Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 31/05/2024.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Rabiatu Kabir Runka

  1. Sakamakon zaɓen Afirka ta Kudu

  2. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye nan muka kawo karshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Sai kuma gobe Idan Allah ya kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, muke cewa mu kwana lafiya

  3. Biden ya yi kira ga Isra'ila da Hamas su amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta

    Shugaba Biden na Amurka ya yi kira ga Isra'ila da Hamas su amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita a yakin da suke yi tsakaninsu.

    Yarjejeniyar za ta sa jami'an Isra'ila su tsagaita wuta ta tsawon mako shida, sannan Hamas ta saki Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su - a kuma saki Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen yari a Isra'ila.

    Yarjejeniyar ta yi tanadin Isra'ila za ta janye daga yankunan Gaza sannan ta kyale a rika shiga da kayayyakin agaji.

    Yayin da za a a ci gaba da tattaunawa, yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki har a kai ga sakin duka wadanda aka yi garkuwa da su.

    Daga nan dakarun Isra'ila su fice daga Gaza Falasdinawa su koma gidajensu su ci gaba da rayuwa.

  4. Tsohon kakakin majalisar Iran zai tsaya takarar shugabancin kasar

    Kakakin majalisar Iran har sau uku kuma tsohon mai shiga tsakani kan harkokin nukiliya, Ali Larijani, ya yi rijistar shiga takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

    Akwai bukatar majalisar amintattun kasar ta sahale wa takarar tasa, wadda a baya ta hana shi shiga takarar.

    Mista Larijani - wanda mai matsakaicin ra'ayi ne - ya yi alƙawarin farfado da tattalin arzikin Iran.

    Kawo yanzu saura makoi hudu a yi zaɓen kasar.

    An dai matso da zaɓen ne sakamakon mutuwar tsohon shugaban ƙasar Ibrahim Rasi a haɗarin jrgin sama.

  5. Kungiyoyin agaji sun yi gargadin aukuwar bala'in yunwa a Sudan

    Kungiyoyin agaji na duniya sun yi gargadin barazanar bazuwar bala'in yunwa a kasar Sudan, matsawar ba a ba su damar shiga yankunan da ke bukatar tallafin ba.

    Sun kara da cewa ana kashe ma'aikatansu da dama, tare da jikkata wasu da muzgunawa wasu da kuma kwace kayan agajin.

    Kusan mutum miliyan tara ne suka tsere daga gidajensu, tun lokacin da yaki ya barke a watan Afrilun shekarar da ta gabata.

    Kawo yanzu duka bangarorin da ke yaki da juna sun yi biris da kiran tsagaita wuta a yakin.

    Kungiyoyin agaji 19 sun sake kiran kare fararen hula domin samun damar shigar musu da kayan tallafi.

    Sun ce munanan hare-hare kan fararen hula, ciki har da cin zarafinsu ta hanyar lalata na ci gaba da karuwa, musamman a asibitoci da makarantu.

    Kungiyoyin da aka haramta wa shigar da kayan agaji sun ce akwai bukatar bayar da dama wajen shigar wa manoma irin shuka.

  6. Jami'an Faransa sun dakile harin da aka shirya kai wa lokacin Olympics

    Jami'an tsaron Faransa sun ce sun dakile wani hari da aka shirya kai wa a birnin Paris lokacin wasan Olympics a ƙarshen watan Yuli.

    Ministan cikin gidan ƙasar ya ce wani yaro dan shekara 18 da aka kama a farkon watannan dan yankin Chechenya, ake zargi da shirya kai harin a filin wasan kwalon kafa na St Etienne.

    Idanuwan Faransa a buɗe suke a yayin wasannan Olympics din, wanda miliyoyin mutane za su halarta domin kallo.

  7. Ko Trump zai iya yin takara bayan samun sa da laifi?

  8. Amurka za ta tallafa don sake gina makarantu da asibitoci a Gaza - Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ana bukatar hanyar sasanci domin kawo karshen yakin yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da daidaita lamurra a kan iyakar arewacin Lebanon.

    Mista Biden ya ce akwai bukatar shugabannin Falasdinawa da na Isra'ila su hada kai domin sake gina Gaza, ta yadda ba za a bar Hamas ta sake mallakar makamai ba.

    ''Amurka za ta tallafa wajen sake gina makarantu da asibitocin Gaza'', in ji Biden.

    Ya kara da cewa shirin zai taimaka wajen sake daidaita lamurran dangataka da Saudiyya da magance barazanar Iran a yankin.

    Mista Biden ya kuma gabatar da kudurin da zai bai wa Isra'ila damar zama mai karfi a yankin.

  9. Yadda giwaye ke kwacen abinci a hannun mutane

    Giwaye a kasar Sri Lanka sun fahimce cewa abinci da sauran abubuwan da mutane ke ci ya fi dadi, don haka suka fara tare mutane a kan ababen hawa domin kwacen abinci.

    A wasu lokutan giwayen kan tsaya a tsakiyar titi, ta yadda babu abin hawan da zai wuce ba tare da an ba su abincin ba.

    Giwayen sun saba da abincin mutane sosai .

    Kalli bidiyon domin ganin yadda giwayen ke tare ababen hawa domin kacen abinci.

  10. Gwamnatin Abia ta sa ladan N25m ga wanda ya fallasa mutanen da suka kashe sojoji

    Gwamnatin jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya ta saka ladan naira miliyan 25 ga duk mutumin da ya bayar da bayanan da za su taimaka a kama mutanen da suka kashe sojoji a jihar.

    Cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Okey Kanu ya fitar, gwamnatin jihar ta aike da sakon ta'aziyya ga babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja kan faruwar lamarin.

    A ranar Alhamis ne wasu 'yan bindiga suka afka wa sojoji a wani shingen bincike a mahadar Obikabia da ke yankin tsaunin Ogbor, tare da kona motar aikinsu.

    Rahotonni sun ce wasu sojojin sun samu tsallake rijiya da baya a harin.

    “Domin samun saukin kama maharan, gwamnati ta yi alkawarin bayar da ladan naira miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama su,'' in ji sanarwar.

    Tun da farko dai sojojin kasar sun dora alhakin harin kan mayakan kungiyar IPOB da takwawarta ta ESN.

    Mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce an kai sojojin yankin ne domin aikin wanzar da zaman lafiya.

  11. Labarai da dumi-dumi, Ƙungiyoyin TUC da NLC za su tsunduma yajin aiki ranar Litinin

    Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na TUC da NLC a Najeriya sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin cimma yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

    Gamayyar ƙungiyoyin sun sanar da hakan ne da yammacin ranar Juma'a bayan wani taro da suka yi inda suka tattaunawa yiwuwar tsunduma yajin aikin.

    A farkon makon nan ne dai manyan ƙungiyoyin ƙwadago guda biyu suka yi watsi da tayin naira 60 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, biyo bayan zaman da suka yi da gwamnatin tarayya, inda a nan ne gwamnatin ta yi tayin.

    Da farko dai sai da gwamnatin Najeriyar ta fara kara naira dubu uku a kan tayin naira dubu 47 da ta yi a baya.

    Su ma ƙungiyoyin ƙwadagon sun rage dubu uku daga naira 497 da suke nema a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.

  12. Trump zai daukaka kara bayan samunsa da laifi

    Tsohon shugaban Amurka, Donal Trump ya ce zai daukaka kara bayan samunsa da laifi da kotun New York ta yi ranar Alhamis.

    Cikin wani jawabi na tsawon miti 40 da ya gabatar wa manema labarai, mista Trump ya ce ''Za mu daukaka kara kan wannan balahira''.

    "Za mu daukaka kara ta hanyoy da dama,'' in ji Trump wanda ya yi korafi kan matakin alkalin kotun.

    Tsohon shugaban ya kuma zargi alkalin da rashin bai wa bangarensa damar kare kansu a shari'ar

    "Bai bar muka gabatar da shaidarmu ba, baya bari mu yi magana, baya barinmu mu yi komai, alkalin azzalumi ne," in ji mista Trump.

  13. Ba a tuhumar Allah kan ƙaddara – Sarki Sanusi

    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce babu wanda zai iya tuhumar Allah dangane da ƙaddara. Sabon sarkin ya faɗi hakan ne yayin huɗubar sallar Juma'a a masallacin sarki da ke Ƙofar Kudu a birnin Kano.

    Huɗubar dai ta mayar da hankali ne kan imani da ƙaddara mai kyau ko marar kyau.

    " Duk wanda ya yi imani da Allah shi kaɗai to dole ne ya yi imanin duk abin da Allah ya ƙaddara. Ba a tambayar ubangiji dalilin aiwatar da al'amura.

    An faɗa mana cewa duk wanda bai yarda da ƙaddara ba cewa daga Allah take, imaninsa bai cika ba. Ya kamata mu zama masu godiya ga Allah a yanayi daɗi ko wuya. Dole ne mu yarda cewa duk abin da ya faru a gare mu ta ƙaddara ce daga Allah, sannan abin da ba mu iya samu ba shi ma daga Allah ne." In ji Sarki Sanusi.

    Daga ƙarshe sarkin ya ja hankalin masallatan da su mayar da hankali kan kwanaki 10 na watan Dhulhijja da ke ƙaratowa.

    "Watan babbar sallah na ƙara tunkarowa wanda kuma yana da matuƙar muhimmanci, ya kamata mu mayar da hankali wajen addu'o'i a kwanakin." In ji Sarki Sanusi.

    Daga nan ne kuma Muhammadu Sanusi ya ja sallar ta Juma'a.

    Da ma dai rundunar 'yan sanda jihar Kano ta ƙaryata labaran da ke yawo a birnin cewa akwai yiwuwar yin arangama tsakanin Muhammadu Sanusi da Aminu Ado Bayero a masallacin.

    Masu sarautar biyu dai sun kwashe mako guda kowa na iƙrarin kasancewa Sarkin Kano.

  14. Dubban 'yancirani na ƙoƙarin shiga Malasiya

    Dubban 'yancirani ma'aikata da galibincu suka fito daga Bangladesh ne ke ƙoƙarin shiga Malasiya, gabanin cikar wa'adin da aka sanya musu. Sama da 'yan cirani dubu 12 ne ke kan layin a filin jirgi na Kuala Lumpur domin su ba da bayanansu ga hukumomi. Da yawa sun baro kasashensu ne a kurarren lokaci, shi ya sa suka gaza shi ƙasar da wuri.

    Wakilin BBC ya ce 'Akwai 'yancirani sama da miliyan biyu da ke aiki a Malasia, kuma mafi yawansu a kamfanonin gine-gine da gonakin kwakwar manja.

    Daga ranar Asabar gwamnatin ƙasar za ta daina karbar 'yancirani da ke neman aiki a Malasia - har sai ta duba yanayin bukatarsu da ke da ita.

  15. Sojojin Isra'ila sun janye daga yankin Jabaliya

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kammala kashi na biyu na hare-haren ramuwar gayyar da take kai wa yankin Jabalya da ke arewacin Gaza, bayan abin da ta kira artabu mafi muni a wannan yakin.

    Cikin sama da mako uku rundunar sojin tace an kai mata hare-hare fiye da 300.

    Wakilin BBC ya ce 'A nata martanin, Isra'ila ta ce ta kashe sama da mayakan Hamas 100 ta kuma lalata hanyoyin cikin ƙasa da suka kai tsayin kilomita 12 tare da gano gawarakin mutum bakwai cikin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su.

    A watan Janairu, Isra'ila ta yi ikirarin ta karbe iko da baki dayan yankin arewacin Gaza, amma dole suka fice daga yankin bayan mayakan Hamas sun koro dakarunta.

    Yaƙi ya ɓarke tsakanin sojojin Isra'ila da mayaƙan ƙungiyar Hamas a watan Oktoba na 2023 bayan da Hamas ta ƙaddamar da hari kan Isra'ila inda mutane 1,200 suka rasu, ta kuma yi garkuwa da mutane sama da 250 a Gaza.

    Ma'aikatar lafiyar Hamas ta ce mutum sama da dubu 36,000 ne aka kashe a Gaza.

  16. 'Ɗaliban Najeriya sama da miliyan tara ne suka nemi bashin karatu'

    Asusun bayar da bashin karatu na Najeriya (NELFUND) ya ce sama da ɗalibai miliyan 9.5 ne suka kai ziyara ofishinta dangane da bashin karatu da za a bai wa dalibai tun bayan buɗe shafin da za a cike takardar neman bashin karatun a ranar Juma’ar da ta gabata.

    Sama da ɗalibai 6,000 ne suka cike takardan neman bashin.

    Yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a taron da aka shirya wa ɗaliban da suka cike takardan neman bashin a ranar Alhamis, shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce sama da kashi 90 cikin 100 na manyan makarantun gwamnatin tarayya sun mika bayanan dalibansu da cibiyoyi kusan biyar da suka rage.

    Ya kuma bayyana cewa nan da makwanni uku za a bude shafin neman bashin ga daliban da ke manyan makarantu na gwamnati domin su samu su iya cike takardun neman bashin karatu biyo bayan korafe-korafen da daliban suka yi.

    Sawyerr ya kuma buƙaci shugabancin manyan makarantun gwamnati da su fara miƙa bayanan dalibansu domin tabbatar da tsarin bayar da bashin cikin sauƙi.

    A ranar 12 ga Yuni, 2023 ne Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu saboda ɗalibai marasa galihu su iya yin karatu a manyan makarantun ƙasar.

    • Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
    • Abin da ya sa daliban Najeriya ba sa samun ayyuka a wasu sassan Birtaniya
  17. Ramaphosa ba zai sauka daga muƙaminsa ba – ANC

    Mataimakiyar babban sakataren jam'iyyar ANC, Nomvula Mokonyane ta sanar wa manema labarai a cibiyar kirga kuri'un zaɓen da aka gudanar a Afrika ta Kudu cewa shugaba Cyril Ramaphosa ba zai sauka daga mukaminsa na shugaban jam'iyyar ba duk da rashin kyakkyawan sakamakon zaɓen da jam'iyyar ta samu.

    Da aka tambaye ta game da yuwuwar tattaunawar hadin gwiwa, Mokonyane ta bayyana cewa, a halin yanzu, jam’iyyar ba ta shiga tattaunawa da wasu jam'iyyu ko ƙungiyoyi ba.

    Ta kuma bayyana cewa a yau ne shugabannin jam'iyyar ANC za su yi taro domin tattauna sakamakon zaben da ke fitowa.

    An shirya gudanar da taron manema labarai da yammacin ranar Asabar.

  18. An kama matar tsohon shugaban Zambiya kan zargin badaƙala

    An kama matar tsohon shugaban ƙasar Zambiya Esther Lungu da ɗiyarta kan mallakar wasu kadarori da ake zargin sun samu ba bisa ƙa'ida ba.

    Esther Lungu da ɗiyarta Chiyeso Katete an kama su ne a jiya Alhamis a birnn Lusaka, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

    Hukumomi sun ce Esther "Ta kasa bayar da gamsasshen bayani kan yadda aka yi ta mallaki wasu rukunin gidaje a babban birnin ƙasar wanda darajarsu ta kai ta dala miliyan ɗaya da rabi."

    Hukumomi sun ce babu tabbacin taƙamaiman ranar da suka mallaki gidajen sai dai bayanai sun nuna sun mallake su ne tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

    Wadanda ake zargin ba su ce uffan ba, sai dai tsohon shugaban ƙasar ya ce za su ƙalubalanci matakin a kotu.

    • Amurka na tuhumar 'yan Najeriya da zamba
    • Hakainde Hichilema: Yadda zaben sabon shugaban kasar Zambia ya karfafa gwuiwar 'yan adawar Afirka
  19. EFCC ta kama wasu mutum 40 da zargin damfara ta Intanet a Akwa Ibom

    Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC ta shiyyar Uyo sun kama wasu mutum 40 da ake zargi da damfara ta intanet a wani samame da suka yi da safiyar yau, Juma'a a wurare biyu daban-daban a jihar.

    Hukumar ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntata na X.

    Mutum 21 daga cikin mazan da ake zargin an kama su ne a garin Eket, yayin da sauran mutum 19 kuma a a Ikot Ekpene aka kama su.

    Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da mota guda ɗaya da kwamfutocin tafi-da-gidanka guda tara da wayoyi 64 da kuma agogo mai kaifin basira

    Hukumar ta ce za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

  20. Sojoji sun tabbatar da kisan jami'ansu biyar a jihar Abia

    Ƴan bindiga sun kashe aƙalla sojojin Najeriya biyar a wani harin ba-zata da suka kai a jihar Abia da ke Kudu maso gabashin Najeriya, yankin da ke fama da rikicin ƴan aware.

    Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar a yau Juma'a, wadda ta samu sa hannun daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin, Edward Buba.

    Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai sojojin sun ɗora alhakin hakan kan ƴan awaren da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra.

    Sanarwar ta ce "Dakarun Najeriya na alhinin mutuwar waɗannan sojoji kasancewar duk wani soja da aka rasa a fagen daga mummunan rashi ne.

    "Amma dai ana ci gaba da bincike.

    "Haka nan kuma wajibi ne ga sojoji su rama wannan mummunan aiki da aka yi wa dakarunmu. Za mu ɗauki mummunar fansa.

    Za mu sauke ƙarfin soji a kan ƙungiyar domin tabbatar da cewa mun kawo ƙarshen ta".

    Najeriya na fama da rikice-rikice da suka hada da ƙungiyar ƴan awaren Biafra da ke ƙaddamar da hare-hare a Kudu maso gabas yayin da Arewa maso yamma ke fama da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa, sai kuma arewa maso gabas da ta kwashe shekara 15 tana fuskantar rikicin Boko haram.

    IPOB na fafutukar kafa ƙasar Biafra ta hanyar ficewa daga Najeriya, inda yawancin ƴan ƙungiyar ƙabilar Igbo ne

    An kama shugaban ƙungiyar Nnamdi Kanu, wanda ke da takardar shaidar zama ɗan Birtaniya a shekarar 2021 a Kenya, wanda yanzu haka ke fuskantar shari'a kan ta'addanci a Najeriya.

    • Lokuta biyar da mutanen gari suka yi wa jami'an tsaro kisan gilla a Najeriya
    • Yadda 'yan bindiga suka sace mutum 30 lokacin sallar asuba a Zamfara