Zanga-zanga ta kaure a birnin Paris bayan wani ɗan sanda ya harbe wani matashi mai shekara 17 saboda ya ƙi tsayawa a lokacin da danjar kan hanya ta tsayar da shi.
Bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna ɗan sandan na saita direban motar da bindiga kafin daga baya aka ji ƙarar bindigar.
Matashin mai suna Nahel ya mutu bayan da harsashin ya ɓula masa ƙirji, duk kuwa da kokarin ceto ransa da likitoci suka yi.
A yanzu dai an tsare ɗan sandan da ake zargi da kashe matashin, inda ake tuhumarsa da aikata kisan kai.
Lamarin dai ya haifar da ɓarkewar zanga-zanga ranar Talata da daddare a unguwar Nanterre, yankin da ke yammacin birnin Paris inda aka kashe matashin.
Kawo yanzu an kama mutum 31 sakamakon zanga-zangar.
- Yadda wani mutum ya caccaka wa yara wuƙa a Faransa
- 'Yan sandan Faransa sun kashe wani a farautar 'yan ta'adda
Nahel ne mutum na biyu da aka kashe a Faransa cikin wannan shekara sakamakon harbin da 'yan sanda ke yi a wuraren bayar da hannu a kan titunan ƙasar.
A shekarar da ta gabata mutum 13 ne suka mutu ta dalilin wannan hanya.
Kafar yaɗa labaran Faransa ta ambato 'yan sandan na cewo matashin ne ya tuƙo mota inda ya haro inda suke da niyyar cutar da su.
To sai dai bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumuntan ba su nuna alamun hakan ba.
Bidiyon ya nuna 'yan sandan biyu na tsaye a kan motar. Inda ɗaya daga cikinsu ke nuna direban da bindiga, inda ya yi harbi a daidai lokacin da direban ya yi yunƙurin tuƙa motar.
Shugaban Faransa ya bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a ''lamunta ba'', yana mai cewa wannan harbi ne na babu gaira babu dalili.