Ayyukan masu haƙar zinare na barazana ga rayuwar al'ummar Ghana
Ghana ta sake komawa kan matsayinta na wadda ke kan gaba wajen fitar da zinare daga nahiyar Afirka bayan ƙarin kashi 32 cikin ɗari a ayyukan haƙar zinaren a bara.
Hukumar Kula da Kasuwanci ta Ghana ta alaƙanta hakan a kan bunƙasar da aka samu wajen ayyukan haƙar zinaren a manya da ƙananan ɓangarori.
Sai dai yanzu ƙasar na fuskantar matsalar muhalli sanadiyyar ƙarin ayyukan haƙar zinaren.
Yanzu haka dazuka da rafuka da ƙoramu duk sun lalace sanadiyyar ayyukan masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba, wani lamari da ya zamo mai haɗari ga al'umma.
Ɓangaren haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba wanda ake wa laƙabi da 'galamsey', na samar wa matasa da dama hanyar rayuwa, musamman a kudancin ƙasar.
Gwamnati da kuma masana na ganin cewa matuƙar ba a kawo ƙarshen matsalar ba to kuwa nan gaba kaɗan dole sai ƙasar ta rinƙa shiga da ruwan sha daga ƙasashen waje.
Hatta ɓangaren noman cocoa na fuskantar barazana, kasancewar ayyukan masu haƙar ma'adanai na lalata gonaki.
A baya gwamnati ta ɗauki matakin tura sojoji domin fatattakar masu haƙar ma'adanan ba bisa ƙa'ida ba, sai dai lamarin bai yi nasara ba.
A 2021 dai Afirka ta Kudu ta zarce Ghana a matsayin wadda ta fi fitar da zinare daga nahiyar Afirka sanadiyyar koma baya a ɓangaren haƙar zinaren.
Sai dai yanzu Cibiyar Kasuwanci ta Ghana ta ce ɓangaren ya samu bunƙasa sosai.