Mace ta farko da ake kyautata zaton 'ta warke' daga cutar HIV

Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon:

An yi amannar cewa wata mace daga Amurka ce ta uku a duniya, kuma mace ta farko da ta fara warkewa daga cutar HIV.

Matar mai matsakaicin shekaru tana da kansa ne inda aka yi mata dashen ƙwayoyin halitta da na wani da ke ƙwayoyin halittarsa suka fi ƙarfin ƙwayar cutar HIV.

A yanzu watan matar 14 ba ta ɗauke da cutar.

Amma ƙwararru sun ce tsarin dashen da aka bi, na amfani da jinin cibiya, yana da haɗari sosai ga mafi yawan mutane masu ɗauke da cutar HIV.