Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Mun bi matakan da suka dace kafin ɗaura aure da mai HIV a Katsina'

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu dawo muku da sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnatin Benue ta kama mutum tara da zargin karɓar kuɗin haraji ba bisa ka'ida ba

    Haɗakar jami'an tsaro a jihar Benue, sun ce sun kama mutum tara da ake zargin suna karɓar kuɗin haraji ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Guma da ke jihar.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa an kama mutanen ne a kan babbar hanyar Makurdi zuwa Lafia, lokacin da suke artabu da matasa a garin Daudu da ke karamar hukumar.

    An samu hatsaniya lokacin da jami'an tsaron da suka kunshi ƴan sanda da jami'an kare hakkin fararen hula ta cibil defense suka je kama uku daga cikin waɗanda ake zargin.

    Ƴan sanda sun yi artabu da matasa a garin Daudu, lokacin da suka yi yunkurin tafiya da waɗanda ake zargin zuwa Makurdi, babban birnin jihar, inda matasan suka toshe wata babbar hanya, abin da ya janyo ƴan sandan suka yi ta harbi a iska domin tarwasa su.

    Daga baya ne jami'an tsaron suka koma garin na Daudu tare da ƙarin wasu sojoji, inda suka kama wasu mutane shida da ake zargi da karɓar harajin ba bisa ka'ida ba.

    An kuma ƙona dukkan kayayyaki da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin.

  3. Jarumar fim ɗin Game of Thrones ta kai ƙarar tsohon abokin zamanta

    Jaruma 'yar Birtaniya Sophie Turner ta kai ƙarar tsohon abokin zamanta kuma mawaƙi Joe Jonas - inda ta roƙi kotu ta sanya shi dawo da 'ya'yansu biyu "gidan da suka saba" zama na Ingila.

    Shahararrun ma'auratan sun ba da sanarwa a farkon wannan wata cewa za su raba aurensu bayan sun shafe tsawon sama da shekara huɗu tare.

    A lokacin sun bayyana rabuwar da cewa za a yi ta ne "cikin girma da arziƙi".

    Sai dai a ranar Alhamis, lauyoyin matashiyar Sophie Turner, mai shekara 27, sun shigar da wata ƙara inda suka kafa hujja da "tsarewa ba bisa ƙa'ida ba" da ake yi wa 'ya'yan ma'auratan a birnin New York.

    Mawaƙin Ba'amurke mai shekara 34 yana neman a ba su riƙon haɗin gwiwa na 'ya'yan nasu mata da Willa wadda aka haifa a shekara ta 2020 da kuma ƙanwarta da aka haifa bara, ko da yake ba a sanar da jama'a sunan da aka raɗa mata ba.

    A cewar takardar ƙorafin shari'ar Sophie Turner, wadda BBC ta samu gani, ma'auratan sun mayar da Ingila ta zama "gidansu na dindindin" a watan Afrilu.

    Takardar ta bayyana cewa Joe Jonas bisa kuskure ya yi iƙirari a cikin takardar rabuwar aurensa cewa yaran waɗanda ke da shaidar zama 'yan ƙasashe biyu, sun zauna a Florida tsawon wata shida kafin ya shigar da buƙatar.

    Turner da Jonas sun amince da barin yaran su kai ziyara Amurka a watan Agusta, inda mahaifinsu ke rangadin wasanni, kamar yadda takardar ƙorafin ta ce, amma matakin wani "shiri ne kawai na wucin gadi".

  4. Shugaban gidan talabijin na Fox ya yi murabus

    Shugaban kamfanin tashoshin yaɗa labarai mafi ƙarfi a duniya, Rupert Modak ya sauka daga muƙaminsa na jagorancin kamfanin na Fox.

    Mista Rupert na da shekaru casa'in da biyu a duniya. Babban ɗan sa Latchlan ne ya maye gurbinsa na shugabancin kamfanin.

    Mista Rupert ya soma aiki ne daga kamfanin jarida na ƙasarsa Austireliya, inda ya kwashe shekaru saba'in yana ginawa tare da faɗaɗa kamfanin nasa a sassa daban-daban na duniya.

    Kamfanin ya sanya Mista Modak ya zama mai ƙarfin faɗa a ji a siyasar Amurka da Birtaniya sai dai duk da haka ana zarginsa da tafka badaƙaloli da dama.

  5. Liverpool ta doke LASK a Europa League

  6. 'Yan sandan Koriya na binciken sojojin Amurka kan zargin fataucin ƙwaya

    Ƴan sandan Koriya na bincken sojojin Amurka 17 da wasu mutum biyar kan zargin fataucin tabar wiwi.

    Wannan ya biyo wani samame ne da aka kai sansanonin sojin Amurka biyu a watan Mayu, da ya haɗa da ɗaya daga cikin babban sansani mai suna Humphreys.

    An kama ɗan ƙasar Philippines da kuma ɗan Koriya ta Kudu a samamen, yayin da masu shigar da kara ke sake duba wasu shari'o'i 22 kan waɗanda ake zargin.

    Wani bayani daga sojojin Amurka ya janyo hukumomin Koriya yin bincike har na tsawon watanni huɗu.

    Wannan dai shi ne ɗaya daga cikin babban zargi da ake yi wa sojojin Amurka a baya-bayan nan.

    Wani haɗin gwiwar samame da ƴan sandan Koriya da sashen binciken manyan laifuka na sojojin Amurka suka yi, ya gano tabar wiwi mai nauyin kilo 77 da kuɗinsa ya kai $12,850 a gidajen mutanen 22 da ake zargi.

    An zargesu da fataucin tabar wiwi zuwa cikin Amurka ta amfani da hanyar aika sako ta gidan waya na sojojin.

  7. Wani mutum ya amsa laifin kashe mutane 14 a Rwanda

    Wani mutum da ake zargi da kashe mutane goma sha hudu a Rwanda ya amsa laifinsa bayan da aka gurfanar da shi gaban kotu da ke Kigali-- babban birnin ƙasar.

    Ana tuhumar Denis Kazungu da laifin kisa da fyaɗe da kuma azabtar da mutane da sace su domin neman kuɗin fansa.

    Mutanen da ya kashen mutum goma sha biyu maza ne sai kuma mata biyu.

    Tun a farkon watan nan ne aka samu gawarwakin mutanen cikin wani rami a kusa da gidan Mr Kazungu da ke kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na ƙasa da ƙasa da ke Kigali.

    Kotun ta yi kuma watsi da buƙatar wanda ake tuhumar bayan ya nemi a yi shari'ar a asirce.

  8. An sallamo 'yan firamare 87 da suka ci biskit mai tabar wiwi daga asibiti

    An sallamo 'yan firamare 87 da aka kwantar a asibiti, bayan sun ci biskit wanda aka haɗa shi da tabar wiwi.

    Yara guda uku ne kawai suka rage a asibiti, inda likitoci ke ci gaba da kula da su.

    Sashen kula da ilmi na lardin Gauteng a Afirka ta Kudu ya ce lamarin ya faru ne ranar Laraba a Makarantar Firamaren Pulamadibogo da ke yankin Soshanguve, arewa maso yamma da Pretoria, babban birnin ƙasar.

    Ɗaliban sun riƙa jin tasowar amai da murɗewar ciki da haraswa bayan sun ci wani nau'in biskit da ake kira 'space cookies'.

    An kai biskit ɗin a gefen titi a wajen harabar makarantar bayan an saye shi daga mai sarrafa abinci.

    Babu tabbaci ko 'yan sanda sun shigar da tuhuma ko kama mai sayar da abincin da aka gano daga bisani.

  9. 'Yan sanda sun sanar da ɗage dokar hana fita a Kano

    Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta sanar da ɗage dokar hana fita ta tsawon sa'a 24, da aka sanya a jihar.

    Mai magana da yawun rundunar, SP Abdulahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da haka a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook.

    A ranar Laraba ne dai rundunar ƴan sandan Kano ta sanya dokar bayan yanke hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna, da ya soke nasarar Abba Kabir Yusuf, tare da ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen gwamna.

  10. Rashin ruwa na tilasta wa mazauna Derna barin garin

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa kimanin mutum 43,059 ambaliyar ruwa ta tilasta wa barin gidajensu a arewa maso gabashin ƙasar.

    Rahotonni na cewa rashin ruwan sha ne ya tilasta wa mutanen barin birnin Derna, bayan da madatsun ruwa biyu suka fashe a lokacin ambaliyar da ta auka wa wani yanki na ƙasar cikin makon da ya gabata.

    Da yawa na barin birnin inda suke komawa wurin 'yan'uwansu da ke biranen gabashin ƙasar irin su Tobruk da Benghazi.

    Yayin da wasu ke komawa biranen Tripoli da Hai Alandalus da Misrata da Ghiryan da kuma Qasr bin Ghasheer.

    Sauran abubuwan da ke tilasta wa mutanen barin birnin sun hadar da rashin abinci da magunguna, kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta bayyana.

  11. Everton na bincike kan cin zarafin da aka yi wa ɗan wasan Arsenal

  12. An gano gawar ɗalibar jami'a a Abuja bayan kwanaki da ɓata

    An gano gawar wata ɗalibar jami'a a Abuja mai suna Blessing Karami, wadda aka sanar da ɓacewarta a ranar 11 ga watan Satumba.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan babban birnin tarayya, Abuja, Josephine Adeh, ta fitar, ta ce an kai rahoton ɓatan ɗalibar ga 'yan sanda ne tun ranar Litinin a makon jiya.

    An ruwaito cewa ɓatan ɗalibar mai shekara 26, da ke Jami'ar karatu daga nesa (NOUN), lokacin da ta bar wurin aiki a unguwar Garki, da ke Abuja.

    Sanarwar 'yan sanda ta ce an gano gawar ɗalibar ne a unguwar Karimo da ke da dazuka.

    Hukumar ƴan sandan birnin Abujan ta ce za ta gudanar da cikakken bincike a kan lamarin domin gano waɗanda ke da hannu a kisan matashiyar.

  13. Majalisar dokokin Indiya ta zartar da dokar keɓe wa mata kujeru a majalisa

    Ƙaramar majalisar dokokin Indiya ta zartar da wani ƙudurin doka da zai tabbatar da keɓe wa mata kashi ɗaya cikin uku na kujerun majalisar ƙasar da kuma a majalisun jihohi.

    A 1996 ne aka fara gabatar da ƙudurin, amma sai aka jingine shi tsawon gomman shekaru saboda adawar da ya sha fuskanta daga wasu jam'iyyu.

    Sai dai a ranar Laraba, majalisa ta zartar da ƙudurin dokar mai taken Lok Sabha inda kusan duk 'yan majalisar suka amince da ita bayan tafka zazzafar muhawara.

    Yanzu dai jazaman ne sai ƙudurin dokar ya samu amincewar Rajya Sabha, wato babbar majalisar dattijan Indiya, kuma shugaban ƙasa ya sanya mata hannu.

    Sai dai dokar za ta ɗauki lokaci kafin a fara aiwatar da ita, don kuwa hakan zai kasance ne bayan an kammala ƙidayar jama'a a ƙasar.

    Aikin, wanda ake gudanarwa duk shekara goma, an tsara yin sa ne tun cikin 2021 amma aka samu jinkiri sanadin annobar korona, yanzu kuma ana sa rai za a yi ƙidayar a shekara ta 2025.

  14. Kalli yadda ruwan rafi ke fitar da launuka masu ban sha'awa

  15. 'Mun bi matakan da suka dace kafin ɗaura aure da mai HIV a Katsina'

    Ana ci gaba da taƙaddama game da tuɓe rawanin Sarkin Kurayen Katsina kuma Hakimin Kuraye, Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu bisa tuhumar ɗaura wani aure tsakanin wasu ma'aurata, cikinsu har da mutumin da ke da cuta mai karya garkuwar jiki a gundumarsa.

    Gwamnati ta ce abin da hakimin ya yi, saɓa doka ne a jihar Katsina, amma wasu na zargin cewa gwamnatin ta sauke shi ne saboda tana da wani aminin gwamna da ake so ya maye gurbin hakimin.

    A ranar Litinin din da ta wuce ne, gwamnatin Katsina ta ce ta amince da tuɓe rawanin basaraken, saboda dokar jihar, da ta hana ɗaura aure ba tare da an san matsayin lafiyar masu niyyar auren ba.

    Sai dai a tattaunawarsu da Ibrahim Isa, Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu ya ce sun bi matakan da suka dace, kafin gudanar da ɗaurin auren:

  16. Indiya ta dakatar da bai wa 'yan Canada biza

    Indiya ta dakatar da ayyukan bayar da biza a Canada tare da yin kira da a rage yawan ma'aikatan diplomasiyar Canadan a Indiya.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tayi tsami tsakanin ƙasashen biyu.

    Hukumomin Indiya sun bayyana barazanar tsaro da ofishin jakadancin Indiya ke fuskanta a matsayin babban dalilin da ya sa suka dakatar da bayar da bizar.

    Dangantaka ta fara tsami tsakanin ƙashashen biyu ne a ranar Litinin lokacin da Firaiministan Canada , ya zargi jami'an India da hannu a kisan da aka yi wa wani mai fafutika mabiyin addinin Sikh ɗan ƙasar ta Canada da aka harba a watan Yunin da ya wuce.

    Zargin da Indiya ta ce bita-da-kullin siyasa ne kawai.

  17. Kotun ƙorafin zaɓe ta tabbatar da nasarar gwamnan Enugu

    Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya, ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Peter Mbah na jam'iyyar PDP a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.

    Tawagar alƙalan kotun uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Kudirat Murayo sun yi watsi da ƙorafe-ƙorafen jam'iyyar LP da dan takararta, Chijioke Edeoga.

    Kotun ta ce masu shigar da ƙarar sun kasa gamsar da kotu da hujjoji kan korafe-ƙorafen nasu.

    Mista Edeoga na zargin Mista Mbah da gabatar da takardar shaidar yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta jabu a lokacin da ya tsaya takara.

    Sai dai kotun ta ce takardar shaidar NYSC ba ta cikin ƙa'idar tsayawa takarar gwamna.

  18. An kori babban sakataren hukumar ƙwallon Sifaniya

  19. Ƴan sanda sun tono gawar mawaƙi Mohbad a Legas domin yin bincike

    Ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya sun kammala tono gawar wani fitaccen mawaƙi a ƙasar, Ilerioluwa Aloba da aka fi sani da Mohbad, wanda ya mutu a makon da ya gabata, domin gudanar da binciken musabbabin mutuwarsa.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

    "An kammala tono gawar, yanzu za a fara gwaji don gano musabbabin mutuwarsa", kamar yadda ya wallafa.

    Mawaƙin mai shekara 27, ya mutu ne ranar Talata 12 ga watan Satumba a wani asibiti a Legas, sai dai ba a bayyana abin da ya yi sanadin mutuwarsa ba.

    Tun bayan mutuwar tasa, magoya bayansa a biranen kudancin Najeriya suka riƙa yin kiraye-kirayen yi masa adalci, musamman a shafukan sada zumunta.

    Hukumomi a jihar Legas sun alƙawarta gudanar da bincike domin gano abin da ya yi sanadin mutuwarsa.

  20. Bazoum ya nemi taimakon kotun Ecowas

    Hamɓararren shugaban ƙasar Nijar Mohamed Bazoum ya shigar da ƙara gaba kotun Ecowas, yana neman kotun ta bayar da umarnin a sake shi daga ɗaurin talalar da sojoji ke yi masa tun bayan hamɓarar da shi.

    Lauyan Bazoum Seydou Diagne, ya ce an shigar da ƙarar ne ranar Litinin domin neman sakin Bazoum, tare da mayar da shi kan karagar mulkin ƙasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi masa cikin watan Yuli.

    “Muna buƙatar a mayar da Nijar kan tafarkin dimokuradiyya ta hanyar sakin Mohamed Bazoum tare da mayar da shi kan karagar mulki, domin ci gaba da mulki har zuwa ƙarshen wa'adinsa", kamar yadda Seydou Diagne, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Matarsa da ɗansa na daga cikin waɗanda ake yi wa ɗaurin talalar tare da Mohamed Bazoum tun bayan hamɓarar da gwamnatinsa.

    Ecowas ta yi barazanar ɗaukar matakin soji don mayar da Bazoum kan karagar mulki, idan duka matakan diflomasiyya suka gaza.