Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'A hukunta jihohin da suka bar mata masu tsohon ciki zuwa aikin hajji'

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan ƙasashe

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Ibrahim Yusuf Mohammed and Mukhtar Adamu Bawa

  1. 'Yan sanda na neman wani mai shirya bidiyon tsokana a Najeriya

    ‘Yan sanda a Najeriya sun yi kira ga duk wanda ya san wani mai shirya bidiyon tsokana a intanet ya ɓatawa, su fito su kai rahoto a kan irin halin da suka shiga.

    Trinity Guy yana yin bidiyo ta hanyar shirya labari a kan tsokanar mutane don wallafawa a shafukan sada zumunta kuma dubban mutane ne suke bibiyar harkokinsa.

    Wasu daga cikin bidiyon da yake shiryawa sukan nuna shi a lokacin da yake roƙon afuwa da magiyar kada a halaka shi, kafin a ji ƙarar tashin wani abu mai kama da bindiga, daidai lokacin da shi kuma zai faɗi magashiyan tamkar wanda aka harbe.

    Irin wannan bidiyo dai na tayar da hankalin mutanen da ke kusa, inda sukan yi matuƙar kaɗuwa, wasu ma su ruga da gudu cikin firgici.

    "Ina ganin ya kamata a kama mutumin. Ya kamata mutanen da kan shiga fargaba ta dalilin bidiyon Trinity Guy su rika kai rahoton masu irin wannan wasan barkwanci saboda yawancin ayyukansu na da alaƙa da aikata laifi da fasikanci, da kuma mugunta," in ji kakakin rundunar 'yan sanda ta Najeriya, Olumuyiwa Adejobi.

    Ya kara da cewa "Wadannan matan na da hujjar yin shari'a sosai a kan mai bidiyon tsokanar."

    Wasu a shafukan intanet sun mayarwa ‘yan sanda martani, suna cewa kamata ya yi rundunar ta yi maganin cin zarafi da rashawar da ta janyo zanga-zangar EndSars ta Najeriya, maimakon ɓugewa da yunƙurin kama masu shirya bidiyon barkwanci don tsokana.

  2. An kashe ‘yan Isra’ila huɗu a Yamma da Kogin Jordan

    An kashe wasu ‘yan Isra’ila hudu a wani harin bindiga da aka kai a kusa da wani kauye da ke Yamma da Gaɓar Kogin Jordan da ke ƙarƙashin mamayen Isra'ila, kamar yadda ma’aikatan lafiya suka bayyana.

    Wasu hudu kuma sun jikkata, a cikinsu har da wanda ya ji rauni mai tsanani, a lokacin da wasu Falasdinawa ‘yan bindiga biyu suka bude wuta a wani gidan abinci da gidan mai da ke kan wata babbar hanya a wajen garin Eli.

    Sojojin Isra'ila sun ce maharan ''yan ta'adda ne masu alaka da ƙungiyar Hamas''.

    Wani farar hula dauke da bindiga ya harbe daya cikin maharan nan take, yayin da dayan ya gudu a cikin motar sata, daga bisani sojojin Isra'ila suka kashe shi a garin Tubas.

    Firaministan Isra'ila ya ce "dukkan ƙofofi a bude suke don ɗaukar ƙarin matakai" don yin martani ga abin da ya kira "harin ta'addanci mai ban tsoro da kyama".

    Lamarin dai ya zo ne bayan karuwar tashe-tashen hankula a Gabar Yamma da Kogin Jordan cikin 'yan kwanakin nan.

    Mai magana da yawun ƙungiyar Hamas ya ce harin, wani martani ne ga farmakin da sojojin Isra'ila suka kai a Jenin ranar Litinin da ta gabata, inda Falasdinawa shida suka mutu.

    Harbin na ranar Talata ya faru ne a kudancin Eli kan babbar hanyar da ke tsakanin garuruwan Falasdinawa wato Ramallah da Nablus.

    Mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila Rear Admiral Daniel Hagari ya faɗa a cikin wata sanarwa cewa 'yan bindigan sun je ne a cikin wata mota daga kauyen Urif mai tazarar kilomita 10 daga arewa.

    Ya kara da cewa sun fara bude wuta a wani gidan cin abinci na hummus da ke gefen hanya, inda suka kashe fararen hula uku, sannan suka harbe wani farar hula a gaban wani gidan mai.

  3. Za a iya hukunta jihohin da suka fi barin mata masu tsohon ciki zuwa aikin hajji

    Ayarin likitoci masu kula da lafiyar maniyyata aikin hajjin bana daga Najeriya da ya je Saudiyya ya ba da shawarar sanya takunkumi ga jihohi masu yawan mata masu juna biyu da suka tafi aikin ibadar.

    Dr Usman Galadima, shugaban sashen gudanarwa kuma jagoran ayarin ne, ya bayar da wannan shawara a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), a birnin Makkah ranar Talata.

    NAN ya ruwaito cewa hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON ce ke samar da wannan aiki don tabbatar da ingantaccen tsarin kula da lafiya ga alhazan Najeriya da ke ƙasar Saudiyya a duk tsawon lokacin aikin Hajji.

    Galadima ya ce, ayarin ya samu labarin mutuwar mata masu juna biyu da suka je aikin hajji a ƙasar Saudiyya duk da kokarin da ake yi na hana su zuwa a irin wannan yanayi.

    Ya tabbatar da cewa wata 'yar Najeriya ta haifi jariri dan wata bakwai ta hanyar tiyata a Madina.

    Jagoran likitocin ya kara da cewa, sun kuma samu rahoto game da matsalolin zubewar ciki da za a iya kiyayewa idan matan da abin ya shafa sun yi rijistar haihuwa a asibitin ayarin.

    Galadima ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a aikin hajji su dage kan kokarin rage yawan mata masu juna biyu da ke zuwa aikin hajji.

    A cewarsa, duk macen da ke son zuwa aikin hajji to ta yi tsari da kyau gami da kaucewa ɗaukar ciki kafin zuwa ibadar.

    Galadima ya ce: “Abin da zan ba da shawara shi ne, mai yiwuwa idan za a iya kafa wasu matakan ladabtarwa ko za a iya aiwatar da su a kan wasu jihohi masu kuskure ko waɗanda ke da wani adadi na mata masu juna biyu.

  4. Tinubu ya mayar da hukumar alhazai ƙarƙashin Shettima

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da mayar da hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da kuma hukumar hajji ta ƙasa (NAHCON) ƙarƙashin kulawar ofishin mataimakinsa.

    Wata sanarwa da Olusola Abiola, daraktan yaɗa labarai a ofishin mataimakin shugaban Kashim Shettima ta ce umarnin wani mataki ne na yin aiki da dokokin da suka kafa hukumomin.

    A zamanin gwamnatin da ta wuce, ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Buhari, hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasar ta kasance a ƙarƙashin ma'aikatar jin ƙan ɗan'adam ne ta tarayya.

    yayin da hukumar alhazai ta Najeriya ta kasance a ƙarƙashin ofishin shugaban ƙasa a wancan lokaci.

    Sanarwar Olusola Abiola dai ta kuma ambato Shugaba Tinubu yana amincewa da wani fasali na yadda ofishin mataimakin shugaban ƙasar zai kasance.

    Da kuma adadin ƙwararrun ma'aikata da jami'an gudanarwa da suka dace da yin aiki a ofishin na Kashim Shettima don sauke nauyin da aka ɗora masa.

  5. Wata mace ta haihu a cikin jirgin saman Legas zuwa Amsterdam

    Wata mace mai juna biyu ta haihu bayan naƙuda ta zo mata ba zato ba tsammani a cikin jirgin KLM da ke kan hanyarsa ta zuwa Amsterdam daga Legas.

    Lamarin dai ya tilasta wa jirgin yin saukar gaggawa a ƙasar Sifaniya.

    Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne cikin daren Litinin, inda daya daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin KLM mai lamba 588, ƙirar Boeing 777, ta fara nakuda.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kai matar wadda ba a bayyana sunanta ba gaban jirgin, inda ta haifi 'ya mace.

    Bayan nan ne sai jirgin ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Barcelona inda ma'aikatan lafiyan da aka kira suke tsaye suna jira

    An ce uwa da 'yar duka suna cikin ƙoshin lafiya.

    Mai magana da yawun kamfanin sufurin jiragen sama na KLM, Marjan Rozemeijer, a ranar Talata ta ce, "Zan iya tabbatar da cewa an haifi jaririyar a cikin jirgin KLM mai lamba KL 588 da ke kan hanyar zuwa Amsterdam a ƙasar Netherlands daga Legas.

    Saboda dalilai na tsare sirrin mutum ba zan iya yin wani ƙarin bayani game da haihuwar ba."

  6. 'An kai wa gidana farmaki duk da yarjejejiyar tsagaita wuta a Sudan'

    Yayin da yarjejeniyar tsagaita wutar kwana biyu da aka cimma a Sudan ke shirin ƙarewa, wasu 'yan kasar sun ce an kai farmaki kan gidajensu bisa abin da ake ganin ya saɓawa yarjejeniyar da aka cimma bisa muradan jin kai.

    Abeer Abdul-Mo'ety ta shaida wa BBC Sudan Lifeline kan yadda wasu mutane kimanin 20 suka haura katangar gidanta a unguwar Manshiya da ke babban birnin ƙasar ranar Litinin.

    "Sun karya kofa tare da kutsawa cikin gidana amma babu kowa a lokacin domin mijina da 'ya'yana sun gudu bayan sun ji karar harbe-harbe a waje.''

    Ta ce wata makwabciyarta ta tabbatar da cewa maharan sun sace duk wani abu mai daraja a gidan.

    Abeer Abdul-Mo'ety ta kara da cewa "Tabbas za a iya mayar da dukiyar da aka rasa, amma ba za a iya dawo da rai ba.

    "Ta yi godiya ga Allah da mutanen gidanta suka kasance cikin ƙoshin lafiya duk da yake suna cikin damuwa saboda sun bar fasfo ɗinsu a baya, kuma ba za su iya komawa gida su dauko ba.

    Tun lokacin da aka fara fadan watanni biyu da suka gabata, mutane aƙalla 305 ne suka ɓace - a cewar shirin bin diddigin mutanen da suka bata.

  7. Emefiele ya maka gwamnatin Najeriya a kotu

    Gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Mista Godwin Emefiele ya shigar da ƙara a gaban wata babbar kotun tarayya, yana ƙalubalantar tsare shi da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ke yi.

    A cikin ƙudurin da ya gabatar, Emefiele ya nemi kotu ta tilasta wa hukumomi tabbatar masa da 'yancinsa na walwala da 'yancin zirga-zirga, don kuwa a cewarsa, babu hujjar ci gaba da tsare shi.

    Sai dai, Ofishin Atoni Janar na Tarayya da kuma hukumar DSS sun ce tsare dakataccen gwamnan bankin yana kan doka.

    Sun kuma ce tsare jami'in ya dogara ne kan wani umarnin kotun majistare don haka suka nemi babbar kotun ta kori buƙatar da Emefiele ya gabatar.

    Sun nunar da cewa kama tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya yana kan tsarin gudanarwa na hukumar ta DSS.

    Yayin da Atoni Janar na Tarayya ya ƙalubalanci hurumin kotun na sauraron ƙarar, saboda ƙudurin da Godwin Emefiele ya gabatar na neman kotu ta jingine umarnin tsare shi ne, maimakon neman a tabbatar masa da 'yancinsa.

    Haka zalika, ita ma hukumar DSS a nata ɓangare ta ƙalubalanci ƙudurin neman beli da Mista Emefiele ya gabatar.

    Daga bisani, kotu ta ɗage shari'ar zuwa ranar 13 ga watan Yuli don yin hukunci kan wannan buƙata.

    A ranar 10 ga watan Yuni ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele daga matsayin Gwamnan Babban Bankin ƙasar, daga bisani kuma hukumar DSS ta sanar da cewa tana tsare da shi.

  8. Real Madrid ta bai wa Joselu riga mai lamba 14

  9. An yi wa ma'aikatan Turkiyya ƙarin albashi

    Ministan ƙwadago da tsaron jama'a, Vedat Işıkhan ya sanar da ƙarin mafi karancin albashi zuwa Lira 11,402. Don haka, ƙarin albashi mafi karanci na yanzu ya kai kashi 34 cikin dari.

    A yau ne kwamitin tabbatar da mafi ƙarancin albashi ya yi taro karo na uku. Vedat Işıkhan, ministan kwadago da tsaro, da shugabannin gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar wato Türk-İş da TİSK duk sun halarci taron.

    Ministan kwadago Vedat Işıkhan ya sanar da ƙarin albashi mafi karancin a matakin wucin gadi bayan taron.

    Minista Işıkhan ya ce, "Mafi ƙarancin albashin abu ne da zai fara aiki na tsawon shekara ɗaya da zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu. Sanarwar ta yau ta nuna cewa an yi ƙarin ne domin hana hauhawar farashi kassara ma'aikatanmu."

    Shugaban gamayyar ƙwadago ta Türk İş, Ergün Atalay ya ce: "Ina fatan za a shawo kan wannan hauhawar farashi, babu wani abin damuwa idan an ƙara mafi karancin albashi kuma hauhawar farashi bai kai wani mataki da ya wuce hankali ba. Amma akwai buƙatar a gaggauta shawo kan lamarin hauhawar farashi a kasuwa,” in ji shi.

    Shugaban ƙwadago ta TİSK, Özgür Burak Akkol ya ce, "Mun yi aiki don samun daidaituwar lamurra. Ina farin cikin cewa na'am ga wannan adadini."

    Mataimakin shugaban ƙasar Cevdet Yılmaz ya kuma ce, "Ina miƙa godiya ga ma'aikatanmu da wakilan masu daukar ma'aikata da suka kammala aikin a ckin hankali, tuntuba da kuma sulhu."

    A ranar 13 ga watan Yunin bana ne aka fara tattaunawa kan ƙarin mafi ƙarancin albashi na wucin gadi. An yi taro na biyu a ranar 19 ga watan Yuni.

    A da dai, mafi ƙarancin albashin ma’aikaci, Lira dubu 10 ne a kowane wata kafin ƙarin da aka yi yanzu.

  10. Ukraine ta yi iƙirarin kakkaɓo jiragen Rasha marasa matuƙa 32

    A daren Laraba ne Rasha ta kai hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka a kan Ukraine.

    Sai dai rundunar sojin Ukraine ta ce ta harbo jirage marasa matuka 32 cikin 35 na Rasha.

    An ƙera wadannan jirage marasa matuka da ke dauke da makamai ne a Iran, wadanda aka harba zuwa wasu garuruwa ciki har da Kiev babban birnin ƙasar.

    Jami'an Ukraine sun ce an lalata gine-gine da dama a harin amma babu wanda ya mutu.

    An harba ɗaruruwan makamai masu linzami kan Zaporizhia da ke kudancin Ukraine.

    Gwamnan yankin ya bayyana cewa, Rasha ta sake kai farmaki a wasu kauyuka takwas da aka kwato daga hannunta.

    A baya-bayan nan dai ƙasar Ukraine ta fara kai wa Rasha harin mayar da martani

  11. Ɓangarorin da ke yaƙi a Sudan na zargin juna da karya sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta

    Bangarorin soji da ke rikici da juna a Sudan na zargin juna da karya sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwana biyu.

    Rundunar sojin Sudan ta bayyana cewa, dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai wani hari a arewacin Darfur a rana ta biyu a jere.

    A ranar Litinin, ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce ba a mutunta yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar ba, har ma sun yi watsi da wani aikinsu don kai sojojin da suka samu raunuka asibiti.

    Tun da farko dai mazauna babban birnin ƙasar wato Khartoum, sun ba da rahoton cewa faɗa ya yi sauƙi, don kuwa ba su ji ƙarar hare-haren da ake kai wa ta sama ba, sannan ba su ji saukar makaman atilare ko tashin wani faɗa ba.

    Masu shiga tsakani na Amurka da Saudiyya sun sanar da tsagaita wuta na tsawon sa'a 72 a ranar Asabar.

    Sai dai ba a yi sau da ƙafa da yarjeniyoyin tsagaita wuta da aka ayyana a baya ba.

  12. Ƙalubale shida da ke gaban sabbin hafsoshin tsaron Najeriya

  13. Kashim Shettima ya sa lambar ƙarin girma ga sabon babban sufeton 'yan sandan Najeriya

    Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya sanya wa Kayode Egbetokun lambar ƙarin girma, a matsayin sabon babban sufeton ‘yan sanda na riko.

    Shettima ya yi hakan ne a lokacin wani taƙaitaccen biki a ofishinsa da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja ranar Talata.

    Cikin muƙaman da ya riƙe a baya, sabon babban sufeton 'yan sandan na riƙo ya taba riƙe mukamin kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas.

    Sauran jami’an da suka halarci taron akwai gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu; da Sufeto-Janar na 'yan sanda mai barin gado, Alkali Baba.

    Sabon babban sufeton ya maye gurbin Usman Alƙali Baba ne, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a matsayin Babban Sufeton ‘yan sanda a 2021.

  14. Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da yaƙi a kan gwamnatinmu - Taliban

    Zabihullah Mujahid, mai magana da yawun kungiyar Taliban, ya mayar da martani ga taron kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan, wanda ya mayar da hankali kan halin da mata ke ciki a Afghanistan, ya kuma ce an kaddamar da farfaganda mai yawa kan kungiyar ta Taliban.

    Mista Mujahid ya rubuta a shafinsa na twitter cewa: "An kaddamar da wata gagarumar farfaganda a kan gwamnatin Taliban ta Afghanistan daga ofishin Majalisar Dinkin Duniya da wasu cibiyoyi da gwamnatocin kasashen yamma."

    A ranar Litinin 29 ga watan Yuni, wakilan kasashe da kungiyoyin da ke halartar taro na 53 na kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, sun bukaci gwamnatin Taliban da ta gaggauta kawo karshen manufofin nuna wariya ga mata, yara da manya a Afganistan.

    Tsananin nuna wariya da ake yi wa mata da 'yan mata shi ne jigon akidar Taliban da gudanar da mulkinta, wanda ake fargabar zai ingiza wutar matsaloli kamar na nuna wariyar launin fata," in ji Richard Bennet, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan hakkin dan Adam a Afghanistan.

    Ya jaddada batun sake bude dukkan makarantu da kayan koyarwa bisa ka’idojin kasa da kasa, da kafa gwamnati wadda ta ƙunshi mutane daban-daban da kuma kawar da wariya a tsarin gwamnati.

    Mista Bennett ya fada a cikin rahotonsa cewa kungiyar Taliban ta sanya takunkumi kusan 50 kan mata da 'yan mata a cikin shekaru biyu da suka wuce.

    Sai dai kakakin Taliban ya kira rahoton na Mista Bennett a matsayin wani bangare na "farfaganda" kuma ya rubuta cewa "ba gaskiya ba ne.

    "Ana aiki da dokokin Musulunci a Afganistan, bijire masu tamkara adawa ce da musulunci.

  15. Gwamnan Kano ya miƙa sunayen kwamishinoni ga majalisar dokoki

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunayen mutane 19 da yake son ya naɗa a matsayin kwamishinoni a majalisar zartarwar jihar.

    A yau Talata ne shugaban majalisar dokokin jihar, Honorabul Yusuf Falgore ya karanto jerin sunayen da gwamnan ya aike wa majalisar.

    Ga jerin sunayen:

    • Comrade Aminu Abdulsalam
    • Hon. Umar Doguwa
    • Ali Haruna Makoda
    • Hon. Abubakar Labaran Yusuf
    • Hon. Danjuma Mahmoud
    • Hon. Musa Shanono
    • Hon. Abbas Sani Abbas
    • Haj. Aisha Saji
    • Haj. Ladidi Garko
    • Dr. Marwan Ahmad
    • Engr. Muhd Diggol
    • Hon. Adamu Aliyu Kibiya
    • Dr. Yusuf Kofar Mata
    • Hon. Hamza Safiyanu
    • Hon. Tajo Usman Zaura
    • Sheikh Tijjani Auwal
    • Hon. Nasiru Sule Garo
    • Hon. Haruna Isa Dederi
    • Hon. Baba Halilu Dantiye
  16. Amurka ta buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta fice daga Mali cikin tsari

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira da a bi a hankali wajen rage yawan dakarun wanzar da zaman lafiya da ke aiki a Mali waɗanda ake wa take da Minusma.

    Hakan na zuwa ne bayan kiran da shugabannin na Mali suka yi ga dakarun da su fice 'ba tare da ɓata lokaci ba.'

    "Mun damu matuka game da illar da wannan shawarar za ta yi kan tsaro da rikice-rikicen da ke shafar al'ummar Mali. Za mu ci gaba da yin aiki tare da takwarorinmu na Afirka ta Yamma domin taimaka musu wajen tunkarar kalubalen tsaro da shugabanci na gaggawa da suke fuskanta," in ji Amurka.

    "Muna maraba da karin shawarwari daga shugabannin kasashen yankin kan karin matakai na inganta zaman lafiya da hana rikici."

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta kara da cewa dole ne gwamnatin Mali, karkashin jagorancin soja" ta martaba alƙawurran da ta ɗauka, musamman batun miƙa mulki ga zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula nan da watan Maris din shekarar 2024.

    Mali na zargin dakarun Minusma, waɗanda aikinsu ke zuwa ƙarshe a makon gobe da 'gazawa' wajen tunkarar matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

  17. Yadda za a kula da mai ciwon sikila lokacin damuna

  18. An ƙaddamar da dokar ta-ɓaci kan satar waya a Kano

    Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ƙaddamar da dokar ta-ɓaci game da satar waya da kuma wasu laifukan da ake aikatawa a birnin.

    Kafofin yaɗa labarai sun ce majalisar dokokin jihar ta nuna damuwa kan matsalolin satar waya da sane da shan miyagun kwayoyi da ma waɗansu laifukan da ke barazana ga zaman lafiyar jihar.

    A wata mahawara da shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar, 'yan majalisar sun amince kan cewa akwai buƙatar a gaggauta magance matsalar kafin ta yi ƙamari.

    Majalisar dokokin ta kuma amince da wani ƙuduri da ya buƙaci gwamnatin jihar ta dauki dukkan matakan da suka kamata domin hukunta waɗanda aka kama da laifi.

  19. Uganda ta kama mutum 20 kan kisan gilla a wata makaranta

    Ƴan sandan Uganda sun ce sun kama mutane 20 da ake zargi da haɗa baki da mayaƙan kungiyar IS da ake kyautata zaton sun kai hari a wata makaranta a ranar Juma'ar da ta gabata.

    Shugaban makarantar da kuma wanda ya mallaki makarantar na cikin wadanda ake tsare da su.

    An kashe mutane 42 – akasarinsu dalibai a makarantar sakandare ta Lhubiriha da ke Mpondwe a yammacin Uganda.

    Da yawa sun kone kurmus a dakin kwanan su.

    Sojojin Uganda na ci gaba da farautar 'yan ta'addar Allied Democratic Forces (ADF), wadanda rahotanni suka ce sun koma kan iyaka zuwa gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango inda suke da sansani.

  20. Jerin sunaye da jihohin sababbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya naɗa

    Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro:

    Mallam Nuhu Ribadu -National Security Adviser (NSA) - Adamawa

    Shugabannin rundunonin tsaro:

    1- Manjo Janar Christopher Gwabin Musa - Hafsan hafsoshin tsaro na Najeriya (CDS) - Kaduna

    2 - Manjo Janar Taoreed Abiodun Lagbaja - Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya (COAS) - Ogun

    3 - Rear Admiral Ekechukwu Ogalla - Babban Hafsan sojin ruwa na Najeriya (CNS) - Enugu

    4 - Air Vice Marshal Hassan Bala Abubakar - Babban hafsan sojin sama na Najeriya (CAS) - Kano

    5 - DIG Kayode Egbetokun - Sifeta-Janar na ƴan sandan Najeriya (IG) - Ogun

    6 - Manjo Janar EPA Undiandeye - Babban jami'in tattara bayanan sirri na trsaro (CDI) Cross River