Wasu kalamai da Kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Muazu Magaji ya yi wadanda ake gani tamkar na nuna murna ne kan rasuwar Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya, sun jawo takaddama.
A sakon da ya wallafa a Facebook, Injiniya Muazu, ya bayyana cewa "nasara, nasara. Najeriya ta tsira, Abba Kyari ya mutu a cikin annoba."
Wadannan kalamai sun janyo masa kakkausan suka daga mabiyansa a shafin Facebook, inda wasu suke cewa bai kamata mai mukami kamar sa ya yi kalamai irin wadannan ba.
Da alama shi ma Malam Bashir Ahmad, mai bai wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shawara kan shafukan sada zumunta na zamani, bai ji dadin kalaman ba.
A sakon da ya wallafa a Twitter ranar Asabar, ya yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya dauki mataki kan wani kwamishinansa.
Bashir Ahmad ya ce ya yi matukar rashin jin dadi bisa murnar da kwamishinan ayyuka na Kano, Injiniya Muazu Magaji ya yi.
Malam Abba Kyari ya rasu ne ranar Juma'a bayan ya yi fama da cutar korona.