Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi
Rufewa
Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawo wa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Birtaniya za ta tura jirage zuwa Isra'ila
Asalin hoton, Getty Images
Birtaniya za ta tura jirage masu sa ido da jiragen sojojin ruwa a gabashin Bahrum domin nuna goyon baya ga Isra'ila.
Ofishin Firaiministan Birtaniyar ya ce jiragen za su fara aiki ne ranar juma'a, domin hana duk wani yunƙuri na shigar da makamai ga ƙungiyar Hamas a yankin.
Tuni dai Amurka ta kai na ta tallafin Jiragen a Isra'ila.
A wani labarain na daban kuma Faransa ta haramta zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa bayan da Hamas ta kai hari a Isra'ila.
Ministan harkokin cikin gida Gerard Darmanin, ya ce akwai yiyuwar masu zanga-zangar su kawo cikas ga zaman lafiya, lamarin da ka iya sanyawa a kama waɗanda suka shirya zanga-zangar.
Faransa da tafi kowace ƙasa a Turai yawan Yahudawa da Musulmai.
Kuma ƙasar na fuskantar zanga-zangar ƙin jinin Yahudawa tun ranar Asabar, lamarin da ya kai ga kama mutane sama da ashirin.
Shugaban sojin Isra'ila ya ce rundunarsa ta gaza wajen kare ƙasar amma sun koyi darasi
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Sojin Isra'ila ya amince cewa sojojin ƙasar sun gaza wajen kare Isra'ila da al'ummarta a lokacin da Hamas ta ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa da sama da ta ruwa.
Laftanal Janar Hezi Helovi ya shaida wa manema labarai cewa ba su iya aiwatar da aikin da ke wuyansu ba, amman sun ɗauki darasi.
Ya ce dakarun ƙasar ne ke da alhakin samar da tsaro a Isra'ila, sai dai sun gaza a safiyar Asabar saboda haka yanzu lokacin yaƙi ne.
Shugaban ƴan adawar Isra'ila Yaa Lapid ya kira harin na Hamas da gazawar gwamnatin Netanyahu da ba za a taɓa yafewa ba.
Shirin abinci Samar da Abinci na Duniya (WFP) ya yi gargaɗin cewa abinci da ruwa na daf da ƙarewa a Gaza.
WFP ya bayyana lamarin da mummunan yanayi. Yankin na fama da tashe-tashen bama-bamai, tare da fuskantar toshewar duk wata hanyar samar da kayan agaji, wanda Isra'ilar ta ce ba za ta janye ba har sai an sako mutanenta da Hamas ta yi garkuwa da su.
Wakilin BBC ya ce rashin ayyukan jin ƙai na ƙara ƙazanta yanayin da ake ciki, yyayin da asibitocin yankin ke cikin mawuyacin hali.
Dubun mutane ne suka rasa muhallansu sakamakon hare-hare ta sama da Isra'ila ke kai wa Gaza.
Fiye da mitim 1, 400 ne aka kashe sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin ɓagarorin biyu.
An bai wa maniyyatan Najeriya wa'adin mako uku su biya miliyan 4.5 kuɗin ajiya
Asalin hoton, NAHCON
Hukumar Alhazan Najeriya ta bai wa maniyyata aikin hajjin bana wa'adin makonni uku da su biya naira miliyan 4.5 a matsayin kudin ajiyarsu.
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne kasancewar makonni uku ne kawai suka rage mata na kammala daidaitawa da masu tafiyar da lamuran aikin Hajji a Saudiyya.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa - hannun mataimakiyar daraktan hulda da jama'a na hukumar, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta ce hukumomin saudiyya sun sanya ranar 4 ga watan Nuwamba domin kammala duk wata tattaunawa da masu kula da lamuran aikin hajji na ƙasar.
Kan haka ne hukumar ke buƙatar samun ƙiyasin maniyyatan aikin hajin bana domin samun damar ƙayyade farashin aikin hajjin banan.
Sanda Usara ta ce fara shirye-shiryen aikin hajin 2024 da wuri ya sa hukumar Alhazan ƙasar da na jihohin ƙayyade kudin ajiya na naira miliyan 4.5
Maniyyata sun koka a kan tsadar kuɗin aikin hajjin bana a Najeriya
'Kuɗin aikin hajjin 2024 na iya kaiwa naira miliyan biyar'
Kawuna sun rabu kan korar da sojojin Nijar ke wa ƙasashen duniya
CBN ya ɗage haramcin bayar da dala ga masu shigar da shinkafa Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Babban Bankin Najeriya CBN ya ɗage haramcin bayar da chanjin dala don shigar da shinkafa da wasu kayyaki 42 cikin ƙasar a wani yunƙuri na tallafa wa kasuwar musayar kuɗi na 'lokaci zuwa lokaci'.
A shekarar 2015 ne CBN ya taƙaita bayar da dala domin shigar da wasu abubuwa ƙasar, yana mai cewa bai su kamata a bayar da dala domin shigar da su ba, kasancewar ana iya samar da su a cikin ƙasar.
To sai dai cikin wata sanarwar da CBN din ya fitar ranar Alhamis, mai ɗauke da sa hannun babban daraktan sadarwa na CBN ɗin, Isa AbdulMumin, ya ce kayyakin da ɗage wa haramcin ya shafa sun haɗar da shinkafa da sumunti da man ja da nama da kaji da sabulu da kayan kwalliya da sauran abubuwa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa a yanzu masu shigo da abubuwa 43 za su iya samun chanjin dala daga babban bankin na CBN.
CBN ya ce a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi
Me ya sa darajar naira ke daɗa karyewa?
FBI na bincikar tsohuwar ministar Ghana
Asalin hoton, MINISTRY OF SANITATION AND WATER RESOURCES FACEBOOK
Hukumar FBI da ofishin mai shigar da ƙara na musamman na Ghana (OSP) na duba kadarori da hada-hadar kudi na tsohuwar ministar tsaftar muhalli, Cecilia Abena Dapaah da abokan huldarta a Amurka.
A cikin wani sako da aka wallafa a dandalin sada zumunta na X, OSP ta ce: "Wannan kokarin hadin gwiwa shi ne na tabbatar da halalcin dukiyar Dapaah da 'abokan hulɗarta, dangane da yadda kuɗaɗensu ke tafiya daga Ghana zuwa Amurka."
Tsohuwar ministar a halin yanzu tana karkashin bincike daga OSP kan zarge-zargen cin hanci da rashawa biyo bayan gano wasu kuɗaɗe sama da dala miliyan ɗaya a gidanta.
Labarin kuɗaden ya kai ga jama'a ne bayan wasu ma'aikatan gida biyu sun sace su - kuma Dapaah da kanta ta kira 'yan sanda.
An tilasta mata yin murabus a lokacin da wasu 'yan Ghana da 'yan majalisar dokokin ƙasar suka yi tambaya kan tushen kudin.
Yanzu haka dai rahotanni sun bayyana cewa tsohuwar ministar ta shigar da ƙara a gaban kotu tana neman a dakatar da ofishin mai shigar da kara na musamman daga bincikenta da mijinta.
Masar ta ce ta bayar da umarnin kai kayan agaji na jiragen duniya zuwa Gaza ta filin jirgin Sinai da ke arewacin ƙasar.
Ƙasar da ke arewacin Afrika ita ce ke kan gaba wajen shiga tsakanin a rikicin da ke faruwa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.
Masar ta nemi Isra'ila da ta kiyaye kai hari ta hanyar Rafah da ta tashi daga Masar ɗin zuwa Gaza, wadda ta riƙa kai wa hari a farkon makon nan.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa Masar ta gargaɗi Isra'ila game da kai harin, kwanaki gabanin Hamas ta kaddamar da hari cikin Isra'il.
Amma Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana rahoton a matsayin na "ƙarya".
An dakatar da jami'in MDD a DR Congo kan cin zarafin lalata
Asalin hoton, UN
Bayanan hoto, Akwai sama da dakarun MDD 14,000 a ƙasar
Shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ya ce ya dakatar da wasu daga cikin jami'ansa bayan wani rahoto ya zarge su da rashin ɗa'a.
Ya ce ba zai iya jure wa cin zarafi ta hanyar lalata ba da kuma ta kowacce irin hanya.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ana zargin wasu jami'ai takwas ne da suka fito daga Afirka ta Kudu.
Shirin wanzar da zaman lafiyar ya fuskanci irin waɗannan zarge zarge a baya.
Majalisar Dinkin Duniya na da dakaru sama da 14,000 a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
UEFA ta ɗage wasan Kosovo da Isra'ila
Mamayen Isra'ila ta ƙasa a Gaza akwai ‘ƙalubale’ – ƙwararren mai ƙiyasta kasada
Yayin da muke ba ku rahotannin cewa rundunar sojojin Isra'ila ta jibge dubban dakarunta cikin shiri a kan iyaka da Gaza, da yiwuwar shiga yanki da mamaye ta ƙasa.
Noam Ostfeld, wani tsohon jami'in leƙen asiri na rundunar sojin Isra'ila, wanda yanzu yake aiki da kamfanin Sibylline mai ƙididdige girman kasadar al'amura, a matsayin ƙwararren masani kan harkokin Gabas ta Tsakiya.
Ya fada wa BBC cewa ga alama Isra'ila na da niyyar kai hare-hare ne cikin hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da Hamas ke amfani da su, wadanda ya bayyana da cewa lamari ne "mai cike da ƙalubale".
“Suna da matuƙar kariya, a tsuke suke sosai, sau da yawa lantarki mai dishi-dishi suke da shi, ko ma ba su da hasken lantarki kwata-kwata.”
Wani zabin kuma a cewar Ostfield shi ne wanda ake tsakiyar tattauna shi wato na “dakarun ƙundumbala” da za su shiga ciki kuma su kubutar da 'yan Isra'ila fiye da 100 da aka yi garkuwa da su.
“Gaba daya dai wannan wani yanki ne mai matuƙar wahalar zuwa yin fada.
"Gaza, yankin birnin ne mai yawan cunkoson jama'a. Duk wani mamaye ta ƙasa da za a kai Gaza, zai zama wani abu mai matuƙar ƙalubale kuma mai yiwuwa za a samu dumbin asarar rayuka daga kowanne bangare.”
Ƴan bindiga sun kashe mutum 1,715 a Najeriya cikin wata uku
Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto na kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro a Najeriya ya ce ƴan bindiga sun hallaka mutum 1,715 a faɗin Najeriya tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2023.
A cikin rahoton wanda kamfanin ya fitar yau Alhamis, ya ce an kashe mutane mafi yawa ne a yankin arewa maso gabashin ƙasar, inda aka kashe mutum 491.
Arewa maso yammacin ƙasar ne na uku a yawna mutanen da aka kashe, inda aka kashe mutum 362.
Jihohin da lamarin ya fi muni su ne Borno da Filato da kuma Zamfara.
Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro a yankunan daban-daban na ƙasar, waɗanda suka haɗa da na ƴan fashin daji a arewa maso gabas da Noko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.
Bugu da ƙari ana fama da matsalar ƴan fashi da kuma masu garkuwa da mutane a arewa maso tsakiya da kuma kudancin ƙasar.
Maguire ya jinjina wa David Beckham
Cutar mashaƙon diphtheria ta kashe mutum 600 a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Sama da mutum 600, waɗanda yawancinsu yara ne suka rasa rayukansu a Najeriya sanadiyyar cutar diphtheria tun bayan ɓullar ta a watan Disamban 2022.
Hukumomi sun ce jimillar mutum 14,000 ne suka kamu da cutar, wanda hakan ya zarta mutanen da suka kamu da ita a lokacin da ta ɓarke a 2011, inda mutum 98 suka kamu.
Kano, wadda ke a arewacin Najeriya, ita ce jihar da ta fi fama da matsalar, inda aka samu mutum 500 da suka mutu sanadiyyar cutar, sai dai hukumomi sun ce lamarin na lafawa a yanzu.
Diphtheria cuta ce ta mashaƙo wadda ke saurin yaɗuwa, kuma tana shafar sassan jiki irin su hanci da maƙoshi.
Haka nan cutar kan haifar da gyambo a ciki ko kuma ta shafi fatar jiki.
Cutar na yaɗuwa ne ta hanyar tari da atishawa daga masu fama da ita.
Duk da cewa ana iya samun kariya daga cutar ta hanyar rigakafi, yawancin yaran da suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar ba su samu rigakafin ba.
An haifi tagwaye sama da 16,000 a Saudiyya
Asalin hoton, saudigazette
Ƙasar Saudiyya ta samu haihuwar tagwaye 16,160 a cikin shekarar 2022, kamar yadda alkaluman kididdiga da Hukumar Kididdiga ta Kasa (GASTAT) ta fitar.
Rahoton GASTAT, wanda aka samu kwafinsa daga Okaz/Saudi Gazette, ya bayyana cewa adadin haihuwa da aka yi a Saudiyya maza da mata a dukkan yankunan masarautar ya kai 417,155 a shekarar da ta gabata.
Yankin Riyadh ya samu adadin haihuwa 96,619 a tsakanin uwayen Saudiyya, waɗanda 4,140 haihuwar tagwaye ne, kuma 226 haihuwar ƴan uku da sauransu.
A yankin Makkah, an yi rijistar haihuwa 82,135, daga cikinsu 3,092 tagwaye ne kuma 162 ƴan uku ne da sauransu.
A yankin Madina an samu adadin haihuwa 31,894, inda aka samu tagwaye 1,200, da kuma ƴan uku 70 da sauransu.
Yankin Asir na kudancin kasar ya bayyana haihuwar mata 32,008 , wadanda suka hada da tagwaye 1,054, da ƴan uku 65 da kuma sauransu.
A cikin wannan lokacin, yankin Jazan ya yi rajistar haihuwa 21,498, wadda an samu tagwaye 788, ƴan uku 39 da sauransu.
Dangane da yankin Al-Qassim, an samu adadin haihuwa 19,714, da suka hada da haihuwar tagwaye 658, ƴan uku 43 uku da sauran su.
Yankin Tabuk da ke arewacin ƙasar ya yi rijistar haihuwa 15,658, da suka haɗa da tagwaye 584 da ƴan uku 17 da sauransu.
Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar EFCC
Asalin hoton, PRESIDENCY
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Ngelale ya bayyana cewa naɗin Olukoyede, na tsawon shekara hudu ne a matakin farko, amma sai majalisar dattawa ta tabbatar da shi.
Sanarwar ta ce shugabancin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa na ƙasar na samun sauye-sauye cikin 'yan watannin da suka gabata, tun bayan hawan Bola Tinubu karagar mulki a ranar 29 ga Mayu.
A ranar 14 ga watan Yunin 2023, Bola Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC, kuma har yanzu yana tsare a hannun hukumomi ba tare da an gurfanar da shi gaban shari'a ba.
Sanarwar ta ce Tinubu ya dakatar da Bawa ne "don ba da damar yin ingantaccen bincike kan yadda ya gudanar da aiki lokacin shugabancinsa".
Matakin ya zo ne bayan zarge-zarge ''masu nauyi'' na tozarta mukaminsa, in ji sanarwar.
Daga nan ne shugaban ya umurci daraktan ayyuka na hukumar Abdulkarim Chukkol ya rike shugabanci EFCC a mataki na wucin gadi.
Ngelale ya ce matakin da shugaban kasar ya dauka na nada Olukoyede a matsayin sabon shugaban EFCC ya samo asali ne daga damar da aka ba shi bisa tanadin dokar da ta kafa hukumar EFCC ta 2004, sashe na 2 karamin sashe na 3.
“Ola Olukoyede lauya ne mai gogewa tsawon shekaru sama da 22 a matsayin mai ba da shawara kuma kwararre ne kan gano laifukan damfara da kuma ƙididdige muhimman bayanai don masu mulki." in ji Ngelale.
Blinken zai gana da shugaban Falasdinawa ranar Juma'a
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas zai gana da sakataren wajen Amurka Antony Blinken ranar Juma'a, a cewar Hussein Al-Sheikh, babban sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar kwatar 'yancin Falasɗinawa.
Jagororin siyasa na Falasɗinawa sun samu rarrabuwar kawuna tsakanin jam'iyyar Mahmoud Abbas Fatah a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma 'yan adawar Hamas masu gwagwarmaya da makamai da ke iko da Zirin Gaza.
Blinken dai ya isa Isra'ila a yau sa'o'i da suka wuce domin nuna goyon bayan Amurka bayan harin Hamas.
Jami'in na Falasdinawa ya kuma fada a cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X cewa Shugaba Abbas zai kuma gana da Sarki Abdullah na Jordan a Amman ranar Alhamis.