Bidiyo: Ce-ce-ku-cen da bai wa Ganduje matsayin Farfesa a Amurka ya jawo

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Batun bai wa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje matsayin farfesa a jami'ar East Carolina ta Amurka ya ta da ƙura a Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta a makon nan.

Mafi yawa masu tsokaci na yin tambaya ne iri ɗaya kan wane ne ya bai wa Ganduje wannan matsayi, tun da jami'ar da aka alaƙanta da ba da matsayin ta musanta yin hakan.

Jami'ar ta ce babu wata magana mai kama da haka tsakaninta da Ganduje, kuma takardar da wani ma'aikacinta ya aike wa gwamnan ba ta samu amincewar mahukuntar jami'ar ba.

Wannan abu ya fusata gwamnatin Kano da shi kansa Gwamna Ganduje, abin da ya sanya suka nemi jami'ar ta bayar da haƙuri sannan a hukunta malamin jami'ar da ya bayar muƙamin "wanda ya yi yunƙurin kunyata gwamnan."

Daga bisani Jami'ar ta East Carolina, ta nuna takaicinta kan yaudarar da aka yi wa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wurin amfani da sunanta domin ba shi muƙamin Farfesa.

Sai dai wannan batu ya tado da irin kwaɗayin wasu jami'an gwamnati da 'yan siyasar Najeriya wajen samun digirin girmamawa da sauran muƙamai a ciki da wajen kasar.