Amurka ta jaddada yunƙurin ficewa daga hukumar makamashi ta duniya

Asalin hoton, Getty Images
Sakataren Makamashi na Amurka, Chris Wright, ya sake sabunta barazanar ficewar kasarsa daga Hukumar kula da Makamashi ta Duniya.
Mista Wright ya shaidawa taron ministocin kasashen kungiyar a birnin Paris cewa, kamata ya yi hukumar ta koma kan aikinta na tabbatar da wadatuwar makamashi.
Ya kara da cewa kamata ya yi ta yi watsi da abin da ya kira, mafarkin da take yi cewa, za a iya cimma lokacin da ba a fitar hayakin mai gurbata muhalli, a bisa yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris a shekarar 2015.
Amma Mista Wright ya nuna cewa Washington za ta yi jinkirin ficewa saboda hakan na iya bai wa China damar mamaye hukumar makamashi ta duniya.














