Tarayyar Turai da ƙasashen duniya na taimaka wa wajen gano inda jirgin ya yi haɗari

Asalin hoton, IRNA
Ƙasashe da dama na tayin bayar da taimako ga Iran wajen gano inda jirgin ya yi hadari tare da ceto.
Zuwa yanzu Rasha da Azerbaijan da Armenia da Iraqi dukkaninsu sun yi tayin taimakawa wajen gano jirgin.
Haka kuma Rasha ta ma yi tayin taimakawa a binciken abin da ya haddasa hadarin.
Ita Hadaddiyar Daular Larabawa ta gabatar da tayinta na taimakawa, ta kuma ce tana tare da Iran.
Turkiyya kuwa tuni ta aika ta tawagar kwararrn masu aikin agaji a tsaunuka zuwa kasar ta Iran, kuma tun da farko Shugaba Tayyip Erdogan ya ce hadarin ya sanyaya masa jiki.
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce, ta shiga aikin taimakawa wajen gano inda jirgin sama mai saukar ungulun da ya yi hadari da Shugaba Raisi da ministansa na harkokin waje yake.
EU ta ce tana amfani da na'urorinta na daukar hotunan tauraron dan'Adam don gano ainahin inda hadarin ya auku.
A wani sako da kwamishinan kungiyar ta Turai kan agaji, Janez Lenarcic ya sanya a shafinsa na X, ya ce EU na taimakawa ne kamar yadda Iran ta nemi agaji daga kungiyar.
Ita kuwa fadar gwamnatin Amurka ta ce an yi wa Shugaba Biden bayani a kan hadarin na Iran.
A nasu bangaren hukumomin Iran din sun ce an tura tawaga wajen 40 ta masu aikin agaji domin gano inda lamarin ya faru.
Masu aikin neman suna amfani da karnuka da kuma kananan jiragen sama marassa matuka a aikin, wanda ke da wuyar gaske saboda tsananin rashin kyawun yanayi da kuma tsaunuka da ke yankin.












