Majalisa ba ta tabbatar da El-Rufai a matsayin minista ba

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Rabiatu Kabir Runka, Ahmad Tijjani Bawage and Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.

    Badamasi Mukhtar ne ke cewa mu haɗu da ku gobe da safe a wani sabon shafin.

  2. Ƴan kenya sun nemi Amurka ta biya su diyya kan harin bam ɗin 1998

    kenya bomb

    Asalin hoton, AFP

    Ƴan Kenya, wadanda harin da aka kai ofishin jakadancin Amurka a 1998, ya rutsa da su a Nairobi, sun sake kira ga Amurka ta biya su diyya.

    Ɗaruruwan mutane ne da suka haɗa da jami’an Amurka suka taru a wani dandali a babban birnin ƙasar ta Kenya, Nairobi, domin taron cika shekara 25 da kai harin.

    A lokacin, harin na bam ya hallaka mutum sama da 200, da raunata wasu da suka wuce 5000.

    Jim kaɗan bayan harin na Kenya, wani bam ɗin kuma ya tashi a ofishin jakadancin Amurkar a Dar es Salaam, a maƙwabciya Tanzania.

    Al-Qaeda ce ta ɗauki alhakin dukkanin hare-haren biyu shekara 25 da ta wuce.

  3. An kashe mutane da dama a harin da Rasha ta kai Gabashin Ukraine

    UKraine

    Asalin hoton, Reuters

    Wani harin da Rasha ta kai garin Pokkrovsk da ke Gabashin Ukarine ya kashe mutane aƙalla biyar.

    Ministan harkokin cikin gida, Ihor Klymenko ya ce harin ya kashe fararen hula huɗu da wani jami'in gwamnati, tare da raunata wasu mutum 31.

    Shugaba Volodymyr Zelensky ma ya ce an samu mutanen da suka mutu a harin, amma bai faɗi yawan su ba.

    Masu aikin ceto na ci gaba da neman zaƙulo waɗanda harin ya ritsa da su.

    Garin Pokrovsk yana da nisan kilomita 70 da Arewacin birnin Donetsk city, anda kuma dakarun Rasha suka mamaye.

    Kafin ɓarkewar yaƙin birnin yana da mutane aƙalla dubu 60.

  4. Lauyoyin Trump sun ce babu shaida kan zargin sa da yunƙurin murɗe zabe

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Lauyan da ke kare tsohon shugaban Amirka Donald Trump, ya ce masu gabatar da ƙara ba su da wata shaida da za su bayar kan cewa ya yi kokarin murɗe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2020.

    John Lauroya ce, Mr Trump ya yi imanin ya yi nasara a zaɓen ba shugaba Biden ba. Lauyan ya ce ana sukar wanda ya ke karewa da take masa ƴancin faɗin albarkacin baki da kundin tsarin mulki ya bashi dama.

    Shari'ar za ta mayar da hankali kan kokarin murɗe zaɓen 2020, kuma za a yi amfani da abubuwan da ya faɗa da aikata a lokacin.

    Masu shigar da ƙara dai sun ce Trump ya matsawa jami'an wasi jihohi kan sauya sakamakon zaɓen.

  5. Majalisa ta amince da naɗin mutum 45 a matsayin ministocin Tinubu

    Akpabio

    Asalin hoton, /Twitter President of Senate

    Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance tare da tabbatar da sunayen mutum 45 daga cikin 48 da Shugaba Tinubu ya aike mata don amincewa da naɗa su minista.

    Shugaban Majalisar Godswill Akpabio ya karanto sunayen da majalisar ta tantance ɗaya bayan ɗaya, yayin da sauran ƴan majalisar suka riƙa amsa tambayar amincewa ko akasin hakan.

    Ga cikakken jerin sunayen waɗanda aka tabbatar a matsayin ministocii:

    • Abubakar Momoh - Edo
    • Betta Edu - Kuros Riba
    • Uche Nnaji - Enugu
    • Joseph Utsev - Binuwai
    • Hannatu Musawa - Katsina
    • Nkeiruka Chidubem Onyejocha - Abiya
    • Stella Okotete - Delta
    • Uju Kennedy-Ohanenye - Anambra
    • Ahmed Dangiwa - Katsina
    • Olawale Edun - Ogun
    • Imaan Suleman Ibrahim - Nasarawa
    • Bello Muhammad Goronyo - Sokoto
    • Nyesom Wike - Ribas
    • David Umahi - Ebonyi
    • Mohammad Badaru Abubakar - Jigawa
    • Lateef Fagbemi - Kwara
    • Doris Aniche Uzoka - Imo
    • Yusuf Maitama Tuggar - Bauchi
    • Farfesa Ali Pate - Bauchi
    • Ekerikpe Ekpo - Akwa Ibom
    • Mohammed Idris - Neja
    • Olubunmi Tunji Ojo - Ondo
    • Dele Alake - Ekiti
    • Waheed Adebayo Adelabu - Oyo
    • John Eno - Kuros Riba
    • Abubakar Kyari - Borno
    • Abdullahi Tijjani Gwarzo - Kano
    • Dr Mariya Bunkure - Kano
    • Ishak Salako - Ogun
    • Bosun Tijjani - Ogun
    • Tunji Alausa - Legas
    • Tanko Sununu - Kebbi
    • Adegboyega Oyetola - Osun
    • Atiku Bagudu - Kebbi
    • Bello Matawalle - Zamfara
    • Ibrahim Geidam - Yobe
    • Simon Lalong - Filato
    • Lola Adejo - Legas
    • Shuaibu Abubakar - Kogi
    • Tahir Mamman - Adamawa
    • Aliyu Sabi Abdullahi - Neja
    • Alkali Ahmed Saidu - Gombe
    • Heneken Lakpobiri - Bayelsa
    • Uba Maigari - Taraba
    • Zephaniah Jissalo - Abuja

    Sauran mutum uku da majalisar ba ta tabbatar da nadinsu ba su ne:

    • Nasir El-Rufai - Kaduna
    • Sani Abubakar Danladi - Taraba
    • Stella Okotete - Delta
  6. Labarai da dumi-dumi, Majalisa ba ta tabbatar da El-Rufai a matsayin minista ba

    Nasir El-Rufai

    Asalin hoton, Facebook/Nasir El-Rufai

    Majalisar Dattawan Najeriya ta ƙi tabbatar da tsohon Gwamnan Kaduna a matsayin minista kamar yadda Shugaba Tinubu ya nema.

    Sauran mutum biyu da majalisar ba ta tabbatar ba su ne Sani Abubakar Danladi daga jihar Taraba, da kuma Stella Okotete ta jihar Delta.

    Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya ce suna jiran rahoton jami'an tsaro kafin su tabbatar da mutanen uku.

    Su kaɗai ne ba su shiga cikin mutum 45 ba da majalisar ta tabbatar a yau Litinin, amma ta tantance su tun daga Litinin da ta gabata da suka fara zaman.

  7. BBC ta bankaɗo cin zarafin tsofaffi a gidan kula da su a Kenya

    Elderly caned at Kenya's PCEA Thogoto Care Home for the Aged

    Asalin hoton, BBC AFRICA EYE

    Gwamnatin Kenya ta ce za ta gudanar da cikakken bincike a gidajen kula da tsofafi masu zaman kansu, bayan wani binciken kwakwaf na BBC Africa Eye ya bankado shaidun da ke nuna yadda ake cin zarafin tsofaffin a wani gidan kula da su a kusa da Nairobi.

    Bidiyon da tawagar Africa Eye ta ɗauka a sirrance, ya nuna yadda ma'aikatan gidan kula da tsofaffin ke duka da hantara da kyara, da ba su abinci a wulakance, da watsi da kula da lafiyar tsofaffin.

    Sai dai mai kula da gidan ya musanta dukkan zargin da akai musu, inda ya ce ana bai wa tsofaffin da ba sa iya cin abinci da kan su kulawa ta musamman.

    Sannan zargin rashin kula da lafiyarsu ma ba gaskiya ne ba.

  8. Majalisa ta tantance Keyamo bayan ya nemi afuwarta

    Festus Keyamo

    Asalin hoton, Keyamo/Twitter

    Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance Festus Keyamo daga jihar Delta a matsayin minista bayan dambarwar da ta mamaye tantacewar da farko.

    Festus Keyamo ya bayar da hakuri a kan kuskurensa na baya, inda ya ƙi amsa gayyatar majalisa ta 9 kan ayyukansa a matsayin ƙaramin ministan ƙwadago.

    A lokacin zaman tantancewar, Sanata Darlington Nwokocha daga jihar Abiya ya fargar da majalisar a kan yadda a baya Keyamo ya nuna "rashin ɗa'a" ga majalisa ta 9, inda ya zargi majalisar da aikata rashawa.

    Tsohon ministan ƙwadagon ya bayar da hakuri sannan ya yi ƙarin haske kan abubuwan da suka faru a wancan lokacin.

    Da farko dai Sanata Darlington ya nemi a dakatar da tantance Keyamo, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce har ya kai ga tsaiko ga aikin tantancewar.

    Daga baya dai majalisar ta dawo ta kuma yafe masa laifin da ya yi a baya.

    Festus Keyamo ne mutum na ƙarshe da majalisar ta tantance daga cikin 48 da Shugaba Bola Tinubu ya aike mata don amincewa da su a matsayin ministoci.

  9. Akwai kura-kurai da son zuciya a zaman shari'ar Imran Khan- Lauyoyi

    Imran Khan

    Asalin hoton, Reuters

    Lauyoyin tsohon firaministan Pakistan Imran Khan sun ce su na shirin ɗaukaka ƙara a kotun ƙoli, kan hukuncin da aka yanke masa na zaman gidan yari.

    Lauyoyin sun ce akwai kura-kurai da son zuciya a zaman shari'ar da aka yi wa wanda suke karewa, da aka yanke masa shekaru uku, saboda gaza bayyana wasu kyautuka da aka yi masa lokacin ya na kan mulki.

    Hukuncin da aka yanke kan wasu shari'o'in na daban kan Mr Khan da kuma ya yi nasara sun dan sanyaya masa zuciya, sai dai babu tabbas ko daukaka ƙarar ta yanzu za ta yi tasirin janye hukuncin da aka yanke.

    Harwayau, lauyoyi da ƴan uwa da magoya bayansa sun nuna damuwa kan tsaron lafiyarsa a gidan kason, amma kawo yanzu hukumar gidan yarin Pakistan ba ta ce uffan ba kan batun.

  10. Zulum ya raba buhunnan shinkafa don rage matsin rayuwa

    Bags of rice

    Asalin hoton, Borno state government

    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanya ido kan shirin rage raɗaɗi da ya ƙunshi tallafin abinci ga iyalai 2,000 a mazaɓar Mafoni da ke birnin Maiduguri.

    Wata sanarwa da Mallam Isa Gusau mai magana da yawun gwamnan ya fitar ta ce manufar rabon abincin ita ce rage raɗaɗin cire tallafin man fetur, kuma yayin rabon an bai wa kowanne gida buhun shinkafa da wake biyu.

    Zulum ya bayyana cewa an zaɓo waɗanda suka ci gajiyar shirin ne daga mazaɓa 27 daga faɗin Maiduguri da kuma mazaɓa 12 daga ƙaramar hukumar Jere.

    Sanarwar ta ce rabon abinci wanda ya ƙunshi buhun shinkafa 54,000 da buhunnan wake 54,000, an bayar ne ga magidantan da suka fi buƙata a cikin ƙananan hukumomin jihar biyu, a cewar gwamnatin.

    Ta ƙara da cewa gwamnatin Zulum ta tashi haiƙan wajen neman dabarun da za su rage illar da hauhawar farashin man fetur ta haifar a kan talakawa, ta hanyar tabbatar da ganin abinci da sauran muhimman ayyuka ga masu tsananin buƙata.

    Da yake jawabi a wurin raba abincin, Gwamna Zulum ya ce buhunnan shinkafar wani ɓangare ne na shinkafa buhu 3,000 da gwamnatin Borno ta karɓa daga Shugaba Bola Tinubu.

    Paliatives

    Asalin hoton, Borno State Government

  11. Dije Aboki: Mace ta farko alƙaliyar alƙalan Kano ta yi rantsuwar kama aiki

    Dije Aboki

    Asalin hoton, KNSG

    Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Mai Shari'a Dije Abbu Aboki a matsayin alƙaliyar alƙalai ta Kano a yau Litinin.

    Ita ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin, kuma an yi bikin ne a fadar gwamnatin Kano bayan majalisar dokoki ta amince da naɗin ta a farkon watan Yuli.

    Da yake jawabi bayan rantsuwar, Gwamna Kabir ya ce an naɗa ta ne "saboda kyawawan ayyukanta wajen tabbatar da adalci a harkokin shari'a".

    "Kin nuna ƙwarewarki a tsawon shekarun aikinki a matsayin babbar mai shari'a da ta himmatu wajen yin adalci," a cewarsa.

    Ta karɓi rantsuwar kama aiki ne bisa rakiyar mijinta Abdu Aboki, wanda shi ma tsohon alƙali ne.

    • Dije Aboki: Wace ce mace ta farko Babbar Alƙaliya ta jihar Kano?
    Dije Aboki

    Asalin hoton, KNSG

  12. Shugaban Majalisar Dattijai ya garzaya fadar shugaban ƙasa

    Senate President

    Asalin hoton, Godswill Akpabio/Facebook

    Rahotanni daga fadar Shugaban Najeriya na cewa Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio ya garzaya fadar shugaban ƙasa ɗazu da rana.

    Jaridun ƙasar sun ruwaito cewa an ga Akpabio a fadar shugaban ƙasa ne da misalin 2:55 na rana.

    Babu cikakkun bayanai kawo yanzu a kan dalilan ziyarar tasa zuwa fadar Aso Rock.

    Sai dai ziyarar ta zo ne bayan majalisar dattijan ta shiga zaman sirri a kan hargowar da ta ɓarke a zauren majalisar lokacin da ake ƙoƙarin tantance Festus Keyamo a matsayin minista.

    Kan ƴan majalisar dai ya rabu biyu ne a kan ko su dakatar da tantance Keyamo, saboda zargin raina majalisa da kiran ƴan majalisar gurɓatattun mutane lokacin da yake minista zamanin gwamnatin Shugaba Buhari.

    An shafe tsawon lokaci ana hayaniya a majalisar kafin daga baya ƴan majaliasar dattijan su amince su shiga ganawar sirri don warware matsalar.

    Daga nan ne aka nemi ƴan jarida tare da Festus Kiyamo su fita daga zauren.

  13. Ecowas za ta gudanar da taron ƙoli kan Nijar a Abuja

    ...

    Asalin hoton, Presidency

    Bayanan hoto, Shugaba Tinubu

    Ƙungiyar ƙasasahen yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO, ta ce za ta gudanar da taron ƙoli a babban birnin Najeriya, Abuja a ranar Alhamis domin tattauna batun Nijar, inda aka yi juyin mulki.

    Wakilin BBC ya ce, a ranar Lahadi jagororin juyin mulkin suka yi watsi da wa'adin da ECOWAS ta ba su na su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki, ko kuma su fuskanci matakin soji.

    Ƙasahen Burkina Faso da Mali sun ce za su tura tawagar haɗin gwiwa domin nuna goyon baya zuwa Nijar.

  14. Mali da Burkina Faso za su tura tawaga zuwa Nijar

    ...

    Asalin hoton, Reuters/ Getty images

    Ƙasar Mali ta ce za ta tura tawagar ta haɗin guiwa da Burkina Faso domin jaddada goyon bayan su ga sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar din.

    Sanarwa na zuwa ne bayan da Sojin na Nijar suka yi watsi da umarnin Ecowas na mayar da mulki ga hamɓararren shugaban bisa karagar mulkin ƙasar.

    Sojojin Nijar sun sanar da rufe sararin samaniyar su da iyakokin ƙasar, sun kuma ce a shirye suke wajen kare ƙasarsu.

    Kawunan ƙasashen ƙungiyar Ecowas ya rabu kan ɗauka matakin soji ga Nijar, koda yake shine mataki na ƙarshe da ƙungiyar tace za ta ɗauka.

    Najeriya da Ivory Coast na kan gaba wajen jaddada buƙatar mayar da shugaba Bazoum bisa shugabancin ƙasar.

    Sai dai shugabannin mulkin soji na ƙasashen Mali da Burkina Faso sun nuna goyon bayan su ga Sojojin Nijar, sun kuma ce zasu shigar masu faɗa madamar Ecowas ta kai ma Nijar hari.

  15. Majalisa ta shiga zaman sirri saboda saɓani a kan tantance Festus Keyamo

    ...

    Asalin hoton, FESTUS KEYAMO/FACEBOOK

    Sanata Darlington Nwokocha ne ya fara gabatar da ƙudirin haka a gaban majalisa, inda ya nemi a dakatar da shi har sai lokacin da ya amince da cewa majalisa na da damar bincikar ayyukan ministoci.

    Hakan ya faru ne sakmakon tirjiyar da ya nuna a lokacin da yake minista a baya, inda ya ƙi amsa gayyatar majalisa.

    Ƙudirin ya samu goyon bayan mafi rinjayen sanatoci, hakan ya sa daga ƙarshe majalisar ta yanke shawarar shiga zaman sirri kan lamarin.

    Festus Keyamo shine ministan gwamnatin Buhari da ya sake shiga cikin jerin sunayen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin minista.

  16. An tantance Dr Mariya wadda ta maye gurbin Maryam Shetty a matsayin minista

    ...

    Asalin hoton, Ganduje/Facebook

    Bayanan hoto, Dr Mariya Mairiga

    Majalisar Dattawan Najeriya ta tantance Dr Mariya Mairiga Mahmoud a matsayin minista daga jihar Kano.

    Dr Mariya dai ita ce ta maye gurbin Maryam Shetty da shugaba Tinubu ya cire sunanta a makon da ya gabata.

    Sauyan sunan Maryam Shetty da Dr Mariya Mairiga ya janyo ce-ce-ku-ce shafukan sada zumunta.

  17. Ƴan Najeriya ne suka jefa kansu halin da suke ciki - Sule Lamiɗo

    Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar hamayya ta PDP ya ce halin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu na tsadar rayuwa da matsi, abin da suka shuka ne suke girba.

    Alhaji Sule Lamido ya ce ƴan Najeriya suna da ilimi da hankali, babu wanda ya yi zaɓe akan tsoro ko jahilci.

    Ku latsa hoton da ke ƙasa domin sauraren tattaunawarsa da Zahraddeen Lawan

    Bayanan sautiKu latsa hoton da ke sama don jin tattaunawar
  18. Italiya ta nemi Ecowas ta tsawaita wa'adin da ta bai wa sojin Nijar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Italiya, yayi kira ga ƙungiyar ECOWAS da ta tsawaita wa'adin da ta baiwa sojojin Nijar na mayar da mulki ga hamɓararren shugaban, Mohamed Bazoum.

    "Hanya ɗaya da za a bi ita ce hanyar diplomasiyya. Ina fatan ECOWAS za ta tsawaita adadin da ta ɗibarwa Nijar," Inji Antonio Tajani, sakataren harkokin wajen Italiya.

    Da yammacin ranar Lahadi ne shugabannin sojojin Nijar suka rufe sararin samaniyar ƙasar bayan da a'adin da ECOWAS ɗin ya cika.

    Sakamakon wannan matakin, dukkan jiragen ƙasashen waje masu ketawa ta sararin samaniyar ƙasar sai dai su sauya hanya ko kuma su koma ƙasarsu ta asali.

    Sojojin sun ce ƙasashen ECOWAS biyu sun fara shirye-shiryen kai hari Nijar, sai dai basu bada hujjar da ke tabbatar da haka ba.

    ECOWAS ba ta fitar da wata sanarwa ba tun bayan da lokacin da ta ɗibarwa sojojin ya cika.

  19. Birtaniya ta buɗe sabuwar cibiyar samar da allurar riga-kafi

    ...

    Gwamnatin Birtaniya ta buɗe sabuwar cibiyar samar da allurar riga-kafi, inda masana kimiyya za su yi aiki tuƙuru domin samun kariya daga ɓarkewar wata annoba nan gaba.

    An gina cibiyar ne a Porton Down,wanda ke sansanin soji da ke kudu maso gabashin Ingila, wurin da ya yi fice kan abubuwan da suka shafi sinadaran haɗa makaman yaki.

    Ƙwararrun masana za su yi nazarin sabbin ƙwayoyin cutukan da aka gano, su kuma samar da rigakafin cutuka.

    Masanan za su fara yi shirin ko ta kwana da samar da rigakafin cutukan da ka iya ɓullowa da zama bala'i a duniya.

  20. An tafi ƙarin lokaci a wasan Najeriya da Birtaniya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yanzu haka dai an tafi ƙarin lokaci.

    Sai dai Super Falcons ce ta fi buga kwallo , inda ta kai hare-hare masu zafi a ragar Ingila.

    Duk kungiyar da ta samu nasara ita ce za ta kai zagayen quarter finals.