Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotu ta umarci INEC ta bayar da damar amfani da katin zaɓen wucin-gadi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ahmad Tijjani Bawage and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Sai da safe!

    Cikin yardar Allah, a nan za mu ɗiga aya a wannan shafin da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke wakana a Najeriya da wasu sassan ƙasashe.

    A madadin sauran abokan aiki da suka buɗe shafin - Haruna Ibrahim Kakangi da Ahmed Bawage, Nabeela Mukhar Uba ke cewa mu wayi gari lafiya.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu. Da fatan za ku tara da mu.

  2. Gobara ta lalata shaguna a kasuwar ƴan katako da ke Bauchi

    Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa wata gobara da ta tashi a kasuwar ƴan Katako da ke Muda Lawal ta ƙone shaguna da dama.

    Lamarin dai ya afku ne da yammacin ranar Alhamis misalin karfe 7 na dare.

    Jami’an Hukumar kashe gobara a jihar a halin da ake ciki suna ƙoƙarin kashe wutar, sai dai kawo yanzu ba a san adadin shagunan da suka ƙone ba.

  3. Ana laluben masu sauran numfashi bayan nitsewar jirgin ruwa a Gabon

    Masu aikin ceto na neman mutanen da suka tsira bayan da wani jirgin ruwa ya nitse a gaɓar tekun Gabon inda mutum biyu suka mutu.

    Kamfanin da ke da jirgin ya bayyana a Facebook cewa jirgin ya ɓule a yayin da yake tafiya daga Port-Gentil zuwa Libreville, babban birnin ƙasar da safiyar yau Alhamis.

    Cikin saƙon da ya wallafa, kamfanin ya ce mutum 121 aka kuɓutar zuwa yanzu kuma an kai su asibiti a Libreville.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito jami'ai na cewa fasinjoji 151 ne a jirgin, abin da ke nufin mutum 28 sun yi ɓatan dabo ke nan.

    Kamfanin ya ce ana ci gaba da aikin lalubo mutanen da ke da sauran numfashi.

    Ƴan uwan waɗanda ke cikin jirgin sun yi cincirindo a kusa da tekun inda suke dakon jin labarin halin da ake ciki.

    "Ɗiyata ta kira ni da tsakad-dare inda ta shaida min cewa wani abu na faruwa," in ji wani mutum da shekarunsa suka kai 50.

    "Ta ce "Baba, muna nitsewa kuma sai na ji shiru," in ji shi.

  4. Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 74 a yankin Neja Delta

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta haɗin gwiwa da sauran jami'an tsaro da ke aiki a Neja Delta sun lalata haramtattun matatun mai 74 tare da kama mutum 71 masu satar man cikin mako biyu da suka gabata.

    Daraktan yaɗa labaran rundunar tsaro Manjo Janar Musa Danmadami ya ce sojojin sun kuma taimaka wajen kare Najeriya daga tafka asarar ɗanyen mai da aka ƙiyasta ya kai na sama da naira miliyan 173 cikin tsukin lokacin.

    Ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ake yi sau biyu duk mako game da ayyukan sojoji a yakin da suke na murƙushe ayyukan ta'addanci a yankuna shida na ƙasar.

    Manjo Janar Danmadami ya ƙara da cewa sojojin sun gano lita 209,000 na ɗanyen mai da makamai 27 da alburusai 468 da jiragen ruwa 2 da motoci 8 sai babura 4 sannan an lalata tankunan ajiyar mai guda 341 sai kwale-kwale 31.

  5. An duƙufa neman zakin da ya ɓalle a Afirka ta Kudu

    Jami'ai a Afrika ta Kudu na ci gaba da ƙoƙarin gano wani zaki da ya ɓalle a wajen Pretoria, babban birnin ƙasar.

    An ga zakin kusa da wata hanyar ƙasa mai nisan kilomita 30 daga yammacin birnin.

    Arthur Crewe, ma'aikaci a wani kamfanin tsaro ya ce an soma binciken da ake domin gano zakin a ranar Laraba kusa da Hennops Hiking Trail.

    Ana amfani da fasahar nan ta drones domin gano dabbar da aka gani lokuta da dama, kamar yadda ya faɗa wa jaridar TimesLive ta Afirka ta Kudu.

    Ya shaida wa News24 cewa yana fatan samun tallafin jirgi mai saukar ungulu.

    Mista Crewe ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu inda ya ce ba lalle zakin ya yi wa kowa komai ba saboda yana cikin daji ne.

    Babu ƙarin bayani kan daga inda zakin ya tsere.

    Wani rahoto da ke cewa zakin ya kashe wani jaki ba gaskiya bane kasancewar mota ce ta bige jakin.

  6. An gabatar da ƙudirin hukunta masu neman jinsi a majalisar dokokin Uganda

    An gabatar da ƙudiri gaban majalisar dokokin Uganda wanda ke neman a hukunta duk wanda aka samu yana bayyana kansa a amatsayin ɗan neman jinsi.

    Idan har aka amince da ƙudirin, za su fuskanci hukuncin ɗauri na tsawon shekara 10 haka ma ƴan luwaɗi da maɗigo.

    Dokar za ta haramta ɗaukar nauyi ko tallata ƙungiyar masu neman jinsi da ayyukansu tare da iza ƙeyar masu gidajen da suka bai wa ƴan ƙungiyar hayar gida zuwa gidan yari.

    Kwamitin majalisar zai yi nazari kan ƙudirin kafin a sake gabatar da shi gaban majalisar domin tafka muhawara a kai.

    Masu fafutuka sun bayyana damuwa cewa yin hakan na iya janyo kai wa waɗanda ake zargi da wannan ra'ayin na neman jinsi hari.

    A 2014 ne, kotun ƙolin ƙasar ta soke dokar yaƙi da masu neman jinsi wadda ta tsaurara ɗaukan matakai kan masu ra'ayin.

    Kusan ƙasashen Afirka 30 ne suka haramta neman jinsi.

  7. An haramta wa ɗan wasan Syria ƙwallo har abada saboda ya doki lafari

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Syria ta haramta wa tsohon kyaptin ɗin ƙasar, Ahmed Al-Saleh ƙwallo har abada bayan da ya kwarfa tare da cin zarafi har ma da tafowa alƙalin wasa yawu.

    Ɗan wasan ma shekara 33, dan wasan baya na ƙungiyar Al-Jaish ya nuna fushinsa kan alƙalin wasan bayan da ya nuna masa jan kati yayin wasansu da Al-Wathba a ranar Juma'a.

    Lamarin dai ya sa ƴan wasa daga duka ɓangarorin rirrike Al-Saleh a lokacin da ya fusata.

    Kwamitin ladabtarwa na hukumar ya kuma ci tarar ɗan wasan da Al-Jaish, waɗanda kuma ba za su iya ƙalubalantar hukuncin ba.

    Hukumar ƙwallon ƙafar ta Syria ta ce Al-Saleh ya ci gaba da zagin alƙalin wasan har bayan da suka koma wajen canja kaya.

  8. Mata 25 da ke takarar gwamna a Najeriya

  9. Ana neman kai ɗaukin jini bayan haɗarin jirgin ƙasa a Legas

    Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi kira ga jama'a da su kai ɗaukin jini yayin da jami'an lafiya ke ƙoƙarin kula da waɗanda suka jikkata sanadiyyar haɗarin jirgin ƙasa a yau Alhamis.

    Cikin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na Tuwita game da haɗarin, Mista Sanwo-Olu ya ce har yanzu wasu da lamarin ya shafa suna cikin wani yanayi.

    Ya ce motar bas ɗin na ɗauke da ma'aikata 85 ne a lokacin da ta yi taho mu gama da jirgin a Ikeja.

    Gwamnan ya tabbatar da mutuwar mutum shida inda ya ce wasu 29 kuma rai na a hannun Allah. Wasu 42 kuma sun ɗan jikkata sai ƙarin wasu takwas da suka kukkurje.

    Ya yaba wa ma'aikatan agaji da sauran waɗanda suka sa hannu a aikin agajin da kuma ma'aikata da ɗaliban asibitin koyarwa na Jami'ar Legas inda ake kula da waɗanda suka ji rauni.

  10. Kotu ta umarci INEC ta bayar da damar amfani da katin zaɓe na wucin-gadi

    Babbar kotun tarayya a Abuja ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta bayar da damar yin amfani da katin zaɓen wucin gadi a zaɓen ranar 18 ga watan Maris na gwamnoni da ƴan majalisar dokokin jihohi.

    Alƙali Obiora Eguatu ne ya bayar da umarnin a lokacin da yake yanke hukunci kan ƙarar da wasu fusatattun ƴan Najeriya suka shigar ta neman a yi amfani da katin zaɓen wucin gadin a babban zaɓen a maimakon na din-din-din.

    Alƙali Egwuatu ya ce an bayar da umarnin ne kasancewar masu shigar da ƙarar suna cikin kundin bayanan hukumar Inec.

    Sai dai alƙalin ya ce bai amsa buƙatarsu ta uku ba da ke neman a bai wa kowane dan ƙasa da ke da katin zaɓen wucin gadi damar kaɗa ƙuri'a.

    Da yake magana da ƴan jarida, lauyan masu ƙarar, mista Victor Opatola ya ce hukuncin nasara ce ga duka ƴan Najeriya da suka sha wahalar yin rajista amma suka rasa samun katin zaɓensu na din-din-din kafin lokacin zaɓen.

  11. Hotunan yadda birnin Ukraine ya koma bayan luguden wuta da Rasha ta kai

    Hotuna suna ci gaba da fitowa da ke nuna yadda birnin Ukraine ya koma bayan wani kazamin hari da Rasha ta kai tsakar dare a safiyar Alhamis.

  12. Shugaban Sudan ta Kudu ya kori ministan harkokin waje

    Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya kori ministan harkokin wajen ƙasar, mako ɗaya bayan sallamar ministocin tsaro da na harkokin cikin gida.

    Babu wani bayani da aka bayar kan sallamar Mayiik Ayii Deng.

    Korarren ministan abokin mista Kiir ne, inda a baya ya taɓa zama a matsayin minista a ofishin shugaban ƙasar.

    Korar da shugaban ya yi wa wasu ministoci na barazanar kawo tsaiko a yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da shugaban 'yan adawa mataimakin shugaban ƙasa Riek Machar.

    Jagoran 'yan adawar ya yi kira da a dawo da ministar tsaro Angelina Teny, wanda mista Kiir ya kora.

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga jam'iyyun da suka kwantar da hankula tare da sasantawa.

  13. 'Yan Afghanistan 91 sun nutse a gaɓar tekun Italiya

    Ofishin jakadancin Afghanistan a Italiya, ya sanar da cewa kawo yanzu 'yan ƙasar 91 aka tabbatar sun mutu a cikin waɗanda suka rasu bayan nutsewar jirgin ruwa a garin Crotone.

    Jirgin ɗauke da gwamman 'yan cirani da bakin haure, ya nutse kusan makonni biyu da suka gabata, inda yawancin fasinjojinsa suka mutu.

    Jami'an kula da gaɓar tekun sun ce mutum 80 sun samu tsira a hatsarin, ciki har da waɗanda suka yi iwo zuwa bakin gaɓa lokacin da jirgin ya nutse.

    Ofishin jakadancin Afghanistan ɗin ta ce cikin mutane 91, an gano gawarwakin 48, inda aka miƙa shaidar mutuwa zuwa ga wasu 46.

    Ofishin ya kuma ce ana yi wa waɗanda suka jikkata a lamarin magani, inda aka kai waɗanda suka tsira zuwa wani wuri, yayin da ba a kai ga gano wasu kuma ba.

  14. Bam ya hallaka gwamnan Taliban a ofishinsa

    An kashe gwamnan Taliban na lardin Balkh da ke arewacin Afganistan sakamakon fashewar wani abu a ofishinsa.

    Mohammad Dawood Muzammil shi ne babban jami'i ma fi girma da aka kashe tun bayan da Taliban ta dawo kan mulki a shekarar 2021.

    Tun daga lokacin dai tashe-tashen hankula sun ragu matuka, amma an kashe fitattun masu goyon bayan Taliban da sauran su a wasu hare-hare da aka kai, wadda da dama suka fito daga kungiyar IS.

    'Yan sandan yankin sun ce ba a kai ga gano musabbabin fashewar bam ɗin ba, sannan babu wanda ya ɗau alhakin harin.

    Sai dai kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya faɗa a shafinsa na Twitter cewa wasu makiya musulunci ne suka kashe gwamnan, inda ya ce ana gudanar da bincike.

    An bayyana cewa Muzammil ya jagoranci yakin da ake yi da mayakan IS a lokacin da yake gwamnan lardin Nangarhar da ke gabashin ƙasar a baya. An mayar da shi zuwa Balkh a watan Oktoban bara.

    Kakakin ‘yan sandan Balkh Mohammed Asif Waziri ya ce fashewar ta faru ne da misalin karfe tara na safe...a cikin hawa na biyu na ofishin gwamnan.

    ‘Yan sanda sun ce akwai wani mutum guda kuma da ya mutu a harin, inda wasu da dama suka jikkata.

  15. Ana fama da ƙarancin dala a Kenya

    Ministan kasuwanci na ƙasar Kenya Moses Kuria, ya ce ƙarancin dala da ƙasar ke fuskanta ya fi karfin gwamnati.

    Mista Kuria ya shaida wa 'yan majalisa cewa ƙarancin dalan ya shafi duniya, amma ya ɗora hakan a ƙasar kan shigo da kayayyakin da ake iya sarrafa su a cikin gida.

    “Ba za ku rika kukan cewa muna da matsalar ƙarancin dala ba, sannan kuma kuna shigo da kaya daga waje,” in ji shi.

    Ya yi kira da a kara karfafa gwiwar masana’antun cikin gida da kuma kare su daga na kasashen waje.

    Babban bankin ƙasar Kenya (CBK) ya umurci bankuna da su takaita dalar da za su bai wa mutane sakamakon ƙarancinta, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito.

    Masu sharhi sun zargi CBK da haddasa rikicin dala, suna masu cewa mai kula da tsarin ya ɓullo da tsauraran dokoki a kasuwar hada-hadar kuɗaɗe ta bankuna.

    Sai dai bankin ya sha tabbatar da cewa Kenya na da isassun kuɗaɗen waje don biyan bukata.

    Darajar kuɗin Kenya na shilling ya faɗi da kashi 9 a kan dala a cikin sama da shekara guda, abin da ya kara janyo tsadar rayuwa a ƙasar.

  16. Akwai shirin tayar da hankali a zaɓen gwamnoni - DSS

    Hukumar 'yan sandan ciki ta DSS ta ce akwai shirin da wasu mutane ke yi na tayar da hankali a wasu sassan ƙasar a zaɓen gwamnoni da ke tafe.

    A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ya fitar a ranar Laraba, ta gargaɗi mutane ko kungiyoyi da su guji yin duk abin da zai tayar da hankali domin kauce wa fushin hukuma.

    A don haka DSS ɗin ta ja kunnen 'yan siyasa da su zama masu bin doka da oda a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke shirin fita rumfunan zaɓe domin zaɓen gwamnoni da 'yan majalisar dokoki a ranar 18 ga watan Maris.

    Hukumar ta ce a shirye ta ke domin kare 'yan ƙasar waɗanda ke da niyyar fita kaɗa kuri'a.

    DSS ɗin ta kuma ce ta shirya tsaf tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro wajen dakile duk wani yunkuri na kawo tashin hankali a lokacin zaɓen.

  17. An kuɓutar da mutum 84 a hatsarin jirgin ƙasa a Legas

    An kuɓutar da gwamman mutane a wani taho mu gama tsakanin jirgin ƙasa da wata motar bas a birin Ikeja da ke jihar Legas.

    Hatsarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum akalla uku.

    Masu aikin ceto sun samu nasarar fito da wasu mutane 84 daga tarkace a safiyar Alhamis.

    Wani jami'in hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, Ibrahim Farinloye ya ce jirgin ƙasan ya fito ne daga Abeokuta zuwa Legas, inda daga nan ya buge wata motar bas ɗauke da ma'aikatan gwamnatin jihar Legas lokacin da motar ta yi kokarin gutsawa daga layin dogo.

    Mutane sun taru lokacin da ake aikin ceto, inda suke kokarin ba da tasu gudummawa.

  18. Shugabar Tanzania ta halarci taron 'yan adawa karon farko a tarihin ƙasar

    A karon farko a tarihin Tanzaniya, shugabar ƙasan Samia Suluhu Hassan, ta halarci taron ranar mata ta duniya da babbar jam'iyyar adawa ta Chadema ta shirya.

    Shugaban jam'iyyar Freeman Mbowe ya yi maraba da halartar shugaba Samia Suluhu, inda ya ce buƙatar taron ne ganin an yi sulhu tsakaninsu.

    Samia, wadda ta yi jawabi ga dubban mutane a wurin taron, ta ce ana ci gaba da sasantawa a siyasar ƙasa, kuma tuni aka ɗauki wasu matakai yayin da wasu kuma ke ci gaba da gudana, ciki har da samar da sabon kundin tsarin mulki.

    A cikin jawabinta, shugaba Samia ta ce an fuskanci matsala kafin fara sulhuntawa saboda wasu a jam'iyyarta mai mulki ba su shirya ba.

    Ta ce, "An yi muhawara da yawa a nan da can, kuma hakan ya bayyana ga 'yan adawar ƙasar. Don haka jam'iyyun biyu suna da wasu daga cikin jama'arta da ba su ji daɗin matakin sulhuntawa na siyasa ba."

    Ita ce shugabar mata ta farko a Tanzaniya, bayan rasuwar John Magufuli a shekarar 2021.

    'Yan adawar sun zargi mista Magufuli da zama mai son mulki, da taka shugabanni da kuma mambobinsu.

  19. 'Yan tawaye sun kashe gwamman mutane a wani hari a Kongo

    Gwamnan lardin arewacin Kivu da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, ya ce 'yan tawayen ADF sun kashe ƙauyawa akalla 36 a wani hari da suka kai yankin.

    Wani mazaunin lardin mai suna Carly Nzanzu Kasivita ya wallafa a kafar sada zumunta cewa 'yan tawayen sun ƙona ƙauyen Mukondi kurmus, kungiya kuma da ke da alaƙa da masu iƙirarin jihadi, amma sun fi mayar da hankali wajen sace albarkatun ƙasa d ake yankin.

    Gwamnan lardin ya yi kira da a kawo ƙarin dakaru zuwa ƙauyukan makwaɓta a birnin Beni da ke kudancin ƙasar domin kare su daga ƙarin hare-hare.

  20. MDD ta ƙara saka wa Sudan takunkumi

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ƙara saka wa Sudan takunkumi da kuma na haramta sayar musu da makamai da ƙarin shekara ɗaya.

    Mambobin kwamitin 15 su ne suka amince da takunkumin bayan ji daga masana da aka ɗorawa alhakin zartas da takunkuman har zuwa 12 ga watan Maris ɗin shekara mai zuwa.

    Ƙasashe 13 sun kaɗa kuri'ar amincewa da matakin, inda China da Rasha suka kauracewa kuri'ar.

    Wakilin China a zauren Dai Bing ya ce takunkuman sun daɗe don haka ya kamata a ɗage su saboda abubuwa sun kyautatu a Sudan.

    Shi ma wakilin Rasha Dmitry Polyanskiy, ya ce takunkuman basu nuna ainihin abin da ke faruwa a Darfur ba, wanda hakan ya hana gwamnatin Sudan samun ci gaba a ƙasar.

    John Kelly wanda ya kasance wakilin Amurka, ya ce ya goyi bayan a ci gaba da sa ido da kuma bayar da rahoton abin da ke faruwa.