ila sun kai hare-hare ta sama a ciki da wajen cibiyar raba tallafin abinci a Gaza, inda mutum 10 suka rasu, kusan 40 suka jikkata.
Hukumar ta ce wannan na zuwa ne "a daidai lokacin da mutane da yunwa ta yi wa katutu suke ƙoƙarin karɓar abinci a cibiyar."
Rundunar tsaron Isra'ila, IDF tana ƙara zafafa hare-hare a Jabalia a cikin ƴan kwanakin nan da suka gabata, inda ta ce tana hare-haren ne a kan ƴan Hamas da suke ƙoƙarin sake haɗuwa domin kai wasu hare-haren.
Sai dai IDF ɗin ta ce tana nazarin bayanan da aka fitar a game da harin na cibiyar, inda kakakinta ya ƙara da cewa hare-harensu na tsayawa ne "a kan ƴan ta'adda kaɗai" kuma ba sa kai hare-hare a kan fararen hula.

Asalin hoton, caf
Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika CAF ta sanar da cewa ta samu bayanai kan abin da yake faruwa tsakanin hukumomin kwallon kafa na Najeria da Libya a wasan neman gurbin shiga gasar kofin ƙasashen nahiyar ta 2025.
CAF ta ce ta tuntuɓi hukumomin kwallon kafar ƙasashen Najeriya da na Libya domin jin abin da yake faruwa game da yadda tawagar Super Eagles ta maƙale a filin jirgin sama da ke Libya awanni masu yawa, bayan nan aka ce su sauka.
A yanzu dai Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika ta gabatar da wannan matsala ga kwamitin ladabtarwarta domin bincike tare da ɗaukar mataki kan wanda ya karya dokar hukumar.
Tuni dai ƴan wasan Super Eagles suka kama hanyar komawa gida Najeriya, bayan Super Eagles ta yi zargin cewa da gangan hukumomin Libya suka sauya filin jirgin da ya kamata su sauka, yayin da ita ma hukumar ƙwallon Libya ke cewa sun fuskanci irin wannan matsalar lokacin da suka je Najeriya.

Asalin hoton, EPA
Amurka ta buƙaci Isra'ila da ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da fararen hula a cigaba da yakin da take yi a ƙasar Lebanon.
Sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Isra'ila Yoav Gallant.
Ana ci gaba da nuna damuwa game da yadda sojojin Isra'ila ta kai wa dakarun wanzar da zaman lafiya hari kai tsaye a ranar jiya Lahadi, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi zargi n cewa da tankokin yaƙin Isra'ila ne aka kutsa cikin wani sansaninta.

Asalin hoton, Getty Images
Burtaniya ta sanar da saka jerin takunkumi kan wasu manyan sojojin ƙasar Iran da ƙungiyoyi sakamakon harin da Iran ɗin ta kai wa Isra'ila ranar 1 ga watan Okotoba.
Mutanen da takunkumin ya shafa sun haɗa da Abdol rahim Mousavi, wanda kwamanda ne na sojojin Iran sannan kuma mamba na majalisar ƙoli ta tsaro ta Iran da kuma Hamid Vahedi wanda shi kuma kwamanda a rundunar sojin saman na Iran.
Mutanen da aka sanyawa takunkuman za su fuskanci haramci tafiye-tafiye da kuma hana su amfani da kuɗaɗensu, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Burtaniyar ta sanar.
Hukumar kula da sararin samaniyyar ƙasar Iran wadda ke ƙera fasahohin da ake amfani wajen ƙera makamai masu linzami da ke gudun ƙifta ido, ita ma takunkumin ya shafe ta ta hanyar hana ta amfani da kuɗaɗ da kadarori.
A ranar 1 ga watan oktoba ne dai Iran ɗin ta ƙaddamar da hari a kan Isra'ila inda ta aike da makamai masu linzami masu gudun kiftawa da Bisimilla fiye da 180.
Sojojin Isra'ila sun ce sun kama mafi yawan makaman.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce taa ci gaba da bincike kan wani matashi da ake zargin ya hallaka kakarsa.
Ƴan sandan sun ce lamarin ya auku ne a ƙaramar hukumar Sule Tantankarkar a jihar ta Jigawa a sakamakon yadda Kakar matashin ta ke yawan tambayarsa yaya jikinsa, shi kuma ya nuna ɓacin ransa cewa baya so amma taki dainawa.
Kakakin ƴansandan jihar Jigawa, DSP Lawan Adam Shiisu ya ce suna tsare da matashin mai shekara 26, kuma ya ce binciken farko-farko da suka gabatar ya nuna cewa yana fama da matsalar ƙwaƙwalwa.
Bugu-da-ƙari DSP Lawan Adam Shiisu kakakin ƴan sandan jihar Jigawa ya ce bayanan da suka tattara sun nuna cewa bai taɓa auka wa wani ba, kuma ya ce za su kai shi asibitin ƴansanda don tabbatar da ikirarin da danginsa suka yi na cewa yana fama da larurar ƙwaƙwalwa.

Asalin hoton, @abikedabiri
Tawagar Super Eagles ta 'yanwasan Najeriya ta kama hanyar komawa gida bayan shafe kusan awa 15 a filin jirgin sama na ƙasar.
Shugabar hukumar 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da hakan a shafinta na X bayan ɗanjarida Adepoju Tobi Samuel ya ce suna shirin shiga jirgin komawa.
Hakan na nufin Najeriya ba za ta buga wasan neman shiga gasar Kofin Afirka ba da aka tsara a gobe Talata da Libya, bayan tashi wasan farko Nigeria 1-0 Libya a makon da ya gabata.
Tawagar ta Super Eagles ta yi zargin da gangan hukumomin Libya suka sauya filin jirgin da ya kamata su sauka, yayin da ita ma hukumar ƙwallon Libya ke cewa sun fuskanci irin wannan matsalar lokacin da suka je Najeriya.
Yanzu kallo ya koma kan hukumar ƙwallon Afirka Caf domin ganin hukuncin da za ta ɗauka game da lamarin.

Asalin hoton, Getty Images
Ministan lafiya a ƙasar Zimbabwe ya sanar da ɓullar cutar ƙyandar biri karon farko a ƙasar.
Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa waɗanda aka samu da cutar sun haɗa da wani yaro mai shekara 11, da wni matashi mai shekara 24, waɗanda suka yi tafiya daga Afirka ta Kudu da Tanzania a cikin watannin Agusta da Satumba.
Sanarwar da ma'aikatar lafiyar ƙasar ta fitar ta ce: ''Yanzu haka an keɓe dukkan mutanen biyu kuma suna samun kula yadda ya kamata''
Sai dai ma'aikatar lafiyar ta ce ''abubuwa sun lafa'' domin haka suke kira ga jama'ar gari ''kada su razana.''
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana dokar ta-ɓaci kan yaƙi da ƙyandar biri ne bayan cutar ta yaɗu daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo zuwa ƙasashe masu maƙotaka da ita.
Ita ma cibiyar yaƙi da yaɗuwar cutuka ta Afirka ta ayyana dokar ta-ɓaci a kan cutar, wadda ta ce tana barazana ga al'ummar nahiyar.

Asalin hoton, LFF
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya (LFF) ta ce ba da gangan aka bar tawagar Super Eagles ta Najeriya yashe a filin jirgi ba, duk da cewa su ma an yi musu hakan a Najeriyar.
“Mun damu matuƙa kan abin da ya faru da tawagar ƙwallon ƙafan Najeriya, gabanin wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Afirka," in ji sanarwar da ta wallafa a shafinta na X.
"Dduk da dai mun yi nadamar abin da ya faru, muna kuma jan hankali cewa irin wannan matsala tana iya faruwa bisa kuskure a kowanne lokaci, ko dai saboda ƴan gyare-yare a filin jirgi ko saboda binciken jami'an tsaro ko kuma wasu ƙalubale na daban daga jiragen saman ƙasa da ƙasa.
''Muna matuƙar mutunta Najeriya, kuma muna bayar da tabbacin cewa ba da gangan aka samu wannan matsala ta karkatar da jirgin tawagar Super Eagles ba.
"Mu ma mun fuskanci irin wannan matsala lokacin da muka je Najeriya a makon da ya gabata, amma ba mu zargi hukumomi da aikata hakan da gangan ba."
Bayan wasan farko da Najeriya ta doke Libya 1-0 a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a ranar Juma'a, an tsara buga wasa na biyu a birnin Benghazi na Libya ranar Talata.

Asalin hoton, NFF
Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya William Troos-Eckong ya jaddada cewa za su baro Libya ba tare da buga wasan neman shiga kofin Afirka ba.
Cikin wani saƙo da yake ta wallafawa a shafinsa na X, kyaftin ɗin ya ce ana zuba wa jirgin da ya kai su mai yanzu haka.
"Yanzu haka ana zuba wa jirginmu mai kuma nan gaba kaɗan za mu tafi gida Najeriya. Mun gode da goyon bayanku," a cewarsa.
Hukumar ƙwallon ƙafar Najeriya ta NFF ta ce 'yanwasan nata sun shafe kusan awa 15 suna jira a filin jirgin, kafin daga baya su kwana a can.
Karanta cikakken labarin abin da ke faruwa a nan: Ba za mu buga wasa da Libya ba - Super Eagles

Asalin hoton, EPA
Ƙungiyar agaji ta likitoci Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce a cikin watanni takwas ɗin farko na wanan shekarar ta bayar da magani ga ƙananan yara 52,725 masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki a arewacin Najeriya.
Shugaban MSF, Dr Christos Christou, ya shaida wa manema labarai a Abuja a ƙarshen mako cewa adadin yara masu fama da ƙarancin abinci mai gina jikin ya ninka a arewacin Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce daga watan Janairu zuwa Agusta, MSF ta tattara alkaluma da ke cewa an samu ƙarin ƙananan yara da ake kwantarwa asibiti saboda da kashi 51 cikin 100.
''Ana cikin haka kuma sauran cutuka masu kama ƙananan yara sun samu damar shiga jikin yara da dama a Najeriya.," in ji shi.
Dr Christou ya ƙara da cewa sun yi maganin sauran cutuka ga ƙananan yara 12,500 bayan waɗanda ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki, lamarin da ke nuna cewa yawansu ya ruɓanya wanda aka samu a bara.

Asalin hoton, NFF
Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu hukumomin Libya sun ƙi amince tawagar ofishin jakadancin ƙasar ya ziyarci 'yanwasan Najeriya da suka maƙale a filin jirgin sama na Libyar.
MInistan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ya ce yana bin halin da tawagar ke ciki "sau da ƙafa" bayan hukumomi sun sauya akalar jirgin tawagar ta Super Eagles zuwa wani ƙaramin filin jirgi maimakon na Benghazi da aka tsara tun dafarko.
"Tun daga daren da ya wuce, ofishin jakadancin ya yi ta magana da tawagar da kuma hukumomin Libya ƙarƙashin jagorancin Jakada Stephen Anthony Awuru," in ji ministan cikin wani saƙo a shafinsa na X.
"Duk da ƙoƙarinmu, hukumomin Libya sun ƙi ba da izinin zuwa birnin Bayda inda filin jirgin yake."
Hukumar ƙwallon ƙafar Najeriya ta NFF ta ce 'yanwasan nata sun shafe kusan awa 15 suna jira a filin jirgin, kafin daga baya su kwana a can.
Karanta cikakken labarin abin da ke faruwa a nan: Ba za mu buga wasa da Libya ba - Super Eagles