Kamala Harris: Abin da ya kamata ku sani game da mataimakiyar shugaban Amurka mai jiran gado
Kamala Harris, mataimakiyar shugaban kasar Amurka mai jiran gado, ita ce mace bakar fata ta farko da ta hau kan wannan matsayi a tarihin kasar.
Mahaifiyar Kamala ce ita kadai ta raine ta har ta girma saboda sun rabu da mahaifinsa tun tana karama.
Kafin zabenta a matsayi na mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris ta rike mukamin antoni janar ta jihar California kuma 'yar majalisar dattawan kasar ce.