Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 30/05/2024
Rahoto kai-tsaye
Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke fatan mu kwana lafiya.
Masu tamaka wa alƙalai a shari'ar Trump sun koma aiki a asirce
Masu taimaka wa alƙalai a shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban Amurka Donal Trump sun koma gudanar da aikinsi a sirrance a rana ta biyu, bayan kammala sauraren bayanai daga wasu manyan shaidu biyu.
Sun saurari jami'an kotun, suna karanta bayanin da tsohon lauyan Trump, Micheal Cohel ya gabatar da kuma David Pecker wanda shugaban wani kamfanin jarida ne.
Dukkansu suna bayar da shaida ne kan abin da ya shafi zaɓen Amurka na 2016.
Mista Trump ya musanta mu'amala da tauraruwar shirya fina-finan batsa da ake zargin ya biya ta kuɗaɗe.
MDD ta yi gargaɗin barazanar fuskantar tamowa tsakanin yara a Sudan
Hukumomin MDD uku sun yi gargaɗin cewa ƙananan yara ka iya fuskantar matsalar tamowa a Sudan sakamakon dogon lokacin da aka ɗauka ana yaƙın basasa a ƙasar.
Asusun Tallafa wa Yara na MDD, Unicef, da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO sun ce akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa domin kare yaran da za su taso nan gaba.
A Zamzam ɗaya daga cikin manyan sansanonin 'yan gudun hijira da ke arewacin Darfur - yaro ɗaya ciki uku da ke ƙasa da shekara biyar yana fama da matsananciyar yunwa.
Hukumomin sun ce abin da zai yi magance yunwar shi ne zaman lafiya, in kuma ba haka ba sa dai samar da kayan agaji
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 624 cikin watan Mayu
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe ‘yan bindiga 624, sannan ta kama wasu 151, ciki har da masu taimaka wa ‘yan ta’adda da aka fi sani da infoma, cikin watan Mayun da ke dab da ƙarewa.
Sojojin sun kuma ce sun ceto kimanin mutum 563 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cikin watan.
Rundunar sojojin ta kuma ce ta nuna damuwa game da kisan wasu jami’anta sha bakwai da aka yi a jihar Delta watannin baya da kuma wani jami’inta da wasu ‘yan ta’adda suka yi a babban kantin sayar da kaya na Banex Plaza da aka yi a kwanan nan, sai dai ta ce ba abinda za ta ci gaba da lamunta ba ne.
Mai magana da yawun kakakin rundunar sojin ƙasar, Manjo Janar Edward, wato Captain Ibrahim Bukar Ali ya shaida wa BBC cewa yaƙi da ta’addanci na neman goyon bayan al’umma tare da samun cikakken haɗin kai da yarda tsakanin jami’an tsaro da fararen hula, kasancewar suna buƙatar jami’an tsaro a tare da su domin tsaron rayukansu da ma dukiya.
Ya ƙara da cwa sojojin ƙasar za su ci gaba da yaƙar ‘yan ta’adda har sai sun samu cikakkiyar nasara a kansu
Kaftin Ibrahim Ali, ya ce rundunar sojin ta kuma samu manyan nasarori da suka haɗa da ƙwace makamai da dama da suka haɗa da bindiga kirar AK 47 411, da kuma harsasai 16,487.
Kazalika rundunar ta ce ta ƙwace ɗanyen mai da kuɗinsa ya kai naira miliyan 705,836 a yankin kudancin ƙasar.
Zaɓen Afirka ta Kudu: An fara fitar da sakamakon farko
Sakamakon farko na zaɓen Afirka ta Kudu da aka fitar ya nuna jam'iyyar ANC mai mulkin ƙasar ce ke kan gaba da 'yar tazarar da ba ta da yawa.
Kawo yanzu an ƙidaya sakamakon kashi 27 na mazaɓun ƙasar, inda ANC ta samu kashi 43 na ƙuri'un, yayin da jam'iyyar ƙawayen 'yan hamayya ta DA ke da kashi 25.
Jam''iyyar EFF ta masu rajin 'yanci ke da kashi 9, sai jam'iyyar MK ta tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma ke da kusan kashi 8.
Ana sa ran samun sakamakaon ƙarshe na zaɓen cikin ƙarshen mako.
Sakamakon farkon na nuna cewa jam'iyyar ANC, ka iya rasa rinjayenta a majalisar dokokin ƙasar, karon farko tun lokacin nasarar Nelson Mandela, bayan yaƙi da wariyar launin fata a shekarar 1994.
Masu zaɓe da dama na zargin ANC ta laifukan cin hanci da rashawa da rashin ayyukan yi a ƙasar.
'Za a iya kai ƙarshen 2024 ana gwabza yaƙi a Gaza'
Wani babban jami'in gwamnatin Isra'ila ya ce akwai yiyuwar yaƙin da ake yi da Hamas a Gaza zai iya kai wa ƙarshen wannan shekarar 2024.
Mai bai wa Firaministan Isra'ila shawara kan tsaro, Tzachi Hanegbi, ya shaida wa gidan rediyon ƙasar cewa, "za a iya kai watanni bakwai nan gaba ana gwabza yaƙin".
Ya kuma ce rundunar sojin Isra'ila ta ƙwace iko a kashi 75 na yankin da ke kan iyakar Gaza da Masar, kuma tana ci gaba da samame a kudancin birnin Gaza.
Haka kuma mazauna Rafah sun ba da rahoton cewa hare-haren isra'ila sun ƙaru, sannan motocin yaƙin Isra'ilar sun kai samame a tsakiya da yammacin birnin kafin su janye.
Wani babban jami'in hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ya yi gargaɗin cewa asibiti ɗaya da ya rage a Rafah zai iya dakatar da ayyuka idan sojojin Isra'ila suka mamaye birnin.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce sojojin na kai hare-haren ta a kan tsari domin kawar da ragowar mayaƙan Hamas da ke Rafah, yayin da Falasɗinawa sama da miliyan ɗaya suka fice daga garin cikin makonni uku da suka gabata.
Gwamnatin Amurka ta ce ba ta tunanin akwai wani shiri na kai manyan hare-hare ta ƙasa wanɗanda ke iya sanadiyyar kawo sauyi a tsare-tsarenta na tallafa wa sojin Isra'ila.
Isra'ila ta jajirce kan shirinta na mamaye birnin Rafah.
Muna so gwamnati ta sa baki a bashin da muke bin kamfanoni - Hukumar lantarkin Najeriya
Hukumar kula da harkokin lantarki ta Najeriya ta ce ta tura wa gwamnatin tarayya buƙatar shiga tsakani kan yadda wasu ƴan ƙasashen waje ba su son biyan bashin da ake bin su na kuɗin wuta.
Hakan na ƙunshe cikin rahoton zango na huɗu na 2023 da hukumar ta wallafa a shafinta.
Rahoton hukumar ya ce a cikin wannan lokacin kamfanonin raba wutar lantarki da wasu kamfanonin ƙasashen waje huɗu ba su biya kuɗin wutar da suka sha har jimillar naira biliyan 97.5.
Ƙididdigar da aka wallafa ta nuna cewa ana bin kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 kuɗi naira biliyan 81, yayin da kuma ake bin kamfanonin ƙasashen wajen naira biliyan 16.5 a zangon ƙarshe na 2023.
An yi wa ƴan awaren yankin Cataloniya afuwa
Majalisar dokokin Spaniya ta amince da wata doka da ta jawo ce-ce-ku-ce wadda ta yi afuwa ga ƴan awaren yankin Cataloniya.
Gwamnatin jam'iyyar ƴan Gurguzu ce ta gabatar da dokar, kuma ta janye wasu ƙararraki da aka shigar kan ƴan awaren, ciki har da waɗanda suka yi yunƙurin ballewa a 2017.
Kimanin ƴan awaren yankin Cataloniya 400 ne za su ci moriyar wannan afuwar.
Majalisar ta amince da dokar ne da rinjayen ƙuri'a shida kacal, abin da ke nuni da yadda aka samu rabuwar kawuna kan batun a majalisar ƙasar.
Sai dai Lardin Madrid da ke ƙarƙashin ikon jam'iyyar adawa ya ce zai ɗaukaka ƙara kan amincewa da dokar, bisa hujjar cewa ta saɓa wa kundin tsarin mulki.
EFCC ta ƙwato naira biliyan 156 a shekara guda
Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin Hanci da rashawa a Najeriya, Ola Olukoyede ya ce hukumar ta samu nasarar ƙwato naira biliyan 156 daga ranar 29 ga waan Mayun 2023 zuwa 29 ga watan Mayun 2024.
Mista Olukoyede ya bayyana hakan ne a lokacin ƙaddamar da wani shiri na musamman kan yaƙi da rashawa ranar Laraba a Abuja.
Ya ƙara da cewa daga kuɗaɗen da hukumar ta ƙwato sun haɗa da na ƙasashen waje da ma kudin intanet wato na kirifto.
Yayin da yake jawabi a madadin shugaban hukumar, sakataren EFCCn, Mohammed Hammajoda ya ce hukumar na nuna damuwarta kan yadda matasa da ɗalibai ke ƙara shiga harkokin damfara ta intanet da aka fi sani da 'yahoo-yahoo'.
''Babu wani dalili da zai sa mutum ya shiga harkar yahoo-yahoo,'' in ji shi.
Hukumar ta EFCC ta kuma ce ta kama kusan mutum 3,175 da laifi cikin shekara guda.
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga shida a Kaduna
Dakarun runduna ta ɗaya ta sojin Najeriya sun kashe wasu 'yan bindiga shida tare da kama wasu mutum uku a wani samame na musamman a ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya fitar ya ce sojojin sun samu nasarar kakkaɓe 'yan bindigar bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ta'addanci a yankin Galadimawa na karamar hukumar Giwa.
Sojojin sun kwato shanu tare da miƙa su ga mutanen yankin.
Daga nan ne sojojin suka hango maharan a dandalin kasuwar Galadimawa.
''Inda aka yi musayar wuta takanin ɓangarorin biyu, kafin daga bisani maharan su arce bayan kisan mutum shida daga cikinsu'', in ji sanarwar.
Bayan ƙaddamar da bincike a yankin ne kuma sojojin suka kama wasu mutum uku da ake zargi da hada baki tare da bai wa 'yan bindigar bayai.
Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato babura biyu tare da wayoyin hannu huɗu a lokacin gumurzun.
Kotun Ƙoli ta bai wa jihohi mako guda su kare kansu kan ƴancin ƙananan hukumomi
Kotun ƙolin Nijeriya ta umarci gwamnonin jihohin kasar 36, su kare kansu cikin kwanaki bakwai kan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar na neman cikkaken 'yancin gashin kai ga ƙananan hukumomi 774 na ƙasar.
A zaman kotun na ranar Alhamis da alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Garba Lawal, kotun ya bai wa gwamnonin jahohi 36 da manyan lauyoyin gwamnatocinsu suka wakilta a gabanta, umurnin shigar da bayanan kare kansu a gabanta a cikin kwanaki bakwai daga yau.
Kazalika alƙalan sun bai wa babban lauya, Lateef Fagbemi umurnin bayyana martaninsa da ke nuna matsayar gwamanati a cikin kwana biyu da shigar da nasu ƙorafin kariya.
A karar da gwamnatin tarayyar ta shigar ta hannun babban lauyanta Lateef Fagbemi ya kuma nemi kotun ta bayar da damar da za a iya tura wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu daga asusun gwamnatin tarayya kai tsaye, kamar yadda ƙundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar.
Ƙundin tsarin mulkin ƙasar ta ba da damar cewa wajibi ne matakan gwamnatoci uku na tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomi su riƙa samun kuɗinsu daga asusun gwamnatin tarayya ba tare da kowane shamaki tsakani ba bisa tsarin dimokradiyya.
Babban lauyan ya kuma ce yin wani abu saɓanin hakan daidai ya ke da karya dokokin ƙasa da ƙundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya bayar da dama.
Gwamnatin tarayyar ta kuma roƙi kotun ƙolin ta yi la’akari da sashe na ɗaya da na huɗu da na biyar waɗanda suka tilasta wa gwamnonin da ‘yan majalisar dokokin jihohi su tabbatar da cikakken tsarin dimokradiyya a mataki na ƙasa ba wai kama karya ba irin yadda ake yi a yanzu.
Kotun ƙolin ta ce dole ne a kammala gabatar da dukkan matakai da musayar bayanai da suka kamata a kan lokaci, inda ta sanya ranar 13 ga watan Yuni don sauraron bayanan ƙarar da gwamnonin za su shigar.
Gwamnonin jihohin na ci gaba da iko da kusan komai na ƙananan hukumomi 774 da ake da su a Najeriya.
Gwamnan Kano ya gana da Nuhu Ribadu
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu a Abuja.
Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya yi muhimmiyar ganawa da Nuhu Ribadun.
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce gwamnan ya gana da Nuhu Ribadun ne kan abin da ke faruwa a Kano na rikicin masarautu.
Dawakin Tofa ya ƙara da cewa mutanen biyu sun kuma tattauna wasu batutuwan da suka jiɓanci zaman lafiya da ci gaban ƙasa a lokacin ganawar tasu.
A ƙarshen makon da ya gabata ne mataimakin gwamnan Kano, Comr. Aminu Abdulsalam ya zargi Nuhu Ribadun da kitsa komawar sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero zuwa birnin, kwana biyu bayan da gwamnan jihar ya sanar da tuɓe shi daga sarauta.
Sai dai ofishin Ribadun ya musanta zargin tare da barazanar maka mataimakin gwamnan a kotu idan bai janye kalaman nasa ba.
Daga bisani dai mataimakin gwamnan ya janye kalaman nasa tare da bai wa Ribadu haƙuri, yana mai cewa da farko ba su fahimci yadda batun yake ba.
Nathan Tella da Osimhen ba za su buga wasan Najeriya da Afirka ta Kudu ba
An buƙaci wani attajiri ya biya tsohuwar matarsa kuɗin rabuwa dala biliyan ɗaya
An umarci wani attajiri a Koriya ta Kudu ya biya tsohuwar matarsa - wadda ƴa ce ga tsohon shugaban ƙasar kuɗin saki dala biliyan ɗaya.
Wannan ya zamo kuɗin rabuwar aure mafi yawa da aka yanke wa wani mutum a tarihin ƙasar.
Chey Tae-won da Roh So-Youn sun yi aure ne a 1988 - shekarar farko ta mulkin mahaifinta a ƙasar.
Roh ta bayyana cewa ta yi tasiri wajen arziƙin mijin nata Mista Chey, sanadiyyar hanya da ta riƙa yi masa.
Rukunin kamfanin Mist Chey, wato SK Group na daga cikin kamfanonin mafiya shahara a duniya a ɓangaren abin da yake samarwa.
A yau Alhamis, kotu ta amince cewa matar na da hakkin samun wani ɓangare na dukiyar tsohon mijin nata.
Lauyoyin Chey sun ce za su ɗaukaka ƙara.
Rashin tsaro ya tilasta wa likitoci dakatar da aiki a asibitin yara na Kano
Kungiyar likitocin Najeriya NMA ta umurci likitocin da ke asibitin yara na Hasiya Bayero da ke Kano da su dakatar da ayyukan da suke yi saboda fargabar fuskantar hare-hare da rashin tsaro.
Sakataren kungiyar NMA reshen Kano, Dr. Abdulrahman Aliyu ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar inda ƙungiyar ta yi ƙarin bayani kan wani mummunan lamari da ya faru a ranar 27 ga watan Mayu, inda wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai wa wasu likitoci mata biyu hari tare da yi musu barazana da bindiga.
Sanarwar ta kara da cewa, "Wasu mutane ɗauke da makamai sun kai wa likitocin da suke gudanar da ayyukansu hari inda suka kutsa cikin ofishinsu da karfi tare cin zarafinsu da yi musu barazana, sannan kuma suka nuna musu bindiga."
Aliyu ya ƙara da cewa, an shafe kusan sa’a guda ana rikicin ba tare da samun wani taimako daga jami’an asibitin ko hukumomin waje ba.
Ya kuma yi karin haske kan wani lamari da ya faru a baya a farkon wannan shekarar, inda wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani jami’in kiwon lafiya da ke bakin aiki a sashen masu haihuwa na Asibitin kwararru na Murtala Muhammad Kano.
Irin wadannan al’amura sun yi tasiri matuka wajen sanya tsoro da zaman ɗar-ɗar a tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya a jihar, in ji Aliyu.
'Tinubu ya ba ni kunya'
Yusuf Suleimon tsohon ɗan gani-kashe-nin Bola Tinubu ne wanda ya bayyana wa BBC cewa ya yi amfani da kuɗinsa wajen ganin Tinubu ya ci zaɓe a shekara ta 2023.
Sai dai bayan shekara ɗaya na mulkin Tinubu, Yusuf ya rasa aikinsa yayin da mahaifiyarsa ke fama da durƙushewar kasuwanci saboda rashin ciniki.
Najeriya ta buƙaci a daina ruwan wuta a Gaza nan take
Najeriya ta yi Allah wadai da kisan fararen hula a Gaza, ta kuma yi kiran a gaggauta wanzar da zaman lafiya a yankin.
Wata sanarwa da ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya fitar ta ce gwamnatin ƙasar ta damu da halin da fararen hula suka shiga yanzu haka a Gaza, saboda yaƙin Isra'ila da Hamas.
Harin baya-bayan nan da Isra'ila ta kai kudancin Gaza a ranar Lahadi 26 ga watan Mayu ya kashe mutum aƙalla 45, mafi yawan su mata da ƙananan yara, lamarin da ya ƙara yawan hare-haren da aka kai kan fararen hula tun bayan ɓarkewar yaƙin.
Sanarwar gwamnatin Najeriyar ta koka da yadda aka riƙa samun rashin mutumta yarjejeniyar tsagaita wuta da cin zarafin ɗan'adam da kuma hana shigar da kayan tallafi Gaza.
Najeriya ta buƙaci a gaggauta komawa tsarin kiyaye ƴancin ɗan'adam, musamman hana kisan gilla da kuma kare fararen hula da ke Gaza daga duk wani harin soji.
Ta kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da Isra'ila da Hamas da kuma Majalisar Dinkin Duniya su ƙara mayar da hankali kawo ƙarshen rikicin Gaza domin tsagaita wuta da kuma ceton fararen hula a yankin.
- Isra'ila ta karɓe iko da mashigar Rafah a Gaza
- Gaza: Ko Isra’ila ta samu biyan bukata bayan wata shida da fara yaki?
Olympiakos ta zama ƙungiyar Girka ta farko da ta lashe gasar zakarun Turai
Kun san yadda ake rera 'sabon' taken Najeriya?
A ranar Laraba ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu ka dokar komawa amfani da tsohon taken ƙasar mai taken 'Nigeria, we hail thee'.
Yanzu sabon taken wanda aka ƙirƙira a lokacin da Najeriya ta samu ƴancin kai a shekarar 1960 zai maye gurbin wanda aka daɗe ana amfani da shi, wato: “Arise, O Compatriots”.