'Ba don Majalisar Ɗinkin Duniya ba, da mun banu da ta'addanci'

Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umaymah Sani Abdulmumin, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wanna shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Bidiyo ya nuna yadda ɗan sanda ya harbi wata mai juna biyu baƙar fata

    ,,

    Asalin hoton, Police handout

    'Yan sanda a jihar Ohio na Amurka sun saki wani bidiyo da ke nuna yadda wani jami'an ɗan sanda ya harbe wata mai juna biyu baƙar fata.

    Ta'Kiya Young, mai shekara 21 ta mutu ne ranar 24 ga watan Agusta a lokacin da aka harbe ta a cikin wata ƙaramar mota a wajen wani kantin sayar da kayayyaki da ke birnin Columbus.

    Bidiyon ya nuna yadda jami'an 'yan sandan ke yunƙurin tuhumar matar bisa zarginta da yin sata a kantin.

    A cikin bidiyon an ga wani jami'in ɗan sanda tseye a gaban motar tata yayin da matar ke yunƙurin tuƙa motar.

    Yayin da ɗayan ke tsaye a kusa da kofar motar, yana yi mata tsawar cewa ta fito daga cikin motar.

    An ga jami'an 'yan sanda biyu na tattaunawa da matar na kusan minti guda kafin a ji ƙarar harbin bindiga.

    Matar dai ta mutu sakamakon harbin bindigar.

  3. Kullum sai na yi magana da Bazoum - Shugaban Faransa

  4. Mahaukaciyar guguwa ta yi ɓarna a yankin Hong Kong

    Miliyoyin jama'a a Hong Kong da yankin kudancin China mai makwabtaka na can sun fake a cikin gidaje da sauran wurare da aka tanada na wucin-gadi, yayin da mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama ta ratsa ta tekun kudancin Chinar.

    Duk da cewa ta gefen kudancin Hong Kong din ta bi to amma, iska mai karfin gaske ta mamaye birnin inda ta kayar da bishiyoyi.

    An kwashe mutum dubu 800 daga lardin Guangdong na China, inda gwamnan ya yi kira ga jama'a da su dauki lamarin fuskantar guguwar mai tafe da ruwa tamkar yanayi na yaki.

    Hukumar kula da yanayi ta China na hasashen guguwar ta Saola ta kasance mafi karfi da za ta sauka a gabar tekun, tun shekarar 1949.''

  5. An fara binciken cin hanci ga kwamitin binciken badaƙalar sayar da guraben aiki

    Jami'an hukumar ICPC

    Asalin hoton, ICPC

    Hukumar da ke Yaƙi da Almundahanr Kuɗaɗe ta Najeriya ICPC ta fara bincike kan zarge-zargen cin hanci da ake yi wa kwamitin majalisar wakilan ƙasar mai bincike kan badaƙalar sayar da guraben aiki a ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.

    Mai magana da yawun hukumar, Azuka Ogugua ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a a Abuja.

    Ogugua ta ce ICPC ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga jaridar Premium Time da ake wallafawa a intanet da kuma shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilan ƙasar mai binciken badaƙalar sayar da guraben aiki, Hon. Yusuf Adamu Gadgi, inda suka buƙaci hukumar ta binciki zarge-zargen da ake yi wa kwamitin.

    Jaridar Premium Time ta wallafa wani labari da a ciki ta zargi wasu mambobin kwamitin da neman shugabannin wasu jami'o'i da na manyan makarantu, su zuba kuɗi a wani asusun banki da sunan cin hanci.

    Labarin ya yi iƙirarin cewa kwamitin na ɗaga ƙafa ga duk makarantar da ta biya kuɗaɗen da 'yan kwamitin suka nema.

    An kuma zargin mambobin kwamitin da tatsar kuɗi daga shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamnati, ciki har da manyan makarantu.

    A ranar Alhamis ne, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Yusuf Gadgi na cewa kwamitin ya rubuta wa hukumar ICPC wasiƙa inda ya nemi ta gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da ake yi wa mambobin kwamitin nasa.

    Shugaban kwamitin ya ce sun rubuta wa hukumar tare da buƙatar ta binciki asusun bankin da aka ce shugabannin makarantun na tura kuɗaɗen cin hancin.

  6. Liverpool ta san makomarta a gasar Europa

  7. Nikki Haley ta ce Majalisar Dattijan Amurka ta zama gidan kula da tsofaffi

    Nikki Haley

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yar takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Republican Nikki Haley ta sake yin kiran a riƙa gudanar da "gwajin tabbatar da lafiyar ƙwaƙwalwa" ga tsofaffin shugabannin Amurka, bayan Sanata Mitch McConnell ya sake ƙamewa a lokacin wani taron manema labarai.

    "Majalisar dattijai wani gidan raino ne mafi alfarma a ƙasar nan," Misis Haley ta faɗa wa tashar talbijin ta Fox News.

    Mitch McConnell ɗan shekara 81, ya zura wa ƙasa ido kawai lokacin da yake tsaye ƙiƙami tsawon daƙiƙa fiye da 30, sa'ar da aka tambaye shi ko zai sake tsayawa takara.

    Wani likita ya ba shi shaidar cewa a likitance yana da lafiyar da zai iya ci gaba da aiki.

    A watan Yuli ma ya fuskanci irin wannan matsala.

    Ɗan majalisar ya jagoranci 'yan jam'iyyar Republican a Majalisar Dattijan Amurka tun daga 2006, kuma ya shahara a matsayin ɗan siyasa mai hikimar da ba ya saurarawa ba, a ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da ɗa'a a tsakanin 'ya'yan jam'iyyarsa.

    Rukunin sanatocin Kentucky ba su fito bainar jama'a sun tuhumi ƙarfin iya jagorancinsa ba, ko da yake suna da zaɓin su kira taro don tattauna batun lokacin da Majalisar Dattijan za ta koma zama a makon gobe.

    Misis Haley, wadda tsohuwar jakadar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya kuma ta taɓa gwamna a jihar Carolina ta Kudu, ita ce 'yar jam'iyyar Republican mafi girma da ta yi magana game da damuwar da ake da ita a kan batun lafiyar Mitch McConnell.

    Ta faɗa wa tashar Fox News a ranar Juma'a: "Ina nufin Mitch McConnell ya yi gagaruman abubuwan bajinta kuma ya cancanci yabo.

    Amma ya kamata ka san lokacin da za ka tafi."

    Misis Haley 'yar shekara 51, ta mayar da hankali wajen yaƙin neman zaɓen shugabar ƙasa a kan muhawarar cewa Amurka na buƙatar sabbin jinin shugabanni.

    "Ina jin cewa muna buƙatar gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa ga duk mutumin da ya haura shekara 75, ba zan damu ba idan ma suka fara yin hakan ga 'yan sama da shekara 50," a cewarta.

  8. Amurka ta yi iƙirarin Ukraine na samun nasara a yaƙinta da Rasha

    Kakakin fadar White House a kan harkokin tsaro, ya ce Ukraine ta samu abin da ya kira gagarumar nasara a cikin sa'a 72 a hare-haren da ta kai wa dakarun Rasha a tsakiyar yankin Zaporizhzhia.

    A farkon makon nan, sojojin na Ukraine suka ce sun kama wani matsuguni a garin Robotyne, wanda hakan ya buɗe musu hanyar kai wa ga manyan birane na kudancin ƙasar, in ji Ministan wajen Ukraine.

    Gwamnatin birnin Kyiv na fama kan yadda za ta iya kutsawa don shiga yankunan da dakarun Rasha suka ja daga, masu tsananin tsaro a Zaporizhzhia, yayin da a ɗaya bangaren take ƙoƙarin ganin ta jure hare-haren da Rashar ke kai wa yankin gabashi.

    Sai dai a nata ɓangare, ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce ta samu nasara mai muhimmancin gaske a wajen birnin Kupiansk.

    Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da dukkanin iƙirarin nasarar da kowanne ɓangare ke yi.

  9. Jadawalin UEFA Conference League: Aston Villa za ta kara da Az Alkamaar

  10. Tottenham ta ƙulla yarjejeniya da Forest kan Johnson

  11. Za a yaɗa shari'ar Trump kai-tsaye a talbijin da YouTube

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Alƙalin da ke jagorantar shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban Amurka - Donald Trump a Georgia kan zargin murɗe sakamakon zaɓe - ya ce za a yaɗa shari'ar kai-tsaye a talbijin.

    Mai Shari'aScott McAfee ya kuma ce za a yaɗa yadda shari'ar ke gudana kai-tsaye a shafin kotun na YouTube

    Ba a dai saka ranar da za a saurari ƙarar ba, amma ana sa ran a shekara mai zuwa ne, lokacin da Trump ke kan ganiyar takarar shugabancin ƙasar.

    Mista Trump da wasu mutum 18 na fuskantar tuhumar haɗin baki wajen murɗe sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na 2020.

    Tsohon shugaban ƙasar - wanda ke fuskantar wasu shari'u guda uku - ya ƙi amsa laifuka 13 da ake tuhumarsa da su a kotun ta Georgia.

    Kotun - wadda ke gundumar Fulton - ta saba yaɗa shari'unta kai-tsaye a shafinta na YouTube.

    To sai dai wannan shi ne karon farko da za a yaɗa shari'ar Donald Trump kai-tseye, kuma ana sa ran za ta zama shari'ar da aka fi kallo a shafin intanet a shekarun baya-bayan nan.

    A makon da ya gabata ne Mista Trump ya kai kansa kurkukun kotun, inda aka ɗauki hotonsa.

  12. Gwamnatin Gombe ta yi wa ma'aikatan jihar ƙarin naira 10,000 a albashinsu

    Gwaman Gombe

    Asalin hoton, Twitter/Gombe State Government

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya

    Gwamnatin jihar Gombe ta amince da yi wa ma'aikatan jihar ƙarin naira 10,000 a albashinsu, a wani ɓangare na rage raɗadin cire tallafin man fetur.

    Yayin da yake jawani ga manema labarai a birnin Gombe, mataimakin gwamnan jihar Dakta Manasseh Daniel Jatau ya ce ƙarin albashin na daga cikin matakan da gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya ke ɓullowa da su domin rage wa 'yan jihar raɗaɗin da suke ciki sakamakon cire tallafin man fetur.

    Ya kara da cewa tun bayan cire tallafin man fetur gwamnatin jihar ke ɗaukar matakai domin tallafa wa 'yan jihar ta hanyar raba kayan tallafi ga mutum 30,000.

    Mataimakin gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar da na burin raba kayan tallafin ga mutum aƙalla 420,000 a faɗin jihar.

    Dakta Jatau ya ce karin naira 10,000 da aka kara wa ma'aikatan ya shafi duka ma'aikatan jiha da na ƙananan hukumomi a jihar, kuma karin ya fara ne daga watan Agusta.

    Da aka tambaye shi zuwa wane lokaci za a ɗauka ana biyan ƙarin albashin, sai ya ce kawo yanzu babu iyaka.

    Tun bayan cire tallafin man fetur ɗin ne gwamnatocin jihohin ƙasar, suka riƙa ɓullo da matakai daban-daban da nufin rage wa ma'aikatansu wahalhalun da suke fuskanta.

    Inda wasu jihohin suka rage kwanakin aiki daga biyar zuwa uku ga ma'aikatan nasu.

    Kungiyoyin ƙwadagon ƙasar na ta kiraye-kiyaren yi wa ma'aikata ƙarin albashi sakamakon wahalhalun da ma'aikata ke fuskanta sakamkon cire tallafin man fetur din.

  13. Ba don tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya ba, da mun banu da ta'addanci - Tinubu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu/Twitter

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

    Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara ɓullo da ƙwararan matakan tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta'addanci, saboda mummunar iillarsa ga zaman lafiyar duniya da yadda yake tarwatsa mutane da ƙara haifar da fatara.

    Ya yi wannan kira ne lokacin da yake jawabi yayin ganawa da ƙaramin sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya kan yaƙi da ta'addanci, Mista Vladimir Voronkov, a fadar gwamnati.

    Shugaba Tinubu ya nunar da cewa ta'addanci ya yi ta mayar da hannun agogo baya ga harkokin ci gaban ƙasa da janyo ƙarin rashin kwanciyar hankali a tsakanin iyalai da al'ummomi, amma ayyukan haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya wajen tunkararsa, sun kasance a tsittsinke kuma ana samun katsewar irin wannan tallafi ga ƙasashe masu tasowa.

    "Jazaman ne daftarin Majalisar Ɗinkin Duniya, ya zama tushen duk wani ƙawance a nan gaba, maimakon bayar da tallafi", a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma'a.

    “Mun yaba da duk abin da kuke yi. Mun san cewa duk da buƙatu da ƙalubalen da ke gabanku, za ku iya ƙarawa a kan ƙoƙarinku. Kun yi rawar gani a ayyukan haɗin gwiwar da kuke yi, amma ta fuskar tallafi a ƙasa, sai kun daɗa ƙoƙari. Sai kun ƙara jajircewa, saboda ta'addanci babban hatsari ne ga dimokraɗiyya, kuma hatsari ne ga ci gaban ƙasa.

    “Ba za a samu bunƙasar tattalin arziƙi da ƙaruwar arziƙi ba, har sai mun kakkaɓe ta'addanci.

    “Jazaman ne mu riƙa tunani a kan buƙatun jama'armu. A cikin 'yar dukiyar da muke da ita yanzu, idan za mu riƙa kashe ɗumbin kuɗi, babu tallafi a kai a kai daga hukumomi kamar Majalisar Ɗinkin Duniya, to ba shakka muna cikin matsala,” shugaba Tinubu ya ce.

    Da yake yaba wa gudunmawar Najeriya ga ƙoƙarin yaƙi da ta'addanci a duniya, ƙaramin sakataren na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce tuni Najeriya ta fitar da tsari a kan riga-kafi da dankwafewa da sulhuntawa, inda ya nanata yabo a kan ƙoƙarin da ƙasar ta yi zuwa yanzu don murƙushe ta'addanci.

    Vladmir Voronkov ya kuma faɗa wa shugaban na Najeriya cewa Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin gudanar da wani Taron Ƙoli kan Yaƙi da Ta'addanci a Abuja cikin watan Afrilun 2024.

  14. Uber ta ƙaddamar da baburan haya masu amfani da lantarki a Kenya

    j

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin Uber da ke gudanar da hayar abubuwan hawa a shafin intanet, ya ƙaddamar da baburan haya masu amfani da lantarki a birnin Nairobi na ƙasar Kenya, a wani abu da kamfanin ya ce shi ne na farko a Afirka.

    Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin ƙasar ke shirin fara amfani da motocin lantarki a ƙasar, a wani ɓangare na rage gurɓata muhalli.

    kamfanin Uber ya ce da farko zai gabatar da baburan 3,000 waɗanda za su iya ɗaukar diraba da fasinja ɗaya.

    Bankin Duniya ya yi ƙiyasin cewa sana'ar Achaɓa ko fannin baburan haya a Kenya na samar da ayyukan yi ga mutum fiye da miliyan 1.5, tare da tallafa wa tattalin arzikin ƙasar da fiye da dala biliyan 1.4 a kowacce shekara.

  15. Brighton ta dauki aron Ansu Fati daga Barcelona

  16. Jiragen yaƙin Najeriya sun yi luguden wuta a wasu sansanonin 'yan ta-da-ƙayar-baya

    d

    Asalin hoton, Nigerian Airforce

    Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kai wani farmaki Juma'a a sansanonin 'yan Boko Haram a Borno da kuma wasu haramtattun wuraren tace ɗanye mai a jahar Ribas .

    Mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar, Edward Gabkwet ne ya bayana haka cikin wata sanarwa da ya fitar Jumu'a a Abuja.

    Gabkwet ya ce farmakin da dakarun sojin ke ci gaba da kai wa a maɓoyar 'yan ta'addan da masu tayar da ƙayar baya da ɓarayin mai, zai taimaka wajen hana su sakat ta yadda ba za su samu damar haddasa matsala ga tattalin arziki da al'ummar da ba su ji ba ba su gani ba.

    Ya ce rundunar Operation Haɗin Kai ta kai farmaki a kusa da ƙauyen Arikna Wojeo bayan samun tabbacin inda maɓoyar ɓata garin ta ke wuraren da suke ci gaba da amfani da su a kudancin Tumbun ku da Tafkin Chadi.

    "An bayar da umurnin kai harin, wanda an samu nasara wajen kai shi sakamakon hayaƙi da wutar da aka lura suna tashi da kuma rahotannin da aka samu daga jama'ar yankunan.

    Ya ƙara da cewa sahihan bayanan da suka samu sun taimaka wajen fallasa wuraren da 'yan ta'adda ke amfani da su wajen ɓoye makamai da sauran kayan da suke amfani da su.

    "A ranar 13 ga watan Yuni an taɓa kai hari wurin, inda aka samu gagarumar nasara kakkaɓe da dama daga cikinsu, alamu sun nuna cewa 'yan ta'addan sun sha luguden wuta a wasu yankuna shi ne su ke sake tattaruwa a wannan wuri", in ji kakakin.

    Kakakin rundunar sojin ya kuma ce an ƙara kai wasu hare-hare a yanki Bille da ke ƙaramar hukumar Degema a jahar Ribas, wurin da kakakin ya ce ya yi ƙaurin suna wajen gudanar da haramtattun ayyukan tace mai.

    Ya ce an kai farmakin ne da zummar hana tare da karya lagon ɓarayin ta hanyar kawo cikas ga ayyukan da su ke yi, waɗanda ya ce na ci gaba da kawo illa ga muhalli da ma tattalin arzikin ƙasa.

  17. Amurka za ta hana biza ga waɗanda suka kawo cikas ga zaɓen Saliyo

    s

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Amurka ta fitar da wata sanarwar da ke cewa za ta hana takardun biza ga waɗanda suka kawo cikas ga zaɓen da ya gudana a watan Yuni a ƙasar Saliyo da ke yankin Afirka ta Yamma.

    "A ƙarƙashin wannan sabon tsari, Amurka ta za ta bi sawun waɗanda ake zargi da yin ƙafar ungulu ga tsarin dimokuraɗiyya ta hanyar yin aringizon ƙuru'u", in ji Sakataren harkokin waje na Amurka Anthony Blinken.

    Bayanin sakataren ya ƙara da cewa, "Amurka za ta hana bizar ga duk wani mutum da aka samu da razana masu kaɗa ƙuri'a ko kuma aka same su da laifin take haƙƙin ɗan'adam a ƙasar.

    Ya ƙara da cewa matakin haramcin zai kuma shafi dangi da makusantan mutanen.

    Sai dai Amurka ba ta bayyana sunayen waɗanda wannan matakin zai shafa ba.

    Shugaban ƙasar mai ci, Julius Maada Bio, ya lashe zaɓen da aka gudanar da kashi 56 cikin ɗari. Yayin da babban abokin adawar sa Samura Kamura ke bi masa da kashi 41 cikin dari na yawan ƙuri'un da aka kaɗa, sakamakon da ya kira da "fashi da rana tsaka". Ya kuma yi zargin an hana masu sa ido na jam'iyyarsa damar lura da yadda aka gudanar da lissafin ƙuri'u.

    Masu sa ido daga ƙasashen waje game da yadda zaɓen ya gudana, sun bayyana cikas da aka samu ciki har da maguɗi.

    Yaƙin neman zaɓen dai ya gamu da ƙalubalai sakamakon tashe-tsahen hankali daga magoya bayan jam'iyyun biyu.

  18. Liverpool ta yi watsi da tayin fam miliyan 150 kan Salah

  19. Shafin X zai fara tattara bayanan jama'a da suka haɗar da na aiki

    x

    Asalin hoton, ELONMUSK

    Bayanan masu amfani da X da kamfanin ke shirin tattarawa sun haɗa da na hotunan fuskokinsu domin sabunta tsare-tsarensa na kariya.

    Duk mutanen da ke amfani da shafin na X na iya zaɓar hoton da suka ɗauki kansu da kuma katin shaida domin a tantance.

    Tsarin ya kuma bayyana cewa X na iya tattara bayanai da suka shafi sirrin aiki da kuma karatun mutum.

    Wannan na iya zama hanyar "tura muku gurabun aikin da aka tallata, da rabawa masu ɗaukar aiki idan ku ka nemi ayyukan".

    Akwai ma labarai da ke yawo da ke cewa kamfanin na X na shirin ɗaukar aiki ne.

    Wasu rahotanni ma na cewa, a watan Mayun kamfanin na X ya mallaki wani kamfani mai ɗaukar ma'aikata da ake kira Lakie.

    Wannan dai shi ne na karon farko da kamafanin ya ɗauki wannan matakin tun bayan da Elon Musk ya sayi kamfanin Twitter a bara a kan dala biliyan 34.7.

    Wannan sabon tsari zai soma aiki a ranar 29 ga watan Satumban 2023.

    Kamfanin na X ya kuma shaidawa BBC cewa 'Zai ba su zaɓin saka Katin Shaida (ID) nasu na aikin gwamnati tare da hoton da suka ɗauka da kansu domin tantancewa".

  20. Chelsea ta ɗauko Palmer daga Man City