Sai da safe
Nan muka zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi.
Za ku iya duba ƙasa don karanta rahotonnin da muka kawo a yau Talata. Sai kuma gobe da safe za ku samu wasu sababbi.
Mu zama lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai daga sassan duniya daban-daban, musamman dai Najeriya da makwabta.
A'isha Babangida, Nabeela Mukhtar Uba and Umar Mikail
Nan muka zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi.
Za ku iya duba ƙasa don karanta rahotonnin da muka kawo a yau Talata. Sai kuma gobe da safe za ku samu wasu sababbi.
Mu zama lafiya.
Wasu daga cikin manyan ƙungiyoyin Musulmi a najeriya sun nuna rashin jin daɗinsu game da asarar rayukan da aka yi sakamakon bama-baman da sojin ƙasar suka harba bisa kuskure kan masu Maulidi.
Lamarin ya faru a garin Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi t jihar Kaduna ranar Lahadi.
Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (Jibwis) da kuma ta Tijjaniyya sun nemi a gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.
Mazauna yankin sun faɗa wa BBC Hausa cewa sun yi jana'izar mutum 100 da harin ya kahse, yayin da hukumar agaji ta Nema ke cewa mutum 85 ne suka mutu.
Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Abdou Halilou:
Jami'an ƙungiyar Hamas sun ce aƙalla mutum 16,248 aka kashe a Zirin Gaza tun bayan fara kai hare-haren Isra'ila.
Ofishin yaɗa labarai na Hamas ya ce sama da 7,000 yara ne, da kuma kusan 5,000 mata cikin waɗanda aka kashe a Gaza a kusan wata biyu da aka shafe ana gwabzawa.
Ta bayana hakan ne cikin wata sanarwa da kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.
Aƙalla mutum 45 ne aka kashe a tsakiyar Gaza, a cewar mai magana da yawun Asibitin al-Aqsa da ke Deir al-Balah bayan wani harin Isra'ila ta sama.
Zuwa yanzu abin da muka sani ke nan, amma za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu.
Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta jaddada cewa babu wani wuri Falasɗinawa za su iya zuwa don ɓuya daga hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza.
"Mun faɗa mun sake faɗa," in ji hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasɗinawa ta UNRWA cikin wani saƙo a dandalin X. "Muna sake faɗa, babu wani gidan ɓuya a Gaza."
Ta ƙara da cewa: "Wahalar da ɗana'dam ke sha kai ba zai ɗauka ba. Cigaba da kai hare-hare da kuma faɗaɗa su zuwa kudancin Gaza na ƙara maimaita bala'in da aka fuskanta a 'yan makonnin da suka wuce."
UNRWA na wannan magana ne yayin da rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta na kai samame a tsakiyar biranen Gaza uku, ciki har da Khan Younis - birni mafi grima a kudancin Gaza.
Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya Janar Taoreed Lagbaja ya halarci jana'izar mutanen da harin rundunar sojin Najeriya ya kashe bisa kuskure ranar Lahadi a jihar Kaduna.
Bayan jana'izar, janar ɗin ya nemi afuwa daga al'ummar ƙauyen Tudun Biri, waɗanda bama-baman suka faɗawa lokacin da suke tsaka da gudanar da Maulidi.
Mazauna yankin Khan Younis a kudancin Gaza na ci gaba da bayyana halin da suke ciki.
Yayin da suke magana da BBC, ana iya jin ƙarar bama-bamai a kusa.
"A firgice muke sosai. Muna zaune cikin yanayi mafi muni," a cewar wata mace. "Ba mu san abin da za mu yi ba yanzu. Za mu iya rayuwa ko mutuwa cikin wannan yanayi."
Wata matar ta ce an tilasta mata barin gidanta tun daga farkon yaƙin, yanzu kuma tana zaune a asibitin European Hospital na Khan Younis, wanda ta ce dakarun Isra'ila sun kewaye shi baki ɗaya.
"Yara da matasa sun firgice, kowa na fargaba da kuma yunwa," in ji ta. "Fatanmu kawai shi ne Allah. Kamar yadda kuke ji, ana ci gaba da luguden wuta yanzu haka."
Cikin wani bayani kan yaƙin da take yi a Gaza, rundunar sojin Isra'ila ta ce yanzu "tana kai samame a tsakiyar Jabalia, da tsakiyar Shejaiya, da kuma Khan Younis".
Ta nuna yadda take ƙara nausawa kudancin zirin bayan Isra'ila ta umarci mazauna Gaza su bar wasu yankunan Khan Younis - birni mafi girma a kudanci - zuwa Tekun Baharrum da kuma Rafah kusa da iyakar Masar.
Tun a farkon yaƙin, Isra'ila ta umarci Falasɗinawan da su gudu zuwa kudanci daga arewaci. Yanzu kuma tana cewa su sake barin kudancin saboda Hamas na amfani da yankin.
Sanarwar ta ƙara da cewa: "Mun shiga rana mafi tsanani tun bayan fara wannan yaƙi - game da yawan 'yan ta'addan da aka kashe, da tsananin ɓarin wuta, da kuma girman hare-hare ta ƙasa da sama."
Qatar na ci gaba da aikin gyara yarjejeniyar tsagaita wuta da ta ruguje tsakanin Isra'ila da Hamas, da kuma matsa lamba kan kawo karshen yaƙin Gaza gaba daya, in ji shugabanta, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.
"Muna ci gaba da aiki don ganin an sabunta yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da kuma rage radadin mutanenmu a Zirin Gaza, amma tsagaita wuta ba shine hanyar magance matsalar ba, buƙatarmu a kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya."
Qatar ce ke jagorantar shawarwarin da bangarorin biyu suka yi, wanda ya kai ga tsagaita buɗe wuta na tsawon mako guda har zuwa ranar Juma'a.
Tun bayan kawo karshen yarjejeniyar - inda bangarorin biyu ke zargin juna da rugujewarta - Isra'ila ta zafafa kai hare-hare a Zirin Gaza a wani ɓangare na burinta na kawar da kungiyar Hamas.
Faransa ta sanar da ƙwace kadarorin jagoran ƙungiyar Hamas Yahya Sinwar a wani ɓangare na sabbin takunkumai da ta ƙaƙaba masa.
A cewar wata doka da aka wallafa a wata mujallar ƙasar, za a ƙwace kuɗaɗe da dukiyoyin Sinwar tsawon wata shida daga 5 ga watan Disamba,
Ba a san yawan kadarorin Sinwar a Faransa ba.
A watan da ya gabata, Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Lord Cameron ya ɗauki matakin ladabtarwa kan manyan jagororin Hamas da masu ɗaukar nauyinta .
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja ya nemi afuwa daga al'ummar ƙauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna, kan wani harin jirgin maras matuƙi da ya kashe mutane a ranar Lahadi.
A wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriyar ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ta bayyana cewa babban hafsan sojin ƙasan na Najeriya ya kai ziyarar jaje a ƙauyen yau Talata inda "ya nuna nadama game da mummunan lamarin."
Janar Lagbaja ya ce lamarin ya faru ne yayin da dakarun sama na ƙasar ke gudanar da wani sintiri ta sama, inda suka tsinkayi gungun mutane "waɗanda suka yi kuskuren fassara abubuwan da suke yi" a matsayin tamkar irin na ƴan fashi, wanda hakan ya sa aka kai musu hari.
Ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike domin "gano inda aka samu naƙasun da ya haifar da wannan mummunan abu," inda za a yi amfani da sakamakon binciken domin daƙile faruwar irin hakan a gaba.
Al'ummar Najeriya da dama sun nuna fusata kan lamarin, wanda shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kai.
Tuni dai hukumar agajin gaggawa ta ƙasa ta bayyana cewa mutum 85 ne suka rasu sanadiyyar harin, yayin da wasu mutanen 60 suka samu rauni, sai dai ƙungiyoyin masu kare hakkin bil'adama na ganin cewa alƙaluman sun zarce haka.
An dai samu irin wannan kuskure a baya, inda hare-haren na sojojin Najeriya ke shafar fararen hula.
Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce adadin mutanen da aka kashe a Gaza tun farkon yaƙin ya kai 15,899.
Kwanaki uku da suka gabata - sa'o'i bayan kawo ƙarshen tsagaita buɗe wuta na mako guda tsakanin Isra'ila da Hamas - jami'ai a Gaza sun ce adadin wadanda suka mutu ya zarce 15,200.
Abokan aikinmu na BBC Verify sun yi nazari a baya kan yadda ake kirga wadanda suka mutu a Gaza.
Isra'ila ta fara kai hare-hare kan Hamas bayan harin da ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, inda ƴan Hamas suka tsallaka kan iyaka suka kashe mutane 1,200 - tare da yin garkuwa da wasu 240.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce ya yi wuri ta tabbatar ko Isra'ila ta yi amfani da shawarar da ta bata na tabbatar da tsaron farar hula a sabbin hare-haren da ta kaddamar a Gaza.
Juliette Touma, jami'ar majalisar dinkin duniya ce da ke aikin agaji a Gaza, ta ce babu tudun mun tsira a Gaza.
Ta ce ko Kudancin Gaza da ake ganin ya na da tsaro a yanzu babu wannan, tawagarmu da ke aiki a yankin sun shaida mana yadda ake ruwan bama-bamai a can.
Sansanonin da suke cike da sama da mutum miliyan daya sun kara cika makil da mutane.
Yayin da kafar yada labaran Falasdinu, ta ce an jefa bama-bamai a makarantu 2 da farar hula ke fakewa a arewacin Gaza.
Wasu hotuna masu sosa zuciya da suka bayyana daga asibitin Nasser a birnin Khan Younis da ke Kudancin Gaza sun nuna yadda jini ke malala a ƙasa bayan shafe tsawon dare Isra'ila na luguden wuta.
Kakakin ma'aikatar lafiya a Gaza ya kira lamarin 'tashin hankali'. Ashraf al-Qudra ya ce gawarwaki 43 aka kai asibitin da safiyar yau, Talata.
Ya ƙara da cewa motocin ɗaukan marasa lafiya na fuskantar cikas wajen zuwa inda mutanen da suka ji rauni suke.
Isra'ila dai ta ce tana kai hare-hare ne kan wuraren Hamas kuma tana bakin ƙoƙarinta wajen rage yawan farar hular da lamarin ke shafa.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana harin jirgi maras matuƙi na baya-bayan nan da aka kai jihar Kaduna wanda ya halaka mutum kusan 100 a matsayin abin tashin hankali da ba a buƙatar faruwarsa.
A sanarwar da Daraktan yaɗa labarai, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, an kai harin ne sakamakon bayanan sirrin da aka samu cewa akwai ƴan bindiga a yankin.
Harin dai ya faru ne dai-dai lokacin da mutane a ƙauyen Tudun Biri suke gudanar da taron bikin Mauludi.
Tuni dai gwamnan jihar ta Kaduna, Uba Sani ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin da ya jikkata wasu gommai.
Rundunar sojin ƙasar ta ce lokaci zuwa lokaci ta kan ƙaddamar da irin wannan hari kan ƴan bindiga da a wani lokacin yake shafar al'ummar gari.
Zuwa yanzu, waɗanda suka jikkata suna samun kulawa a asibitin gwamnati a jihar.
Jihar Kaduna na fama da matsalar tsaro inda tsawon shekaru, ƴan bindiga ke kai hare-hare tare da yin garkuwa da jama'a don neman kuɗin fansa.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce za a dakatar da yaƙi na ɗan lokaci a Kudancin Gaza, kamar yadda ta wallafa a shafin X.
"Za a tsagaita buɗe wuta a yankin Rafah har zuwa ƙarfe biyu na rana agogon ƙasar domin a ba da damar shigar da kayan agaji,". in ji rundunar.
Wani saƙo cikin harshen Larabci ya nuna cewa za a samu lafawar yaƙin a El Geneina mai maƙwabtaka.
An dai saba ɗaukar irin wannan matakin a yankuna da dama na Gaza.
Tun bayan wargajewar yarjejeniyar dakatar da yaƙin da Hamas ranar Juma'a, rudunar sojin Isra'ila ke zafafa hare-hare a yankin.
Kungiyar dattawan Arewa (ACF) ta yi Allah-wadai da harin da aka kai da jiragen yaƙi marasa matuka a yayin wani taron mauludi a unguwar Tudun Biri, jihar Kaduna a ranar 3 ga Disamba, 2023
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar inda ta buƙaci da a gudanar da cikakken bincike na gaskiya kan lamarin.
Ƙungiyar ta kuma bayyana lamarin a matsayin rashin ƙwarewa wajen tattara bayanan sirri.
Rundunar sojin Najeriya dai ta amince da kai harin, inda ta bayyana shi da “rashin hankali”. Rahotanni sun nunar da cewa an samu asarar rayuka, inda mutane kusan 80 galibi yara da mata ne ke fargabar sun mutu tare da jikkata wasu da dama.
Ƙungiyar ta bukaci sojoji da su fito da cikakkun bayanai don magance fargabar jama'a.
"Muna baƙatar a yi cikakken bincike, ta hanyar gaskiya da bude ido kan lamarin, don tabbatar da hakikanin abin da ya faru da wadanda ke da hannu da kuma fayyace adadin rayukan da aka rasa da kuma jikkata; Da dai sauransu. Kuma Duk wanda aka samu da laifin ko ƙwararru ko gazawar aiki dole ne a hukunta su sosai" in ji sanarwar
"Ya zama wajibi gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakin kare muradun wadanda abin ya shafa ba jami’an sojin Najeriya da suka aikata wannan aika-aika ba."
"Dole ne a biya diyya ga iyalan waɗanda suka mutu daidai da darajar diyya ta Musulunci"
"Domin dawo da kwarin gwiwar jama'a, dole ne sojojin Najeriya su nemi afuwar al'ummar ƙasar da lamarin ya shafa. Bugu da kari, a matsayin alamar gaskiya, ya kamata sojojin Najeriya su gaggauta gudanar da ayyukan jinya da sauran ayyukan farfado da al’umma a cikin al’umomin da abin ya shafa."
"Ya kamata babban hafsan tsaro ya umarci dukkan jami’an soji da su samar da ingantacciyar dabara don gujewa tabarbarewar abubuwan da suka faru a Tudun Biri, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.", sanarwar ta ƙara da cewa.
An ɗaure wani mai tashar Youtube shekara shida a gidan yari saboda yadda ya rikoto da jirgin sama saboda samun ƴan kallo sannan kuma ya yi wa masu bincike a Amurka ƙarya a kan haka.
Trevor Jacob mai shekara 30, ya wallafa bidiyon jirgin a Disambar 2021, inda ya yi iƙirarin haɗari ne.
Ya yi fitar burgu daga cikin jirgin ɗauke da sandar riƙe waya don ɗaukar hoto inda ya diro ƙasa ta hanyar amfani da saukar lema.
Miliyoyin mutane ne dai suka kalli bidiyon.
Jacob, wanda tsohon ɗan wasan Olympics ne ya amsa aikata laifi a farkon wannan shekarar.
Masu gabatar da ƙara a California sun ce da yiwuwar Jacob ya aikata hakan ne domin neman suna da samun mabiya.
Rundunar tsaron Isra'ila ta ce dakarunta suna ci gaba da nausawa sansanin ƴan gudun hijra na Jabalia da ta yi wa ƙofar rago a arewacin Gaza.
Rundunar ta ce ta kwace iko da cibiyoyin sojoji wanda daga nan Hamas ta ƙaddamar da hare-hare.
Ta kuma ƙwace wata cibiyar Hamas inda ta gano wasu makamai da taswirori.
Wani bidiyo da IDF ta yaɗa ya nuna yadda luguden wuta ya ruguza wani gini da aka bayyana a matsayin na dakarun Hamas".
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kaduna ta ce aƙalla mutum 85 ne, kawo yanzu, aka tabbatar sun mutu a harin da aka kai jihar.
Hukumar ta samu bayanai daga hukumomin yankin cewa tuni aka yi jana'izar mutanen da suka rasu, ana kuma ci gaba da yin bincike.
Tun farko dai rundunar sojin saman ƙasar ta musanta hannu a kai harin.
A jiya Litinin ne, Majalisar Dattawan Najeriya ta lashi takobin gudanar da bincike kan harin kuskuren da rundunar sojin kasar ta kai, da ya janyo asarar rayuka.
Harin dai ya faru ne yayin da mutanen ke tsaka da taron Mauludi da suke yi duk shekara.