Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/10/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/10/2024

Taƙaitattu

  • Hukumar zaɓen Rivers ta ce ba gudu ba ja da baya kan zaɓen ƙananan hukumomi
  • PDP ta buƙaci mambobinta su shiga zaɓen ƙananan hukumomin Rivers
  • Abubuwa shida kan zaɓen ƙananan hukumomi a Rivers mai cike da taƙaddama
  • Jihohin Najeriya huɗu na gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a yau
  • An kashe shugaban sashen soji na Hamas tare da iyalinsa a Lebanon- rahotonni
  • Ƙasashen duniya na rubibin kwaso mutanensu daga Lebanon

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Shugaban Faransa ya yi kiran a gaggauta tsagaita wuta a Lebanon

    Emmanuel Macron

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yu kiran a gaggauta dakatar da buɗe wuta a Lebanon.

    Ya yi kalaman ne da yawun kungiyar kasashen da ke amfani da harshen Faransanci, wanda Lebanon mamba ce a cikinsu.

    Mr Macron ya kara da cewa ya yi nadamar matakin da firaiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ɗauka na kai samame ta ƙasa.

    Dubban magoya bayan Falasdinawa ne sukai maci a biranen Faransa da wasu kassashen duniya, tare da kiran a dakatar da buɗe wuta a Gaza, da kawo ƙarshen tashin hankali a yankin gabas ta tsakiya.

  2. Ƴan sanda sun ƙaddamar da bincike kan fashewar wasu abubuwa a jihar Rivers

    Ƴan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴan sandan jihar Rivers ta ce ta fara bincike kan tashin wasu abubuwan fashewar a birnin Fatakwal da sanyin safiyar Asabar.

    Kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko, ta ce abubuwan sun fashe ne a sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar da kuma wani a Rumuodumaya, hedikwatar ƙaramar hukumar Obio/Akpor.

    Ta ce: “Fashewar farko ta tashi ne a sakatariyar APC da ke kan titin Aba da misalin ƙarfe uku na safe, inda jami'in tsaron da ke wajen ya bayar da rahoton ganin wata baƙar mota ƙirar Hilux ta fice da gudu bayan tashin abin fashear.

    “Ta biyu kuma ta tashi a sakatariyar ƙaramar hukumar Obio/Akpor inda ta tarwatsa wani sashi na ginin da kuma gidan injin bayar da wuta''

    Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan ta fitar ta ce sashin binciken manyan makamai na rundunar ya kwashi wasu daga cikin abubuwan da aka samu a wajen kuma ya fara bincike domin gano inda suka fito da ɗaukar mataki na gaba.

    Rundunar ƴan sanda ta ce ba zata yi ƙasa a gwiwa ba wajen zaƙulo masu hannu a fashewar biyu.

  3. Ƴan sanda sun kama jagoran adawa a Pakistan

    Pakistan

    Asalin hoton, epa

    Jam'iyyar tsohon firaiministan Pakistan, Imran Khan ta ce ƴansanda sun kama ministan yankin Khyber Pakhtunkhwa, Ali Amin Gandapur.

    Jam'iyyar ta ce ƴansandan sun kutsa cikin gidansa da ke birnin Islamabad. Babu tabbacin ko an kama shi ne a hukumance.

    Ali Amin Gandapur yana daga cikin fitattun ƴan jam'iyyar PTI, kuma ya je babban birnin ƙasar ne domin shiga zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.

    An ci gaba da zanga-zanagr a kwana na biyu, inda ƴansanda suka rufe hanyoyin wucewa kuma an katse layukan waya.

    Akwai kuma rahoton kama masu zanga-zanga da dama a ranar juma'a.

  4. Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a Beirut

    Beirut

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a kudancin Beirut, wajen da cibiyar Hezbollah ta ke.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragen yaƙin ta sun kai hari a cibiyoyin gudanarwar ƙungiyar Hezbollah a babban birnin ƙasar Lebanon.

    Wani jami'in Hezbollah ya ce ƙungiyar ta daina samun zarafin magana da Hashem Safieddine, wanda ake tunanin shi ne zai gaji tsohon shugabanta, Hassan Nasrallah da aka kashe.

    Ma'aikatar lafiya a Lebanon ta ce harin Isra'ila na ranar Juma'a ya kashe mutum 25, kuma wasu fiye da 120 sun samu raunuka.

    Hezbollah ma ta harba makaman roka da yawa a arewacin Isra'ila, inda rahotanni ke cewa harin ya fada kan gidajen mutane.

  5. An fara rigakafin ƙyandar biri a DRC

    ƙyandar biri

    Asalin hoton, Getty Images

    An fara rigakafin cutar ƙyandar biri a birnin Goma na gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

    Ma'aikatar lafiya a Kinshasha ta ce an ɗauki matakin ne domin yaƙi da yaɗuwar cutar, wadda ta kashe kusan mutum dubu ɗaya a bana.

    Kashi 70 na mutanen da cutar ta kashe a ƙasar ƙananan yara ne ƴan ƙasa da shekara biyar.

    Za a fara yin rigakafin ne ga tsofaffi da ma'aikatan lafiya da ƴan uwan mutanen da suka kamu da cutar.

    Ƙungiyar tarayyar Turai da Amurka sun bai wa DRC agajin rigakafin ƙyandar biri d yawan shi ya kai fiye da dubu ɗari biyu.

  6. Jam'iyyar Imran Khan ta zargi 'yansandan Pakistan da tsare mata minista

    Imran Khan

    Asalin hoton, Reuters

    Jam'iyyar tsohon firaministan Pakistan, Imran Khan, ta ce 'yansanda sun tsare babban ministan lardin Khyber Pakhtunkhwa, Ali Amin Gandapur.

    PTI ta zargi 'yansanda da yin amfani da ƙarfi wajen kutsawa cikin gidansa da ke Islamabad, babban birnin ƙasar.

    Ba a dai sani ba ko kama shi aka yi a hukumance ba.

    Ali Amin Gandapur na ɗaya daga cikin manyan jagororin jam'iyyar PTI da suka je Islamabad domin shiga zanga-zangar adawa da gwamnati.

    Yau ne dai aka shiga kwana na biyu a zanga-zangar.

    'Yansanda sun rufe wasu titunan birnin yayin da aka katse sadarwar intanet da na wayar hannu.

    An kuma kama gomman masu zanga-zanga a ranar Juma'a.

  7. Ambaliya da zaftarewar ƙasa sun yi ajalin mutum 16 a Bosnia

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Wata mummunar ambaliya da zaftarewar ƙasa a tsakiyar Bosnia-Herzegovina sun yi sanadiyyar mutuwar mutum 16, yayin da garuruwa da ƙauyuka suka yanke bayan rushewar gidaje da dama.

    Wasu wurare da lamarin ya fi ƙamari irin su Jablanica, wani gari da ke tsakanin manyan biranen Sarajevo babban birnin ƙasar da kuma Mostar.

    Rahotonni sun ce mutane da dama sun ɓace, yayin da aka ayyana dokar ta ɓaci a ƙasar.

    Ministan harkokin gine-gine na ƙasar, Vojin Mijatovic ya ce ƙasar ta fuskanci mummunan bala'i, sai dai ya yi kiran a kwantar da hankula.

    Ana dai ci gaba da aikin ceto a faɗin ƙasar domin nema mutanen da har yanzu ba a gani ba.

  8. An girke tarin jami'an soji a yankin Amhara

    Rahotonni daga jihar Amhara da ke arewacin Ethiopia sun ce an girke tarin jami'an sojojin ƙasar a yankin cikin mako biyu da suka gabata.

    Majiyar tsaro da ƙungiyar Amnesty International sun ce an kama mutane da dama ciki har da jami'an yankin bisa zargin haɗa baki da ƙungiyar Fano ta mayaƙan ƙabilar Amhara.

    To sai dai BBC ba ta iya tantance wannan iƙirari ba, yayin da hukumomi suka taƙaita shiga yankin.

    Tun a shekarar da ta gabata gwamnatin tarayyar Ethiopia ta ayyana dokar ta ɓaci a yankin Amhara, bayan da masu tayar da ƙayar baya suka faɗaɗa hare-hare kan dakarun ƙasar tare da ƙwace iko da wasu garuruwa.

  9. Hotunan ɓarnar da aka samu a Beirut bayan shafe tsawon dare ana luguden wuta

    Ga wasu daga cikin hotunan irin ɓarnar da aka samu a birnin Beirut bayan shafe tsawon daren jiya ana luguden wuta a birnin.

    Tun da farko dai sojojin Isra'ila sun fitar da gargaɗi daga mazauna wasu sassan birnin da suka ce yankunan da Hezbollah ke zaune a wurin.

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, EPA

    ..

    Asalin hoton, EPA

  10. Fiye da mutum 200,000 ne suka tsere daga Lebanon zuwa Syria - MDD

    Masu tsere wa yaƙi

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar dinkin Duniya ta ce fiye da mutum 200,000 ne suka fice daga Lebanon zuwa Syria mai maƙwabtaka ''sakamakon hare-haren Isra'ila ta sama''.

    Babban kwamishinan Majalisar mai kula da 'yan gudun hijira, Filippo Grandi, ya ce wannan adadi ya ƙunshi 'yan Labanon da 'yan Syria, da ke zaune a Lebanon.

    A nata ɓagare gwamnatin Lebanon ta ce adadin mutanen da suke fice daga ƙasar zuwa Syria ya kai 300,000.

    Wani hari da Isra'ila ta kai jiya Juma'a ya faɗa kusa da mashigar kan iyakar ƙasashen biyu, lamarin da ya hana ababen hawa bi ta mashigar.

    Sojojin Isra'ila sun ce kai harin ne kan mayaƙan Hezbollah a kusa da mashigar ta Masnaa, wadda suka yi iƙirarin cewa ƙungiyar na amfani da ita wajen safarar makamai zuwa Lebanon.

    A yanzu mutane na ci gaba da bi ta mashigar da ƙafafunsu, domin ficewa daga ƙasar.

  11. Ƙasashen duniya na rubibin kwaso mutanensu daga Lebanon

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Ƙasashen duniya na ci gaba da kwaso mutanensu daga Lebanon, yayin da jiragen sama ke tashi daga filin jirgin saman birnin Beirut, duk da hare-haren da ke gudana a wasu sassan birnin.

    Manyan jiragen Birtaniya uku ne suka tashi da ɗaruruwan fasinjoji yayin da ake sa ran na huɗun zai tashi ranar Lahadi.

    Aƙalla ƙasashe 23 ne ke ƙoƙari kwaso mutanensu daga ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Inda wasu ke samun tikiti a jiragen ɗaukar fasinja, yayin da wasu kuma ke aika jiragen soji domin kwaso mutanen nasu.

    Ko a yau ma jirgin sojin saman Koriya ta Kudu ya kwashi 'yan ƙasar 97 daga Lebanon zuwa gida.

  12. An samu fashewa a sakatariyar APC ta tsagin Tony Okocha a jihar Rivers

    Apc

    Asalin hoton, APC

    An samu wata babbar fashewa da ta lalata ginin ofishin sakatariyar jam'iyyar APC tsagin Tony Okocha, a jihar Rivers, da ke kan titin Aba a Fatakwal, babban birnin jihar.

    Fashewar - wadda ta faru ranar Sabar da asuba - ta lalata babbar ƙofa da sauran ƙofofi da tagogin sakatariyar.

    Lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da al'ummar jihar ke gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a faɗin jihar mai cike da taƙaddama.

    Yayin da yake zantawa da gidan talbijin na Channels, shugaban tsagin jam'iyyar, Tony Okocha ya yi zargin cewa harin wata maƙarƙashiyar siyasa ce.

  13. Hezbollah ta ce ta harba rokoki kan sansanin sojin saman Isra'ila a kusa da Haifa

    Hezbollah ta ce ta harba makaman roka kan sansanin sojin saman Isra'ila na Ramat David da ke kusa da birnin Haifa a arewacin Isra'ila.

    A wasu bayanan na baya-bayan nan ƙungiyar ta ce wani harin makaminta mai linzami ya faɗa kan wata tankar yaƙin Isra'ila a kusa da kan iyakar Isra'ila da Lebanon.

    Kawo yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba game da batutuwan, to amma an ji ƙarar jiniyar ankararwa a faɗin arewacin ƙasar da safiyar yau.

  14. An kashe shugaban sashen soji na Hamas tare da iyalinsa a Lebanon- rahotonni

    Rahotonni daga Lebanon na cewa an kashe shugaban sashen rundunar soji ta Hamas, Saeed Atallah tare da iyalinsa a Lebanon.

    Jaridar Filastin mai alaƙa da Hamas ta bayar da rahoton kisan Atallah a sansanin 'yan gudun hijira na Tripoli da ke kudancin Lebanon tare da iyalinsa.

    Ita ma jaridar An-Nahar ta ƙasar Lebanon ta ce an kashe shi tare da matarsa ta 'ya'yansa biyu.

    Wani hari ta sama - da jaridar An-Nahar ta danganta da jirgin Isra'ila maras matuƙi - ne ya tarwatsa gidan da Atallah tare da iyalinsa ke zaune.

    Yayin da har yanzu Hamas ba ta tabbatar da mutuwar Atallah ba, ƙungiyar Jihadin Falasɗinawa (PIJ), mai ƙawance da Hamas ta tabbatar da kisan Atallah tare da matarsa da 'ya'yan biyu mata.

  15. Jihohin Najeriya huɗu na gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a yau

    Masu aikin zaɓe

    Masu zaɓe a jihohi huɗu a Najeriya sun fara kaɗa ƙuri'a don zaɓen sabbin shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli.

    Jihohin da ake gudanar da zaɓukan a yau sun haɗa da Rivers da Benue da Akwa Ibom da kuma jihar Jigawa.

    Ana hasashen cewa jam'iyyu masu mulkin jihohin ne za su lashe duka zaɓukan ƙananan hukumomin da na kansiloli.

    Ko a baya-bayan nan ma zaɓukan ƙananan hukumomi da aka gudanar a wasu jihohin ƙasar, jam'iyyu masu mulkin jihohin ne suka lashe duka kujerun.

    Wannan wata al'ada ce ta zaɓukan ƙananna hukumomi a Najeriya, lamarin da masu sharhi ke ganin cewa na daga cikin abubuwan da ke rage wa zaɓukan ƙananan hukumomin karsashi da farin jini.

    Haka kuma wasu na fargabar hakan ka iya kawo cikas ga hukuncin kotun ƙolin ƙasar, na bai wa ƙananan hukumomin cikakken 'yancin cin gashin kai.

  16. PDP ta buƙaci mambobinta su shiga zaɓen ƙananan hukumomin Rivers

    ..

    Asalin hoton, PDP

    Jam'iyyar PDP ta ƙasa a Najeriya ta yi kira ga mambobinta a jihar River su shiga zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ake gudanarwa a yau Asabar.

    Tun da farko dai PDP ta ce ba za ta shiga zaɓen ba, sakamakon umarnin wata kotu da ta ce a dakatar da gudanar da zaɓen.

    To sai dai cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa, Hon. Debo Ologunagba ya fitar ya yi kira ga 'yan jam'iyyar da su fito domin gudanar da zaɓen kamar yadda dokar ƙasa ta ba su dama.

    Ita dai hukumar zaɓen jihar ta ce ba gudu ba ja da baya kan aniyarta na gudanar da zaɓukan a yau Asabar.

    Shi ma gwamnan jihar wanda ɗan jam'iyyar PDP ne, ya kafe cewa sai an gudanar da zaɓen, yayin da duka 'yan takatar da yake mara wa baya suka koma jam'iyyar APP inda suke takarar a can, lamarin da ya sa wasu ke ganin cewa gwamnan na kan hanyar ficewa daga PDP.

    To sai dai har yanzu gwamnan bai bayyana 'ƙarara', cewa zai fice daga PDPn ba.

  17. Hukumar zaɓen Rivers ta ce ba gudu ba ja da baya kan zaɓen ƙananan hukumomin jihar

    ..

    Hukumar zaɓen mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta ce ta kammala shiryawa tsaf! domin gudanar zaɓukan ƙananan hukumomin jihar a yau Asabar.

    Rundunar 'yansandan jihar ta ce ba za ta samar da tsaro ba a lokacin zaɓen, saboda yin biyayya ga umarnin kotu.

    A cikin makon da ya gabatan ne dai wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da umarnin ɗage zaɓen.

    Lamarin da ya sa jam'iyyar PDP da APC a jihar suka gudanar da zanga-zanga tare da ƙaurace wa zaɓen.

    To sai dai hukumar zaɓen jihar ta nuna rashin amincewarta da hukuncin kotun, sakamkon samun hukuncin wata babbar kotun jihar Rivers.

    Jami'in hulɗa da jama'a da wayar da kan masu zaɓe na hukumar, Tobin Tamunotonye ya ce hukumar zaɓen jihar za ta gudanar da zaɓukan na yau ba gudu ba ja da baya.

  18. Assalamu alaikum

    Masu bin shafinmu na BBC Hausa kai-tseye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku labaran halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu.