Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ba mu da nufin komai sai alheri ga 'yan Najeriya - Remi Tinubu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Bankwana

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi kai-tsaye.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu - za mu dawo muku da sabbin labarai.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnatin Zamfara ta ce za a riƙa kai yara makaranta kyauta

    Gwamnatin jihar Zamfara ta ce daga yanzu kyauta za a riƙa kai ƴara makarantar kyauta.

    Gwamna Dauda Lawal Dare, shi ya bayyana haka a wani taron kwamitin zartaswa na jihar da ya jagoranta a gidan gwamnati.

    Gwamnan ya ce ɗaliban makaranta, musamman ma na firamare, za su mori zuwa makaranta kyauta karkashin tsarin rage wa mutane raɗaɗi da suke ciki.

    Haka nan ma, gwamnatin jihar ta ce za a raba wa iyalai marasa galihu 2,000 kayan abinci, wanda yana karkashin tsarin rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur.

    Gwamnatin jihar ta Zamfara ta kuma ce za ta samar da motocin bas guda 50 domin rage wa ɗalibai wahalhalu da suke fuskanta a ɓangaren sufuri a faɗin jihar.

  3. Badaru ya nemi jin abin da sojoji ke buƙata don kawo ƙarshen rashin tsaro a Najeriya

    Sabon ministan tsaron Najeriya, Muhammmad Badaru Abubakar da takwaransa, Dakta Bello Matawalle sun fara aiki a hedkwatar ma'aikatar tsaro ta tarayya a ranar Talata.

    A jawabinsa bayan karɓar ragamar aiki daga Dakta Ibrahim Kana, Babban Sakataren ma'aikatar, Badaru ya ce zai sake duba rahotannin da aka gabatar a baya dangane da halin da tsaro yake ciki a ƙasar.

    Ya ce zai yi haka ne da zimmar ganin an daƙile matsalar rashin tsaro da kawo zaman lafiya a faɗin ƙasar.

    Ministan ya ce ba za su ci amanar da Shugaba Bola Tinubu ya damƙa musu ba, don haka ya buƙaci hafsoshin tsaron ƙasar su gabayar da masa da bayanin abubuwan da suke buƙata da za su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya.

    "Za mu miƙa wa Shugaban ƙasa jerin abubuwan da ake buƙata, kuma ina da yaƙinin cewa zai riƙa sa ido.

    "A shirye shugaban ƙasa yake domin ba mu dukkan goyon baya a yunƙurinsa na ganin mun samu nasara, saboda mutum ne mai hazaƙa wanda ba ya son a samu gazawa.

    "Ƙasarmu, mun san cewa muddin babu tsaro, ba za a samu masu zuba jari ba, kuma matuƙar babu zuba jari, tattalin arziki ba zai ci gaba ba."

    Badaru ya tabbatar da cewa jagorancinsu zai kawo gagarumin canji a ɓangaren tsaron Najeriya, inda ya ce ba zai yi wasa da muƙamin nasa ba.

    Shi ma a jawabinsa, ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce dakarun Najeriya sun nuna ƙwazo da jajircewa ta musamman a tsawon lokaci.

    “Ta’addanci da ayyukan ‘yan fashin daji da ƴan ta-da-ƙayar-baya da rikice-rikice na ƙabilanci na haifar da babban ƙalubale ga tsaron Najeriya.

    “Aikin da ke gabanmu, ba abu ne mai sauƙi ba. Duk da haka ina da yaƙinin cewa idan muka samu goyon bayan abokan aiki da sadaukarwar sojojinmu da kuma jajircewar duk 'yan Najeriya, za mu shawo kan duk wani ƙalubale a ɓangaren tsaro," in ji Matawalle.

  4. Dakarun Isra'ila sun harbe wani ɗan fafutuka a lokacin samame

    Dakarun Isra'ila sun harbe wani ɗan Pakistan mai shekara 17 a wani jerin samame da suka kai cikin dare a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Mazauna yankin sun ce an kashe Abu Kharj ne a kauyen Zababdeh, kusa da birnin Jenin bayan da sojojin suka shiga tare da fara sa-in-sa da mazauna birnin.

    Sojojin ba su ce uffan ba kan mutuwar mai fafutukar, amma sun ce Falasɗinawa sun harba abubuwan fashewa.

    Shaidu sun ce dakarun sun harbe matashin ne kusa da wani gida da suka yi wa ƙawanya.

    Kungiyar mayaka ta Falasɗinawa mai suna Islamic Jihad ta yi iƙirarin cewa Abu Kharj ya kasance mayakinta a ɓangaren kai ɗaukin gaggawa.

    Samamen da sojojin suka kai a wurare akalla 20 a faɗin Yamma da Kogin Jordan na zuwa ne bayan kashe Isra'ilawa guda uku a wasu mabambantan hare-hare da ake zargin ƴan bindiga a Pakistan da kai wa a wannan mako.

    Wata kungiyar fursunoni ta Falasɗinawa ta ce an tsare kusan mutum 50 a samamen na cikin dare, inda kuma suka zargi Isra'ila da lalata gidajen mutane.

    Haka nan ma, an jikkata wani Bafalasɗine a wani samame a daren litinin, bayan harbinsa a kai da sojojin Isra'ila suka yi kusa da kauyen Nablus.

    Hotunan bidiyo sun nuna mutumin yana gudu don zuwa wajen wani da aka jikkata kafin harbin ya same shi.

  5. Ba mu tattauna da NNPP da PDP don kafa jam’iyyar haɗaka ba - LP, Daga Khalifa Shehu Dokaji

    Jami’iyyar Labour a Najeriya ta musanta cewa tana tattaunawa da takwarorinta na NNPP da PDP don kafa jam’iyyar haɗaka domin tunkarar jam’iyya mai mulki ta APC a zaɓe mai zuwa.

    Jam’iyyar faɗi haka ne bayan da wasu daga cikin jaridun Najeriya suka ruwaito cewa ana wata ganawa tsakanin ‘yan takarar shugabancin ƙasar na PDP Atiku Abubakar, da na NNPP Rabi’u Kwankwaso, da kuma Peter Obi don haɗewa waje guda.

    Mai magana da yawun LP na ƙasa Dakta Tanko Yunusa, ya ce abun da suka sani shi ne, akwai tattaunawa ta fahimta da ake yi tsakani ɗan takararsu da na NNPP da kuma na PDP, wanda kuma ba shi da alaƙa da batun haɗewa ko wani abu makamancinsa ba.

    Haka kuma Dr. Tanko Yunusa ya ce ko da za a haɗe ma to sai dai a ba su jan ragamar ta fi da komai, kuma a sa su gaba.

    Ku latsa ƙasa don sauraron tattaunawarsa da Khalifa Shehu Dokaji

  6. Yadda Wike ya tayar da ƙura bayan naɗa shi ministan Abuja

  7. Ba mu da nufin komai sai alheri ga 'yan Najeriya - Remi Tinubu

    Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu ba ta nufin komai ga ƙasar sai alheri, duk da wahalhalun da ƴan ƙasar ke ciki saboda cire tallafin man fetur.

    Remi ta buƙaci ƴan Najeriya su dubi irin nasarori da za a samu nan gaba, ba kawai ga ƙalubalen da ake fama da shi a yanzu ba, inda ta ce akwai nasara mai kyau a gaba.

    Ta bayyana ne lokacin da ta karɓi baƙuncin matan hafsoshin tsaron Najeriya da ta babban sufeton ƴan sanda waɗanda matar babban hafsan tsaro Mrs Oghogho Musa ta jagoranta.

    Mai ɗakin shugaban Najeriyar ta ce gwamnatin mijinta na yin duk abin da ya kamata don tabbatar da ganin ta rage wa ƴan ƙasar raɗaɗin da suke ciki bayan janye tallafin fetur. Ta ƙara da cewa ƴan Najeriya za su fara cin moriyar manufofin gwamnatin matuƙar abubuwa suka fara daidaita.

    Ta ce kundin ayyukan gwamnatinsu na Renewed Hope, shi ma yana mara wa gwamnati, don haka ta roƙi goyon baya daga wajen matan hafsoshin tsaron.

    "Muna ƙoƙarin ganin mun gina abubuwan da yaranmu da ma waɗanda ba a haifa ba, za su taso su gani sannan su yi alfahari da shi.

    Za mu tabbatar da ganin tattalin arzikin Najeriya, ya ci gaba," in ji Remi.

  8. An kammala ceto yaran da suka maƙale a cikin mota mai reto a waya

    Ministan cikin gida na Pakistan ya ce an ceto rukunin yara guda uku na ƙarshe daga cikin motar waya wato cable car, wadda ta maƙale a tsakiyar hanyarsu ta tsallaka kwarin da ke tsakanin manyan tsaunuka lokacin da suke tafiya makaranta.

    Abin da ke nufin an kawo ƙarshen aikin ceton yaran wanda ya shafe tsawon sa'o'i.

    Tun farko, an kuɓutar da mutum huɗu daga cikin motar wadda ta ɗauko jimillar mutum takwas ciki har da ƙananan yara shida, amma sai ta maƙale a tsakiyar wayar da take tafiya ta jikinta a saman wani kwari mai zurfi cikin yankin Battagram na ƙasar Pakistan.

    Motar wayar ta maƙale ne a wani wuri mai nisan ƙafa 900 a saman wani kogi da ke tsakanin tsaunuka masu nisan tafiyar mil ɗaya, lamarin da ya zama wani abu mai wahala da hatsari ga ma'aikatan ceto.

  9. Gobara ta kashe mutum 18 a Girka

    An gano gawawwaki 18 a wani kasurgumin daji bayan ɓarkewar wuta a arewacin Girka a cikin kwanaki huɗu da suka gabata, a cewar hukumar kashe gobara ta ƙasar.

    Rahotanni da aka samu da farko ta nuna cewa waɗanda suka mutu za su iya kasancewa ƴan ci-rani.

    Zuwa yanzu wata tawagar bincike ta nufi dajin Dadia don gano musabbabin gobarar.

    Wutar ta ƙona yawancin wurare a lardin Evros da ke arewacin ƙasar ta Girka, wanda yake kusa da iyaka da Turkiyya.

    Lamarin ya kai ga kwashe mutane daga wani asibiti da ke birnin Alexandroupolis.

    Cikin waɗanda aka kwashe daga asibitin sun haɗa da jarirai sabbin haihuwa da kuma marasa lafiya da ke buƙatar agajin gaggawa, inda aka ta fi da zu cikin kwale-kwale zuwa tudun tsira.

    Tun da farko an bayyana gano gawar wani da ake zargin ɗan ci-rani a wani kauye kusa da teku, inda aka kuma aika sakonnin gaggawa ga mutane na ganin sun bar wurare masu haɗari.

  10. Ƙwararru sun nemi ƙarfafa dokar ba da gudunmawar sashen jiki a Najeriya

    Ƙungiyar ƙwararrun likitocin dashe ta Najeriya (TAN) ta yi kira da a samar da dokar da za ta fayyace tsarin ba da gudunmawar sassan jikin ɗan'adam a ƙasar.

    Ƙungiyar ta faɗa a ranar Talata cewa matakin zai taimaka wajen inganta harkokin ba da gudunmawar sashen jikin ɗan'adam da bunƙasa ayyukan dashen sashen jiki da rage mace-mace da taƙaita fita ƙasashen waje don neman lafiya ga 'yan Najeriya.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ambato ƙungiyar ta yi kira a samar da dokar ne a yayin babban taron masana kimiyyar na shekara bi-biyu mai taken "Bunƙasa Aikin Dashen Sashen Jiki a Najeriya: Halin da ake Ciki Zuwa Yanzu".

    A wata maƙala da ya gabatar don nuna muhimmancin dashen sashen jikin ɗan'adam, Farfesa Adewale Akinsola, wani babban likitan ƙoda, ya ankarar da cewa marasa lafiya da yawa suna mutuwa a lokacin da suke zaman jiran gudunmawar sashen jiki da kuma aikin dashe.

    "Muna buƙatar sake nazarin dokoki da tsare-tsarenmu na dashen sashen jiki, muna buƙatar tuntuɓar lauyoyi da ƙungiyoyin fararen hula da kuma sake bitar dokoki don sanin abin da za mu gabatar wa gwamnati.

    “Muna buƙatar tsaurara sharaɗin `samun yarda’ a lokacin da mutum yake raye ko daga mutumin da ke kan gargarar mutuwa.

    “A lokacin da mutum yake raye, yana iya amincewa zai ba da gudunmawar ƙodarsa ko tata idan rasuwa ta zo, amma dangi ne a ƙarshe suke da alhaki, kuma suna iya ƙin amincewa,’’kamar yadda ya nunar.

    Farfesa Adewale Akinsola ya kuma buƙaci gwamnati ta wayar da kan mutane game da muhimmancin ba da gudunmawar sashen jikin mamaci, kuma a ɓullo da tsarin inshorar lafiya don yin magani ga wasu masu cutukan ajali a farashi mai rangwame.

    Shi ma da yake gabatar da tasa muƙala, shugaban ƙungiyar ƙwararrun likitocin dashen sashen jikin ɗan'adam ta Najeriya, Farfesa Fatiu Arogundade ya zayyana batun kuɗi da hanyar samo sashen jiki don yin dashe da raunanan kayan aiki a matsayin wasu daga cikin ƙalubalan da ke kawo nakasu ga aikin dashen sashen jiki a Najeriya.

    Ya kuma ce kafa wata doka da za ta inganta harkar ba da gudunmawar sashen jikin mamaci, za ta taimaka wajen rage mutanen da ke zaman jiran samun dashen sashen jiki da kuɓutar da rayuka da kuma inganta matsayin lafiyar al'umma.

    “Mun bi diddigi kuma mun tattauna game da ɗaukacin harkar dashen sashen jiki sannan mun san abubuwa sun ɗan inganta kaɗan.

  11. An ceto yara biyar da suka makale cikin wata mota mai tafiya ta waya

    Sojojin Pakistan sun ce an samu nasarar ceto yara biyar waanda suka makale cikin wata mota mai tafiya ta waya.

    Sun ce zuwa yanzu sauran ƙarin mutum guda uku da ke cikin motar, da suka haɗa da yaro ɗaya da kuma matasa biyu.

    An fara ceto yaro na farko ne ta hanyar amfani da jirgi mai suakar ungulu, yayin mazauna yankin kuma suka ceto yaro na biyun ta hanyar amfani da igiya.

    Hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna cewa.

  12. Abdulsalami ya miƙa wa Tinubu rahoton ziyarar da suka kai Nijar

    Shugaban tawagar da kungiyar ECOWAS ta tura zuwa Nijar domin tattaunawa da shugabannin sojin ƙasar Abdulsalami Abubakar, ya ce yana ganin za a samu mafita daga wannan takaddarmar ba tare da amfanin da karfin soja ba.

    Janar Abdulsalami mai ritaya ya faɗi haka ne bayan da ya miƙa wa Shugaban kungiyar Bola Tinubu rahoton ziyarar da suka kai Nijar a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

    Ya ce ziyarar da suka kai Nijar ta yi alfanu sosai kuma hakan ya buɗe kofar tattaunawa da za ta sanya a warware rikicin.

    A yayin ziyarar dai tawagar ta gana da shugaban gwamnatin sojin Abdurrahman Tchiani da kuma hamrarren shugaban kasar Mohammed Bazoum:

    "Mun fara tattaunawa da sojojin, sun kuma faɗi maganganu da dama. Rahoton abin da ya wakana ne na kawowa shugaban ƙasa," in ji Abdussalam.

    Ya ce za su yi duk abin da ya kamata don ganin an bi hanyar diflomasiyya wajen warware rikicin ba tare amfani da karfi ba.

    "Ba bu wanda yake son shiga yaƙi, saboda ba shi da alfanu. Amma, shugabanninmu sun faɗa cewa muddin hanyar diflomasiyya ta ki aiki, to fa akwai alamar amfani da karfi".

    Cikin waɗanda suka halarci ziyarar miƙa wa shugaba Tinubu rahoton, akwai shugaban hukumar Ecowas, Dakta Omar Touray, da shi shugaban tawagar da Ecowas ta tura Nijar, Janar Abdulsalami Abubakar da kuma mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

    • Bazoum ya shaida mana matsalolin da yake ciki – Tawagar Ecowas
    • Abin da malaman Najeriya suka tattauna da sojojin juyin mulkin Nijar
  13. An tuhumi Diezani Alison-Madueke kan zargin cin hanci a kotun Birtaniya

  14. Wace ƙungiya ce Brics kuma mece ce manufarta?

  15. Mutane da dama sun makale cikin wata mota mai tafiya ta waya

    Mutane da dama da suka haɗa da ƙananan yara da ɗaliban makaranta sun makale a cikin wata mota ta musamman mai tafiya bisa wayar wuta a lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke arewa maso yammacin Pakistan.

    Tun da safiyar yau ne motar ta makale a sama yayin da ƙasan ya kasance teku.

    An yi ta amfani da jirage masu tashin angulu wajen ganin an ceto su, sai dai lamarin ya citura.

    Sojojin Pakistan dai na ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da wasu yara bakwai ɗalibai da ke hanyar zuwa makaranta da wani malaminsu da suka makale a cikin motar a sama.

    Aikin ceton zai ɗauki lokaci saboda iska mai ƙarfi da ake yi a yanki wanda yake kawo cikas.

    Rahotanni na cewa masu aikin na ƙoƙarin amfani da ragar ceto.

    Wani jami’in ƴan sanda a yankin ya ce wani bakanike ne ya kirkiro da motar mai tafiya bisa wayar wuta.

  16. An dawo da 'yan Najeriya baƙin haure daga Libya

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, an mayar da wasu 'yan Najeriya 161 daga kasar Libya zuwa gida, a wani shirin sa-kai da Majalisar Dinkin Duniya ke tallafawa.

    Sun isa ne a wani jirgi daga Tripoli zuwa babban filin jirgin saman Legas ranar Litinin.

    Daga cikin wadanda aka mayar da su ɗin akwai mata 75 da ƙananan yara shida wadanda aka tsare a wuraren tsare mutane a ƙasar Libya.

    Ministan cikin gidan ƙasar ya bayyana cewa, an dakatar da mutum 102 daga cikin waɗanda aka mayar da su gida a kan iyakar Libya da Tunisia.

    Libya dai ta kasance wata babbar hanya da bakin haure 'yan Afirka ke bi a ƙoƙarinsu na tsallakawa Turai ta tekun Bahar Aswad ba bisa ƙa'ida ba.

    Wani jami'i a ofishin jakadancin Najeriya a Libya, ya tabbatar wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa baƙin hauren sun zaɓi koma wa gida ne da son ransu, ba tare da an tilasta musu ba.

    Ya kuma bayyana cewa waɗanda suka koma ɗin sun gamsu su koma Najeriya, domin “babu wani wurin zama kamar gida.

  17. Tarayyar Afirka ta dakatar da Nijar bayan juyin mulki

    Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da Nijar daga dukkan ayyukanta bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023.

    Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU ya yi kira ga daukacin kasashe mambobin ƙungiyar da sauran kasashen duniya da su ƙaurace wa duk wani matakin da zai halasta mulkin soja a Nijar.

    Ta sake nanata kira ga jagororin juyin mulkin da su saki zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.

    Tuni dai kungiyar kasashen yammacin Afirka ta Ecowas ta yi barazanar daukar matakin soji domin mayar da shi kan karagar mulki.

    Gwamnatin Nijar ta ce ba za a iya mayar da ƙasar ta farkin demokuraɗiyyya ba har na tsawon shekaru uku, amma kungiyar Ecowas ta yi watsi da hakan da cewa ba za a amince ba.

  18. Trump ya ce za a kama shi ranar Alhamis

    Toshon shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai je Georgia a ranar Alhamis domin gabatar da kansa a kan tuhume-tuhumen da ake masa na neman juya sakamako da kuma katsalanda a cikin harkokin zaben shugaban kasar da ya gabata.

    Ana kyautata tsammanin idan ya je za a dauki hoton yatsunsa da shi kansa.

    Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, tsohon shugaban na Amurka ya bayyana tuhumar da ake masa a matsayin bi ta da kullin siyasa.

    Tun da farko alkalin da ya bayar da belin Mr Trump ya sanya masa ka'idoji a kan amfani da kafafen sada zumunta.

    Trump dai ya musanta dukan zarge-zarge 13 da ake yi masa, ciki har da ƙin biyan haraji da bayar da bayanan ƙarya.

  19. Mutanen Nijar da na Arewacin Najeriya al'umma ɗaya ce - El-Rufa'i

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shawarci Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta dakatar da shirin amfani da ƙarfin soji a Jamhuriyar Nijar.

    A wani saƙo da El-Rufa'i ya wallafa a shafinsa na X, wato Tuwita a yau Talata, ya bayyana mazauna Arewacin Najeriya da Nijar a matsayin ƴan'uwan ​​juna.

    Ya ce "Tabbas mutanen Nijar abu ɗaya ne kuma al'umma ɗaya ce da na Arewacin Najeriya. Ya kamata mu kauce wa wannan yaƙin basasa tsakanin ƴan'uwa."

    Tsohon gwamnan ya yi wannan gargadin ne biyo bayan sanarwar da shugabannin tsaro na kungiyar ECOWAS ta yi cewa sun shirya yin amfani da karfin soji a Nijar domin dawo da habararren shugaban kasar, Muhamed Bazoum kan mulki.

    A taron da suka yi na ƙarshe a ƙasar Ghana, Manyan hafoshin dakarun Ecowas sun ce sun tsayar da ranar da za su tura dakaru zuwa Nijar domin tunkarar gwamnatin mulkin Janar Abdoulrahamane Tchiani domin dawo da mulkin demokuradiyya.

    • Ecowas ta ce hafsoshin sojinta sun sa ranar shiga Nijar
    • Abin da ake nufi da matakin amfani da ƙarfin sojan Ecowas
  20. Afirka ta Kudu na karɓar baƙuncin taron Brics

    Wakilan kungiyar kasashen Brics - da suka hada da China da Rasha da Indiya na haduwa domin gudanar da taro a Afirka ta Kudu.

    Ƙungiyar, wadda a halin yanzu ta kunshi ƙasashe biyar, tana tunanin shigar da karin kasashe kamar Iran da Argentina.

    Mahalarta taron suna kallon ƙungiyar ta Brics a matsayin ma'auni ga abin da suke gani a matsayin tasirin kasashen yamma a kan cibiyoyin duniya.

    Duk da yake a tarihi ana kallon shi a zaman dandalin tattaunawa kawai, mahimmancin ƙungiyar Brics yana ci gaba da haɓaka.

    Sanadiyyar karuwar rashin gamsuwa da mamayar yammacin duniya, sama da kasashe 20 sun nuna sha'awar shiga wannan kawance.

    Jami'ai a Afirka ta Kudu sun ji dadi sosai sakamakon matakin da aka dauka kan shugaban Rasha, Vladimir Putin, bayan sammacin kotun duniya na kama shi bisa zargin aikata laifukan yaki a Ukraine wanda hakan ya sa ya na kaurace wa halartar taron.

    Ana sa ran taron zai tattauna kan tsara sabuwar turba ta tafiyar da lamurra a doron duniya da kuma sake fasalin Majalisar Dinkin Duniya.

    Wannan lamari na samun goyon baya, musamman tsakanin kasashen Afirka.