Yariman Bakura: Matawalle ne jagoran APC a Zamfara

Bayanan bidiyo, Yariman Bakura: Matawalle ne jagoran APC a Zamfara

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon Yariman Bakura:

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Sani Yariman Bakura ya ce dole ne kowanne da jam'iyyar APC a jihar ya amince cewa Gwamna Mohammed Bello Matawalle ne jagoran jam'iyyar a jihar.

Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da BBC Hausa.

Tsohon gwamnan wanda kuma tsohon Sanata ne da ya wakilci jihar a majalisar dattawan kasar, ya ce a ka'ida shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne jagoran APC a Najeriya, don haka shi ma gwamna shi ne jagoran jam'iyyar a jihar.

Yana mayar da martani ne ga kalaman tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari da tsohon dan majalisar dattawa Kabiru Marafa wadanda suka yi fatali da rahotannin da ke cewa Gwamna Mohammed Bello Matawalle ne jagoran jam'iyyar APC a jihar.

Sun bayyana haka ne a hirarsu da BBC Hausa jim kadan bayan sun gana da Gwamna Nasir Elrufai na jihar Kaduna ranar Laraba.

Kalaman nasu tamkar martani ne ga rahotannin da suka ambato shugaban riko na jam'iyyar ta APC, Maimala Buni, yana cewa Gwamna Matawalle shi ne jagoran APC a Zamfara bayan ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Sai dai Abdulaziz Yari da Kabiru Marafa - wadanda gwamnan ya tarar a cikin jam'iyyar ta APC - sun ce ba za su yarda a yi musu hawan ƙawara ba.

"Abu guda ne ba mu yarda da shi ba, inda shi Gwamna Maimala ya ce [Matawalle ne jagoran APC] domin babu shi a cikin tattaunawarmu wadda muka yi da gwamnoni guda shida.

Abin da muka amince shi ne a je a kaddamar da Bello a dawo. Abin da muka amince a matsayin abin da za mu bayar a jam'iyya da abin da za mu dauka a gwamnati. Amma da muka je an yi takaddama mun tarar da an yi tsari in ji wasu cewa idan an je a rusa jam'iyya. Ba a rusa jam'iyya domin babu wanda yake da ikon rusa ta," in ji shi.