Bankwana
Nan muka kawo ƙarshen labaran namu na yau, sai kuma gobe.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya sa sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza
Nan muka kawo ƙarshen labaran namu na yau, sai kuma gobe.
Adadin mutanen da suka mutu ya kai 16, sanadin rushewar wani gini mai hawa biyar a arewa maso yammacin Syria.
Ana zaton har yanzu akwai mutanen da ɓaraguzai suka danne a birnin Aleppo inda abin ya faru.
Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Syria da ke Birtaniya tace hari ya sanya mutane barin muhallansu a lardin Afrin da ke arewaci.
Rahotanni na cewa ambaliyar ruwa ce ta rarake ƙasan ginin, abin da ya janyo rushewarsa kenan.
An yi amannar rikicin Syria ya raba mutane masu yawa da muhallansu, kuma shi ne ya janyo lalacewar gidaje da dama.
Akasarin ƙasashe mambobin ƙungiyar Haɗin Kan Larabawa ta Arab League sun ƙaurace wa taron da gwamnatin haɗin kan Libya ta shirya, wadda ke zaune a birnin Turabulus.
Biyar ne kawai daga cikin mambobi 22 na ƙungiyar suka aika da manyan jami'an difilomasiyyarsu, inda babban sakatarenta ma ya ƙi amsa gayyatar. Masar da Daular Larabawa da Saudiyya, duka ba su tura wakili ba, saboda suna mara wa gwamnatin adawa da ke gabashin Libya baya.
An fara tayar da jijiyoyin wuya ne lokacin da firaministan riƙon-ƙwarya, Abdul Hamid Dbeibah, ya ƙi sauka daga mulki bayan ya gaza gudanar da zaɓe a watan Disambar 2021.
Rikici tsakanin gwamnatocin ya jawo tashin hankali a Turabulus a shekarar da ta gabata.
An naɗa mace Bafalasɗiya ta farko a matsayin malamar Kirista a birnin Ƙudus.
An naɗa Sally Azar a Cocin Lutheran da ke Tsohon Birnin, inda ɗaruruwan masu yi mata fatan alheri suka taru daga sassan duniya da kuma waɗanda suka kalli bikin ta intanet.
Sally Azar ta ce tana fatan ta zama abar koyi ga mata da kuma sauran coci-coci a yankin.
Kiristoci ba su da yawa a yankin Falasɗinawa da Isra'ila da kuma Jordan - kuma da yawansu 'yan ɗariƙar Orthodox ne na Girka da kuma Katoilika na Latin Amurka, waɗanda ba sa barin mace ta zama fasto ko mai wa'azi.
Manchester City ta doke Wolverhampton da ci 3-0 a wasan makon na 21 a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Etihad.
Erling Haaland ne ya ci dukkan kwallayen a wasa, wanda ya fara cin ta farko saura minti biyar a yi hutu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne dan wasan ya kara na biyu a bugun fenariti, sannan ya zura na uku a raga a minti na 54, minti hudu tsakani da na biyu.
Karo na hudu kenan da Haaland ya zura uku a raga a gasar Premier League a kakar nan.
Erling Haaland ya ci kwallo 25 cikin kwallo 74 da ya buga raga tun bayan zuwansa Premier.
Ya zarta ɗan wasan da ya fi yawancin kwallo a tarihin ƙungiyar Sergio Aguero, wanda ya ci kwallo 25 a cikin 150 da ya buga a wasanninsa na farko a ƙungiyar.
A tarihi Alan Shearer ne kawai ya fi Halaand yawan cin kwallo uku a kaka daya, inda ya ci kwallo uku sau biyar a kakar 1995-96, shi kuma Halaand na da hudu a wannan kakar.
Halaand ya karya tarihin manyan 'yan kwallon Premier da suka taba cin kwallo biyar a wasanni ƙalilan, Ruud van Nistelrooy ya ci kwallo uku sau hudu a wasanni 65, Luis Suárez a 81, Alan Shearer a 86 sai kuma Robbie Fowler a 89, amma shi Halaand a wasa 19 ya ci.
Masu ceto na taimakawa wajen zaƙulo mutane daga ofishin magajin garin birnin Mogadishu na Somaliya bayan harin da masu iƙirarin jihadi na Al-Shabab suka kai.
Zuwa yanzu babu tabbas game da yawan mutanen da lamarin ya ritsa da su kuma ma'aikatan ba su iya kaiwa ga ginin ba saboda ɓarin wuta da ake ci gaba da yi.
A shekarar 2019, Al-Shabab ta ragargaza ofishin da bam, har ma ta kashe magajin garin.
A 'yan watannin nan, an ƙwace garuruwa da yawa daga hannun ƙungiyar sakamakon hare-haren da dakarun gwamnati ke kai mata.
Ita kuma tana mayar da martani ta hanyar ƙara ƙaimin hare-hare kan jami'an gwamnati da na rundunar soja.
Fitaccen dan wasan kwallon kafar Portugal Cristiano Ronaldo ya shirya tsaf domin fara buga wasansa na farko a kungiyar Al-Nasr ta Saudiyya da ya koma.
Wasan da za a buiga tsakanin Al-Nasr da Al-Ettifaq za a fara shi ne da misalin ƙarfe 5:30 na agogon GMT.
Ronaldo ya buga wasan da Riyad All Star suka buga da PSG inda ya ci biyu a wasan da aka tashi bPSG na da 5 Riyad na da 4.
Kamar yadda rahotanni ke ambatowa cewa Cristiano zai rika karbar dalar Amurka miliyan 200 a shekara, wanda shi ne kudi mafi yawa da za a biya wani ɗan kwallon kafa a duniya.
Ronaldo ya koma Al-Nasr daga Manchester United a wani yanayi na rashin jituwa, sakamakon btattaunawar da ya yi da 'yan jarida ya soki shugabannin kungiyar.
Gwamnan jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ya ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu a jihar.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan ya fitar, ya ce hutun zai bayar da dama ga 'yan jihar su karɓi katin zaɓensu a wurare daban-daban da hukumar zaɓen ta ware domin karɓar katin a faɗin jihar.
''Babban zaɓen da ke tafe na da matuƙar muhimmanci, dan haka ya kamata mu magance matsalar ƙarancin karɓar katin zaɓe da shiyyar kudu maso yamma ke fuskanta'', in ji sanarwar.
A ranar 25 ga watan Fabrairun da ke tafe ne dai za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.
A ci gaba da kawo muku labarai 12 da alkalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo a bana, a yau za mu kawo muku labari mai taken 'Mai Kyau'.
Wanda Maryam Nafisa Usman Tafida da ke Rigima a jihar Jigawa ta rubuta Badariyya Tijjani Kalarawi ta karanta
Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta samu nasarar kama hodar ibilis da tabar wiwi da aka shiga ƙasar da ita daga ƙasashen Brazil da Canada a a biranen Enugu da Legas.
A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar Femi Babafemi ya sanya wa hannu, ta ce hukumar ta kama ƙwayoyin tramadol miliyan 1.7 a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar, tare da kama mutanen da ta daɗe tana nema a jihohin Osun da Kano da Ondo da Edo da Abuja babban birnin ƙasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ''Jami'an hukumar NDLEA da ke aiki a filin jirgin saman Akanu Ibiam da ke Enugu da masu aiki a tashar jirgin ruwa na Tican da ke Legas sun samu nasarar daƙile yunƙurin shigo da kilogiram 126.95 na hodar ibilis da tabar wiwi ƙunshe cikin ƙwalayen ganyen shayi da ababen hawa daga Brazil da Canada''.
Sanarwar ta ƙara da cewa a filin jirgin saman Enugu an kama wani fasinja mai suna Eze Christian Ikenna mai shekara 42, da ya shiga ƙasar daga Brazil ranar 20 ga watan Janairun, bayan da aka binciki jakar da ya zo da ita inda ka samu hodar ibilis da ta kai nauyin kiligiram 16.2.
Rundunar sojin Amurka ta ce dakarunta sun kashe mayaƙan al-Shabab 30 a wani hari ta sama da suka kai wa mayaƙan.
Lamarin ya faru ne a kusa da garin Galcad mai nisan kilomita 260 daga arewa maso gabashin Mogadishu babban birnin ƙasar.
A 'yan kwanakin nan dai dakarun Somaliya da mayaƙan al-Shabab na faɗa da juna a ƙoƙarin da ɓangarorin biyu ke yi na karɓe iko da garin
Rundunar sojin Amurka mai aiki a Afirka ta ce a ranar Juma'a mayaƙan na al-Shabab sama da 100 suka kai wa tawagar sojin Amurkan hari tare da kashe sojoji bakwai.
Ma'aikatar yaɗa labaran Somaliya ta ce an kashe gwamman mayaƙan ƙungiyar a lokacin harin.
Tun 2006 ne dai ƙuniyar al-Shabab ke faɗa da gwamnatin ƙasar a ƙoƙarin da take yi na kawar da gwamnatin ƙasar tare da kafa nata.
A yayin da aka samu nasarar fatattakar ƙungiyar daga birnin Mogadishu da wasu biranen ƙasar, al-Shabab ta ci gaba da ƙaddamar da hare-hare kan sojoji da fararen hula a ƙasar.
A ranar Litinin da ta gabata gwamnatin ƙasar ta ce dakarunta da na mayaƙan sa kai sun ƙwato garin Harardhere, wanda ya kasance babban gari da ke hannun ƙungiyar tun 2010.
A Gobe Litinin 23 ga watan Janairu ne dai BBC za ta gudanar muhawarar 'yan takarar gwamna jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya
Wani ɗalibin jami'ar Fasaha ta tarayya da ke Akure a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ya rataye kansa a ɗakinsa.
Rahotonni sun ce ɗalibin na aji uku a jami'ar inda yake karantar fannin fasahar zane-zanen kayayyaki.
Jaridar Punch a Najeriya ta ambato wata majiya na cewa abokan marigayin ne suka fara gano gawarsa, bayan da suke je ɗakin suka tarar da shi a kulle, suka yi magana suka ji shiru daga nan suka yanke shawarar karya ƙofar, inda suka same shi a rataye ya mutu.
Mai magana da yawun run dunar 'yan sandan jihar Misis Funmilayo Odunlami ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ƙara da cewa tuni aka kai gawar ɗakin ajiye gawarwaki tare da kuma ƙaddamar da bincike domin gano abin da ya janyo ɗalibin ya rataye kansa.
Tarihin cibiyar harkokin siyasar ƙasa da ƙasa ta Chatham House da ayyukanta da kuma tasirinta kan siyasar duniya.
Gwmnatin tarayyar Najeriya ta amince da ƙarin albashi ga ma'aikatan tasoshin jiragen ruwa na ƙasar
Ministan sufuri na ƙasar Mu'azu Sambo ne ya bayyana haka a ƙarshen makon da muke ciki a lokacin da ya halarci bikin bayar da kyaututtuka da hukumar da shirya wa ma'aikatanta.
Mista Sambo ya yaba wa jagorancin hukumar game da ƙoƙarinta wajen jin daɗi da walwalar ma'aikata.
Haka kuma ministan ya jinjina wa Babban manajan hukumar bisa abin da ya kira ''ƙoƙarin'' da ba a taɓa gani ba da hukumar ta yi wajen tara kuɗin shiga ga ƙasar.
Babban Manajan hukumar Bello-Koko ya gode wa gwamnatin tarayya dangane da ƙarin albashin da ta yiu wa ma'aikatan hukumar .
Hukumar tattara bayanan sirri kan sha'anin kuɗi ta Najeriya ''Nigerian Financial Intelligence Unit'' (NFIU) ta ce haramcin da take ƙoƙarin sanyawa kan cire kuɗi daga asusun gwamnatin tarayya da na jihohi abu ne da zai taimaka wa gwamnonin ba cutar da su ba.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar ta hannun jami'inta na hulda da jama'a Ahmed Dikko sa'o'i bayan ƙungiyar gwamnonin ƙasar ta soki sanarwa da hukumar ta fitar ranar 5 ga watan Janairu, ta umartar bankuna da su dakatar da bai wa gwamnoni kudaɗe daga asusun gwamnati daga ranar 1 ga watan Maris mai zuwa.
“Sabuwar dokar da hukumar NFIU ke shirin ƙaƙabawa game da sha'anin shige da ficen kuɗi baya cikin tsarin dokokin da ayyukan hukumar'' Kamar yadda ƙungiyar gwamnonin ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
Ƙungiyar gwamnonin ta kuma kafa kwamiti mai mambobi shida da za su tattauna da babban bankin ƙasar domin duba batun matsalolin sha'anin harkokin kuɗi da ƙasar ke fuskanta.
A martanin da hukumar ta NFIU ta fitar ta ce a shirye take domin hada kai da kwamitin da ƙungiyar gwamnonin ta kafa domin wayar musu da kai game muhimmancin sabon kuɗurin.
''Sannan abun da muke ƙoƙarin aiwatarwa bai saɓa doka ba. Mun bayar da ƙa'idar ne domin magance tarin bincike da muka hango wa gwamnonin. Mun sanya ƙa'idar ce domin taimaka wa gwamnonin ba don cutar da su ko wani ma'aikacin gwamnati ba'' kamar yadda sanarwar da NFIU ta fitar.
Sannan kuma hukumar ta ce a baya ta sanya makamanciyar wannan doka kan ƙananan hukumomi, inda aka kai ta kotu, amma kuma sai ta yi nasara a kotun.
Shugaba Lula Inacio da Silva na Brazil ya kori Shugaban rundunar sojin ƙasar, makonni biyu bayan kutsen magoya bayan Jair Bolsonaro da ya gada.
A cewar ministan tsaro Jose Mucio, lamarin ya haifar da rashin amincewa da juna tsakanin rundunar soji da gwamnati, kuma abu ne da dole a ɗaukar masa mataki.
Yanzu haka ana tsare da gwamman sojoji da 'yan sanda da ake zargi da haɗa baki da masu boren a lokacin.
Za a maye gurbin Janar Julio Cesar de Arruda da Janar Tomas Ribeiro Paiva, wanda na hannun damar Shugaba Lula da Silva ne.
Gwamnatin soji a Burkina Faso ta buƙaci sojojin Faransa da aka girke a ƙasar da su tattara nasu inasu su bar ƙasar.
Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce gwamnati ta sanar da soke yarjejeniyar da ta ƙulla da su, wadda ta ba su damar zama a ƙasar, kuma tana so su fice daga ƙasar nan da wata guda.
Ko a ranar Juma'a sai da aka gudanar da boren ƙin jinin Faransa, inda wasu ke kiran kamfanin tsaro na sojin hayar Rasha na Wagner da ya taimaka wajen ceto ƙasar.
Ana zargin rundunar ta musamman mai sojojin da yawansu yakai 400 da gaza taɓuka komai wurin daƙile ayyukan masu tayar da ƙayar baya a ƙasar, wanda kuma shi ne maƙasudin girke su.
Sai dai gwamnati a Paris ta ce ba za ta daina taimaka wa Burkina Faso ba wurin wannan yaƙi, duk da ƙin jinin Faransa da ƙasar ke nunawa.
Mayaƙa masu tsatstsauran ra'ayi sun bazu a yankin shekaru goma da suka wuce, kuma bincike ya nuna cewa daga Mali suka shiga ƙasar.
Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako, da fatan an yi karin kumallo lafiya.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa tare da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Ku kasance tare da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara a kan labaran da muke wallafawa.