Asuba ta gari
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu kasance gobe da safe idan Allah ya kai mu don samun wasu sababbi.
Ahmad Tijjani Bawage da Mukhtar Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.
Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu kasance gobe da safe idan Allah ya kai mu don samun wasu sababbi.
Ahmad Tijjani Bawage da Mukhtar Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya.
Ministan Kuɗin Najeriya, Wale Edun, ya bayyana cewa ƙasar ba za ta ci gaba da dogaro da cin bashi ba kudi don yin kasafin kuɗin shekarar 2024.
Edun ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar dattawa da ke bin diddigin tsarin kashe kuɗin gwamnati karkashin jagorancin Sanata Sani Musa.
Ministan kuɗin ya shaida wa kwamitin cewa, hanya mafi dacewa da Najeriya za ta iya samar da kasafin kuɗinta ita ce ta kashe makudan kuɗaɗe wajen samar da ababen more rayuwa.
Ya ce ƙasar na da tarin bashi a kasa, kuma ya kamata a rage yawan bashin da gwamnati ke ciyowa.
Wale ya ce a bayyane yake yanayin da muke ake ciki a yanzu, ba lokaci ne na cin bashi ba a duniya har ma da ƙasa baki ɗaya.
Ƴan sandan Kenya sun kama wasu mutane takwas da suke zargi da hannu a wata gagarumar damfara da suka ce ta kai dala tiriliyan 439.
Alkaluman sun bayar da mamaki yayin da suka kai kusan dalar Amurka sau 200 a faɗin kasuwannin duniya.
A wani sako da hukumomin ƙasar suka wallafa a shafukan sada zumunta, sun ce waɗanda ake zargin sun yi ikirarin jigilar kuɗaɗe daga Togo zuwa Dubai kuma suna buƙatar hakan ta yiwu daga wasu 'yan ƙasar Holland guda biyu.
Mutane da yawa sun aza ayar tambaya game da adadin kuɗin da ƴan sandan suka bayar, sai dai hukumomin ƙasar sun ce jami'ai a Netherlands ne suka bayar da shi wanda har yanzu ba su ce uffan ba kan lamarin.
Kamar yadda muka ruwaito, sojojin Isra'ila na ci gaba da bincike a asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza - cibiyar kiwon lafiya mafi girma a Zirin Gaza.
A karshen watan jiya ne dai rundunar tsaron Isra'ila ta zargi Hamas da samun babban sansaninta a karkashin Al-Shifa.
Ta ce ta yi amfani da wasu na'urori ƙirar 3D don hango abin da ake zargin hanyar sadarwa na karkashin ƙasa da ɗakunan sarrafawa.
Wani mai magana da yawun rundunar ya ce akwai mahaɗa daga asibitin zuwa hanyoyin karkashin ƙasa, kuma akwai hujjar cewa ɗaruruwan mayakan Hamas sun ɓoye a asibitin bayan harin da aka kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
Daga baya Amurka ta ce leƙen asiri da ta yi ya tabbatar da kalaman Isra'ila game da amfani da asibitin da Hamas ta yi - ko da yake Hamas ta sha musanta hakan.
Isra'ila ta ce dakarunta sun shiga asibitin ne kimanin sa'o'i 36 da suka gabata. Sun ba wa 'yar jaridar BBC, Lucy Williamson damar shiga, inda suka nuna mata kayayyakin da suka ce sun gano - ciki har da bindigogi 15, rigar da harsashi ba ya rasata, da sauran kayayyaki da suka haɗa da kwamfuta.
Har yanzu dakarun ba su nuna shaidar wani sansanin Hamas ko hanyoyin a karkashin asibitin ba kamar yadda ta yi iƙirarin kasancewarsa a watan da ya gabata.
Shugaban hukumar ƴan gudun hijirar Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce yayi ammanar cewa ana ƙoƙarin gurgunta masa ayyukansa a Gaza da gangan.
Philippe Lazzarini ya ce an sanya hukumarsu wani yanayi marar kyau, yayin da sai sun roki mai da za su iya yin ayyukan jin ƙai, yanayin da ya kira da mafi muni.
Hukumar ta MDD na taimakawa mutane sama da dubu ɗari takwas a Gaza.
Isra'ila ta dakatar da shigar da fetur tana mai cewa Hamas za iya amfani da shi.
Bankin Raya Afirka (AfDB) ya zargi jami'an tsaro a Habasha da kama ma'aiktansa biyu ba bisa ka'ida ba da kuma cin zarafinsu.
A cewar wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce lamarin ya faru ne a Addis Ababa, babban birnin ƙasar, makonni biyu da suka gabata.
An tsare ma'aikatan biyu ne waɗanda ba a bayyana sunayensu ba na sa'o'i da dama - ba tare da wani bayani a hukumance ba – har sai da aka samu labarin kama su, Firaminista Abiy Ahmed ya shiga tsakani tare da ba da umarnin a sake su cikin gaggawa, in ji sanarwar bankin.
AfDB ya kira faruwar lamarin "mummunan lamari na diflomasiyya," inda ya ce shigar da ƙorafi a gaban hukumomi.
Bankin na ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗar kuɗi na ƙasar Habasha kuma shugaban bankin, Akinwumi Adesina, yana da kyakkyawar alaƙa da Firaminista Abiy Ahmed.
A cikin watan Satumba, AfDB ya amince da sama da dala miliyan 100 don tallafawa inganta samar da wutar lantarki a Habasha.
Jami’an tsaro ba su ce uffan ba kan zargin kuma yunkurin da BBC ta yi na samun martani bai yi nasara ba.
Sojojin Isra'ila sun ce sun gano gawar wata ƴar ƙasar mai suna Yehudit Weiss kusa da wani asibitin Gaza mafi grima, wanda Hamas ta yi garkuwa da shi a harin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoba.
A wata sanarwa da dakarun tsaron Isra'ilar suka fitar, sun ce sojojin ƙasar suka gano gawar daga wani gini kusa daura da asibitin Al-Shifa.
Sun ce sun gudanar da wani bincike kuma sun sanarwa iyalan matar da suka gano gawarta.
Sanarwar ta kuma ce an yi garkuwa da Weiss a gidanta da ke birnin Be'eri, kusa da iyakar Isra'ila da Gaza.
Ɗan takarar jam'iyyar adawa a Laberiya Joseph Boakai na gaban shugaba mai ci George Weah a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa.
Sakamakon zaɓen da aka fitar kawo yanzu, wanda ke zuwa bayan tattara kuri’u sama da 5,000 daga cikin rumfunan zaɓe 5,890, ya nuna cewa Mista Boakai na da kashi 50.58, shi kuma shugaba Weah na da kashi 49.42.
A zagayen farko, dukkan mutanen biyu sun yi kankankan - inda ɗan takara na uku ya samu kashi 2 na kuri'un.
Shugaban ƙasar Weah da Mista Boakai ba su samu sama da kashi 50 na kuri'un da aka kaɗa a zagayen farko na zaɓen ba, lamarin da ya janyo aka je zagaye na biyu.
Ƴan takarar guda biyu sun fuskanci juna a zaɓen shekarar 2017, wanda aka kammala bayan zuwa zagaye na biyu wanda shugaba Weah ya samu nasara cikin kwanciyar hankali.
Ana sa ran samun sakamakon zaɓen duka a cikin kwanaki 15.
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan jihar Zamfara, a matsayin wanda bai kammala ba.
A hukuncin da ɗaukacin alƙalanta uku ƙarƙashin Mai shari'a Sybil Nwaka suka amince da shi, kotun ta soke halascin zaben Gwamna Dauda Lawal Dare na ranar 18 ga watan Maris din 2023.
Kotun da yammacin ranar Alhamis a Abuja, ta kuma bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomin Zamfara uku, da suka haɗa da Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukkuyum.
Ta ce kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar Zamfara, ba ta yi la’akari da hujjojin da masu ƙara suka gabatar ba – wato jam'iyyar APC .
Kotun ta kuma yi watsi da sakamakon da jam’iyyar APC da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC suka bayar na ƙaramar hukumar Maradun.
Don haka ta umarci hukumar zabe (INEC) ta gudanar da sabon zabe a ƙananan hukumomin uku, inda ba a gudanar da zabe ba a baya, ko kuma ba a ƙidaya sakamakon wasu tashoshin zabe ba.
Dan takarar jam'iyyar APC a zaben watan Maris, Bello Matawalle ne sake kalubalantar hukuncin da karamar kotun zaben jihar Zamfara ta yanke, wanda ta kori shari'arsa bisa hujjar cewa ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji.
Tsohon gwamnan na Zamfara, wanda a yanzu yake rike da mukamin karamin ministan tsaro, yana neman wa'adin mulki na biyu ne bayan karewar mulkinsa na tsawon shekara hudu.
Wani kare da aka samu a raye a gefen gawar mai ita makonni 10 bayan sun ɓace a tsaunin Colorado ta rayu ne ta hanyar farautar ƙananan dabbobi, in ji masu ceto.
Rich Moore, mai shekaru 71, tare da Jack Russell terrier, Finney, sun yi niyyar hawan tsaunin Blackhead a ranar 19 ga watan Agusta, amma ba su dawo gida ba.
An gano gawar Mr Moore a ranar 30 ga watan Oktoba, tare da Finney a gefensa. Masu ceto sun ce tsira da karen ya yi "kyakkyawan labari ne".
Delinda VanneBrightyn, na ƙungiyar sa kai ta Taos masu aikin ceto, ta ce masu aikin ceto sun yi wani bincike na tsawon kwanaki da bai yi nasara ba a gaɓar yammacin tsaunin da ke tsakanin inda motar Mista Moore ke ajiye.
Makonni bayan haka wani mafarauci ya gano gawar Mista Moore a cikin tsaunin San Juan - kimanin kilomitoci 2.5 gabas da kololuwar - tare da Finney wanda ke raye.
An tura jami'an ceto zuwa tsaunin washegari. An kai karen zuwa wurin likitan dabbobi kuma yanzu yana tare da dangin Mista Moore.
Mai magana da yawun sojojin Isra'ila, Laftanar Kanal Jonathan Conricus ya faɗa wa BBC cewa dakarun tsaron ƙasar na aiki don bankaɗo abin da ta kira asibitin Hamas da ke karkashin ƙasa a birnin Gaza - sai dai ta ce hakan zai ɗauki tsawon makonni biyu.
Hamas ta musanta gudanar da wani sansani soji a karkashin asibitin.
A cikin dare, dakarun tsaron ƙasar sun bar wakiliyar BBC Lucy Williamson shiga cikin asibitin Al-Shifa - kuma sun nuna mata kayayyaki da suka ce na Hamas ne, ciki har da makamai da kuma wasu kadarori.
Har yanzu, dakarun ba su kai ga nuna hujjojin cewa akwai sansanin sojin Hamas ba ko wurin ɓuya na karkashin ƙasa a asibitin.
Sai dai, Conricus ya ce: "Ba mu yi bincike cikin asibitin gaba-ɗaya ba kawo yanzu - ko kusa ba mu yi ba."
Dangane da batun cewa akwai gini na karkashin ƙasa kuwa, ya ce: "Muna fatan kai wa inda ginin yake tare da yaɗa hotunan bidiyonsa."
Kotun ɗa'ar ma'aikata ta bayar da belin shugaban hukumar karbar ƙorafi da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Kotun - wadda ke zamanta a Abuja - ta ba da belin Muhuyi ne bisa sharaɗin ajiye naira miliyan biyar tare da mutum biyu mazauna Abuja da za su tsaya masa, sannan su nuna shaidarsu ta kwakkwaran aikin da suke yi, kuma su bayyana shaidar karfin samunsu.
Dole ne kuma masu tsaya wa Muhyi Rimin Gado su gabatar da ƙananan hotunansu da na wanda suke tsayawan.
Haka kuma kotun ta ce dole ne Muhuyi ya gabatar takardar shaida daga wani fitaccen mutum mazaunin Abuja da ke aiki ko sana'a a babban irnin.
Shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamne Tiani ya bayyana a karon farko cikin bainar jama'a a wajen fadar shugaban kasa, tun bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli.
A baya dai, shugaban majalisar mulkin sojan ta CNSP, ya sha fuskantar suka daga bangarori daban-daban a Nijar, saboda rashin fita wajen fadar shugaban kasa a bainar jama'a.
Janar Tiani ya fita wajen fadar shugaban kasar ne a yau Alhamis, inda ya halarci taron rantsar da mambobin sabuwar hukumar yaki da cin hanci ta kasar (COLDEF), da kuma mambobin Babbar Kotun kasa ta Cour d'Etat da ke yi wa tsoffin shugabannin kasa da manyan jami'an gwamnati shari’a.
A ranar 26 ga watan Yulin wannan shekara ne, Janar Tchiani ya hambarar da Shugaba Bazoum Mohamed daga kan mulki, abin da ya sanya sabbin shugabannin sojin kai ruwa-rana da kungiyar Ecowas da kuma manyan Kasashen Yamma masu kawance da Nijar.
Ecowas dai tun da farko ta bai wa sojoji masu juyin mulki wa'adi su mayar da Bazoum a kan mulki ko kuma ta yi amfani da karfin soja a kan kasar. Lamarin da ya haifar da zaman dar-dar da tankiya musamman tsakanin Nijar da kungiyar Ecowas da kuma Faransa wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka.
Karin bayani kan halin da ake ciki a asibitin Al-Shifa da sojoin Isra’ila suka shiga tun safiyar ranar Laraba.
Ma’aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce dakarun Isra’ila sun lalata sashen ɓangaren kula da ɗaukar hoton jiki na asibitin bayan da wani hari ya faɗa kan sashen da ke kula da masu lalurar mafitsara.
Jami’an lafiyar sun ce duba likitoci da waɗanda suka jikkata da mutanen da ke neman mafaka a asibitin wanda shi ne mafi girma a Gaza.
BBC ba ta iya tabbatar da wannan iƙirari ba, amma tana ƙoƙarin ganin ta binciko ainihin abin da ke faruwa a asibitin.
Tawagarmu da ke birnin Kudus ta yi ta ƙoƙarin neman likitoci uku a asibitin ta hanyar kiransu a waya ko tura musu saƙonni, tun safe, amma har yanzu ba a same shu ba.
To sai dai ba mu sani ba ko hakan na da alaƙa da rashin sabis da kamfanonin ke fuskanta sakamakon rashin man fetur da za su tashi injinansu.
Kotun daukaka kara ta sanya Juma'a, 17 ga watan Nuwamba, a matsayin ranar yanke hukunci kan karar da gwamnan Kano ya daukaka, inda yake kalubalantar soke nasarar zabensa.
Abba Kabir Yusuf ya garzaya gaban kotun daukaka kara, bayan kotun korafin zabe ta jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba, ta rushe nasarar da ya samu, inda ta ce abokin takararsa na jam'iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna ne halastaccen wanda ya ci zabe.
Kotun dai ta kafa hujjar hukuncin da ta yanke ne a kan kuri'u sama da 165,000 da ta soke daga cikin abin da Abba Kabir Yusuf na NNPP ya samu, saboda rashin sa hannu da kwanan wata da kuma hatimin hukumar zabe. Jam'iyyar APC, ita kuwa ta roki kotun ta yi watsi da karar da Gwamna Abba Kabir ya daukaka.
Hukuncin kotun daukaka karar na zuwa ne kwana goma cif bayan alkalan kotun da ke zama a Abuja, sun saurari bahasin dukkan bangarorin da ke cikin shari'ar, tare da sanya hukuncinsu a mala, sannan suka ce za su sanar da ranar yanke hukunci nan gaba.
Wata takardar kotun daukaka kara da BBC ta gani, ta lissafa APC da NNPP da kuma INEC a matsayin wadanda ake kara. Sannan ta ce kotun za ta fara zaman yanke hukunci daga misalin karfe 9:00 na safe.
Shari'ar zaben gwamnan Kano na daya daga cikin shari'o'in zabe mafi muhimmanci tun bayan kada kuri'a a babban zaben kasar cikin watan Fabrairu da Maris.
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya tana fatan kotu za ta dawo mata da kujerar gwamna, wadda ta kubuce daga hannunta, zuwa hannun jam'iyyar adawa ta NNPP, yayin da NNPP ke alla-alla ta tsira da kujerar gwamna daya tilo da ta samu bayan zaben 2023.